Showing 168001 words to 171000 words out of 495987 words
Chapter 57 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
da haka kema kiyi kokarin idan kinyi aure ki haifar da haka a gidan aurenki , kulawa mai kyau ina yiwa dady, ina kwantar masa da hankali bana damunsa da bani bani ,idan kudi zai bani bana amsa sai idan ya zama dole ke sawa na amsa , shiyasa banga abinda zance yayi min ba yaki yi min , sai dai idan bai dashi , Allah dai yaja da ranshi "
afra tace "ameen ".
Suna zaune suna ta hira har uku da minti hasim " bari na tashi ga la'asar har ta kusa ya kamata a soma haramar abinci dare ". afra tace" mai za'a daura mummy ?" Ke da kanki ke ciwo ki bari idan su mufeeda sun dawo sai su d'aura ko da yake ga islamiyya zaku jiya baku je ba lallai su shirya yau suje ke kuma zuwa gobe kya je nayi aikin da kaina ."
"ai tunda na sha magani naji sauki zan yi aikin islamiyya dai naje gobe idan Allah ya kai mu " Mummy tace " afra na lura baki son karatu gashi nan Kisna ma ta dauko halinki na rashin son karatu mace babu karatu akwai matsala kar fa a cireki cikin 'yan walima "Allah mumy ba haka bane walima kuma dole ayi dani bayan dayawa ma yan ajin basu san komai ba kudi zasu biya ayi musu walimar "to ke dai ki maida hankali karki yi walimar zuku azo ana tambayarki karatu ki kasa "zan kokarta "okay ki duba frizer kiga akwai raguwar kaya a ciki a yiwa dady farfesu cat fish yace ai masa " Afra ta mike cikin sanyi jiki ta nufi kitchen ta duba taga akwai saura har yayi kankara ta debo ta samu yar madaidaiciyar rabo , ta bude famfo ta tara ruwa jim kaɗan ta kashe famfo ta ajiye ta saka kifin a ciki roban domin kankarar ta narke , ta fito parlour ta zauna tana kallon tv".
mummy ta Mike tace bari naje nayi sallah na dawo muyi aikin tare ganin afra na kallon tv yasa mummy ta dan tsaya tace "kije kiyi sallah kou " afra tace "to haɗe da mikewa ta nufi dakinsu ,karfe hudu da minti goma gabad'aya yaran gida suka dawo daga school , suna cire kayan school mumy ta umarce su da saka kayan islamiyya tare da daura alwala dan gabatar da sallah , mufeeda ta yiwa kisna wanka bayan tayi sallah taci abinci , tana ƙoƙarin saka wa kisna kayan islamiyya kisna ta tubure tana kuka "wallahi aunty mufeeda bazani islamiyya ba ki kyaleni kullum sai malama tayi min bulala ni banason bulala tana kuka tana zame wandon makarantar da mufeeda ta saka mata ta fito parlour da gudu tana ihu bazata islamiyya ba har da birgima a kasa mummy daga cikin d'aki ta kwallawa mufeeda Kira tace "kyaleta zata zo daga baya ,dungure mata Kai mufeeda tayi sannan ta dubi afra data dauki Kisna ta rungume ajikina tace "afra bazaki bane kema "?"Ke sai gobe zani suka fito tare da zahra suka wuce dan tuni Aliyu da madu da samir sun kama gabansu dan dama basa jiransu zuwa islamiyya .."
Mummy ta fito tana kokarin zama kisna ta boye a bayan kofa dan kar mummy tace akaita islamiyya ,
mummy tace "har kin gama komai Afra tace" na kusa dai "yaran duk sun wuce islamiyya ?"Eh duk sun tafi sai kisna ,rabu da jairar yarinyar nan so take ta dinga kin zuwa islamiyya kamar ke kuma bazai yiwa ba karatu dole kuyi . "ai mummy duk kece da wannan mai kan karas din ke shagwa'bata inji cewar samir daya dawo ɗaukar hula "ai dole na shagwa'bata Samir uwa guda ai ba'a bar sawa bace amman akan islamiyya kowa zai jimu suka sa dariya banda Afra data haɗe rai kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa ta zabga masa harara tana cewa " naga alamun suna kake son saka min to wallahi yau ya zamo karo na karshe da zaka Kirani da mai kan karas ".ya dauki hularsa yana tafiya yana cewa "baki isa ki sani dole ba sai nayi ra'ayi yar rainin hankali kawai ,kisna dake la'be a bayan kofa jin fitar samir ta rarrafo ta fito ta matso kan kafe ta zauna tana dariya sai ganin samir sukai ya dawo a lokacin da yake daf da ficewa daga parloun , aiko yana gama tsayawa ya zuba ma kisna rankwashi a tsakiyar kanta "ba dai kina biyewa wannan mai kan karas din ba tana gudun karatu kema kina gudun karatu zaki sani ne "?"Maza tashi mu wuce Ina kayanta mummy daita zan wuce Kisna na jin haka ta sake bare baki tana kuka har da birgima , "kai Samir zan bata maka rai fa ,rabun min da yarinya ta fada tare da janyo kisna jikinta tana rarrashi ya fita yana murmushi. "
"Mummy mai za'a dafa idan an sauke parfesun?" Mummy ta yatsina fuska tana fadin "ni yau na rasa me za'a d'aura kije store ki dauko doya Afra ta shiga ta kwaso guda biyu ta fito tana nunawa mummy ,"mummy guda biyu ya isa ? "Eh sun yi kawo na fere".
"haba mummy gani meye amfanina kije ki kwanta ki huta ".Mummy tace "kwanciya yanzu da yamma nan kafin tace wani abu Afra har ta gama fere doya ta shiga Kitchen domin wankewa , mummy na zaune rungume da kisna tana Kallonta tana tofa mata addu'a a zuciyarta kuma take yabawa da afra duk wanda ya aureta zai yi alfahari daita matsalarta dai kyamar talaka wannan kuma halin uwarta ta dauko , sam bata son talaka ya rabeta sai masu arziki idan kaga tana haba haba da mutun to mai arziki ne talakawa kuwa banza ne agurinta ."
Jim kaɗan Afra ta gama da farfesu tazo ta fadawa mummy sannan ta d'aura doya ta shirya ferfesun acikin kula mai daukar zafi mummy tace" sannu Afra Allah yayi albarka ya baki miji na gari Afra batayi magana ba saboda kunya, ta koma Kitchen tana buɗe tukunya dan gani ko doyar ta nuna taga da saura kisna ta taho da gudu tana kiran yunwa naje ji aunty Afra "sorry my baby yi hakuri na kusan gamawa yanzu zan kammala ".
Nan kisna tasa shagwa'bar data saba tana bubbuga kafa a kasa "to ki goyani kafin abinci yayi tayi dariya tace "ke dai babu abinda kike so arayuwarki kamar goyi . "Ai kece kika saba min dan haka Allah sai kin goya ni tayi tsalle zata hau bayanta ,Afra tayi murmushi tana cewa "autan mummy daga ke babu wata ".Ita kuwa kisna sai dariya take tana ƙoƙarin hayewa bayan Afra "har doki zaki min "kince yunwa, kince goyo yanzu kuma doki bari kici abinci duk zan yi miki my baby Kisna tace "to my mumy "mummy'? afra ta fada tana zaro ido waje tare da kamo kisna jikinta " ni ba mominki bace ni sister ɗinkin ce tace to "muje kici abinci "ki samin da nama ."Ba nama bane kifi ne autan mummy ta duba taga abincin ya karasa ta kashe gas ta samu faranti ta zuba mata suka fito "amman ni kadai zan ciye abinci na ko" ."Sosai babu wanda zaki bawa ".Tace "sai ke da mummy nah kawai zan bawa ,Afra na dariya tace "to autan mummy mun gode ta zaunar daita ,a lokacin da yaran gidan suka fara shigowa daya bayan daya suna yiwa mummy sannu da gida mata suka wuce bangarensu maza ma suka wuce part dinsu suka yi shirin zuwa massalaci dan lokacin sallah yayi ,Afra ta dubi mufeeda da zahra tace "tunda kun dawo ku raba abinci suka amsa mata da" to " bata koma Kitchen din ba sai mufeeda ce ta shiga ta rarraba abinci ta zuba a kula ta kai dinnig table tana kammalawa ta nufi daki dan yin Sallah bayan sun yi Sallah mufeeda ta fito ta danna kararrawar dake bayyanar da kammala shirya dining sannan ta ɗauki abinci baba mai gadi da direba ta kai musu ...."
Mummuy kuwa tuni ta fada wanka saboda tasan dady ana yin isha'i yake shigowa kafin ya shigo tayi wanka da sallah, data idar ta samu humura da kulacca mai kyau ta shafa da mai me kamshi, duk tabi lungu da sako na jikinta ta murza ta dauko rigar bacci mai kyau mara shara shara ta saka ta dauko turaren wuta irin wanda ake haɗawa amare tayi amfani dashi , idan kaga mummy bazaka CE itace ta haifi badamasi ummi da Samir madu da kisna ba har ma kayi tunanin tana da siriki saboda yanayin tsarin jikin da Allah yayi mata komai cassss cassss daidai jikinta tamkar yarinya yar talatin duk lokacin data yi irin wannan shirin dady kamar ya cinyeta saboda kauna uwa uba ga kamshi ta ko'ina dady na matukar son kamshi shiyasa Bata rabo da turaruka kala dabam dabam tsab ta gama shirinta ta daura after dress akan kayan ta fito a lokacin yaran basu shigo ba tukunan ,ta zauna akan kafet tana jiran shigowar dady can sai gashi ya shigo ta mike ta karbi jakarsa da laidar daya shigo dashi tana yi masa sannu da zuwa ,ya rungumeta tsam ajikinsa yana shinshina kamshinta " ina son kamshin nan ranki shi dade gaki nan kullum kamar yarinya mutun ko yayi niyyar kara aure dole ya hakura ". tayi murmushi "dady baka rabo da tsokana ,"idan zakayi aurenka kayi mana menene na salaha acikin zai yi magana tace "muje ka huta karka tsaya tsokanar faɗa ya wuce ciki tana biye dashi zuwa falonsa sai data bishi har uwar dakansa ta cire masa hula "duk kayi zuru zuru yau kamar kayi ciwo yana dariya yace "akwai ki da kallon kurulla ya akayi kika gane haka "?
"Yanzu bani da kowa sama da kai a duniya gaba-daya tunanina da komai nawa yana kanka , idan ban kula da kai ba wa zan kula da? "kai ma kasan dole na dinga lura da yanayinka ta karasa maganar tana shiga bayi ta haɗa masa ruwa ta fito "na haɗa maka ruwan wanka ka shiga kayi ko kaji dadin jikinka"Yace "ina bukatar hutu sosai Amman nasan ba yanzu ba , karshen shekaran nan badamasi zai dawo gida , Kinga da kasuwanci yaron nan ya karanta da gabad'aya ayyukan zasu dawo garesa ni kuma na huta , shiyasa na kwallafa raina akan waɗan nan yaran suma gashi kowannensu yace buga kwallo zai yi"gaskiya ne kana bukatar hutu amman dole su Aliyu su hada aiki biyu buga kwallo da kasuwanci idan sun yarda idan kuma basu yarda ba su hakura da kasuwanci dan ina bukatar na ga kana samun hutu yayi murmushi ya shige bayi ."
A can parlour kuwa gabad'ayansu suna zaune akan dinnig table kowane gabansa plet din abinci ne ,kowa ya ci abinsa ya rage ban da muradi daya cinye tas saboda shi mutun ne mai tsananin son doya da tuwon shimkafa sam shinkafa zalla da kayan kwalama basu damesa ba shi dai ya samu abu mai tauri baya son Mai ruwa shiyasa idan tuwo za'a yi tukawar farko mumy take dibar masa ,afra ta kalleshi tace "su bamburu bawan ciki ko yaushe za'a koyi cin abinci a rage ,mutun kamar dan abinci aka halittosa ta karasa maganar tana kwashewa da dariya ,duk suka bita da ido babu wanda ya tayata dariya Samir ya bude baki zai mata magana muradi ya da dakatar dashi tare da d'ago kyawawan idanunshi ya zuba mata take ta daburce ta kasa kallonsa ta ɗauke idanunta tana jan tsaki "ko kallon uwar me yakewa mutane ? shiru yayi yana jin yadda tsanartab ke sake samu mazauni acikin zuciyarsa sau tari daman shi tsanarta mutun shine abu mafi sauki da zuciyarsa ta iya bare ita da yake jin kamar kaya yafi minti biyar yana hukuntata da idanunsa babu shiri ta dauki kisna ta bar parloun tana gunguni "wai me yasa bazaka bude baki ka ciwa wannan yar rainin hankalin mutunci ba ganin fa kana kyaleta ne yasa iskancita ke gaba ? "bari naje na fito maka da shegiya "no barta kawai a kwai lokacin nadama zai zo mata har ma ya aureta iya abinda ya faɗa kenan ya mike ya bar gurin zuciyarsa na tuttukin bakinciki daya bayan suka mike suka bar parloun gabad'aya.."
Dady na fitowa daga bayi idanunsa akan mummy yayi mata murmushi yace "hmmmmm " Ta dubesa da murmushi akan fuskarta itama tace "hmmmmm din nan ban yarda dashi ba akwai magana a bakinka yace "sosai kuwa gani nayi bakya tsufa salaha daga shigata bayi har naga kin sake canzawa ki dai bi a hankali kin kusan ɗaukar wata suruka ....."
tasa dariya tana kallonsa "Allah idanunka ne ke ganin haka Amman kowa ya kalleni yasan na tsufa 50 something fa ".Cikin barkwanci da yake mata ya fada mata batun auren afra da badamasi mummy ta sha mamaki jin abinda ya faɗa tace "daman suna soyayya ne ko kuwa dai kune kuka ga dacewar haka zaku hadasu?"
"Shine da kansa ya fadawa marwan tun da dadewa to sai yau marwan din yake sheida min sai na kira badamasin dan na sake jin ta bakinsa ,shine ya tabbatar min da gaske ne da zarar ya dawo yake son ayi aure mummy ta zaro ido waje "bashi da lafiya guda nawa Afra take duka shibiyar gareta ko shashida fa ? "To ma ya fada mata ne da zai wani ce yana dawowa za'a yi aure idan kuma bata son shi fa......"? Murmushi kawai dady yayi " d'ana ne fa badamasi ta yaya kike tunani Afra zata ce bata son shi kiyi addu'a ki kuma masa fatan samun nasara ".
"Shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi yasa muna raye za'a yi yace ameen "amman dai ku bari ta gama karatunta na gaba da secondary "aa suna gama karatun secondary gaba-daya zan aure dasu wace ta kawo miji shikenan wace bata kawo ba zan samo mata tace "Allah ya taimaka muje kaci abinci ".
Ya dan harareta ta gefen ido yana fadin "ke kinci abinci ne ?" ta masa wani kallo da su kadai suka san manufarsa "ai kasan bana cin abinci sai da kai sai dai idan baka nan shima kaɗan nake ci". Suka fito daga dakin zuwa dining table ta zuba masu suka fara ci suna hira dady yace "wai ina mutuniyata kisna ne najita shiru ?" Dariya mumy tayi tace "yar shagwa'ba da rigima kenan tana gurin mutuniyarta killa ma tayi bacci dady yace "ai wannan mammartamu bata da matsalar rayuwa gashi tana son Afra za'a Sha daga idan zatayi aure ,"wannan gaskiya ne idan kace Afra to ka gama da zuciyar kisna "yau rigima tayi sosai ita bazata makaranta islamiyya tunda nake haihuwa ban taba haifar yar da bata son zuwa karatun addini ba irin kisna har gara ma idan afra zata ba'a fiyye samu matsala ba ko da yake tace malamar islamiyya ke dukanta ko za'a yi mata magana tayi hakuri ta daina saboda a samu tayi karatun "idan bata son zuwa ki rabu daita sai samo mai koya mata a gida kamar ina ganin zai fi "karatu cikin mutane yafi gaskiya zan so tayi cikin yara y'an'uwanta "to shikenan zan sa ayi min kiran shugaban makarantan nasu ya karasa maganar yana canzawa da wata "yau fa na sha wuya a office kuma ga baki kala kala gashi yawanci duk mata ne kinsan kasuwanci da mata