Showing 282001 words to 285000 words out of 495987 words

Chapter 95 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

kana mai yakinin ubangijinmu na jinka kuma bazai wofitar da lamarinka ba kayi hakuri babana da sannu Allah zai bawa kisna miji wanda yafi abubakar nazir da taufik  ina son ganinka kamar da , hakan zai mana dadi tun daga lokacin da abubuwan suke ta faruwa bana bacci dady kullum cikin addu'a nake yiwa kisna a duk sallarta Allah ya zama gatanmu ya yaye mata gabad'aya ya karasa maganar yana mai daura kanshi akan cinyar dady yana siyayar hawaye tunda ya fara magana dady ya tsura masa ido cikin matukar yabawa harshensa da dogon tunani da jinjina fikirarsa  ya iya tsara lafazi mai sanyi da kwantar da hankali bawa ko shakka babu maganganunsa sun shigesa sun zauna masa a inda bazasu goge ba domin duka gaskiya ya fada masa dan haka yaja doguwar ajiyar zuciya har da murmushi sannan ya ajiye cup din hannusa da yake ta faman juyawa  ya daura akan sumar muradi tare da tsura masa ido "hakika dana ina alfahari da samunka a matsayin dana na godewa Allah kaima na gode maka kuma inshallahu zanyi iyakar kokarina na manta komai  zanyi amfani da duk abinda ka fada min  na gode Allah yayi maka albarka cikin murna da jin dadi muradi ya goge hawayensa ya d'ago yace "amen dady .." Shiru sukayi dady na kallonsa yana jin tamkar ya nemi alfarma auren kisna agurinsa sai dai yasan da wuya mumy ta yarda tunda ta nuna masa a fuskarta da kalaman bakinta bazata yarda ba yaje ya nema cikin danginsa ya bawa "ya'akayi dady akwai abinda kake son cewa?
"uhmmmm kawai ina neman wanda zan bawa auren kisna ne sam zuciyata tafi bukatar na aurar daita kaje kayi tunanin wanda za'a bawa ita ko acikin abokanka wanda ya yarda ka sanar min"no dady zan dai yi tunanin mafuta "shinkenan sai naji daga gareka ya mike ya fita ya bar dady zaune yana tunanin rayuwa daren sam muradi ya kasa bacci sai juyi yake yana tunanin hanyar da zai kawowa dady sauki acikin lamarinsa har gari ya waye bai samu mafuta ba dan haka ya shirya ya tafi gidan aunty ummi a gajiye ya shigo falonta  yana shigowa ya zube a  kan kujera  ya cire hullar dake kanshi ya ajiye a gefensa ya daura hannunsa a daidai mararsa yana shafawa a hankali yana furzar da iska   kusan minti goma yana  rigingine a zaune  sannan ya zaro wayarsa a daidai lokacin aunty ummi ta fito tana tari tana cewa "a'a muradi ne da safiyar nan ? " Ni ne lafiya meke damunki ?"wallahi mura ce gata nan ta min mugun kamu ya gida yasu mumy da dady  ?"qalau qalau kowa yake "ya wannan mara jin maganar ?"saboda ita ma nazo dady yace na bincika ko cikin abokaina idan da mai son aurenta ,ni wallahi kunya nake ji kamar tallarta fa za'a yi ? "To me za'a yi da wuce haka ka tallata musu ita kawai mai son arha ta kwasa take ya hade rai "ke da nazo neman shawara gurinki shine zaki bata min rai "to me zance ni bari na kira maka auta ku gaisa "karki soma wallahi dan ko kallon arziki bazata samu ba "yarinyar nan fa tana bala'in sonka yana jinta yayi mata banza tamkar bai ji abinda tace ba "kana jina fa ina magana ? "Uhm me kika ce ?"nace auta na bala'in shekaranjiya wasu yan'uwansu hajiyarsu suka zo su biyu suna nan masu kama da juna wai daya  yana sonta sun zo kasan me tace yayi mata banza tasan yana jinta dan haka ta cigaba "wai ce musu tayi ita tana da miji wai har da cewa idan wanda zata aura ya kamasu sai sun gane basu da wayo nayi nayi ta kulasa tace sam wallahi tallahi bazata kulasa ba ita aliyu take so na fada maka babu wanda zai sace zuciyarta   ita kai take so karta kara ganin kafarsu a gidan nan.

"  shegiyar yarinyar bata da kunya ta iya fada miki wai ni take so "yayi maganar yana jan tsaki "ikon Allah me tayi daga tace tana sonka sai zagi "me zan ce da ma ta kama kanta dan babu abinda zanyi da wata soyayya yanzu ban tashi aure ba bazan bata wa yar kowa time ba idan na tashi aure zan duba daidai da rayuwata daga yau ki bata shawara ta dinga kula masu sonta Aliyu bashi da lokacin aure a sheakaru uku masu zuwa "amman tana sonka "to ni bana sonta "to to shinkenan maida wukar sai dai bazan iya fada mata ba da kaina taje ta hadiye zuciya ta mutu "kinga muyi abinda ya kawoni sun dade suna neman mafuta a karshe dai yace zai ma kisna registration ta rubuta weac kafin a san abun yi sannan suka ci-gaba da tautaunawa kafin daga bisani sukai sallama kofa yaje gida ya fadawa dady shawararsa kin yarda yayi da kyar ya shawo kansa ya amince .."

****

Bayan wata biyar a hankali kisna ta bude  murfin bayan  mota  ta fito sanye da uniform din takuwa international school   dake ogba tana taku cikin sanyi jiki bata tsaya jiran muradi daya rakata ba ta wuce sai babban falon gidansu sannan ta tsaya a tsakiyar parlour'n kasancewar ganin dady da wani bako ta duka har kasa ta gaishe da bakon da bata san ko waye ba ya fadada murmushi akan fuskarshi yana fadar "zo nan sakina mu gaisa a she haka kika girma ?"
Ta karasa gaban mutumin sosai tana murmushi ya shafa kanta tare da cewa "kun gama exam lafiya ?"
"Lafiya  "ta bashi amsa "da kyau may God help you yanzu in result ya fito me zaki karanta ? "a'a aure zan mata inda ka ganta din nan bazan bari ta kara gaba ba masu natsuwa   da hankali wadan da basu dameni ba ban bari sun kara gaba ba sai wannan ina ai ma nayi kokarin barinta rubuta weac shim wallahi darajan Aliyu taci if not haka zata kare rayuwarta "kisna  ta haɗe rai jin abinda dady yace sannan tace "to ni  karatu zanyi" "mutumin ya riko hannuta"me zaki karanta ?" banker   nake so na karanta ya gyada ", that's gud my daughter Kinga sai mu tafi London dake kiyi karatunki a can tayi tsalle ta fada jikin dady tace "dan Allah dady ka yarda Allah  da gaske zanje zan tsaya nayi  karatu "murmushi dady yayi yace" a'a aure zan miki ga duk wanda ya yarda zai aureke nan take ta bata rai "sadaka zakayi dani kenan"? tayi maganar kamar zatayi kuka "itace tafi dacewa dake ai".
"a'a dady tafi ƙarfin sadaka wannan da kake gani nan gaba sai ta dinga firgita maza uncle bash ka shirya tafiya daita inji cewar muradi daya shigo a lokacin ya karaso kusa dady da uncle bash ya durkusa har kasa ya gaishesu sannan ya samu guri ya zauna kisna ko kallon inda yake batayi ba illa jin haushin abinda yace dan ta sam bata son shi ya fiyye shishigi "bari naje na cire uniform madadin ta wuce sai ta duka gaban uncle bashi "dan Allah karka fasa zuwa dani yayi dariya "inshallahu zan tafi dake Allah yasa result dinki yayi kyau "ameen ta  fada tare da mikewa ta nufi hanyar dakinsu toilet ta fada ta watsa ruwa ta fito ta tsaya gaban madubi tana tsane jikinta da towel .."

Alhaji realwan ya kalli abokinsa Alhaji bashir yace "yau dai kaga yar albarka diyarka mai jin magana gata nan muna ta fama daita yau lafiya gobe akasin haka abun dai sai addu'a "sakina auta amman duk shirmen yan fari aka bata but har da shagwaba seriously ina son ka bani ita tayi karatun digiri dinta agurina ko babu komai za'a samu saukin al'amura idan bata nan komai zai daidaita da izinin Allah "ban son tafiyarta saboda bana iya nesa da ya'yana amman damuwar kisna tayi yawa kullum sai ta saka uwarta kuka  har yanzu salaha tana cikin damuwa da kuka gaba-daya bata haiyacinta akan kisna watakila barin kisna kasar nan zai kwantar da hankalinta bugu da kari muradi ya dade yana wannan tunanin akanta Alhaji Bashir ya dafa kafadan dady "kayi hakuri kowa da yadda kuruciyarsa take wata rana zakayi mamakinta "Allah yasa a tare suka amsa da muradi wanda ya mike "dady kasa a ranka karshen wahalarmu yazo da zarar ta kara girma zata san ciwon kanta wani abun idan an tuna mata sai taji haushi ya karasa maganar yana tafiya dady ya bisa da kallo har ya daina ganinsa"kaga yaron nan hankalina yafi kwantawa dashi nafi son na bashi auren kisna akan wani sai dai ina jin tsoron halinta kartazo ta dagula masa lissafi abinda bazan lamunta ba kenan a taba min Aliyu  ina raye "kana da gaskiya duk uba na gari zai yi alfahari ace Aliyu sirikinsa ne koni na dade ina masa kwadayin mata a gidana saboda hankali da nagarta uwa uba natsuwa a hankali suka ci-gaba da tautaunawa akan rayuwar duniya har sanda mumy da zee suka  karaso hannunsu  dauke da manya manyan  kuloli '"ranka shi dade ga abincin gargajiya dan nasan har ka manta da tuwo dan haka sai a tuna baya Alhaji bashir yayi murmushi irin nasu na manya "haba uwar gidan realwan ai idan na manta tuwo zan manta da asalina ya karasa maganar tare da janyo kulolin abinci  ya bude miyar kuka wanda yaji kayan kanshi ne da naman karamar dabba ,dayar kuma kamshin farfesun bindin sa ne ke tashi ya saki murmushin a hankali suka soma cin abinci."


kisna ta shirya cikin doguwar riga baka mai adon duwatsu grenn ta daure gashinta da kyallen rigar yan kunneyenta kalar rigar jikinta ta saka takalmi plat kai tsaye gurin mai aikinsu ta nufa a kitchen ta tsaya gaban asabe mai aiki rike da kugu "asabe hadin  salad din dankali da kwai zaki min sannan ki hada min da fruit tana gama magana bata tsaya jin mai zata ce ba ta juya dakin mumy ta nufa saman kujera ta sameta gefenta ta zauna ta ɗora kanta a saman kafadar mommy tace "mom waye wannan mutumin dana ji ance uncle Bashir ta ɗan kalleta "abokin mahaifinki ne da sukayi karatu tare tun suna yara bayan sun gama karatu ya wuce kasar London a can ya haɗa karatunsa bayan ya gama kasar ta nemi ya zauna yayi mata aiki a can  a kasar London yayi auri  tun kina yarinya da yazo bai sake zuwa ba sai yanzu kisna tayi dariya "mumy yace dani zai tafi kuma wai na cigaba da karatuna a can mumy tace "ai sai dadynki ya amince "zai ma amince inshallahu ni gabad'aya kasar ne ya fita min raina kisa baki ya barni "Allah yasa idan kin tafi ki manta da wannan yaron "ba ameen ba ta fada tana mikewa tsaye "bari naje naga ko asabe ta gama abinda na sata ta soma kokarin barin gurin "ai soyayyar Musa a zuciyata mutu ka raba yana nan tamkar rai da ajali yanzu zanyi wannan tafiyar ne dan na inganta rayuwar mu dashi tana wannan maganar ta shiga kitchen "..

******

Bayan wata biyu   jarabawansu kisna ta fito ana aka fara shirye shiryen tafiyarta London  tare da uncle bash duka yan gidan suka yo musu rakiya har bakin mota kasancewar ranar asabar ce ba aiki kowa yana gida har zata shiga mota tayi tunanin ta tafi da waya kodan kiran musa dan tasan da wuya a bata waya tunda ta lura har da son ta manta shafukan rayuwarta aka barta , a hankali ta fito daga cikin mota "ina kuma zaki mumy ta tambayeta ?"akwai abinda namanta dashi ta shige falo da sauri ta soma kokarin cire wayar mumy a caji dake parlour sai ga muradi  turus tayi taja ta tsaya saboda ganinsa da tayi tsaye yana kallonta sanye da kanana kaya masu matukar kyau da tsada  kallon sama da kasa tai masa sannan taja tsaki ta cigaba da cire wayar daga caji sautin muryarsa taji "me zaki da wayar ?" Da hanzari ta mike tana kallonsa idanunta cike da ɓacin rai kamar tayi masa rashin kunya sai kuma ta kasa bata so ya shigo ba ya isketa ba a hankali ta fara magana "number zan dauka "number wa zaki dauka ?ta sake yin shiru tana dubansa da zaginsa a zuciyarta "ina ganin lokaci yayi da zaki manta komai ki fuskanci rayuwarki dan zuwa yanzu kinsan inda ke miki ciwo kece zaki gargadi kanki ba sai an zauna ana tunatar dake ba dan yanzu idan akace ki saka hannunki a wuta bazaki saka ba , wannan shine lokaci na karshe da wata muamula ko halaka dazata sake hadaki da wannan yaron mai kama da katantawar mutukar kina son zaman lafiya a rayuwarki dani ,ki lura sosai kin kalli kanki fi karfin wannan mai siffar katantawan ko maciji zan ce I don't know ,"idan lokacin da zaki rike waya yayi nayi miki alkwarin da kaina zan siya miki duk wayar da kike so koda ta kai million daya ce dan haka ki dawo taitayinki ". tsaki taja a ranta ta  ajiye wayar ta sakar masa harara ta  juya tayi gaba abinta har airport suka rakasu sai da suka ga tashin su sannan suka dawo kowa na murna kisna zatayi tafiya mai nisa zata manta Musa a rayuwarta gabad'aya suna zaune kusa da mumy akan kujera suna farinciki mumy ta dubi  ƴaƴanta cike da farinciki most especially muradi  kaunarsu  na cigaba da ratsa zuciyarta ta shafi kansu daya bayan daya tana mai yiwa Allah godiya daya azurtata da kyawawan ya'ya wadan da suke qaunarta fiyye da komai a duniya   .."


Misalin ƙarfe shadaya na dare  suka sauka a filin jirgin   London  isarta kasar ta haifar mata da farinciki mara misaltuwa musamman lokacin da suka iso tangamemen gidan mai kama da aljanna duniya isarsu parlour'n ta shiga zare idanuwa tamkar ba dare ba saboda hasken fitilu da gudu kyakkyawar yarinyar uncle bash ta iso ta rungumeta tana fadar" You Are welcome my sis matar gidan wacce suke tsananin kama da yarinyar ta janyota jikinta duk cikin harshen turanci suke mata sannu da zuwa sannan suka nufi katon falon , kisna ta gaishe su cike da girmamawa tamkar dama can tasansu haka suka hau hira kafin daga bisani aka kawo mata abinci iri iri  sai data natsana sannan kausar tajata zuwa daki dan nan zata  zauna tun a daren data sauka ta sheidawa Musa yayi murna sosai sun dade suna tsara yadda zasu yi aure idan ta dawo har biyun dare .


  rayuwar kausar da kisna  gwanin ban sha'awa a London idan kagansu tamkar sun shekara da sanin juna sun saba matuka har kisna ta labarta mata soyayyarsu da Musa tana hawaye kausar ta goge mata hawaye tana bata hakuri duk da dai ita bata san meye so ba dan bata taɓa soyayya ba balle tasan azabarta amma tana da yakinin kisna na cikin wani mawuyacin hali wanda ya zama wajibi a tausaya mata . mutanen gidan suna nuna mata kulawa da so da qauna yadda ya dace shiyasa ma kewar gidan bata dameta da yawa ba bugu da karin tana hira da musa da wayar kausar tana jin dadin gari sosai , karatun kisna ya kankama sosai kullum  uncle bash zai kai su  makaranta mumyn kausar  ta dawo dasu gida babu ruwan ta da kowa karatunta kawai take sai dai zuciyarta na Nigeria gurin dan  oduduwa,  sai dai ta dawo shiru shiru babu yawon hayaniya  natsuwa ta fara zuwa mata  batun tsokana babu dan bata da wanda zata tsokana kausar ce ita kuma ta ɗan ja baya da lamarinta saboda yadda taga tana biyewa Musa dan wani lokaci sai dai kaji kisna tana nishin a cikin bargo manne da waya, sam bata sakewa samari fuska idan kaga tana murmushi to tana waya da Musa ne   yau ma kamar kullum suna wayarsu ta iskanci da Musa takaici ya rufe kausar ta mike a kufule tana fadar "gaskiya al'amarinki  da akwai gyara sai ki dinga biyewa namiji haka wallahi zai kaiki ya baro gaskiya ni banason irin haka idan ba haka zan fadawa dady ya fadawa dad dinki ni wallahi bani da lokacin soyayya ta juya ta fita ta bar mata dakin ita kuma kisna cigaba da wayar ta"jeki wahalliya baki da rabo ne , da kin samu kamar Musa da gudu zaki mika wuya al'amarin kisna yana bawa kausar mamaki ta yadda bata damuwa da kowa sai kanta dana saurayi hatta mahaifiyarta bata nemanta sai dai ita ta kira wayar mumy tace a bata waya su gaida komai dai musa idan kina son kuyi hirar arziki daita to dole sai ya zamanto na shi ne ..."

Akwana atashi babu wuya a gurin Allah sai ga kisna ta share shekara uku a kasar London kuma har lokacin bata taba zuwa hutu ba ko tace zata zo sai iyayenta suce ta zauna idan ta kare gabad'aya uncle bash ya siya mata dan kareriyar waya ya bata saboda a wannan shekara zata rubuta jarabanwarta na karshe wanda daga shi sai naija , bayan kwana biyu da gama karatun kisna ta fara shirye shiryen komawa ƙasar haihuwarta kananan kaya ta siyawa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login