Showing 246001 words to 249000 words out of 495987 words
Chapter 83 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
gabad'aya ganin ta sauke numfashi da atishawa "mumy tana raye fa suka hada baki gurin fadar haka a tare mumy da muradi suka karaso kansu muradi yayi saurin dukawa a gabanta ya kai hannu ya amsheta a hannu ya badamasi ya tsura mata idanunshi yana Kallonta hawaye na tsiyoyo daga kwarnin idanunsa cike da tausayawa yace "sannu Kisna ......"iya abinda ya iya fada kenan yayi shiri ya kasa karasa magana cikin raunin ciwo taja numfashi da kyar ta sauke tana runtse idanunta tare da rike gefen kungunta da hannu "yanzu kisna kin zabi mutuwa akan a hukunta musa?"inji cewar mumy kafin kace me tuni mutane sun cika gurin kowa na fadan albarcin bakinsa "wani mutun yace wannan yarinya Allah kadai yasan ya'yan da zaki haifa a duniya sama ba daya ba,ba biyu ba har uku ki iya fadowa ,gaskiya ku kaita aikin soja kawai shi zai fi dacewa daita muradi ya d'ago ya kalli mutumi cike da bakinciki a fili yace sai kazo ka kai ta tunda kai ne ubanta zuciyarsu cike da rauni suka ɗauke zuwa gida "...
Mmm Sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 36
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
.....Suna zuwa gida muradi ya ɗauke cak ya nufi cikin gida daita ya kwantar daita akan doguwar kujera mai zaman mutun uku yana Kallonta ta runtse idanunta gam alamun bata son kallonsa gashi bata so ya ɗauketa ba , gabad'aya haushinsu take ji "mai yasa bata mutu ba a sanda ta fado ta huta da rayuwar duniya . ita fa da tayi rayuwa babu musa gara ta mutu dan wani irin zazzafan so take masa wanda take jin bazata iya wata rayuwar jin dadi ba idan bata tare dashi , gabad'aya yan'uwanta suka zakayeta suna Kallonta suna kukan zuci yayinda mumy ke zubar da hawaye wasu na sake gangaro wa tana korowa dady abinda ya faru aiko yana gama ji ya hau bala'i cikin tsananin fushi da tashin hankali ",yar iskar yarinya kawai idan kin mutu kin mutu kafura dan wuta zaki direct tunda kina sane kike son yiwa Allah ganfanci shi kuma wanda zaki kashe kanki akanshi ya rayu ya auri wata shashar banza shashar wofi kawai ban da haukan kuruciya irin naki me zakiyi da wannan yaron ?" Yaron da ko ganina yayi bai san ya girmama ni bare ya bude baki yayi min gaisuwar mutunci amman shine mutumin da zaki iya kashe kanki akanshi , daga yau idan kika sake kula yaron nan sai na yafeki acikin ya'yana kar ma kice ni mahaifinki ne ta inda dady yake shiga bata nan yake fita ba ,bai taɓa takaici da bakinciki abinda take yi ba irin na yau da tayi kokarin kashe kanta a karon banza cike da jin haushi yace ,kai ku tattara mata kayanta ta bar min gida taje can gidan iyayensa su karanta cikin ɓacin kowanensu ke Kallonta yaga yadda zata yi react zata bashi hakuri ko kuwa zata fi buƙatar barin gidan sai dai dukkanin alamu sun nuna ko ajikinta da abinda dady ya faɗa yayinda a zuciyarta tace "da za'a tattarata din akaita gidansu da gaske zatafi son haka ai ."
Kuka mai ciwo aunty afra ta rushe dashi tana faman zance zuci "wayyo Allah wannan irin bala'i ne ya samu ita da kisna acikin lokacin ɗaya sun kamu da wahalallaliyar soyayya ,
Ita soyayyar Aliyu data mata kamun kazar kuka bata san ranar da zata fita a ciki ba , kisna kuma soyayyar musa wacce sam bata dace da rayuwarta ba kai gabad'aya babu gara a cikin halin taskon da suka tsinci kansu domin duk zuciyarsu bata dace da masoyan da suka kamu da soyayyarsu ba duk maganar da'ake a falon muradi bai ce komai ba illa qirjinsa dake zafi da bugawa da karfi , a natse ya mike ya shiga dakin mumy ya dauko man zafi ya dawo ya ajiye a daidai gefen kanta yana satar kallonta har lokacin idanunta na runtse tana furzar da iska wanda da gani zaka fahimci na bakinciki ne ya juya a sukwane ya shiga Kitchen ya d'auko ruwa mai sanyi ya dawo ya d'aga kanta ya zaunar daita gabadaya warin maza ya buso daga jikinta ya kaiwa hancinsa ziyara gashi jikinta yayi wani irin azababben zafi saurin ɗauke numfashisa da hannunsa yayi ya kasa had'iye miyo , bancin mutane dake tsaye akanshi suna da matukar mahimmanci a rayuwarsa da babu abinda zai sa ya cigaba da tsayuwa a kusa daita, dan wani irin wari take kamar na buntsoro take ya fara addu'a a cikin ransa Allah yasa wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu da yaron ba , dan irin wannan da wuya ace babu abinda ya shiga tsakaninsu idan kuwa hakan ta kasance a tsakaninsu hakika ta cuci kanta kuma ta cuci mijinta ..".
Haka ya cije ya daure ya kai goron ruwan bakinta "ki bude bakinki Kisha ruwa "yayi maganar cike da tausayawa har ta bude bakin taji sautin muryarsa ne sai ta bude idanunta dake runtse fessssss akanshi , take kwayar idanunsa ya tsarke cikin juna wani irin bugawa zuciyar muradi yayi da matsanancin karfi wanda ya rasa dalilin haka, kwayar idanunta dake cikin nashi ke kara masa jin tsananin faduwar gaba mara misaltuwa gaba-daya yaji kuzarinsa yayi kasa saboda tasirin idanunta da kyar ya aro jarumta ya sanyawa gangar jikinsa sannan ya sake bude baki "ki daure ki sha ruwa kiji sanyi ". cike da jin haushinsa ta kawar kwayar idanunta da bakinta gefe tana yatsina fuska kamar wacce taga mugun abu a ranta tace "uban 'yan shishigi kawai a zahiri kuwa cewa tayi "bana sha ta fada a takaice tana jin haushi ".
Bai ce mata uffan ba ya ajiye roban ruwan ya lakato man zafin ya ɗan yaye gefen kugunta daya lura ta nan ta buge ya soma ƙoƙarin shafa mata man aboniki , tayi saurin buge masa hannu "wai meye haka ne ? tayi maganar a fusace bai damu ba ya sake kai hannunsa ta sake bugewa da karfi "ni ka kalleni dan Allah banaso ? " ta karasa maganar tana kuka samir ya karaso da sauri ya ɗauketa da wani gigitaccen mari yana huci "kina hauka ne?" ko kuma wancan dan iskanka ya koya miki shaye shaye ne ko sa'anki ne shi dan ma kin samu zai taimakaki?" ko dan Kinga an kyaleki ba'a miki komai ba zaki kawo wa mutane iskanci ? ta dafe kuncinta daidai inda marin ya sauka tana kallon Samir hawaye na bin kuncinta "ka min daidai Samir karawa shegiya ta dawo haiyacinta inji cewa mumy ,aiko kamar jira yake ta fadi haka ya d'aga hannunsa zai ƙara mari muradi yayi saurin rike masa hannu cikin zafin nama da tsananin ɓacin rai yake kallon Samir da mumy shima samir din kallonsa yake da muryarsa a hargitse yace "why mumy?"Mai yasa bazaku barta ba ? " dan Allah ku barta haka da me zata ji ?"Yanzu ku bakwa tausayinta as age dinta ace ta tsinci kanta cikin wannan halin ?" ai abar tausayi ce ita wallahi ni ina bala'in tausaya mata ina jin kamar na dauke kuruciyarta na maida kaina , dan ko ni na tsinci kaina cikin halin da take ciki dole a tausaya min bare ita kamar yarinya yar shekara shabiyu zuwa shauku a duniya ya karasa maganar yana tsaida idanunsa sosai akan Samir "Kai kuma Samir to be your last warning da zaka mareta wallahi idan ka sake tabata zamu samu matsala da kai ."mun dade bamu samu matsala ba muddin akan wannan shegiyar yarinyar ce da ........""karka sake zaginta da kalmar shegiya muradi ya yi maganar a fusace yana huci kamar zai shake wuyan Samir , dady ya shige part dinsa na kasa cike da takaici da bakinciki ya barsu suna sa'insa a tsakaninsu ,Afra ta matso kusa da kisna tana wani kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta ta rungumeta tsam ajikinta batare da ta damu da warin da take ba zuciyarta na zafi ta fara magana cikin muryar kuka "kisna kiyi wa Allah kiyi hakuri ki rufa mana asiri ki rabu da yaron nan kullum ke kadai ke shan wahala shi yanzu haka yana can gidansu kwance a bayan uwarsa ya barki cikin damuwa da tashin hankali ta fadi haka saboda ita kadai tasan yadda kisna ke ji a zuciyarta so ba karya bane sai dai ita dince bata kai soyayyarta inda ta dace ba karami yaro wanda duka bai bata ya wuce 4 to 5 year ba ,bama wannan ba shaye shayen da yake uwa uba rashin kunya sam bai dace daita ba"...
" ki rabu dashi kisna kiyi min alkwarin zaki rabu dashi ki tausaya mana dan Allah ,wallahi idan an barki dashi wahala zaki sha a gidansa inji cewar zainab ,kisna Kuka, mumy kuka , Afra kuka hatta zainab kuka take tana shawarta kisna data rabu da musa "dama kun daina kuka kuna hasarar hawayenku dan wannan yarinyar bata jin magana ,
zuciyarta bata da kyau ,a yadda nake Kallonta zata iya kashemu akan yaron nan inji cewar madu "wallahi kamar ka sani bakar zuciya gareta da shegen nacin jaraba Samir ya karasa maganar zai zuba mata tankwashe a tsakiyar kanta muradi ya sake riƙe masa hannu " wancan yaron yafi dacewa kaje kama dukan mutuwa amman ita dukan data sha akanshi ya isa haka dan Allah ku barta haka wallahi ina jin zafin dukan da kuke mata har cikin raina yayi maganar kamar zai yi kuka "kana tausayinta alhalin ita bata tausayinkanta gashi kai din ma bata barka da rashin mutuncinta "babu komai duk abinda zata min ta min babu ruwanka .."Mumy ta numfasa sannan ta soma magana cikin zafin zuciya ",Wallahi kisna muddin kika nace sai yaron nan zaki aura bazan yafe miki ba , kuma zan cireki cikin ya'yana kamar yadda mahaifinki ya faɗa ke ko kin aureshi auren bazai yi albarka ba wallahi ko mutuwa nayi kuka yi aure ban yafe ba kuma na dinga damunku kenan dan na dinga zuwa muku a mafarkinku ruhina bazai barku kuyi rayuwa mai kyau ba " . ta karasa maganar tana kuka har da shesheka muradi ya karaso gareta cikin tsananin tashin hankali "haba mumy dan Allah kiyi hakuri ki daina fadar haka kowani bawa da irin tasa qaddara muyi fatan babu qaddarar aure a tsakaninsu ya kamota ya zaunar daita ya dauko goron ruwan daya daukowa kisna ya bata "ki sha ruwa mumy inshallahu ma bazasu yi aure ba wanda kiku bata shi zata aura ....."
Tsaki kisna taja "kinibabban banza kawai kalli yadda ya wani zakalkalewa ai sai kazo ka hana , auren ni da Musa kamar anyi an gama idan kuma anyi mutu ka raba ". Kuka mumy ta cigaba da yi gwanin ban tausayi "dan girman Allah mumy ki rufa mana asiri ki tausayawa rayuwarta ki daina kuka zubar hawayenki ba karamin maseefa da tashin hankali bane gareta madadin abubuwa suyi sauki sai suyi gaba dan Allah ki daina kuka ta kai hannu ta goge hawayen wasu na sake zubowa "Kiyi hakuri mumy Kiyi mata addu'a shi tafi bukata "naji muradi na gode kwarai da gaske Allah ya albarkaci rayuwarku gaba-daya ita kuma Allah ya shiryeta shiri na addinin musulunci "ameen ya furta a kasan makoshinsa shi kansa ji yake kamar yayi kuka bayan bakinciki abinda mahaifinsu yayiwa mahaifiyarsu wannan shine bakincikin da sake yiwa zuciyarsa kawanya wallahi da bawa na yayewa wani bawa maseefa daya cirewa kisna dan ta samu sausauci .."
Zainab ta kamota "muje daki ki yi wanka ki huta dan Allah kiyiwa kanki faɗa tunda mumy da dady sunki amincewa da Musa ki ciresa a ranki ke bama rashin amincewarsu ba kinyi kankatar da lamari na soyayya , ta nufi daki daita tana mata nasiha suna shiga dakin kisna ta fixge jikinta tana watsa mata mugun kallo mai haɗe da harara "dan Allah Malama ki rabu