Showing 423001 words to 426000 words out of 495987 words
Chapter 142 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
gaskiya naga sakarcinki yaushe zaki samu miji irin muradi ki wulakantashi irin haka mijin da mata dayawa suke neman su kasance a karkashinsa Allah bai basu ba , wallahi mijinki abun alfahari ne ba kuma a samun masu irin hakurinsa idan kuma ransu ya ɓaci ba'a iya control dinsu ,yanzu dai Allah ya baki dama ta biyu ta karasa maganar tana numfasawa ."
"Bari ke dai safy ai kisna tayi sakarcinki sai dai mun godewa Allah data dawo ta fahimci rayuwa kuma ta gane gaskiya ake fada mata inji cewar aunty zee kisna ta lumshe idanunta ta bude su akan safy sannan ta fara magana cikin sanyi murya "shine abinda yasa kika ga ina wannan hakurin da kike ganin kamar na cika naci ko na cika makale masa ni nasan abinda nake yi nazo ne dan gyara kuskurena na baya Kinga kuwa dole nayi hakuri da abinda idanuna zasu gani , zan cigaba da hakuri dashi amman banda na duka , koda yake wannan an wuce gurin tun ranar da yaji nace zanyi tsirara na fita na karad'e unguwar nan bai sake yunkuri ba ".gabadayansu suka kwashe da dariya"kai kisna kice dai har yanzu da sauran halin ana ta'bawa , yanzu ke sai ki fita tsirara ? "safy ta tambayeta tana dubanta tana dariya.
"bazan fita ba gaskiya amman shi ya dauka da gaske fitar zanyi tunda yasan hali " safy ta amshe da cewar "dole ya dauka da gaske ne saboda yasan hali tunanin yayi zaki iya aikatawa gaskiya Kisna labarinki akwai ban dariya akwai shirme akwai tausayi da fari fa dariya abun ya dinga bani sam ban dauki maganar so serious ba amman daga baya kuka na dingayi sun dade suna hira sallah ne kawai ke tayar dasu har zuwa sanda muradi ya shigo tare da sallamarsa suna ganinsa kowacce ta shiga hankalinta saboda yadda ya hade rai tamkar yaga mutuwarsa shi kuwa yayi haka ne a dalilin ganin safy , kisna na ganinsa ta mike ta isa gabansa ta amshi jakar hannunsa bai dubeta ba ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarsa tare da faɗin " sannu da zuwa world best , "yauwa ya fada a can kasan makoshi Idanunshi na kan safy yana tunanin abinda zai fada mata ta bar masa gidansa dan baya bukatan zuwanta zumunci ne sayi da mijinta.
Kisna ta nufi hanyar upstairs tana tafiya tana dubansa gabanta na faduwa har ta kurewa step yana kokarin bude bakinsa safy ta rigashi "sannu da zuwa uncle Aliyu ya aiki ?"yayi mata banza tamkar ba dashi take ba aunty zee ta sauke numfashi tana masa alamun ya amsa itama ya shareta ya daina kallon inda take ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondansa yana tafiya a hankali "kayi hakuri akan abinda ya faru wallahi zaman jiran dawowarka nake na baka hakurin abinda ya faru rana nan ,wallahi duk naji shirmen da kisna tayi maka a bakin nasir sam bata kyauta ba rayuwar duniyar ma guda nawa take ?".ya numfasa " kawai baki san komai ba zaki dinga shiga hurumin da ba naki ba, wallahi safy ina mugun ganin girmanki dan da wata ce tayi min abinda tayi Allah kadai yasan yadda zanyi daita yanzu abubuwan da nayi mata ai ya qara sawa tasan me duniya take ciki kuma ta shiga hankalinta"kwarai kuwa ai na qara shiga hankalina shiyasa kaga inata baka hakuri suka ji sautin muryarta "world best na gane kurena bai ce mata komai ba ya dauki hanyar upstairs." ta biyosa abaya cikin sauri ya shiga d'aki.
safy ta dubi aunty zee "kisan kuwa uncle Aliyu na mugun son kisna laifinta ne ya hana soyayyar tasiri?" ni zan fada miki wannan kinga irin damuwar daya shiga a lokacin da abun nan ya faru kafin daga baya nawal ta shigo rayuwarsa ,Allah ya qara daidaita tsakaninsu dan wallahi nafi sonsa da kisna kawai dan sunyi matukar dacewa Allah yasa a fasa auren nan da nawal ,rufawa kanki asiri da muradi yaji kin fadi haka ba'a gama kashe wata wutar ba zaki Kunnowa kanki wata .Kisna ta dubi muradi dake kwance flat akan gado bayan ta cire masa takalmin kafarshi da safa "dan Allah ka kara hakuri bai dubeta ba sannan bai buɗe Idanunshi ba amman yaji farinciki acikin zuciyarsa kuma ya hakura jin yaki magana kuma tasan bazai yi ba tunda ya dauki wasu mintuna ta sauko ta shiga bayi ta haɗa masa ruwan wanka ta fito "na hada maka ruwan wanka ka shiga kayi jikinka akwai alamun gajiya idan kayi zakaji dadi still shiru yayi mata ta nufi kofar fita "bari naje muyi sallama da safy tana karasa fita ya mike ya shiga bathroom .
Ta karaso inda suke suna ganinta suka kwashe da dariya itama kisna dariyar take safy tace "kai kisna kina bala'in tsoron uncle Aliyu yanzu idan za'a yi harka ya kenan ?" wai ma me kika masa naga kamar fa ya sauko ? kisna ta amshe maganar "eh to ya dai fara saukowa last two weeks ne fa ya kwana yana karanta tahirin rayuwarsa data mahaifiyarsa da wanda nayi masa a ranar ma nayi kuka ina bashi hakuri to dai alhamdullahi dan koda ya dawo yaci abinci babu wata matsala sai dai ku ci-gaba da tayani addu'a Allah ya huci zuciyarsa gaba-daya ni ko bazai soni ba ya barni na zauna cikin kwanciyar hankali "barema yana sonki ki dai cigaba da hakuri tunda kinsan inda aka fito kece da laifi , tare suka fita har aunty zee ta rakasu suna qara mata nasiha aunty zee ta nufi part dinta yayinda safy ta shiga motarta ita kuma ta juya cikin juyayi kai tsaye kitchen ta shiga domin daura abincin dare .
Bayan sallahr isha'i yana zaune falo akan kujera yana tura sakonni ta soma kokarin sanye da wando da riga da kadan rigar ta wuce cibiyarta ta tufke gashin kanta a tsakiyar kai batare data daura komai akanta ba saboda bata cika son dankwali ko hula ba sai ya zame mata dole sai kamshi ke fita ajikinta mai tsayaya zuciya tun tahowarta hankinsa ya rabu gida biyu wani na kanta wani na kan aikinsa sai dai ko da wasa bai d'ago ba har sanda ta karaso ta tsaya gabansa cike da ladabi tace " sannu da aiki an gama shirya dinnig kamar yace ya koshi sai kuma ya tuna ai ya hakura da komai daya faru yakamata yanzu ya dinga kawar da wasu abubuwa , ya mike jiki a sanyaye tayi gaba da sauri taja masa kujera ya zauna ta soma kokarin zuba masa tuwon shikafa miyar wake wanda yaji naman kaza ta fara tura masa ruwan wanke hannu sannan abinci tana ganin ya fara ci ta zauna ta haɗa tea ta bude wata madaidaiciyar kula ta dauki naman kaza soyayye ta fara ci tana kurban ruwan tea shiru falon ya ɗauka tamkar babu mutane komai a natse take yinsa , ya dan saci kallonta ta kasan Idanunshi shigar jikinsa tayi masa kyau ,yana qaunar ganin matatsa cikin kananan kaya irin wanda ke sanye a jikinta ya rasa dalili da duk tattara abubuwan da yake maseefar so atare da mace , "ta cigaba da motsa bakinta a hankali tana tauna nama tana sha tea ya ji kamar yace tasa hannu zuci tuwon tare dan bai ga abinda ta zai mata ba amman miskilancinsa ya hana , tana gama wa ta mike ta kan kujera ta dauki wayarta ta shiga yana gizo tana ganin tashinsa ta mike ta kimtsa gurin ta kai komai kitchen ta wanke a daren ta gyara ko'ina ta fito ta nufi dakin baccinsu lokacin tuni yayi bacci cikin rigar bacci mai bud'ad'd'en gaba take taji wata irin muguwar sha'awarsa ta tsarga mata tana bala'in qaunar qirjinsa barin ma nipples dinsa dake makale da qirjinsa ga kansu baki gashi zai yi dadin sha ai bata san sanda shaukin ya dibeta ta fada jikinta ta shiga sarrafa kan nipples dinsa da harshenta , cikin bacci yaji alamun ana sarrafa shi ,ya ɗan bude Idanunshi kadan dake cike da bacci ya zuba mata yana furta "ya Salam a cikin ransa yayinda ita sam bata lura daya farka ba kawai ta cigaba abinda take ,ta dade tana sarrafashi kuma yana jinta kafin daga baya ta mirgina ta kwanta bata wani jiba bacci ya ɗauketa shi kuwa gbdy kasa komawa baccin yayi jijiyarsa ta dinga wani irin kumburi tana mikewa alamun tana bukatar abincin ruhinta matsowa yayi ya fixgota zuwa jikinsa ya kamkameta sosai yana sauke numfashi.
Duk wani abinda dace Kisna tana yi masa ta kowani bangare bata ragesa da komai ba sai gurin auratayya, shima bata hanashi kanta ba shine bai yi ra'ayi ba duk sanda ya bukata zata bashi babu rowa a tsakaninsu dan itama tana cikin tsananin bukatarsa ,idan kuma ya cigaba da miskilanci bai bukata ba su cigaba da zama haka , sai da wasa da jikinsa ne bazata daina ba duk yana sane da abinda take sai dai babu yabo babu fallasa to ita dai ko a haka ma ya tsaya taji dadi Cikin wannan lokacin ta lura miskilancinsa ya dan ragu fiyye da sauran lokutan baya da komai tayi fada da bala'i ne zai biyo baya yanzu bai hanata sarrafa jikinsa koda kuwa Idanunshi biyu ya nuna yana jin wani abu ne ajikinsa bazai ba har jijiyarsa tana ganin yadda take mikewa amman sam yaki yunkurin kusantatar ."
******
Kwanaki suna raguwa har suka dawo sati biyu bikin muradi nan suka fara shirin tahowa naija har nasir da safy , tun satin aka shiga gyaran gidan mumy inda baki zasu sauka , ranar asabar cikin doki kisna take tsaye a falon ta matsu ta bar kasar zuwa kasar haihuwarta sam kamar ba wacce za'a wa kishiya ba ,bini bini ta leka haraban gidan ta dawo cikin falo a karo na karshe tace "taso muje aunty zee an gama perking din kaya a mota ,aunty zee ta mike tana murmushi suka fito tare suka shiga bayan mota suka nufi gidan nasir suka daukesa sannan suka kama hanyar zuwa airport basu wani dade ba jirginsu ya tashi yayinda gidan mumy ya rikice da yan'uwa kowa yana daukin ganin kisna Mumy tasa aka yanka kaji masu yawa sannan tasa akayi farfesu mai rai da lafiya aka tanadar musu , da yamma suka sauka lokacin tuni mumy ta tura direba da su aunty ummi tare dasu zahra daukosu a airport da mota biyu suka nufi airport direba tare da aunty ummi , yayinda zahra ke tuka dayar motar ita da mufeeda kisna na tsaye a filin jirgin tana wurga idanuwa so take taga ta inda yan'uwanta zasu fito daga bayanta taji an makalkalota tana waigawa sukai ido hudu dasu aunty mufeeda rungumesu tayi ajikinta tana murna ganinsu gabadayansu murna ganin juna suke kafin daga bisani suka nufo gida cikin motocin da suka zo dashi .."
Tun mota bata gama tsayawa ba Kisna ta soma kokarin fitowa tana faman kiran suna mumy burinta kawai taga iyayenta tana shiga ta saka kara saboda ganin granny ta fada jikinta da sauri tace "cikani yar nema daga zuwa ki zaki nemi nurkurkusani dariya ta saka tana fadar "haba hajiyata daga na dan rikeki zaki min sharri daga xuwana ? dan Allah ina mumy ita kawa nake son ganin tace tana ciki akwati na boyeta Kisna ta bi bayanta tana fadar "kai tsohuwa gaskiya ya'yanki na fama dake yanzu haka ake tarbon bako bari naje naga sanyin idaniyata "maza jeki yar nema duk kin cikani da magana ta nufi cikin dakin mumy alokacin da su muradi suka shigo daya bayan daya bakinsu dauke da sallama granny ta amsa tana washe musu baki "barkanku da zuwa mazajena yan albarka ba irinsu ban fadi suna ba muradi ya isa gabanta ya gaisheta daita "sannu Aliyu an sauka lafiya ?"lafiya lau hajiyata ya gida da fama da jama'a ?'alhamdulillahi mun godewa Allah samir da nasir suka gaisheta sannan suka zauna tare da mumy kisna ta dawo falon tana makale daita kamar yarinya.."
Muna saida ingantattun maganin mata masu kyau da nagarta wanda ko da kudinka sai da rabonka tsimi , zumar Mata, gunba, gari insertion,kaza,zakara ,
jigida dadai sauransu.
1.Tsumi Yana saukarwa mace niima Kuma bazataji wuyar jimai ba.
2. Zuma Tana taimakawa wurin Jin sha'awa Kuma itama Tana taimakawa wurin jindadin jima'i.
3.insertion( Dan matsi) daban dabanne akwai Wanda ke matse mace kuma yake saukar da ruwan ni'ima sannan akwai na mallaka , idan ana bukata a tuntubi wannan number
234 815 945 0159..
Mmn sudais
[7/19, 5:33 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 62
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, voil lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
granny ta kalleta ta ta'be baki tana cewa "shegen son jiki kawai yarinya kamar mage ai fa kin dawo kenan da ya'yanki zataji ko dake ? "dukkanmu meye ruwanki nida uwata kinga banason shishigi hajiyata kina wani bud'ewa mutane baki duk goro gbdynsu suka kwashe da dariya banda muradi dake satar kallonta yana jin wani irin abu na yawo a gabadaya ilahirin jikinsa " yaushe rabon ya ganta cikin farinciki haka ?, bama zai iya tunawa ba gaskiya a dalilin rashin kulawarsa gareta , wani irin qaunarta yaji yana bin jinin jikinsa musamman yanzu da take nuna tsananin qaunarsa da kulawa garesa ganin zata kalli inda yake yayi saurin dauke Idanunshi akanta , parlour'n ya cika da hayani masu aiki suka hau fito da kulolin abinci suna ajiyewa akan dadduma dake shimfide a tsakiyar falon , tuwon shikafa da miyar alaiyahu da ferfesun kazar da mumy tasa akayi musu da farar shimkafa da stew , jollof din kuskus wacce taji hanta ,abinci dai kusan kala biyar masu rai da lafiya dan tasan yaranta ba daga nan ba akwai ci ,plet da spoon tare da ruwa da lemuka aka jera musu kowace ta zubawa mijinta , bayan sun gama cin abinci hira ta sake barke a tsakaninsu , basu tashi ba sai gurin sallah magrib mazan suka nufi massalaci , kisna ta kalli Aunty rukkaya da aunty surayya tace "kowacce ta tashi ta kama gabanta sai gobe ma cigaba daga inda muka tsaya ta k'arasa maganar tare da juyawa ta nufi dakinsu na kasa da safy "muna nan muna jiranki yau babu bacci kwana zamuyi muna hira ", murmushi tayi batare data juyo ba tace "wannan lokacin na uwata ne suka karasa shigewa , d'akin ya sha gyara sosai sai kamshi ke tashi , ta fito ta barta tayi sallah ta huta ita kuma ta shiga d'akin mumy ."
Sai dasu aunty ummi sukayi sallah sannan kowacce ta kama gabanta da zumar zasu hadu gobe bayan sun wuce kisna da mumy suka shiga hirar yaushe gamo mumy ta janyo wata karamar akwati ta bude sababbin kaya ne sheke acikinsu na alfarma "ga kayan nan mamana ki duba Allah yasa dinkunan suyi miki, cike da farinciki kisna ta soma duba kayan tana cewa "koma basuyi ba sunyi bare ma nasan mamana gurin iya zaben kaya ,wayyo Allah mumy kin kasheni da dadi wallahi ,na gode Allah ya bar min ke." "ameen mamana ki gwada wanda yayi yawa a mayar wa tela ya gyara miki ,haka ta dinga daukar kayan tana gwadawa daya bayan daya mumy na yabawa babu wanda bai mata ba kamar telan ya aunata, bata fito daga d'akin mumy ba sai wajen tara shima ta fito ne dan ta gaida mahaifinta anan taga su Aryan suna kwance akan gadonsa sunyi bacci tun zuwansu bata gansu ba sai yanzu suna gidan ya madu , yaji dadin ganinta sosai har ma ya sakar mata fuska suka hira kadan wanda yaushe rabon ta samu haka daga garesa yayita saka mata albarka aiko farincikinta ya nunku a zahiri ake iya gano murnarta ,ta dawo d'akin mumy suka ci-gaba da hira har shadayan dare suna labari mumy na fada mata irin makudan kudin da muradi ya kashe a sabon gidansa babu abinda bai zuba acikinsa ba mamana , suma dangin amarya yace karsu zo da komai "kuma sun yarda da hakan ?inji cewar kisna ,ina fa waɗan nan iyayen karyar zasu yarda ke baki ga bala'in da akayi da uwar amarya ba ,kamar fa za'a fasa auren sai dana saka baki,amman duk da haka sai da sukaje gidan,