Showing 75001 words to 78000 words out of 495987 words
Chapter 26 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
ɓacin rai ne , karkayiwa rayuwar aurenku nakasu alhalin kuna bukatar juna ,ka tsaya ka duba rayuwar ƴaƴansu uwar wani da ɗan wani sai Allah babu wanda zai iya kula dasu Aryan kamar kisna, ka barta a gindin ƴaƴanta da ita kadai suka saba sannan ina kake tunanin zata idan ka saketa tunda kasan abinda dady yace mata kayi hakuri dan Allah ta tarkashe maganar kamar zata yi kuka ...."
d'akin ya dauki shiru na wani lokaci sannan sautin muryar kisna ya karade dakin " aunty zee ki daina bashi hakuri dan girman Allah ki bar shi yayi duk abinda zuciyarsa ta yanke masa akaina ko dady da mommy sun ki amsata amatsayinsu na iyayena zan bi duniya ,zan kwashe yarana mubi duniya tare dan bazan bar ko daya ba ya sake d'agowa a matukar fusace yana kallonta da jajayen idanunshi da suka canza kala "da wasu yaran zaki bi duniya ? Yayi maganar kamar zai cinye ta "idan zaki bi duniya ki bi duniya ke kadai kar ma ki tsaya a iya duniyar mutane ki zarce zuwa wata duniyar daban i dont fucking care amman ban da ya'ya na ...." ya karasa maganar a zuciye yana baro inda yake ya iso gabanta ya tsaya suna fuskantar juna "idan kin shirya yawon duniya ki tafi ke kadai karki sake ambato ya'yana a ciki okay idan ba haka ba zan kasheki da kai kaina ya karashe maganar yana nuna mata yadda zai yi daita ".
a hassale tace "lokacin dana yi d'awainiyya da cikinsu kana ina "? ta kai hannuta qirjinshi tana nuna shi jijiyon wuyanta na mikewa sabida tsananin tashin hankali da jin dacin maganarsa " kana ina nace ? " kana ina na ɗauki tsawon kwanaki ina nakudarsu sannan na haifeshi kana ina "? "kasan yadda ake daukar ciki ko kasan yadda ake nakuda bare ka faɗa min magana akan ya'yana ka bani amsa tambayarka nake ? ta dinga zuba masa magana tana nuna qirjinsa tare da turesa tamkar mahaukaciya sabuwar kamu shi kuma yana ja baya ganin kamar ta soma fita haiyacinta yasa a zuciye ya damki kafad'unta ya haɗeta da bango dakin "shut up kisna !!!! I said shut up or else I will get you lost on second are you insane ? ya cigaba da magana cikin zafin rai "ko kina hauka ne kike ture ni " ?"Ko kin soma shaye shaye ne ko kuma tsohon haukan rashin mutuncinki ne ya motsa "? " alright ai nasan bazaki taba canzawa ba dan idan kayi shekara dari baka haɗu da mutun ba duk ranar daka haɗu dashi karka tambayi halinsa dan halinsa na nan bai canza ba , da wannan halin kike tunani zaki mallaki zuciyar Aliyu never in history? " Aliyu yafi karfinki yayi miki nisa da.....
"Papa Me yasa kake sa mommy Kuka ? Suka jiyo sautin Muryar aryan yana kuka har da shesheka " kullum kana sa mommy kuka bana sonka tunda kana sa mommy kuka daga yau kai ba papa dina bane, babu ni babu kai ".ya riko hannun aryan da niyyar rungumeshi yaron ya fixge hannunsa ya karasa jikin kisna yana goge mata hawaye "stop crying mommy ,I will tell Grandma to punish him wasu hawaye suka zobo mata ya sake goge mata ta karasa ta dauki areef ta saba shi a kafad'anta ta rike hannun aryan suka bar d'akin ."
"kaga abinda kake kokarin haddasawa ko ?" wannan karamin yaron da bai san meye damuwa ba amman yau saboda ganin uwarsa cikin damu...........
"ya damu ko kuma ana son gurbata min tunanin yaro ya dauka ni din mugu ne "dan girman Allah kayi hakuri ya Aliyu komai ya wuce karka sake tada maganar nan plz numfashi ya sauke jikinsa yayi matukar yin sanyi saboda ganin yadda aryan ya nuna reaction dinsa akan kisna ya juya ya fita zuwa haraban gidan kanshi kamar zai kama da wuta nasir ya dake zaune ya kalli samir "tashi mu bishi mu shawo kanshi , Samir ya masa banza ganin haka yasa nasir ya mike ya fita,Aliyu yana tsaye hannunsa daya dafe da goshinsa dayan hannunsa yana cikin aljihunsa nasir ya karaso ya rike hannunsa ya nufi lambun gidan dashi batare da yace masa uffan ba shima ya bishi a baya har suka shiga ya zaunar dashi ya koma ya dauko ruwa mai dan sanyi ya ɓalle murfi ya mika masa "ka sha kaji sanyi a hankali ya amsa ya kafa bakinsa a bakin goran bai sauke ba sai daya shanye tasssss .
Yana ajiye goron nasir ya fara magana cikin fushi ta inda yake shiga bata nan yake fita ba "karka ɗauka ko na shigarwa kisna ne a'a ina fada maka gaskiya ne a matsayina na d'anuwanka kuma abokinka saboda bai dace ba ko wata kayiwa haka ba kisna ba zan tsaya tsayin daka naga na faɗa maka gaskiya shima Samir sam bai ji dadin abinda kayi ba ya dai kasa saka bakinsa ne bisa wani dalili nashi ,ko baka duba darajan kowa ba ka duba Samir mutumin da rayuwarsa ne kawai bazai iya baka ba ,mutumin da kai da kanka ka sha fada min yadda kuka yi rayuwa tare haba muradi ai ko mutuwa tana jin kunyar idon iyaye ,ya'yan nan fa ƴaƴanta ne bazata so abinda zai cutar dasu ba sannan duk sonka dasu bazaka Kai ta ba, nasir ya dade yana masa magana jikin Aliyu ya sake yin sanyi sai lokacin ya fara tunanin yanayin da Samir ya shiga a lokacin da yake wa kisna tujara "kenan haushinsa Samir yaji ko me .."? Yayiwa kansa tmbayar yana duban nasir ƙwaƙwalwarsa na sake shiga caji "Idan kuwa haushinsa Samir yaji lallai jini ba karya ba "amman har an zo lokacin da samir zai yi fushi atsakaninsa da kisna ? sun dade zaune a lambu nasir na nusar da Aliyu gaskiya bai dai kula sa ba haka bai ce masa ya hakura ba illa iskan da yake furzarwa .."
Misalin ƙarfe biyar mommy ta shigo parloun aunty zee ce da safiyya suna zaune " assalamu alaikum ta furta a hankali tana karasa shigowa gabad'aya suka maida hankalinsu gareta "wa'alaiki salam tare da mikewa suka amshi laidodi dake rike a hannunta ta zauna akan kujera "ya Allah ta furta a hankali ina waɗan sojojin suke ban ji motsinsu ba"?
Safiyya da aunty zee suka kalli juna sannan aunty zee tace "suna sama tare da mammansu bari na kawo miki ruwa ki sha sai naje na dauko miki su ta karasa maganar tana shiga Kitchen bayan kamar second biyar ta fito hannuta rike da jug da glass cup ta tsiyaya ruwa ta mika mata ta ajiye sauran a saman table sannan ta juya ta hau sama mommy ta kalli safiyya "ina nasir ko suna bangaren Samir ne ko suna lambu "?
"Eh suna lambu "ta bata amsa da haka suna zaune aunty Zee ta dawo "mumy bacci suke daga su har mammansu ta fadi haka ne dan kar mommy ta d'ago komai "bacci a daidai wannan lokacin ki koma ki tasota ga waya nan na siyo mata ta bude ladar data shigo dashi ta mikawa aunty zee wayar "gashi nan ki tasheta ki bata "kai mommy gaskiya ta gode kisna zata dawo online kenan ? "Gaskiya wayar tayi kyau sosai " dubu ɗari biyar kenan a kudinmu na nigeria zaro ido aunty zee tayi "haka waya yake da tsada anan ?"sosai kuwa ai wayoyi sunfi sauki a Nigeria nan dai aunty zee ta dinga jan mumy da hira daga karshe nasir ya kira safiyya a waya tayi musu sallama ta wuce aunty zeey ta shiga Kitchen domin daura abincin dare .."
Haka nan jikin mommy ya dinga bata akwai abinda ya faru a gidan da bata nan dan har kusan takwas din dare bata ga yaran ba haka bata ga kisna ba hankalinta yaki kwanciya gashi ita ta kalli abincin da aunty zee ta kawo mata bata jin zata iya sanyawa cikin komai batare da ta daura idanunta akan jikokinta mafi soyuwa acikin ranta ba ,ta mike ta sanya silifas ta fito daga d'akin ta karasa bakin kofar dakinsu har zata tura sai tayi tunanin watakilla Aliyu yana ciki tayi knowking tare da sallama ......"
Aliyu ne ya taso sanye da jallabiya dan maroko kalar dark blue jallabiyar tayi masa kyau sosai abunka ga fari sol ya bude kofar ganin mommy tsaye ya sha jinin jikinsa sai dai yayi kokarin sanyawa jikinsa jarunta cike da girmamawa yace "barka da dare mommy , kina bukatar wani abu ne "?Girgiza masa kai tayi kana tace "yaran nan nazo dubawa tunda na dawo daga kasuwa ban sanya idanuna akansu ba daga su har uwarsu shiru yayi dan shi kansa baya son mommy tasan abinda ya faru ,idan ya hanata ganinsu zata fahimci wani abu idan ya barta ta ga hannun areef hankalinta zai iya tashi fiyye dana yanzu duk da bawani ciwo bane ,hannu dai yayi sanyi ne saboda shock din daya samu , matsawa yayi gefe ya bata hanya ta shigo d'akin akan gado ta hago su kwance lullu'be cikin bargo kisna na zaune a gefensu jingine da gado ta tafka tagumi tana ganin mommy ta sauko tana wayancewa ",mommy kiyi hakuri kin jini shiru ko wallahi tunda kika fita kaina ke ciwo shine na kwanta har yanzu ma ban daina jin ciwon kan ba momy ta zuba mata ido tana nazarinta sannan ta karasa gurin yaran ta shafa kansu tayi kasa da hannuwanta zuwa kirjinsu taji numfashinsu na sauka yadda ya kamata ta rankwafo ta sunbuci goshinsu ta dawo ga kisna "kiyi kokari kiga likita kada ki tsaya gida shan magani a tare kisna da Aliyu suka d'ago suka kalli juna qirjinsu na mahaukacin bugawa da wani sauri mommy kuwa tana gama magana tayi musu sai da safe ta fita Aliyu ya kulle kofar ya hau saman katifa ya yi rigingine rungume da hannuwansa duka a qirji yana tunanin maganar mumy da alamun ta dauka ko ciki ke ga kisna ..?
Har kusan dayan dare kisna bata runtsa ba tana kwance kusa da ya'yanta shima ba runtsawa yayi ba tunani ne ya sha kanshi ta kai hannu ta janyo laidar da aunty zee ta shigo mata dashi d'azu tana dubawa wasu zafafan hawaye ne suka zo mata "uwa kenan "hakika duk wanda ya rasa uwa yayi kuka tasan ta siya mata wayar ne a matsayinta na yarta da kuma kwantar mata da hankali dan ta zauna da Aliyu gashi wanda ake wa dan shi yaki kwantar da kai su zauna lafiya ta mike dan saka wayar a caji motsin laidar ya tadda areef ya Mike zaune Aliyu yayi saurin kamoshi jikinsa ya rungume shi "zaka ci abinci ne?Yaron ya girgiza masa kai yana cewa ",papa tea "
da sauri ya sauko yana ƙoƙarin fita kisna ta rigashi fita dole ya dawo ya zauna rike dashi bata dade ba ta dawo hannunta rike da cup din tea ta amshesa a hannun Aliyu ta soma bashi can shima Aryan ya farka ta dauko shi ta bashi sauran tea din da areef ya sha ta kwantar dashi ta shiga bayi dan bata jin zata iya runtsawa ta d'auro alwala ta fito wanda zuwa lokacin ya kwantar da areef a kusa da aryan sai dai idanunsu biyu yana lallabasu dan su koma bacci .."
Tana zaune byn ta idar da sallah ta fashe da kuka yaranta dake kwance suka sauko a gigice suka karaso gareta suka rungumeta kuka take suma suna kuka kamar ana zarar ransu kuka yaran suke sosai saboda ganin halin da take ciki gashi dai basu da cikakken wayon da zasu ce ga dalilin kukanta sai dai suna jin zafin halin kunci da mahaifiyarsu take ciki a hankali ta rungumesu ajikinta tana ci-gaba da kuka "Allah kasa papa ya daina saka mommy kuka kasa ya bata farinciki , ki daina kuka kinji mommy duk aryan yake magana shi areef ganin mamansa da d'an'uwansa na kuka ne yasashi kuka "na gode d'ana na daina kuka kaji babana Allah yayi muku albarka na gode muku ,kuma na godewa Allah daya azurtani da samu ya'ya irinku masu tausayi Allah yayi muku albarka ta karasa maganar tana shafa kansu ....."
Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Free page 13
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰
Muryarta a dake tace "bawan Allah kayi hakuri ni din matar aure ce fa" wani irin kallon raunin wayo yayi mata sannan ya gyara tsayuwarsa tare da zube hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa yana wata irin dariya har ya neman d'aga murya , cike da matsanancin tsoro ta matsa baya da sauri haɗe da rike hannun d'anta gam dan ba karamin tsoro ya bata ba , a zahiri ake iya hango tsananin tashin hankalinta waige waige ta soma yi tana neman hanyar guduwa ciki zolaya yace "dakata ! dakata!! mana Karki gudu dan duk inda kika shiga a kasar nan wallahi sai na zakuloki matsawar kina cikin garin nan na mallakawa zuciyata ke ".Yayi maganar hankalinsa kwance yana nuna ta da ɗan yatsansa yayinda idanunshi ke tsaye kyam akanta yana mata wani irin kallo yana cigaba da dariyar da yake dan shi karya ya dauki maganarta ...
"a matukar tsoroce ta dubeshi kamar zatayi kuka tace "dan Allah malam ka daina kallona haka wallahil azim ni matar aure ce har ma da yara biyu ..." ta karasa maganar idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye .
Cak dariyar dake kwance akan fuskarshi ta 'bace zuwa mummunar ɓacin rai sannan yayi shiru yana kare mata kallo sama da kasa zuciyarsa na wani irin tsalle da bugawa , sam bazakace matar aure bace komai na jikinta irin na yammata ne hatta shigar jikinta yammata dayawa suna yi irinta yayi maganar acikin ranshi "oh my goodness ya furta a fili yana dafe goshinsa ,"amman ko waye wannan mutumin daya aureki ya cuceni ya cuci rayuwata ya gama dani kalar matar dana dade ina nema na aura wayyo Allah naga samu naga rashi tawa ta sameni a fili yayi maganar yana Kallonta da narkakkun idanunshi , hankalin kisna ya sake tashi ita ba maganarsa tafi daga mata hankali ba zuwan ahlinta tafi jin tsoro dube dube ta soma tana addur kar Allah ya kawo Aliyu ko ya samir guri, numfashi ta sauke saboda babu alamunsu hatta su anty zee bata ga kyallinsu a gurin ba dan haka ta sanyawa jikinta natsuwa tare da gyara tsayuwar ta ,bangaren Aliyu kuwa gabad'aya ya manta da wata halitta kisna suka zo tsabgar gabansa kawai yake yana gwadawa areef takalma , duk wanda ya daukar masa sai ya d'aukarwa aryan .."
Mutumin ya lumshe idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa akan jin abinda ta faɗa masa yanzu ,cikin murya mai cike da kasala ya cigaba da fadin "gaskiya gaskiya wanda ya aureki ya kassara min rayuwa , ina ji ajikina koma waye ya aureki baya sonki sai dai kasancewar mata nada raunin zuciya zaki iya son shi dan baku san mutanen da suka dace da rayuwarku ba ..."bata san sanda dariyar maganarsa ta subuce mata ba tayi murumushi tana toshe bakinta da hannuta, aryan ya d'ago kanshi ya kalleta ya sake maida idanunsa akan mutumin dake tsaye ,"kin san wani abu"?ya tambayeta yana tsareta da idanunsa ,taki cewa komai saboda qirjinta dake bugawa da sauri "idan ace ni na aureki bazan Iya barin ki fita ko'ina batare dani ba, irin kulawa da soyayyar da zan baki sai kin ce na rage yayi yawa zan lalla'ba....." saurin katseshi tayi ta hanyar fadin "dan Allah ka wuce tare da mijina muke fa idan ya gamu komai zai iya faru ".ya zaro ido waje cike da mamaki "shine ya barki haka gaskiya hasashena ya tabbatar gaskiya, wallahi baya sonki "hasashenka bai tabbata gaskiya ba ni dai dan Allah ka rufa min asiri ka bar bibiyata hakan zai iya haifar min da babban matsala da mijina wanda bazan so faruwar haka ba ".
"shikenan ya zanyi da rayuwata zanyi duk yadda kuke so sannan zanyi addu'ar Allah ya kawo tsautsayin da mijinki zai sakar min ke na aureki cikin kankanin lokaci dan bana son a dauki lokaci batare dana mallake ki ba yayi maganar tare da mika mata badir din kudin kasar "ga wannan ki sha ice cream ke da boy taki amsa tace " bana bukatar haka daga gareka , sannan ba Ameen ba akan addur da kayi yanzu saboda ina tsananin son mijina duk runtsi bazan so rabuwa dashi ba .."
Tabe baki yayi kawai yana Kallonta sannan ya mika wa aryan hannu alamun yazo gareshi aryan yayi saurin makale kafad'a ,"har yanzu jikina yana bani baki da aure sai dai musamman zan sa a binciko min komai naki ina tabbatar miki nan da wani lokaci zan san komai akanki ya kamo hannun aryan da dabara ya daga shi sama yana masa wasa "ya sunanka boy "? Aryan daya jishi a sama yana yawo daman abinda yake so kenan ya wangale masa baki yana cewa "aryan ..." "Wooooowwww nice name " aryan kace