Showing 204001 words to 207000 words out of 495987 words
Chapter 69 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
da wannan al'amari daya faru ."
Afra ta sake kallon Aliyu cikin zafin zuciya kamar itace mai sarka "wai me kake nema a rayuwarka ne Aliyu ? " anyi maka komai na jin dadin rayuwa , an inganta rayuwarka ta kowani bangare ,an nuna maka gatan daka rasa har ana kokarin fitar da kai karatu wata uwa duniya am maka komai Aliyu amman shine zaka buge da sata ......" ? "Kenan duk satar daake a cikin gidan kaine kake yi amman mumy ta cireka ciki ?"
A hankali ya furta kalmar "sata" cikin tsananin bakinciki yana duban fuskar mumy wacce ta dawo tamkar hadari tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ciki , a hankali Aliyu ya soma girgiza mata kai hawaye na ciccikowa a cikin kwarnin idanunshi ,jikinsa a sanyaye ya mike ya soma d'aga zara zaran yatsun kafafunsa zuwa inda mumy take zaune tamkar an dasata qirjinta banda bugawa da sauri babu abinda yake , hankalin Aliyu yayi mugun tashi da ganin yanayin mumy dan bai taba ganin yanayinta ya sauya haka ba , mumy ta kalleshi kawai da idanunta da suke cike da matsanancin ɓacin rai tuhumar da Afra tayi masa yayinda Aliya yake Kallon mummy a matukar tsorace ,
Kallonta yake sosai don tabbatar da abinda ke zuciyarta "zata yarda ya aikata abinda Afra ke jifansa dashi ko kuwa zata karyata ta ?"Cike da sanyin jiki ya d'aura kanshi akan cinyarta jikinsa na wani irin rawa yana ƙoƙarin yin magana ya sake jiyo Muryar Afra "wallahi wannan yaron zai 'bata mana tarbiyyar gida idan ba'a ɗauki mummunar taki akanshi ba wannan fa sata ne kirikiri ,gashi yasa an zargi Samir alhalin bashi ya dauka ba ......"
"Karki ce haka Afra sam haka bai dace ba ki bari a tambayeshi aji yadda akayi sarka ta kasance a cikin jakarsa ba wai ki zargeshi da laifin aikata sata ba "inji cewar ya badamasi ya katse mata hanzari yana duban fuskar mumy da dady gabansa na wani irin faduwa dan kallon yanayinsu kadai zai fahimtar da mutun irin takaicin da maganar Afra ta jefa zukantasu . "Ban gane kar nace haka ba ? "kana nufin sharrin nayi masa kenan bayan ga zahirin gaskiya kowa ya gani da idanunsa ? " wanene shi da baza'a faɗi illar abinda yayi ba ? "Babu wani dogon bincike ma da za'a tsaya yi ko ace zarginsa ake tun da ga gaskiya ta bayyana akan idanun kowa shine ya ɗauki sarka da ake nema tsawon lokaci ba wani ba ta k'arasa maganar tana kallon Aliyu wanda ya d'ago a lokacin ya zuba mata kyawawan idanunshi masu cike da tsantsar bakinciki da tsanarta a cikin zuciyarsa "Ki daina fadar son ranki akan dan'uwana saboda wannan ba gaskiya bane sharri ne da makirci , dan'uwana bazai taɓa aikata wannan kazamin halin ba samir ya fada a zuciye kamar zai rufeta da duka ..."
"Me kace ?".
"Abinda kunnenki ya jiyo miki shi na faɗa ya bata amsa haɗe da maka mata ƙatuwar harara yana jan tsaki "abun mamaki wai akama barawo dumi damu da kayan da'ake nema amman ana danganta hakan da son rai ko kazafi , "wai kai din nan me yake damunka ne kana kallon gaskiya amman kake ƙoƙarin dannewa ?" i think har kai sai da mumy ta zargeka akan kai ka d'auki sarka nan shine dan bakin munafurci irin na......"
"Ke dan Allah malama kiyiwa mutane shiru, wai ace mutun bazai iya gane natsatse da wanda ba natsatsen ba ,ta yaya kike expecting muradi zai aikata irin wannan halin ? Aunty ummi ta fada cikin matsanancin fushi tare da mikewa tsaye ta fuskanci Afra dake tsaye qirjinta na bugawa da matsanancin karfin , mumy da dady kam har lokacin kasa magana sukayi saboda tsananin mamakin karfin halin Afra ko sarkata ce iyakacin abinda zatayi kenan bare ba nata bane ."
"Allah sarki muradi nasan bazaka taɓa aikata haka ba , na nasan wannan ma yaudararka akayi aka saka maka Sarkar nan cikin kayanka dan a haɗaka dani amman har abada hakan bazai taɓa faruwa ba da naga wannan ranar da zaka dauki abun wani gara mutuwa ta riskeni da wuri mumy ta fada a fili hawaye na wanke mata fuska ....
"wannan ba yaudarasa aka yi ba halinsa ne fa mumy ki ma daina hasarar hawayenki akan yaudararsa akayi aka sa masa yana sane da zaman sarka shine ya ɗauketa gashin nan yayi magana mana idan har bashi ya ɗauka ba ..."
"Enough Afra Karki sake danganta dan'uwana da kalmar sata ya badamasi ka fad'awa matarka ta daina , ka ja mata kunne idan ba haka ba wallahi za'a yi ruwan bala'in a cikin gidan nan ke idan ma ɗaukar sarka yayi ina ruwanki ince sarkar ta mommy ce ba taki ba meye naki na zakalkalewa da tada jijiyar wuya "?"Bare ma nasan Aliyu bazai dauketa ba dady ya faɗi haka yana Kallonsu daya bayan daya gabad'ayansu ransu a bace yake ,itama Afra ta dai fadi haka ne amman yau muke da Aliyu a gidan nan , aiko sata akayi na cire Aliyu ciki sawun masu sata saboda ba zai taɓa aikata haka ba ,dan shi mutum ne mai amana da kamewa dattijo a cikin yara dan haka karki sake cewa shine ya ɗauki sarkar nafi yarda da saka masa akayi ko dai wani abu dabam ya karasa maganar yana furzar da iska "..
"Sau tari akance tsanar mutun shine abu mafi sauki da zuciya take saurin iyawa ga wani shashi na muguwar zuciyar wani mutun ,
kuma idan mutun yace baya sonka ko ya dawo yace yana sonka karya ne". "tabbas haka ne dan yau na yarda da haka kuma duk runtse nasan Afra bazaki taɓa qaunar Aliyu acikin zuciyarki ba , kuma babu wanda ya aikata wannan makircin sai ...."
"Kayi shiru Samir abar maganar sarka dai tawace ko ?"da suka gyada mata kai "to na barwa muradi ita halak malak yayi duk yadda yake so daita idan bai so ya yar , kuma ban yarda ya ɗauki sarka ba saboda d'ana ba barawo bane "wani sanyi da farinciki ne suka ziyarci zuciyar Aliyu a lokacin ɗaya tamkar wanda akawa albishir da gidan aljanna , take yaji duk duniya bashi da kamar mumy sannan ya ji qaunarta ta ninku akan wanda yake mata ,
a hankali ya d'ago kyawawan idanunshi waɗan da suka wadatu da gashin ido , ya haɗa idanunshi dana mumy cikin sanyayyiyar muryarsa yace "mummy .........."Saurin katse tayi ta hanyar cewa "Karka ce komai bare ma ka tsaya kare kanka saboda ban yarda ka aikata wannan halin ba, tashi kawai ku tafi inda zaku , take jikin Afra yayi mugun sanyi dan bata so abun yazo cikin sauki haka ba ,bata so sunki yarda daya aikata haka ba taso zukatansu su yarda kuma su amince da shine ya dauka kafin shirinta na biyu ya bayyana wanda take saka ran dole ya bar gidan ko yaki ko ya so ..."
Suna cikin wannan halin Kisna ta karasa shigowa parlour'n da gudu tana tsalle hannunta rike da jakar makaranta , turus tayi tana kallonsu daya bayan daya ,a hankali idanunta ya sauka akan sarka ,tayi saurin zaro ido waje tana dafe kirji ganin haka yasa Afra kamota jikinta da sauri "oyoyo baby nah kin dawo me yasa kika shigo babu sallama"? tayi maganar tana daga sama tare da kai bakinta daidai saitin kunneta "karki sake kice nice na ɗauki sarkar nan idan ba haka ba zan saka miki kyankyaso a wandonki ,a dan firgice Kisna ta girgiza kai kanta alamun bazata fada ba sannan ta soma ƙoƙarin zamowa daga jin Afra ,
ta ajiyeta " je kiyiwa mumy da dady sannu da gida ." Kisna ta k'arasa jikin dady ta rungumeshi ya sauke ajiyar zuciya tare da mayar da hankalinsa kan Aliyu yana shafa kan kisna "mumy kiyi hakuri naga kamar ranki ya ɓaci ba son zuciya bane ,haka zalika ba duk zuciyar kowa bace zata iya yarda da ba Aliyu ne ya ɗauki sarkar nan ba saboda ganinta cikin jakarsa wanda nima shine dalilin da yasa na tuhumeshi , "koma waye ya ɗauka yasa akayi zarginsa Allah ya saka masa dan wannan ba dabi'a bace mai kyau..."inji cewar mumy .
A fusace Samir yace "Allah dai ya tona masa asiri a bayyanan nasi , Allah ya jarabeshi da akata sata dumu damu yaji yadda ake ji haka kawai ba'a son ganin mutun cikin farinciki wallahi bazamu amince da wannan tsarin ba Samir ya karasa maganar yana hararar afra .
Shiru Afra tayi tana bin Samir da idanu kafin daga baya ta dubi Aliyu da ya mike tsaye tace "kayi hakuri bisa ...."Hannunsa kawai ya d'aga mata ya wuce jiki a sanyaye tabi bayansa da kallo mumy ta yunkura ta mike ta bar parlou'n ,aunty ummi ma ta mike ta yafa mayafinta ta dauki jakarta ta rataya "Allah ya kyauta ta fada tana nufar kofar fita daga falon batare datayi musu sallama ba ,parloun ya rage daga Afra sai ya badamasi da dady da kisna dady yayi gyaran murabus yana duban afra yace "gaskiya afra kinyi wauta da yarinya ko kuma kai tsaye nace kinyi hauka ta yaya zaki yi irin wannan zargin ga Aliyu kuma a gaban mahaifiyarsa bayan kinsan irin qaunar dake tsakaninsu ? "Sau tari ina fada miki ki daina tsanar Aliyu ke dashi abu guda ne agurin uwar marayu kina keta masa mutunci ya badamasi yace "ni sai yau nasan bata da hankali sannan bata daukeshi matsayin danuwanta ba "zance banza kenan afra ta fada acikin ranta a shekara kai shasha ne da kake tunanin zan daukeshi tamkar dan'uwana ?kasa zaman falon Afra tayi ta wuce bangarenta cike da bakinciki rashin samu nasarar da tayi " yanzu ne ta sake jin matsananciyar kiyayyar Aliyu a ranta bata san yadda zatayi ba so take ya bar gidan ta kowani hali ,zafi take ji sosai a tsakiyar zuciyarta , tana jin muddin Aliyu ya sake kwana a cikin gidan mutuwa zatayi " .
Akan hanyarsu muradi ta zuwa filin kwallo maganar sarkar suke da Samir ,"ka share wannan yar iskar yarinya sam rayuwarta batayi ba nasan duk makircinta ne itace ta shirya komai dan kawai a tsaneka abinda bata sani ba kai din ajin farko ne acikin zukatanmu Samir yayi magana yana daura hannunsa daya a kafad'an Aliyu ,"wallahi ban san me nayiwa Afra ba , shiyasa fa kaga nake Allah Allah takardunmu su fito mu bar kasar gaba-daya ,dan gaba bansan abinda zata bullo min dashi ba ,na rasa laifin me nayiwa Afra a duniya da bata kaunar ganina cikin kwanciyar hankali "babu abinda ka mata mugun halin ne kawai irin na mahaifiyarta gareta basa son ana rabarsu har suka karasa filin wasa magana ɗaya suke ranar babu wani abun kirki da muradi ya tabuka a fili saboda faduwar gaba da damuwa .."
daren ranar har kusan ɗaya da wani abu muradi na zaune a d'aki ya kasa runtsawa , gabad'aya ya rasa meke masa dadi ,hannuwansa duka ya da'ura saman kanshi dake mugun sara masa kamar zai rabe gida biyu tsabar damuwar da zuciyarsa take ciki gashi dai babu wanda ya amince da shi din barawo ne amman hankalinsa yaki kwanciya zuciyarsa ta kasa samun natsuwa burinsa kawai yayi nisa da gidan idanunwansa sunyi jazur tamkar garwashin wuta hawaye ne kawai ke tsiyayowa daga kyakkyawar idanunsa ,shi dai yasan bai taɓa aikatawa Afra wani laifi ba a iya tsawon rayuwarsa a gidan ,bata da hujjar tsanarsa bare ta dinga binsa da bita da kulli ,hujjarta ɗaya ce mahaifinta ya taimakesa akan hanya, amman ya rasa dalilin daya sa ta kasa manta haka sannan ta kasa yarda da cewar shi din jinin mumy ne .."
Samir ya bude ido ya ganshi zaune dafe da kanshi ajiyar zuciya ya sauke mai karfi yà matso kusa dashi ya dafa kafad'ansa "dan Allah ka cire damuwar nan a cikin zuciyarka , mumy fa da kowa dake cikin gidan babu wanda ya yarda , Duk mun san sharrine ake ƙoƙarin yi maka ,kuma ko waye mun barsa da Allah ka kwanta ka huta "bazan iya runtsawa ba bari kawai nayi alwala nayi sallah ya yunkura ya mike da kyar dan har lokacin kanshi bai dana ciwo ba ,ya fito bayan yayi alwala ya fuskanci Ubangijinsa tun yana iya kirga sallar nafila har ya daina daga karshe dai yayi raka'a daya yayi sallama ya daga hannunsa sama ya soma yiwa Allah kirari da kyawawan sunayensa hawaye na gangaro masa sai gurin karfe uku na dare bacci ya d'aukeshi , washegari da zazzafan zazzaɓi da matsanancin ciwon kai ya tashi ko saukowa daga katifa bai yi ba, Samir ne ya fahimci halin da yake ciki ya sanarwar mumy .a rud'e ta shigo dakin tare da ya badamasi da yake Lahadi ne bai fita aiki ba kuma lokacin da Samir din ya shigo yana fadawa mumy suna tare yana sake bata hakuri akan abinda Afra tayi jiya ,juyawa yayi da sauri ya koma bangarensa ya dauko kayan aiki ya fito cikin sauri ,haka nan zuciyar Afra ta tsinke taji wani mumnunar faduwar gaba "ko mai ya faru kuma tayiwa zuciyarta tambayar kamar ta biyosa dan sanin halin da ake ciki sai kuma ta fasa tayi zamanta qirjinta na