Showing 360001 words to 363000 words out of 495987 words
Chapter 121 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
zuwan masa daki daki kamar alokacin komai ya faru ya ɗan matsa inda ya hango digon shashin spam dinsa a bedshit ,nan da nan idanunsa suka qara canzawa "me yasa abubuwa suka faru haka ?"me yasa ya kusanceta dole ? ya fada a fili cikin sanyin murya ya dade agurin yana daurawa kansa laifi sannan ya sulale a kasa zuciyarsa na zafi ya kwanta flat a kasan tayis yana balbale botiran gaban rigarsa ,ya soma juyi rungume da hannuwansa duka a qirji yana jin wani irin yanayi ajikinsa kamar wanda aka tsinkata ya mike ya fito falo yayi shiru yana kallon hotunanta har Idanunshi ya kan wani karamin hotonta ya kai hannu frem dinta dake kan abun tv ya manna a qirjinsa ya koma d'akinsa zuciyarsa na wani irin rawa yana jin wata irin yanayi na ratsashi shi duk daukar da yake bazai taba damuwa ba idan ya rabu daita tunda a tunaninsa baya sonta baya ga sha'awarta da yake ji a she abun ba haka bane lallai ya tabbaka babban kuskure a rayuwarsa kuma zuciyarsa batayi masa adalci ba tunda har ta kamu damuwa adalilin rashinta jin an dafa shi ta baya gabansa ya doka yaki juyowa dan yasan ko waye ,sai dai bazai bari yaga abinda ke manne da qirjinsa ba sai zamo wani sabon al'amari , kai tsaye bathroom dinsa ya shiga batare daya juyo ba ya ajiye hoton ya fito ya iske Samir tsaye kallonsa Samir yayi yace",me kake ka boye ?" sannan zaman uwar me wannan yarinyar take maka a gida? ta fito ta kama gabanta tun wuri ",a kidime muradi yake kallonsa dan idan zai fahimci maganarsa sosai kisna yake nufi da sauri ya zagaye sa ya fita daga dakinsa bai ganta a falo bab ya shiga dakinta zaune ya ganta tana hada kayanta acikin akwati , naunauyen ajiyar zuciya ya sauke take duk wani abu dake damunsa ya nema ya rasa dagowa tayi ta kallesa gabanta na faduwa kar shima yayi mata irin abinda Samir yayi mata yanzu "kisna....." sunanta daya kira ya sata jin faduwar gaba fiyye da yadda take ji ta sunkuyar da kanta ta cigaba da abinda take "ina kika kwana jiya ? tayi shiru har sai daya sake maimaitawa sannan tace "anan gidan na kwana ta bashi amsa jikinta a sanyaye numfashi ya fesar kana ya juya yana kokarin fita yaci karo da Samir zai shigo dakin ya janyo kofar ya kulle "meye haka ?"dady ne fa ya aikoni yace na tabbatar ta tatttara kayanta ta bar gidan nan "naji zan fada mata" a'a yanzu nake bukata hakan idan ba haka ba na rantse da girman Allah idan na shiga dakin nan sai nayi gunduwa gunduwa da namanta " . naji zata wuce yau din nan da kaina zan fitar daita wai ma meye na daukar zafi tunda ba kai tace bata so ba, ni ne bata so kuma nayi mata abinda ta dade tana bukata daga gareni "tunda har bata sonka ni son me zata min ?" Wallahi kaji na rantse bana qaunar kisna yanzu zan wuce amman wallahi ka tabbatar data bar gidan nan kar na dawo na sameta ta tafi duk inda yayi mata dadi dan dady yace kar yaga kafarta a gidansa ya sallamawa duniya
Wannan ne sako aka abani kuma na isar ni zan wuce ya karasa maganar yana juyawa".
muradi ya dafe goshinsa da hannunsa daya yana ciza lip's dinsa sannan ya koma cikin d'akin ya tsura mata ido yana kallonta kafin daga baya ya shiga tayata hada kayanta kamar ya tambayeta ko tayi ladama zata cigaba da zama dashi ya mayar daita amman daya tuna wacece kisna sai yayi shiru da bakinsa akwati biyu suka cika suka fito falo ta tsaya tana kallon tv stand bata ga hotonta ba babu inda bata duba ba sai da bata ganin ba yadda bata tambayesa ba haka shima bai ce mata yana gurinsa ba suka fito haraban gidan ya bude Boot dinsa ya saka akwatunan ta shiga gaban mota ya shiga yajasu "ina kika nufa yanzu ? ya tambayeta "kai ni gidan Alhaji marwa numfashi ya furzar sannan ya dauki hanyar gidan yana cewa "bazaki nisanci inda afra take ba amman dai .....sai yayi shiru har tsakiya sitiroom din alhj marwan ya Kaita da akwatinanta alhj marwa yana ganinsu ya mike yana qara jin tausayin muradi dan bakaramin hasara kisna tayi ba ita kuma mahaifiyar afra ta hade rai cikin kulawa muradi yace "Alhaji ga kisna nan na kawo ta zauna agurinku har zuwa sanda su dady zasu huce "ba dai a gidan nan ba yadda uwarta ta wulakanta min 'ya a bayyanan nasi wallahi kisna bazata zauna a gidan nan ba sai dai ka zabi daya cikin biyu ko ni ko ita a gidan kisna tayi raurau da idanuwa zata yi kuka muradi ya zuba mata ido tare da girgiza kai "jeka muradi kaji inshallahu zan san abun yi "kenan ka zabi zama daita kenan ?"eh na zabeta iyakar abinda muradi ya iya ji kenan ya fice yana duba agogon hannunsa bayansa kisna tabi da kallo hawayen da take rikewa suka gangaro mata tasa hannu a hankali ta share tana jin kamar tace ya dawo ya tafi daita "tashi ga daki can ki shiga ki ajiye kayanki inji cewar alhj marwa ta mike ta nufi dakin ta zauna a bakin gado kawai sai siririn hawaye kuma ya kufce mata ita dai bata san yadda alhj marwan suka kare da matarsa ba dan kusan a daki ta wuni gashi ko abinci bata aiko mata ba da daddare ma bata bata abinci ba shiyasa ta kasa bacci har sai asuba ya saceta ".
*****
Satin mumy biyu a asibiti aka sallameta a wannan kwananki mumy ta samu lafiya sai dai fa tayi rama sosai sannan ta kurawa muradi ido tana hawaye gashi dai kamar mai lafiya sai dai babu alamun kuzari a tattare dashi yayinda ko da wasa kisna bata tako gidan ba ranar da alhj marwan ya sanawar dady cewar kisna na gidansa ya rufeshi da fada da bala'i yana cewa "babu ruwana taje rayuwa ce kuma ka fada mata tattara ta bar gidanka dan ma gidana ne tunda gidan dan'uwansa ne kuka kisna tayi lokacin da'ake fada mata sakon dady su kuwa ahlin mumy boye damuwarsu sukayi saboda gudun tashin hankali musamman muradi shi ke dawainiyar komai na mumy da zarar an bukaci abu kafin wani ya yunkura yayi ya dai tabbata dan halal wanda yasan ya kamata kowa addu'ar alkhairi yake masa har granny na cewa "ina wa sakina bakinciki rabuwa da muradi yaro ne na gari mai tausayi da jin kai wannan qauna da yake nunawa salaha da realwan ko iyayensa sai haka mumy kanyi murmushi wani lokaci kuma hawaye ya zubo mata ita tasan irin hasarar da kisna tayi shine abinda ke daga hankalinta har ma yasanyata kuka ."
Ranar da mumy ta cika sati biyu da fitowa wanda yayi daidai da wata daya da mutuwar auren kisna ya badamasi ya kira dukkanin yan'uwansa bai ware muradi ba dan ya rigada ya zama su suma sun zama shi gbdy duk a tsorace suke ya zare farin glass din idanunsa yana kallonsu cike da tausayawa sannan kai tsaye yace "a zahirin gaskiya abinda ya faru da mumy bazan iya boye muku ba dan bamu saba boyewa juna komai ba, mumy dai ta tsallake rijiya da baya ne kuma cikin Allah aka yi nasara bamu rasata ba dan matsalolin da suke jikinta yanzu manya qalubali ne ga rayuwarta mumy ta bar kanta cikin wani hali na tsawon lokaci wanda hakan ya haddasa zuciyarta ta kamu da ciwon gabadaya suka zaro idanu a tsorace suna kallonsa ya badamasi ya numfasa yana cigaba da cewa "zuciyar mumy ta kamu dan har ta fara kumbura wanda ke nuni da komai zai iya faruwa bazan boye ma kanmu dan irin wannan ciwon shine babban tashin hankali sai muguji abinda zai bata mata rai shine matakin karshe kafin muga abinda Allah zai yi idan zuciyar ta cigaba da ciwo dole za'a mata aiki duk wani magani da za'a bata ko aikin a zuciyar bazai kai kulawarmu ba dan hawan jininta ma ya hau gbdynsu hawaye suke zubarwa sun hakikance bakincikin kisna ne yasanyata ciwon zuciya tunani muradi yayi nisa ya bar jikinsa yana cikin tsananin tashin hankali har sanda ya badamasi ya kirasa bai sani ba "muradi ......" yayi firgigib ya tsurawa masa ido "kai ne farinciki mumy dan hk ka qara kwantar da hankalinka domin kuwa kwanciyar hankalinka shine zai kawowa mumy sauki "inshallahu ya masi ni yanzu tunanin barin kasar ma nake zan koma egypty da zama kaga duk wani abu da zai faru da rayuwata mumy bata gani ba bare hankalinta ya tashi na gode na gode da soyayyarku gareni nida dan'uwana Allah ya barmu tare "ameen suka amsa gbdy suna masu tausaya masa yana gama fadar haka ya mike baya ko ganin gabansa babu shakka shima nan gaba za'a samesa da ciwon zuciya dan yana jin ciwon zuciya sbd irin teantion din dayake dauka babu wanda ya sanar da mumy komai sai muradi ne yayi karfin halin cewa mumy "ki taimakeni ki cire damuwar nan a ranki muddin kina son ganina tsaye bisa kafafuna ya fadi haka ne dan yasan matsayinsa a zuciyarta tace "muddin ina ganin wannan fuskar cikin farinciki lallai nima zanyi farinciki lafiya kuma sai an yi mamakinta amman ganinka cikin tashin hankali zan shiga fiyye da naka "inshaallahu mamana bazan sake damuwa ba na gode Allah ya qara miki lfy da nisan kwana ya karashe mgnr yana daura kanshi a kan cinyarta ,ta daura hannuta akan sumar kanshi tana shafawa tana jin wani sanyi na ratsata Allah ya sani tana qaunar muradi da zata rasa komai data mallaka abar mata shi ya isheta karasa sauran rayuwarta data saura "...
Kisna kwance a daki duk ta rame ta fita haiyacinta tayi baki kana kallonta kasan tana cikin damuwa kuma bata jin dadin gidan dan iskanci da take agidanta da gidan babanta babu damar yinsa a gidan hjy Hafsah ,duk ta sallame masu aikinta ta sakarwa kisna ragamar aikin komai na gidan,sai tayi girkin ma ta gama bazata bata ba sai ta ga dama ga zagi da gorin bata iya girki ba "yadda uwarki ta bautar min da 'ya haka zan bautar dake babu duka babu zagi wahala da yunwa ma sun isheki da kafafunki zaki gudu ai kuwa acikin wannan dan kankanin lokacin gidan ya fita ran kisna kullum sai tayi trying number musa ko zata samu sai dai kalma ɗaya computer ke fada mata layin na rufe haka zata zauna tayita kuka yanzu haka ma kuka take a kwance da take dan fara jin nadamar abinda tayi zuciyarta ta shiga rudani kamar ta kira muradi tace ya maidaita amman da zarar ta tuna shi din umarnin iyayenta yake bi sai ta fasa ,aunty afra ta Kira ta zayyano mata komai akan abinda mahaifiyarta ke mata tace " "hakuri zamu taru muyi nima a nan hakuri nake a gidan granny kinsan zawarci no easy Allah dai yasa baki yanko ticket mai yawa ba "bangane hausarki ba ?"ma'ana kina gama idda kiyi aurenki ki huta ". naunayen ajiyar zuciya ta sauke "ki tayani addu'a Allah yasa na samu Musa a waya shine last hope dina "zaki sameshi ki ci-gaba da jaraba kiransa dan nafi son ki aure musa da rayuwa da wannan banza , idan wannan soyayyar ta tsaya haka ba'a yi aure ba gaskiya batayi ba da ikon Allah sai kin auresa kin haifa masa yara masu kama dashi ta karashe mgnr tana dariyar mugunta "na gode aunty afra shiyasa nake son wallahi har kin yaye min kashi saba'in acikin damuwata nan suka ci-gaba da hira afra na zugaata ."
****
Bayan wata daya dady ya fara yiwa muradi shirin tafiya zuwa kasar egypty Samir shima yace bazai zauna ba ƙafarsa kafarshi dan haka dady ya haɗa dashi dan yasan yadda shukwarsu take zai wuya suyi nisa da juna ,yau tun safe dady ya dauki muradi suka fita basu nan basu can sai yamma lis suka dawo Cikin sati biyu abinka da harka manya sannan kuma akwai kudi ga kyawun takardunsu tuni suka zama sababbin dalibai wadan da zasu hada phd dinsu akan kasuwanci kafin su wuce muradi yasa aka sako musa tunda daman saboda kisna yasa aka daure masa shi yanzu tunda babu ita acikin rayuwarsa cigaba da rikesa din me zai yi ? nan suka bar kasar har zee da Junior dan wata uku suka fara karatunsu da himma da kwazo duk da kokarinsa da kuzarinsa kaso dari babu saba'in Amman yana iyakar kokarinsa ,yana yi karatu da daddare kuma kusan ka'ida ne ya ware na kadaita Allah domin mika masa kokonsa akan rayuwarsa data dan'uwansa wanda yanzu yake jin duk duniya shine komai nashi idan ya gama ya ɗan kwanta dan runtsawa sai tunanin kisna yazo masa rayuwar da sukayi wani abun yayi murmushi wani tsaki wani hawaye baya sankara an kira assalatu saboda haka duk dare baccinsa ragagge ne cikin kankanin lokaci abubuwa suka dan fara masa sauki har yayi tunanin sun bude kasuwanci su anan dan hk ya shawarata da dady kai tsaye ya amince a can naija kuwa madu ne ya maye gurbin muradi da Samir a ma'aikata yayinda sadiq shima ya qara samun cigaban rayuwa koma nace rayuwarsa ta sauya sosai ..
*****
Cikin hargagi hjy Hafsah ke cewa "wai ita wannan yarinyar ta dinga zama damu kenan wallahi na gaji da zama daita yadda 'yata bata samu farinciki ba itama babu wannan acikin gidan nan "wai me yarinyar nan tayi miki ne Hafsah ?"wannan al'amari qaddara ce fa ita taki yar me yasa taki zaman lafiya a gidanta yakamata ki dawo hankalinki anan ta daga masa hannu ranta a bace "alhj ina matukar ganin kimarka "mutuwar auren kisna qaddara ce ta afra ce ba qaddara ba ko ?" Koma dai menene zaman ya isa haka tun turi tattara ta bar min gidana ta koma gindin iyayenta nima yarinya ta dawo hannuna ranar bala'i har gurin granny bataji dadi abinda Hafsah tayi ba Amman data tuna Itama kisna yar iskace sai tace " a gaiskiya ya kamata ta kama gabanta ta bar musu gidansu su zauna lafiya kisna na samun labari ta fara kuka wiwi "shikenan kowa ya tsanane na shiga uku dan Allah hjy ki barni iddata sai na bar miki gidanki "baki isa ba wallahi sai kin tafi ai kinsan hanyar gidan shi wanda kika kashe aurenki saboda shi ?" kisna na cikin wannan tashin hankali sai ga isa ya shiga cikin maganar ,alhj marwa na fita daga gidan yace akira masa yarinyar ai yana ganin kisna ya fara dande baki yace "gaskiya aunty ki barta kawai na zuwa wani lokaci duka wata nawa tayi ne ma ?"cikin na biyu gaskiya nagaji da ganinta amman tunda kace abarta zan barta nan da wata hudu a tattara abar min gida kije ki kawowa dan'uwa abun sha dan kin wani tsaya kina kallon ko godiya bazaki masa ba mara mutunci bazaki , daura min ciwo yadda kika daurawa uwarki ba isa kanin hjy Hafsah ne shine ɗan sauransu karatu yake har lokacin yaki aure duk ya kai aure har ya wuce sai dai mugun mazinaci ne ".
Banda hawaye babu abinda kisna take , kullum cikin yunwa take gashi bata jin dadin bakinta ko an bata abinci ma ba iya ci zatayi ba idan tayi yunkurin barin gidan tunanin inda zata ke daga mata hankali ta gwamaci ta cigaba da zama a gidan alhj marwan dan batasan inda zata ba zata rayu a haka ko kusa idanunta basa samun bacci har zuwa sanda za'a kira assalatu ,zazzafan zazzaɓi ya rufeta sai datayi kwana biyar tana kwance da kyar ta mike yau ta shiga wanka ta gasa jikinta sosai tana kukan zuci dana fili bata sanar wa kowa ba tunda ko tasanarwa matar gidan ma babu abinda zatayi saboda haushinta da take ji dan laifin karshe bala'i za'a yi a gidan haka ta dinga jinya a boye tana kuka da gatanta da komai ta dawo abar wulakantawa kamar a mafarki ta shiga neman layin musa aiko ya shiga take ta watsatake ta dawo normal Kira uku tayi sannan ya ɗauka aiko ta fashe masa da kuka take ya fahimci mai kuka ", ifemi ykk ya kwana biyu ?"cikin kuka tace me kayi aka kai jail ?"babu abinda nayi ina zaune cikin abokaina akazo aka daukeni zuwa saks kwana biyar aka wuce dani jail har yanzu da nake mgnr bansa wanda yasa aka kamani ba kuma ya hana belina "nan hira ta barke ta fada masa aurenta ya mutu yayi shiru yana sauraronta "har yanzu ina kan bakana idan zaka aureni "me zai hana idan iyayenki sun yarda "karka damu idan ma basu yarda ka kama daki kawai mu tare ...."kamar gaske zaki tare din?" Allah da gaske nasan baka da kudi daki ɗaya ma ya ishemu kaje side din oko ina ka kama anan suka kawo karshen maganarsu ranar ta manta wani halitta muradi a rayuwarta burinta ta kammala iddarta suyi aure da musa tun daga ranar wayarsu ta dawo kullum suna makake da juna a waya "..
Bayan wannan wahalar da azabar yunwa da hjy Hafsah ke wa kisna sai wani sabon al'amari daya kutso kai cikin rayuwarta shine kanin Hajiya hafsa ya fara sanyata gaba kwadayi da maitarsa sun fara fitowa fili har indan tana kusa baya natsuwa isa wani irin mutun ne dan akuya mara kunya mara tarbiyya muddin zuciyarsa ta kwadaitu da mace sai yaci tun zuwansa gidan daya ganta ya fara jin wani abu a game daita a dalilin haka ne ma gbdy yace a barta a gidan ya tattaro daga hotel