Showing 51001 words to 54000 words out of 495987 words

Chapter 18 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

tattare da bakin ciki ".

Kisna na  shirya kaya  aunty  zee na dauka tana  maida wa cikin wordrobe  tana  bata  hakuri , wani  sabon kuka ne ya kufce  mata , hawaye sai turereniyar zubowa suke daga cikin kwarnin idanunta "mai   kike son nayi aunty  zee   shine fa  da kanshi yace na bar masa gida  "? Tayi maganar cikin tsananin  kuka wanda da kyar muryarta  ta fito  "nasani  amman  dan  girman Allah  kiyi  hakuri ko zaki tafi ba yanzu  ba  saboda tashin hankalin da mommy  zata  shiga  Sam Sam mommy  ba zataji dadi  faruwar haka ba.  tayi maganar tare da juyowa  ta kalli  inda  Aliyu  ke tsaye har lokacin tamkar  babu wani halitta dake motsi agurin, ya aliyu  ka bata  hakuri dan Allah  sannan  ka dakatar  daita dan gaskiya   kayi  kuskure abinda kayi sam   bai dace ". Bazan yayi  daita  qirjinshi na wani irin dokawa da  karfin gaske  "saboda me zai  bata hakuri bayan bai ga abinda yayi  mata  ba  ,idan  zata zauna ta zauna  idan  zata  tafi ta dade   shi  dai bazai  wani  dakatar daita  ba  yayi maganar  aransa yana furzar da iska mai zafi ....

   kisna ta sake  rushewa  da wani sabon  kuka  mai matukar cin rai ganin  ko  kallonsu Aliyu  bai yi ba bare  ya  kula aunty zee dake masa magana   ,ta  d'aura  kanta  a kafad'arta   aunty zee numfashinta na barazanar  daukewa saboda kukan da yaci  karfinta   "kisna  !kisna!!  Aunty zee  ta ta kira sunanta  a rude  tare  da rungumeta  a  jikinta  suka zauna a bakin gado  tana cigaba da kiran sunanta , da kyar kisna ta janyo numfashi ta sauke zuciyar na mata wani  irin  azababben  zafi  da  ciwo ,   aunty zee ta mike ta tsiyaya mata ruwa  a  glass  cup  ta mika mata "ki sha ruwa kisna ko  zaki  ji  sanyi  babu mutsu kisna  ta amsa cup din ta kai bakinta ta  kurbi  kadan  ta mikawa aunty zee  sauran ,aunty zee ta amsa ta ajiye ta  cigaba da bata  baki  .
cikin  haka  aryan  ya shigo dakin yana  kuka aliyu  ya juyo  a hankali yayi taku daya  yana  ƙoƙarin kamoshi  zuwa garesa , amman  tuni   yaron ya  karasa gurin uwarsa dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta , ya haura saman  gadon ya rungumeta  ta baya yana  furta mata  kalmar  "sori  mommy , papa ne ya saki kuka kou  ?" Ki yi shiru Ki daina kuka zan rama miki  kinji  ".
kukanta ne  ya  qara  akan wanda take tabbas ya'ya  rahma  ta  juyo  ta rungumeshi  ajikinsa tana sheshekan kuka  tamkar ranta zai fita,hawaye  tausayinsu ne  ya shiga gangarowa  aunty zee  Aryan ya soma ƙoƙarin raba jikinsa dana kisna ",mumy bari naje na rama miki "a hankali ta shiga girgiza masa kai tana kuka gumi na tsatsafo mata ta ko'ina ajikinka matse aryan tayi gam saboda kokarin fixgewa da yake kokarin yi ajikinta yadda take kuka haka arayan da aunty zee ke kuka gaba-daya an rasa wanda zai rarashi wani   ."

Sautin kukansu ne ya soma damun Aliyu a   natse  ya  fita daga d'akin  yana jan dogon tsaki ya shiga  d'akin da areef  yake  kwance  ya  zauna  a  gefensa tare da tsura masa  idanunshi  yana kallonsa, ganin yadda  numafashinsa ke sauka a hankali yasa shi  sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare ya  d'aura  hannunsa akan sumar  yaron yana shafawa a hankali  yana  jin wani irin sanyi mara misaltuwa a zuciyarsa , dan da wani abu ya samu d'ansa da sai yayi distroye rayuwarta  ,sai  yayi mata abinda har ta  koma ga Allah bazata mantawa  dashi ba taimakonta daya d'ansa yana numfashi kuma ko yanzu bazai barta ba har sai yaga mikewar d'ansa tukunan zai saurara mata    ..."

"Idan   kika ji  ancewa  mutun yayi  hakuri   bisa wani abu daya faru to an cucesa  ne ,ki qara hakuri kisna  idan kika  bar gidan Aliyu da sunan yaji ko rabuwa  dashi  ina zaki "?"kin san dai baki  da inda zaki sannan baki da masauki  a gidan dady  idan  kin  manta  abinda  dady  yace bari  na tuna  miki "cewa yayi matukar ba ziyarar arziki ce  zata kowaki  gidansa ba  baya son  ganinki da suna matsala dan   baki a masauki a gidansa, kuma duk  ranar da kika kashe aurenki da Aliyu  sai  dai  ki  nemi wani uban amman  ba shi ba, zan rokeki  da ki kara  hakuri kisna  ki zauna a d'akinki  kada ki ɗauki maganar Aliyu  da  mahimmcin  da zai sa ki  bar gidan nan ". wani sabon kuka ta rushe mata  dashi  tare da zubewa kasa bisa gwiwowinta ta kamkame Aryan dake rungume ajikinta  "shikenan  haka  zan kare rayuwata cikin  kunci da maseefa da tashin hankali "? "mai yasa  dady da mommy suka  kasa fahimtata akan  ya Aliyu "?
"Mai yasa suka fi son shi akan ni da suka yi silar zuwana  duniya "?
  aunty zee ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali ta amshi aryan a hannunta sannan kamota ta zaunar daita tace   "  wannan soyayya daga Allah ce kisna  da kuma  kyautatawar  da yayi musu, kin sani na sani kowa ma ya sani a cikin yan'uwa  Aliyu mutumin kirki ne   ,ni yanzu babu abinda zan ce miki daya wuce  kiyi  hakuri sannan kiyi  ƙoƙarin ki  adana damuwarki  kafin mommy  ta dawo gidan nan  ta fahimci  wani abu , sannan waɗan nan kayan suma ki karasa  maidasu cikin  wardrobe  zanje muyi magana da  ya Aliyu  ta k'arasa maganar tana fita daga."

   kai  tsaye parlou'n kasa ta  zarce  domin yin magana da Aliyu sai dai bata  samesa anan  ba  sai nasir da Samir  da Safiyya ta  samu   zaune shiru  tamkar  waɗan da aka turo musu  da sakon   mutuwa , ta Kallesu daya bayan daya sannan tace "ina ya  Aliyu ko ya fita ne "?Safiyya da nasir ne  suka hada baki gurin   ta bata amsa da  bai sauko ba yana sama ,
yayinda   har lokacin samir  ya kasa furta komai  sannan  ya kasa aiwatar da komai dan jin zuciyarsa yake kamar zata kama da wuta yau da wani ne ba Aliyu ba yayiwa kisna irin wannan wulakanci Allah ne kadai zai rabusu  amman akan Aliyu babu abinda zai  iya yi ko dady yaji yayi magana akan   lamarin sai ya bata masa rai bare matsayin Aliyu ya zarta komai a zuciyarsa ..."

Har aunty zee ta juya zata   koma sama  ta  tsaya batare data juyo ba tace  "dan Allah  abban  Junior  ka dawo  daidai  kar mommy ta dawo ta fahimci  wani abu  ,wannan matsalar tsakaninsu  ne kuma  inshallahu komai  zai  dawo normal yanzu batare da bata lokaci ba , tsakanin miji da mata  sai  Allah ko mutun ya shiga faɗansu  kunya zai ji tayi masa hannunka  mai  sanda saboda lura da tayi gaba-daya yanayinsa ya sauya  tana gama fadar haka  ta hau sama da sauri  ta   shiga dakin mommy ,nan ta samesa zaune ya tasa areef gaba yana kallonsa hawaye na tsiyayo wa daga idanunshi  jin  motsin shigowar mutun  yasa yayi saurin ɗauke hawayensa da hannunsa , sai dai  ya makaro dan  ta  rigada ta gani  .
    girgiza  kai aunty zee tayi sannan  ta  samu  guri  ta zauna akan  kujera tana kallonsa sai data numfasa sannan ta kira sunansa a natse " ya  Aliyu  .... Bai amsa mata ba haka zalika bai waigo inda take ba ,sanin datayi yana sauraranta yasa ta cigaba da magana "dan Allah ya Aliyu ka canza ,a zahirin gaskiya  ban ji dadin  abinda  kayi wa kisna ba , kuma  nasan ko mommy tana nan kai zata bawa rashin gaskiya akan abinda ya faru "."ina  dalilina  nayi  haka , barinta gidan nan shine  abinda zuciyata ta yanke akanta  idan taga zata iya ta cigaba da zama a gidan   idan bazata iya  ba ga hanya nan dan Allah Karki sake bata hakuri  akan lallai sai ta zauna  ki bari ta wuce duk inda zata dan nima nafi bukatar haka  "."Uhmmm  Aliyu ka kuwa masan abinda kake faɗa kama ajiye  batun aurattayar  dake tsakaninku     kai da kisna yan'uwa ne na na jini kasawa ranka  kisna Aliyu suna tare muddin rai mutuwa ce kawai zata rabasu  "stop saying that zainab I don't like what you are doing Ina nugun ganin girma da mutuncinki saboda ke din mai mutunci ce kowa ya sani ...... ".

  "bazan  daina  fadar  haka ba ya  aliyu  saboda bayan jinin na y'an'uwanta akwai wani jini na musamman  dake gauraye acikin jininku   ko kaki ko kaso kisna da Aliyu  abu guda ne  "dan Allah ki daina  faɗar haka kina maseefar  taba min  rai  wallahi "",Babu wani ɓacin rai   hakuri ma  ya kamata  kaje ka  bata saboda kayi mata ba dade ba .  "wannan maganar ma  ba mai yiwa ba ne dan Allah  ki daina fadar haka banaso ina ganin girmanki  zainab  saboda me zan bata hakuri "? "Laifin mai  nayi   da zan bada wani hakuri  "?  yayi mata tambayar ajere ransa na sake ɓaci  sannan ya cigaba da magana cikin zafin zuciya "bana tunanin abinda nayi ya sa'bawa Shari'a   to saboda me kike tunanin  zan bata hakuri "? yayi maganar yana rike hannun areef yana jin yadda hannunsa  yayi sanyi  "yanzu kana son fahimtar dani cewar ba kayi kuskure ba Kenan "?"Yes of course ban yi komai ba wallahi ,kin kasa dai  fahimtata ne kawai saboda kina ganin kamar nayi kuskure alhalin ni Kuma  nasan babu kuskure dana akan za'a kashe min da.... .....".....
yayi  shiru ya kasa karasa maganarsa  yana  kallon kofar d'akin ,itama aunty zee  kofar  tabi da kallo ganin kisna ta gani tsaye  idanunta na tsiyayar da  ruwan hawaye muryarta cikin kuka tace  "ki yarda aunty zee  bai yi min  laifin komai ba ,ni kuma daman na ɗauki laifina  ya dai kasa min uzuri ne amman nasan nice da laifi wallahi tunda nasan halinsu aryan basa zama guri daya ". ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi da ciwo suka sake gangaro mata .
"ni  kaina a yanzu zanso rabuwa dashi
sai  dai bazan iya kallon idanunshi nace na tsaneshi   ko nace  bana bukatar rayuwata dashi ba   saboda darajan  ya'yana, bazan  iya kallon idanun uban ya'yana nace banason shi bana bukatarsa arayuwata  ko bana bukatar had'uwa dashi a lahira ba kamar yadda ya fada min   ".

A matukar fusace yace "kinji ba kinji abinda wannan wawiyar take  cewa ko zainab  wato ma  darajan ƴaƴanta takewa komai ?  "ai daman  nasan abinda ke zuciyarki kenan shi yasa nake son rabaki da su gaba-daya na canza musu wa.........."tayi saurin katse masa hanzari ta hanyar cewa " duk abinda zaka faɗa ya  Aliyu  ka fada amman bazaka  taba canzani agurinsu arayan ba  saboda nice nan na dauki cikinsu na tsawon   wata tara da kwanaki kuma nayi na kudarsu  ...." Ni yanzu   Abinda zaka min   tunda baka bukatar zamana  da kai  ka taimaka ka wankeni  agurin mahaifina   tunda nayi iyakar ƙoƙarina naga mun sasantar kanmu muyi   zaman lafiya da juna   amman kaki ," ba dai baka son zama  da kisna ba ? yayi shiru tare da jan tsaki "to  ka taimakawa rayuwata ka  wankeni agurin iyayena kafin ka sawakemin aurenka dake kaina  wallahil azim ina bukatar takardar saki daga gareka ,ka sake ni ka huta rayuwarka nima na huta " .

tunda ta fara magana ya dauke kanshi akanta sai dai  jin maganarta ta karshe   yasa Ya  d'agowa idanunshi  a hankali yayi mata wani    kallon banza sannan  ya  ɗauke kanshi ya cigaba da kallon areef zuciyarsa na masa wani irin tuttukin bakincikin, sosai aunty zee ta tausayawa halin da kisna  take ciki gashi dai a shirye take data sadaukar masa da rayuwarta amman ya kasa fahimtar kisnar  da data yanzu akwai bambamci  "ya Aliyu karka biyewa zuciyarka kayi hakuri dan Allah,  karka biyewa maganar kisna tana cikin ɓacin rai ne , karkayiwa rayuwar aurenku nakasu  alhalin kuna bukatar juna ,ka tsaya ka duba rayuwar ƴaƴansu uwar wani da ɗan wani sai Allah babu wanda zai iya kula dasu Aryan kamar kisna, ka barta a gindin ƴaƴanta da ita kadai suka saba  sannan ina kake tunanin zata  idan ka saketa tunda kasan abinda dady yace mata kayi hakuri dan Allah  ta tarkashe maganar kamar zata yi kuka ...."

d'akin ya dauki shiru na wani  lokaci  sannan sautin muryar kisna ya karade dakin " aunty zee ki daina bashi hakuri dan girman Allah   ki bar shi yayi  duk abinda zuciyarsa  ta yanke masa  akaina  ko dady da mommy sun ki amsata amatsayinsu na iyayena  zan bi duniya ,zan kwashe  yarana mubi duniya  tare dan bazan bar ko daya ba  ya sake d'agowa   a  matukar fusace yana kallonta da jajayen idanunshi da suka canza kala  "da wasu yaran zaki bi duniya  ?  Yayi maganar kamar zai cinye ta "idan zaki bi duniya ki bi duniya  ke kadai kar ma ki tsaya  a iya duniyar  mutane  ki zarce zuwa wata  duniyar  daban i dont fucking care  amman ban da ya'ya na ...." ya karasa maganar a zuciye yana baro inda yake ya iso gabanta ya tsaya suna fuskantar juna "idan kin shirya yawon duniya ki tafi ke kadai karki sake ambato ya'yana a ciki  okay idan ba haka ba zan kasheki da kai kaina ya karashe maganar yana nuna mata yadda zai yi daita ".

  a hassale tace "lokacin dana yi d'awainiyya da cikinsu kana ina "?  ta kai hannuta  qirjinshi tana nuna shi jijiyon wuyanta  na mikewa  sabida tsananin  tashin hankali da jin dacin maganarsa " kana ina  nace ? " kana  ina na  ɗauki tsawon kwanaki    ina nakudarsu  sannan na haifeshi kana ina "? "kasan yadda ake daukar ciki ko kasan yadda ake nakuda bare ka faɗa min magana   akan ya'yana   ka bani amsa tambayarka nake ? ta dinga zuba masa magana tana nuna qirjinsa tare da  turesa tamkar mahaukaciya sabuwar kamu shi kuma yana ja baya ganin kamar ta soma fita haiyacinta  yasa a  zuciye  ya damki kafad'unta ya haɗeta da bango  dakin "shut up kisna !!!! I said shut up or  else I will get you lost on second are you insane ? ya cigaba da  magana cikin zafin rai  "ko kina hauka ne kike ture ni  " ?"Ko  kin  soma shaye shaye ne  ko kuma  tsohon haukan  rashin mutuncinki ne ya motsa "? " alright ai nasan bazaki taba  canzawa ba dan idan kayi shekara dari baka haɗu da mutun ba duk ranar daka haɗu dashi karka tambayi halinsa dan halinsa na nan  bai canza ba , da wannan halin  kike tunani zaki  mallaki zuciyar Aliyu never in history? " Aliyu yafi karfinki yayi miki nisa da.....

"Papa Me yasa kake sa mommy  Kuka  ?  Suka jiyo sautin Muryar aryan yana kuka har da shesheka " kullum kana sa mommy  kuka bana sonka tunda kana sa mommy kuka  daga yau kai ba papa dina  bane, babu ni  babu kai ".ya riko hannun aryan da niyyar rungumeshi yaron ya  fixge  hannunsa ya karasa  jikin kisna  yana goge mata hawaye "stop crying  mommy ,I will  tell Grandma to punish him wasu hawaye suka zobo mata ya sake goge mata ta karasa ta dauki areef  ta saba shi a kafad'anta ta rike  hannun aryan suka bar d'akin ."

  "kaga abinda kake kokarin haddasawa  ko ?" wannan karamin   yaron   da bai san  meye damuwa ba amman yau   saboda ganin uwarsa cikin damu...........
"ya damu ko kuma ana son gurbata min tunanin yaro ya dauka ni din mugu ne "dan girman Allah kayi hakuri ya Aliyu komai ya wuce karka sake tada maganar  nan plz numfashi ya sauke jikinsa yayi  matukar yin sanyi saboda ganin yadda aryan ya nuna reaction dinsa akan kisna    ya juya  ya fita zuwa haraban gidan kanshi kamar zai kama da wuta nasir ya dake zaune ya kalli samir "tashi mu bishi mu shawo kanshi , Samir  ya masa banza ganin haka yasa  nasir ya  mike ya  fita,Aliyu  yana tsaye hannunsa daya dafe da goshinsa  dayan hannunsa  yana cikin aljihunsa nasir  ya karaso   ya rike hannunsa ya nufi lambun gidan  dashi  batare da yace masa uffan ba shima ya bishi a baya har suka shiga ya zaunar dashi ya koma   ya dauko ruwa mai dan sanyi  ya ɓalle murfi ya mika masa "ka sha kaji sanyi a hankali  ya amsa ya  kafa bakinsa a bakin goran bai sauke ba sai daya shanye tasssss  .
Yana  ajiye goron nasir  ya fara magana cikin fushi  ta inda yake shiga bata nan yake fita ba "karka ɗauka ko na shigarwa kisna ne a'a ina fada maka gaskiya ne  a matsayina na d'anuwanka  kuma abokinka saboda  bai dace ba ko wata kayiwa haka  ba kisna ba zan tsaya tsayin  daka naga na faɗa maka gaskiya shima Samir sam bai ji dadin abinda kayi ba   ya  dai  kasa saka  bakinsa ne   bisa wani dalili nashi  ,ko  baka duba darajan kowa ba ka duba Samir mutumin da rayuwarsa ne kawai bazai iya baka ba ,mutumin da kai da kanka ka sha fada min yadda kuka yi rayuwa tare haba muradi ai ko mutuwa tana jin kunyar  idon iyaye ,ya'yan nan fa ƴaƴanta ne bazata so abinda zai cutar dasu ba sannan duk sonka dasu bazaka Kai ta ba, nasir ya dade yana masa magana  jikin Aliyu ya sake yin sanyi sai lokacin ya fara tunanin yanayin da Samir ya shiga a lokacin da yake wa kisna tujara "kenan haushinsa Samir   yaji  ko me  .."? Yayiwa kansa tmbayar yana duban nasir ƙwaƙwalwarsa na sake shiga caji "Idan kuwa haushinsa Samir yaji lallai jini ba karya ba "amman har an zo lokacin da samir zai yi fushi atsakaninsa da kisna ?    sun dade zaune   a lambu  nasir na nusar da Aliyu gaskiya bai dai kula sa ba haka bai ce masa ya hakura ba illa iskan da yake furzarwa .."


Misalin ƙarfe biyar  mommy ta shigo parloun  aunty zee ce da safiyya suna zaune " assalamu alaikum ta furta a hankali tana karasa shigowa gabad'aya suka maida hankalinsu gareta "wa'alaiki salam tare da mikewa suka amshi  laidodi dake  rike a hannunta ta zauna akan kujera "ya Allah ta  furta a hankali ina waɗan sojojin 

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login