Showing 249001 words to 252000 words out of 495987 words

Chapter 84 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

dani duk kin dameni kamar ba dake aka kulla min munafurci ba ,wai ma ina ruwanki da rayuwata ne da kike son samir na taba cewa karki so shi ?"Samir dabam musa dabam, idan irin Samir kike so babu wanda zai hanaki aurensa ke musan ma da natsatsen ne koda yake yoroba za'a iya barin ki aure shi tunda muslimi ne , gashi ance shaye shaye yake kuma har yanzu maman shi tace kudin abinci take bashi ,da me zai kula dake idan kin aureshi "babu ruwanki da abinda zai kula dani ko kasa zai bani ina son shi haka kuma karki sake tsoma bakinki cikin maganata idan ba haka ba zamu samu babbar matsala ,kiyi harkarki nayi tawa babu dole ta soma taku tana dingisa kafa tare da rike kugu ta shige bayi tana jan tsaki ,zainba tayi sororo tana bita da kallo "lallai kisna tayi nisa a son musa .." a parlou'n ma kowa maganar suke tayi kafin daga baya kowa ya kama gabansa, yayinda muradi ya kudurta a ransa gobe zai sa ayiwa musa dukan mutuwa sai dai take wani bangaren na zuciyarsa ya kwabesa akan hukuncinsa da zai ɗauka dan komai zai iya kwabewa gara ya nemi hanyar kuburta da kisna daga sharrinsa akan ya dauki matakin dukan yaron dan dukan da zai sa a masa zai iya tashesa aiki yana kwance rungume da hannuwansa a qirji gaba-daya ya nemi bacci ya rasa sosai yayi zurfi cikin tunanin rayuwa .." hakan yaji dumin hawaye na gangaro masa kawai ya rushe da wani irin kuka don a ganinsa shine abinda ya kamacesa , tunani yake yana son newa kisna mafuta bazai iya barin musa ya cigaba da cutar da rayuwarta a karon banza ba Allah Sarki mumy tana da kokari sosai akan tarbiyar yara ya'yan da ba nata ba ma tayi rawar gani akansu ,mufeeda Zahra afra aunty ummi duk a gidan suka yi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali sai ita kadai data rage mata a rayuwa kuma diyar data fi kauna a duk fadin duniya duk abinda mumy zata so dole shima ya jajurce akanshi duk da yasan ta tsaneshi tsana mafi girma amman bazai taba barin rayuwarta ta muzanta ba zai yi duk abinda zai yi akan ta dawo natsuwarta a hankali ya mike ya fice daga dakin Samir dake lura dashi ya bishi da kallo batare daya ce masa uffan ba dan kamar an kulle masa baki illa dai shatatar hawaye da yake ilahirin zuciyarsa na kunna tunda muradi yake juyi yana kuka shima ya rasa natsuwarsa yasan tunda ya zubar da hawaye akan lamarin yana cikin tsananin bakinciki halin da kisna take ciki kai tsaye dakinsu kisna ya nufa wanda rabon da da shiga dakin ya jima sosai tun tasowarta yayi sallama ya sameta ta baje a kan katifa tana juyi rike da gefen kugunta dake mata ciwo tana ganinsa ta zuba masa idanuwa batare data amsa sallamar da yayi ba har sanda yayiwa kanshi gurin zama a gefenta idanunsa sunyi jazur tamkar garwashin wuta saboda kukan da yayi a kallon da yake mata ya ɗan fahimci jikinta yayi sanyi dan babu alamun hayaniya a tattare daita muryarsa a tsarke yace "ina don zamuyi magana dake ".ta yunkura ta mike zaune tana masa kallon sama da kasa fuska a bace sannan ta kalli inda zee ke kwance sannan ta dawo da dubanta ga muradi yace murya a sanyaye "ki faɗa min me kike so anan duniya ni Aliyu na dauki alkawarin zan miki shi dan ki rabu da yaron nan iyayenmu su samu kwanciyar hankali ?yatsina fuska tayi saboda jin abinda yace sannan ta juya zatayi kwanciyarta yayi saurin riko tafin hannunta batare daya shirya wa hakan ba ta tsira masa ido kawai shima kallonta yake gabansa na faduwa "ki faɗa min wallahi zan miki dan kwanciyar hankalinki dana mu ","babu abinda za'a min daya wuce abarni nayi rayuwa da Musa"Musa da kike gani ba mutumin arziki ba sannan ba masoyi bane wallahi daya yana da nagarta da zaki yi rayuwar jin dadi dashi as age dinki zan yarda kuyi aure "Ni ka sakar min hannu kuma ka fice daga dakin wallahi ni shi kawai za'a bani nayi farinciki ta sanya hannu ta goge hawayen da suka samu nasarar zubowa daga kwarnin idanunta ",me zakiyi da wannan yaron zan sake nusar dake ba aure ba hatta tarrayarki dashi ma guba ne "ni ka daina fada min haka idan zama da kai a gurin daya bai zama guba ba ta yaya tarrayata da Musa zai zama guba? muradi ya zuba mata rinannnun idanunsa wadan da suke cike da bakincikin jin furucinta ransa yayi mugu mugun ɓaci har zai sake cewa wani abu sai kuma ya fasa ganin bazata fahimcesa ba ya mike jikinsa a sake ya fice ta bishi da kallo ta ja tsaki "mahaukacin banza kawai da wofi me kake dashi da maye min gurbin Musa a rayuwata kai din ma da mahaifina ne ya taimaki rayuwarka ya yantoka daga shingi bazan har yanzu baka da abinda zaka bani nayi farinciki " .

Gabad'aya kan dady ya kulle zaune kawai yake a bakin gado yana tunani sai dai ya rasa mafuta ɗauka akan musa duk inda aka je aka dawo shi za'a bari aciki matsala saboda shi ke da diya mace , ji yake tamkar zai mutu dan wani irin zafi zuciyarsa ke masa yayinda kansa ke mugun sarawa "mai ya kamata yayi domin kubutar da rayuwar 'yarsa ? A hankali ya mike tsaye ya soma sintiri a dakin kwakwaluwarsa na tunani bangaren mumy kusan tana cikin irin halin da dady yake ciki sai dai ita ta d'auro alwala tana kan dadduma tana kaiwa Allah kukanta tana jin radadi rayuwar da kisna ta daukarwa kanta mumy ta fashe da wani irin kuka mai kona zuciya tare da daga hannuwansa da hawaye shabe shabe da muryar kuka tana cewa "ya Ubangiji kana jinmu kana ganinmu da ikonka muka samu kanmu a cikin wannan halin da muke ciki kaine mai tsarawa bawa rayuwa cikin iliminka , mun san kai ka qaddaro mana wannan jarabawa ba don baka son mu ba sai dan ka jarabi immaninmu ina rokonka Ubangijin a'arshi mai girma ka saisauta mana ka hadamu da abinda zamu iya ka kawo mana sauki cikin lamurramu ka duba rayuwar kisna ka yanke mata wahala ka bamu hakurin da rashin jin maganarta ,kasa taji maganarmu albarkacin fiyyayen halitta
har zuwa washegari dady bai san abinda ya kamata yayi ba ,bayan yayi wanka ya kintsa ya kira d'an'uwansa Alhaji marwan sun dade a cikin turakarsa suna tautaunawa akan matsalar kisna kafin daga baya Alhaji marwan yace zai fad'awa malam sharu domin ya tayasu da addu'a tare da yi musu farraku sannan a hada mata da rubutu dangana tana sha da wannan shawarar suka rabu ."

Bangare afra itama tana cikin damuwa fiyye da kisna dan har damuwa tasa tayi miscarege ta suma batasani ba a dalilin ciwon cikin daya turnuketa bata tashi sanin inda take ba sai data kwana ta yini a asibitin mijinta sannan ta farfado ta ganta akan gadon asibiti ta rasa babynta tayi kukan bakinciki duk da bata son ya badamasi amman taji zafi da radadin zubewar cikin da batasan dashi ba ,tunda ta farfado tasan abinda ya faru babu abinda take sai kuka da bakinciki halin data tsinci kanta da tunanin halin da zata bi ta kubutar da zuciyarta dan bayan damuwar da tashin hankali da take ciki na halin da kisna take ciki har da bakinciki kamuwa da son muradi ya haifar mata da komai gaba-daya ta rasa me yake mata dadi a duk fadin duniya bata son ya badamasi sai muradi shi kuma anan duniya babu halittar daya tsana sama daita dan ko bude Idanunshi bai so ya ganta ta juya ta kalli bangon dakin hawaye na bin kuncinta kullum cikin nadama da danasanin abinda tayi masa take a wannan karon zata yi yunkurin yin addu'ar domin neman sausauti agurin Allah dan yadda take jin zuciyarta zata iya komai akan ta mallaki muradi sosai dangi sukayi bakinciki rasa cikin afra har kuka sai da ya badamasi yayi sai da mumy tayi ta rarrashinsa .."

Alhaji marwan ne ya dauki nauyi komai kuma shi ke amso rubutun ya kawo wa kisna ,sanin da mumy tayi idan ta barta ta sha rubutun bazata sha ba zata iya zubarwa yasa take tsareta "ki sha da niyyar rabuwa da wannan yaron kinji mamana Allah yaye miki wannan maseefar dan Allah ki tausaya min ki hakura dashi ni mahaifiyarki ce zan dange da miki addu'a idan ma wani abu sukai miki Allah ya karya alkadarinsu , ina umartanki kibi umarnina ki gaugauta ciresa a ranki idan kika min haka wallahi duniya zata miki dadi saboda banason ki da yaron nan ,wallahi banci kisa a haramu ne a muslinci to da zai iya kashe yaron nan saboda yana dagula min lisafi , ki duba kiga yadda yayi sanadiyar da kika ruguza karatunki tun daga js 1 har zuwa 3 baki tsaya kin yi karatun kirki ba yanzu wannan masoyi ne .....?
Duk maganar da mumy take jinta kawai kisna take yi aranta kuwa cewa tayi " duk abinda zaku bani bazai yi tasirin da zai rabani da soyayyar musa ba son musa a jinina yake kuma bazan iya rabuwa dashi ba muna tare Muddin rai .."

Mmm Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
  CUTAR DA KAI
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 37
~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.



.....Tun da kisna ta fado aunty  ummi   da zahra basu zo gidan  ba sai yau  mufeeda ce tazo tun kwana biyu da faruwar abun ,koda aunty ummi ta  ga kisna bata mata faɗa  ba kamar yadda ta saba saboda Aliyu yaje har gidan yayi mata magana dan ya samu labarin akan fadan datayi mata kwanaki yasa ta gudu ta bar gida   ,suna zaune gabadayansu a falo suna hira  aunty ummi ta kalli mumy  tace  "mumy surukarki tace a gausheki  fa ."wacece Kenan  kuma wa take so a cikin ya'yana ? "Muradi   mana wallahi  autar sa'adatu ta mato  sosai akanshi gashi ko yaje gidan baya mata kallon arziki , Aliyu na jinta yayi bala'in haɗe rai tare da runtse idanunshi yana shafa goshinsa ..'

Mumy tayi murmushi irin nasu na manya sannan tace "Allah sarki Sa'adatu shi yasa dai idan ta ganni take  jin kunyata a she d'ana ake so  "wallahi  shi take maseefar so kullum tana bangarena tana son taji ana maganarsa duk ranar da zai buga kwallo kuwa bata da natsuwa da kwanciyar hankali ,haka zakiga ta kasa tsaye ta kasa zaune har sai taga ya lashe  idan kinga   yadda take min sai abun ya baki mamaki , ta kalleshi ya wani haɗe rai kamar ana hirar mugun abu tunda  baka zama surukina ba ai sai ka zama  surukin Abban fadel  dan gaskiya yarinyar tayi  idan ka aureta  zaka ji dadin rayuwa daita yarinya ce wacce zaka yi control  d'inta yadda kake so gashi  bata da damuwa zahra tace "duk a nawa kike wannan campaign din ?  samir yayi murmushi " da dai kin bata hakuri   dan zuciyar wannan  babu komai acikinta sai buga wasa da mamansa yayi karasa maganar yana nuna mumy , " idan  Kinga  yadda mata ke  rikicewa  akanshi sai kin sha  mamaki  ,idan yana waje fa mu mata ne ,dan mata basa kallonmu a matsayin maza sai dai  babu wace zakiji yace tayi masa ko ta burgeshi sai dai kullum cikin jin tausayin mata masu kawo kansu gareshi yake , sam sam daga matan turawa har namu na hausa  basa  gabansa  ,in gaya miki goshin  zamu dawo  daga england wata yarinya yar kasar coria  ta Sha  mari a gurinsa akan ta rungumeshi   saboda taji dadin wasan da yayi  bata san  wannan miskililin  ba'a yi masa  gwaninta ta wannan bangaren ba   wallahi bazan iya lissafa miki adadin matan da suka sha mari akan shishige masa da suke yi ba ya karasa  maganar yana kwashewa da  wata dariya  "ki fadawa kanwar mijinki banda shishigi dan naga yadda take rawar jiki shekaranjiya da mukaje dan ta sha mari  agurinsa ba wani abu bane ".
duk suka kwashe da dariya banda  aunty ummi data ji  haushin Samir shi da zai taya ta shawo kanshi shine zai buge da bata banzar labari ,muradi yaja  tsaki tare da mikewa ya fita daga  falon  "kin gani ba wai a zuwan an   dameshi da zance mata ,irinsu ne kuma basu iya soyayya ba idan suka tashi yi duk rude suke kaji suna baby suna marairaicewa Samir ya karasa maganar yana sake kwashewa  da  dariya.. "

Aunty ummi ta barsu sai da suka saida dariyarsu shi da zahra sannan  ta dubi mumy tace "mumy ki bincika anya  aljanar dare bata auri muradinki ba  kuwa duk macen data nuna tana son shi sai yace a'a ko yabawa akayi dashi ba'a burgeshi ...?
  Murmushi mumy tayi "bashi da wata aljana kawai dai lokaci ne bai yi ba idan lokacin yayi da kanshi zai kawo matarsa ,haka fa haroon mahaifinsa yake da farinjini yammata sai dai mace bata daura idanunta akanshi ba sai ta rud'e gashi daman komai nashi ya dauko babu abinda ya bari hatta tafiyarsa irinta ubansa ne"Allah sarki gaskiya mai tsanani kyau ne muddin shi Aliyu ya dauko inji cewar zahra "komai fa yadda kika ga muradi haka yake dan shi sadiq hajiya kayi tace kalar fatar uwarsu ya dauko mumy ta karasa maganar tana numfasawa tare da shiga tunanin d'anuwanta aunty ta kalli mumy tace " kuna waya kuwa dashi dan kwanaki naji kince kunyi waya "gaskiya tun daga wannan lokacin daya fahimci nice bai sake daga kirana ba daga karshe ma na daina samunsa ina matukar qaunar dan'uwana a kusa dani kowa na cikin gatanshi ban da shi kullum cikin addu'a nake Allah ya karkato da hankalinsa zuwa gida ta karasa maganar kamar zatayi kuma "ameen suka amsa dashi   daga  hirar  mahaifin Aliyu hirar kisna  suka dawo sun jima suna hira daga karshe aunty ummi tace a bata kisna ta tafi daita gidanta  tayi mata kwana biyu ,mumy tace "a'a anan ma da muke kulawa daita ba'a tsira ina ga gidanki  da kowa shiga bangarenki yake no excuse , har ta fita baki sani ba gara dai nan din   sai gurin  yamma aunty ummi da zahra suka bar  gidan kullum daren duniya daga mumy har dady basa bacci suna tsaye bisa kafafunsu domin kaiwa Allah kukansu , dady ne ya riga mumy sallamewa yayi lazimi sannan ya daga hannuwansa duka sama cikin kaskantar da kai a gurin ubangijinsa "ya Allah ka shirya min sakina ka sanyawa zuciyarta natsuwa Allah ka sani ban taba aikata zina a rayuwata ba Allah ka tsare min farjinta kada ka bawa wani bawa damar keta mata haddi Allah na yarda da qaddara mai kyau da akasinta na dauki wannan jarabawar a matsayin kaddarata Allah ka bamu ikon cinyeta ka shirya yara masu irin halinta shiri na addinin musulunci kasanyawa mahaifiyarta hakuri da juriya haka yayita addu'a har kusan asuba .."

Tsawon wata biyu kenan shiru Kisna ba'a je ko'ina  ba, ta ɗan  kwantar da  hankalinta   dan haka natsuwa taxo mata  ,ta ƙara kyau ta murmure ba kamar lukutan baya ba sai dai zuciyar na gurin musa haka shima bangarensa yana matukar son ya sanyata a idonshi ya sha zuwa unguwar sai dai tsoro na hanashi tunkarar gidan  

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login