Showing 198001 words to 201000 words out of 495987 words

Chapter 67 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

ajiyar zuciya da idanu ya bita cike da tausayawa shima ya raba gefenta ya kwanta tare da janyota jikinsa ya rungumeta tsam ajikinsa ranar bata runtsa ba har sai da zuciyarta ta hasko mata Aliyu cikin bala'i da irin mataki da zata ɗauka akan shi ,sai data gamsu da hukunci zuciyarta sannan bacci ya samu nasarar d'aukarta cike da mafarkinsa ...."

Washegari afra taje bangaren mumy domin bata hakuri bisa shawarar da zuciyarta ta bata dan samun damar aiwatar da shirinta yadda ya kamata , mumy ta kalleta ido cikin ido tace " wallahi afra kin bani mamaki ba Aliyu daya kasance jinina ba ko karen gidana ban dauka zaki iya masa abinda kike wa aliyu ba , muradi fa dana ne dan dan'uwana da muka fito ciki guda sam ban tsamaci haka ba wai ma a ina kika jiyo wannan zance da tsirarun mutane kadai suka san dashi ? " afra tayi shiru har sai da mumy ta sake tambayar tana yi mata kallon banza sannan tace "Ni dai Kiyi hakuri sannan ki bawa muradi hakuri kuskure ne da sharrin shaidan bazan sake ba "kin san Allah muddin kika ga na hakura kin fada min wanda ya fada miki ko kuma a inda kika jiyo zance ..."Afra ta runtse idanunta saboda sanin halin mumy data yi mace ce mai matukar hakuri da sanin Yakamata sai dai fushinta bai da kyau tasan tunda ta dage sai taji to sai taji sannan za'a samu zaman lafiya , a hankali ta bude idanunta ta tsurawa mumy wacce ta maida hankalinta wani bangaren tana girgiza kafarta daya "Kiyi hakuri mumy babu inda naji wannan zance sai a bakinki ke da ........"kafin ta karasa mumy ta jiyo tana jefa mata wani mugun kallo zuciyarta na bugun tara tara wanda yasa afra gaugawan yanke maganarta babu shiri , ganin irin wulakantaccen kallon da mumy ke mata yasa tayi saurin sunkuyar da kanta kasa sannan ta cigaba da maganar data fara "tabbas mumy a bakinki naji ke da hajiya rabi kafin bikinmu a lokacin da kuka kebe kuna tautaunawa akan batun dawowar zainab gidan nan "kenan labe kike min idan nayi baki kau ? afra tayi saurin girgiza mata kai alamun a'a "sam ba haka bane mumy lokacin ina kokarin kawo mata abun sha ne idan baki manta ba "shine aka ce Kiyi amfani da wannan kalmar dan ki sake tabarbare masa rayuwa a lokacin da zuciyarsa ke sake bushewa ,ina kokarin naga ya manta komai ya fuskanci rayuwarsa data saura amman ke kullum cikin son tozartashi kike yanzu ke rayuwar muradi bata baki tausayi ? a ran afra tace "ko daya babu ta inda zan tausaya masa domin shine halitta na farko dana tsana kuma nake masa mummunar addu'a da fatan afkuwa cikin maseefar rayuwar "gaskiya afra ki canza hali dan matsayin diyata na daukeki ba matsayin suruka na daukeki ba zuciyata , ina jinki tamakar su ummi Kiyi gaskiya a tsakaninki da muradi dan shi din abun tausayi ne , bakya son shi bai zama dole ki so shi ba amman karki nufi shi da sharri da bakaken zantuka dan zuciyata bazata dauki haka ba ".
"inshallahu mumy zan canza Kiyi hakuri zan canza domin samun rabauta nima nasan nayi kuskure kuma zan daina duk abubuwan da nake masa zan rikesa tamkar dan'uwana idan har ban karbi gaskiya daga gareki ba tun yanzu sai yaushe ? "naji dadi kwarai da gaske da kika fahimci mahaifiyarki " mumy ta saki ranta tana kamo hannun afra ka zauna da mutun da zuciya daya shi zai sa kaji dadin gardin dake cikin rayuwar duniya da hawa turba mai kyau , idan ka shuka alkhairi ba wani kayiwa ba kanka kayiwa , haka zalika akasin sa dan Allah ki canza ki manta komai rayuwa bata da tabbas sannan bama da ishenshi lokaci a duniya tana gama jin karshen maganar mumy taji hawayen bakinciki ya silalo mata "ina bazan iya manta wannan cin zarafin da yayi min ba koda zan mata komai sai na rama, sai nayi distroyen komai nashi da rayuwarsa mumy ta rungumeta tana rarrashinta dan ta dauka kukan nadamar abinda tayi take tun daga lokacin afra ta dan rage wasu abubuwa har tana sakarwa muradi fuska har idan ana magana tana sakashi cikin hirarsu wanda shi sam baya kaunar haka kullum bakincikinta sake mamaye zuciyarsa yake shi ,da yake ganin mahaifiyarsa tana cikin rahmar Allah dan babu tabbacin zuciyarta ta koma zuwa ga mahaincinta da kafrici , dan babu tabbas din yin ridda a cikin kudin tarihin mahaifiyarsa, ta dai ce zata koma addininta amman babu wanda zai tabbatar gaskiyar haka sai Allah , duk abinda take kallonta kawai yake a dage dan duk wanda yace bai kaunarka to bai kaunar ...."

Mummuy na zaune a falo ita da muradi suna magana afra ta shigo dan yanzu kusan a bangaren mummuy take yini saboda takunkumin da Aliyu ya saka na hana Kisna zuwa gurinta, zafi goma da a shirin bazata jurar rashin Kisna ba , haka bazata bar Aliyu ya shata banza ba , sai ta rama abinda yayi mata, ta kowani hanya " sannuku ta faɗa sannan ta samu guri kusa da mummy ta zauna ,mummy ce kawai ta amsa mata cikin sakin fuska dan ta lura yanzu ta ɗan sauya ba kamar da ba dan idan da ne bazatayi jami'i ba ita kaɗai zatai gaisar ."
"Mummy ki taimaka ki bada kudin nan ayi mana aiki mu samu club mai kyau wallahi kudin da zamu samu sau daya yafi riban wannan kasuwanci da kike magana akai "ni dai naki ban hanaku buga wasa ba amman dole sai an karanci kasuwanci dan ragewa mijina sauƙin ayyuka ,Afra tayi musmushi tace "kai mummy kina dai ji da dady fa "dole ne afra dan shima yana ji dani ,cikin tsigar wasa Aliyu yace "shikenan mummuy zan san abun yi, zan san duk yadda zanyi na samu kudin da zamu yi join din karamin club dan a fara damawa damu .
"ni dai babu ruwa idan kaje ka matsawa rayuwarka babu ruwana kasuwanci nace a fara karanta kafin buga wasan kwallo itama tayi maganar cikin tsigar wasa suka cigaba hirarsu suka share afra ..."

******

Da misalin karfe takwas na dare dady ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama yana gyara zaman babbar rigsrsa yayinda muradi da Samir ke biye dashi a baya rike da laidodi har guda biyu wanda damammiyar fura da nono da rufaida yougth ne a ciki , babu kowa a cikin filin falon dan haka kai tsaye part dinsa ya nufa ya cire babbar rigarsa ajiye akan gado sannan ya zauna yana kwance agogon dake d'aure da tsintsiyar hannunsa , cike da girmamawa muradi ya suruna ya ajiye laidar hannunsa ya juya ya fice daga dakin Samir na ƙoƙarin fita dady yace "samir ungo nan kaje gurin Bature mai Nama ka siyo nama Samir ya tsaya domin amsar sakon dady ya ciro wallet dinsa ya zaro fararen 'yan dubu dubu guda biyar ya bawa samir "gashi siyo na dubu biyu dabam na dubu uku dabam sannan kafin ka wuce aiken ka turo min uwar amarayu Samir ya amsa da "to sannan ya karbi kudin ya fito daga dakin yana fita dady ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka bai dade ba ya fito ya goge jikinsa ya fesa turare ya zira jallabiya fara sol ya zauna ya dauki wayarsa ,bai jima da zama ba sai ga sallaman Samir a kofar dakin yana daga zaunen da yake ya bawa samir izinin shigowa Samir ya shigo cikin dakin hannunsa daya rike da laidar nama yayinda dayan hannunsa ke rike da Kisna cike da girmamawa ya rusuna ya ajiye laidar dan shima ya koyi wasu daga cikin dabiun muradi dan baya bawa babba abu a tsaye ,Samir ya fita da sauri kasancewar ana jiransa a waje Kisna ta karasa jikin dady "dady me ka siyo min ?" Yace fura ce sai nama "ta yatsina fuska " kasan nifa banason shan furar da kake siyowa baya min dadi "kwantar da hankalinki mamana na siyo miki rufaida yougth sannan ga nama nan da zafinsa yayi maganar haɗe da mikewa ya dawo kasa kan roug ya zauna tare da janyo Kisna ya zaunar daita gabansa dashi "zauna mamana muci nama ya bude laidar nama wanda ya lura da girmansa kadan ne bai kai dayan girma ba tare da bude takardar "Bismillah mamana".

A hankali suka fara cin nama suna hira har suka cinye na dubu biyu tass kasancewar shima yana son nama sosai sannan yace ta dauki na dubu uku ta kaiwa mumy ɗakinta tunda har lokacin bata shigo ba , daukar laidan nama tayi ta nufi kofar fitowa daga sitroom din dady madadin ta shiga dakin mumy kamar yadda aka aiketa sai kawai taja tsaki "bazan kai wa mumy ba dan idan na kai bada Samir da madu kadai zasu ci ba har da wannan muradin sai ya ci gara na kaiwa babba mai gadi mu cinye ta nufi kofar fita haraban gidan gurin baba mai gadi dake zaune yana sauraron yar karamar radiyonsa ta nufa .
yana ganinta ya washe mata baki "a'a mai rikicin gangance da wannan lokaci "? Kisna autar hajiya kenan ga tsoro ga ban tsoro fada da gaskiya tsoro ne me kika zo min dashi ne ? Yayi tambayar yana sake fadada fuskarshi da Murmushin "Kisna ta yatsina fuska kamar koda yaushe sannan ta zauna akan bancin da baba mai gadi ke zaune ta bude laidar hannunta tace "baba mai gadi zakaci nama ? Ya gyada mata kai tare da "cewa eh mai rikicin ganga fada da gaskiya tsoro ne a gurinki dama .. ......"mu ci nama baba mai gadi ta katseshi ta hanyar fadan haka yayi murmushin yana cewa "godiya nake uwar dakina Allah shi yaraki naga girmanki yasa hannu suka soma ci yana ci yana zuba mata santi da surutai har suka cinye Nama 3k tasssss...."

Can cikin gida kuwa dady ya fito daga tukararsa ya shiga dakin mumy dake tsaye tana kokarin gama shiri dan taje ta samesa , ya shigo da sallama ta cikin mirrow ta kalleshi tayi Murmushin "ranka shi dade sannu da zuwa ka gaji da jirana kou "?"Na gaji har nayi wanka yayi maganar yana kallon mumy baya gajiya da kallonta ita kuma bata gajiya da gyara kanta kullum tana nan kamar ranar sukayi aure kallonta ya cigaba da yi tun daga yatsun kafafunta har zuwa fuskarta a hankali ya taka zuwa inda take tsaye "shiryarwa ta isa haka aji dani ko nayi kundinbala na dauko yar shila".
manya idanunta da suka fara manyata ta zuba masa "har yanzu ban hanaka kara aure ba kuma bana bakinciki ba dan bana kishinka ba saboda Allah ne yace ayi idan ma kana bukatar taimakona zanyi ".
ya sake matsota sosai yana cewa "wani irin taimako uwar marayu zata min dan nasanta da alfarma da adalci ?"zan biya maka sadakin amarya tayi maganar atakaice "dady yayi Murmushin sannan yace "nan fa daya ban da wannan a canza wani alfarmar sadaki mai sauki ne a dauki bangaren wahalar aure gaba-daya ya karasa maganar yana dariya "bari naje falo na jiraki har juya zai fita daga dakin sai kuma ya tsaya "ina Kisna take ? "ba kuna tare daita ba ?" eh muna tare daita na bata nama ta kawo miki mumy ta bude baki zatayi magana kenan sai ga Kisna ta shigo dakin tana tsalle "yauwa gata nan ma ina naman da nace ki kawowa mamanki ? Kisna tayi shiru tana kallon dady tamkar wacce tayiwa sarki karya har sai daya sake magana sannan tace "na kai mun cinye da baba mai gadi" "what kuncinye da baba mai gadi shi aka ce ki kai wa ? Mumy tayi maganar tana kwashewa da dariya ."

"Ya Salam wannan wacce irin futananniyar yarinya ce shi nace kikawa da kika kama hanya kika kai masa shima saboda rashin tunani da rashin sanin ciwon kai ya zauna kuka cinye wannnan nama mai uban yawa , wannan yarinya wannan yarinya bakyau jin magana wallahi ? Yanzu uwar marayu wani hukunci zaki mata? mumy ta sake kwashewa da wata dariya sannan tace "me kuwa zan mata dady "? "bazaki mata dukan tsiya ba ,"yau da kanka bayan baka son ana dukan yara? "bana so amman yau wannan mamar ta cancanci duka".mumy ta kasa cewa komai sai dariya take shi kuwa dady abinda yafi masa ciwo ai sunci wanda ya siyowa tare, da rashi kirki da mugunta irin nata ta salwanta dana sauran hannu ya kai ya kamo kunnenta yayo hanyar waje daita yana cewa "sai na cire wannan kunnen rashin jin maganar ya murde aiko take tasa masa kuka tana fixge kunnenta tare da cewa "Allah ya isa...." dady ya tsura mata ido yana kallonta cike da mamaki jin abinda tace mumy dake biye dasu a baya tace "ai idan dai Kisna ce kadan kaji na rasa yadda zanyi da yarinyar nan gashi idan tayi abu sam bazakace ita ce tayi ba kalli yadda take kuka zaka dauka idanunta ake kwakulewa? suna cikin magana Samir da muradi suka shigo muradi ya kamo Kisna jikinsa yana tambayar "wa daki Hajiya kayi ? Kisna Ta fixge daga jikinsa tana cigaba da kukanta mumy tace "Allah ya isa tayiwa dady "what ? Suka hada baki gurin fadan haka shida Samir aiko batare da bata lokaci ba Samir ya samo igiyar caji ya shiga labta mata akafafunta wani karar ta sake saki tana susu gurin sannan yace "maza ki wuce kan kujera ki zauna babu mutsu ta haye ta zauna akan kujera tana kuka "yi mi shiru kona kara miki na sake jin kinyiwa wani Allah ya isa zaki ga abinda zan miki, take ta kama bakinta tana sheshekan kuka tana kallon inda yayi shashin wayar caji a kafarta duk suka samu guri suka zauna suka cigaba da tautaunawa akan matsalar Kisna jifa jifa take kallon kafarta tana kallon Samir ..."au kallon shashin bulalar kike ? bakya son duka amman kin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login