Showing 3001 words to 6000 words out of 495987 words

Chapter 2 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

qaunar  kallon fuskarta  ,ta  k'arasa  inda  yake  kwance ta durkusa  a  gabansa "nasan  nayi  maka laifi  kuma  na  roki  afuwarka  ya   kamata  ka tausaya ka  yafe  min haka   bana  son  na  cigaba da zama  makiyayarka  kamar yadda ka  ɗauka  saboda mu samu  damar inganta rayuwar ya.....

"dan  Allah  malama bana  son   takura  bacci nake  ji  kije  kawai  bana son  kusancimu tare .
"ammmm to dan Allah ka tashi  ka  koma saman  gado ka  kwanta   ni sai na  kwanta a  kasa " kije ki  kwanta  kawai  bana bukatar  haka  ya k'arasa maganar  yana runtse idanunshi  gam , mikewa tayi  jiki a sanyaye kamar zata  yi  kuka  ta hau saman  gadon ta kwanta ta  janyo  bargo  ta lullu'be  rabin  jikinta  ta jingina  bayanta da abun  gado sai  dai   ta  kasa runtsawa  sai  faman tunanin yadda zata shawo  kanshi  take .."

Matsowa  tayi  ta dawo bakin  gadon  ta  tsura masa  kyawawan  idanunta   tana kallon  yadda yake sauke numfashi  ,a hankali qirjinta  ke dokawa, ta dinga   jin   kamar zuciyarta  zata fito daga qirjinta , tuni  hawayen  suka wanke  mata fuska tausayin kanta ya kamata "daman  tasan dole sai  ta fuskanci irin wannan  matsalar atare dashi , gashi  ita yanzu    babu  abinda  tafi bukata kamar  kulawarsa da samun  zaman lafiya a tsakaninsu "

  "wallahi  bazan taɓa yarda ba sai nayi galaba  akanka , sai na mallaki zuciyarka kamar yadda ka  mallaki  tawa cikin sauki batare dana shiryawa hakan  ba   tayi maganar  a kasan ranta  tana cigaba  kallon fuskarsa  bata  san sanda gigin soyayya  ya sauko daita   daga  saman  gadon ba ,  ta ra'ba  ta  kwanta a gabansa  ta  zare pillow dake  manne a qirjinshi ta  maye  gurbin  pillow  dake  qirjinshi ,cikin rashin  sani  ya rungumeta  tsam ajikinsa yana sauke numfashi  , cikin  sanyayyiyar muryarta  tace "dan Allah ya Aliyu  kayi  hakuri  ka barni  na rayu  a karkashin ka   "ta k'arasa maganar  gabanta na tsananin  fad'uwa , tasan bancin  kuskurenta na baya   da  babu abinda zai  hana  aliyu  sonta ..."

Sake  shige  masa  tayi ta zuba  masa kyawawan  idanunta  tun  daga kan kwantaccen  sumar kanshi  take  bi  da wani mayataccen  kallo ,
Sosai  ta  fuskartashi   tare  da  kai fuskarta daidai  nashi  tana zuko numfashinsa  ,wani  irin  sanyi taji  yana ratsa  sansar  jikinta  , laulausan  tafin  hannunta   ta  kai cikin rigar  baccinsa   ta  kife hannunta  akan   qirjinsa  dake  kwance  da gashi tamkar  na  jarirai ,a hankali  ta  soma murza kan  nipple's   d'insa  wani irin  yanayi ya tsinci kansa   cikin   bacci ,ya shige  jikinta   batare daya  san  yayi hakan ba, lumshe  ido  tayi dan dadi" ina   ma idonsa biyu  yake rungumeta daita  cikin kulawa da farinciki ?"Ina ma zai bata  dama  daya sha mamakinta , dan kuwa sai  tayi  nasarar dasa soyayyarta a cikin zuciyarsa batare daya shiryawa hakan ba  "
lip's  dinta  ta d'aura  akan  lip's  d'insa ta kamo  tana tsotsa  a hankali  tamkar ta samu sweet  tana murza kan nipple's  d'insa , wani irin zirrrrrrrrr  yaji a gabad'aya ilahirin  jikinsa mai kama da shocking , wani irin zabura  yayi  saboda sakonta  yaje masa har cikin  'kwa'kwaluwarsa  ,a hankali  ya  bude idanunshi  ya  zuba mata  fuskarsa  dauke da damuwa  mai tattare da miskilanci,  sake shige masa  tayi  tana sauke numfashi  dan gabad'aya yanayinta ya fara sauyawa   "ba tsaya 'batawa  kanshi  lokaci ba ya  fizgeta a jikinsa yayi  jifa  daita kamar  wata  ƙaramar  yarinya."

qara  ta  saki mai sauti tare  da rike daidai  kugunta  da  hannuta ɗaya  tana ciza lip's dinta "kina  hauka  ne ? "ko ance  miki nima ɗan iska ne  irinki  da zaki wani kawo  min wasan iskanci"?runtse idanunta tayi  sai  ga hawaye sharrrrrrr  daga   idanunta sun  zubo  "wallahi  idan baki  kiyayeni  ba  zan 'bata miki  rayuwa , zan karyaki  kuma na karya banza  dan  ko  gurin mai d'auri  bazan  kaki  ba wawa  wawiyar  bazan kawai  da  bata san ciwon  kanta  ba "
Yana gama fadar haka  ya koma ya kwanta  tare da  juya mata baya.

a hankali sautin kukanta ya  dinga  tashi a  d'akin   kusan  minti  goma ta ɗauka  tana zaune tana  kuka  rike  da gefen kugunta "wayyo  kuguna  wayyo  dady , wayyo mummy , wayyo aryan  ,wayyo  arif  zan mutu  ......"
duk  yan  gidansu babu wanda  bata kira ba , yana  jinta yayi mata banza  a ransa yace" baki ga  komai  ba  tukunna,  ba  dai takamarki  naci ba ?  "sai  na maida rayuwarki  abun kwantaccen  ,sai canza miki  kamani , sai miki illa a rayuwarki  ta yadda mutane idan sun ganki  zasu kasa   ganeki , sai data  ci  kuka  mai  isarta sannan   ta  rarrafo ta dawo  inda  yake kwance  ta  zauna tana sake  girka  sabon  kuka da kiran  zan  mutu ,mutuwa zanyi  ka  kira min babana  da  mamana mutuwa  zanyi  ya Aliyu  "ya  tashi  zaune a matukar  fusace  "ooooooooo  wai  meye haka   ne  da zaki hanani bacci  ?  "Kuguna  ke  ciwo  mutuwa  ma zanyi ka  daina min ihu idan na mutu  ai ka huta "
"sosai  kuwa wallahi na huta  da  jaraba  da naci " ta  tsurawa  kwayar idanunshi  ido tana kallonsa cike da mamaki, "laila  a illalla muhammadur rasulullah Sallallahu alaihi wasallam  ta shiga  furtawa  tana runtse idanunta  numfashinta na  sama da kasa " "ke ........" yayi  magana tare  da  girgiza kanta  cikin  tashin  hankali, fuskarta ta sake narkewa tana  ƙoƙarin zu'bewa a kasa  "ke  ki bude idonki  mana, kin  budewa tayi  ta  tsaya batare  da ta kai kasa  ba  , ta ɗan kanne idonta  ɗaya  daman bawani  ciwon kirki taji ba so  take ya bata kulawa,  numfashi ya sauke  yana  furzar da iska  ,yayinda  idanunshi ke  kanta yana karanta yanayinta  gabad'aya ya gama  fahimtarta dan haka  ya mike tsaye da hanzari .

" Maza  ki  tashi  tsaye"
"ai bazan  iya tashi ba "what ?  ya furta a fusace. "bazan  iya tashi ba  ta sake furtawa a shagwa'be  idonta na tsiyayan  ruwan hawaye"
" ki  tashi tsaye nace, wallahi  idan  baki tashi ba  zanyi kwallo dake sai kanki  ya bugu da bangon d'akin nan  shegiyar kwalmashashiya  kawai mai  fuskar  alade  ,zaki tashi  ko kuwa  sai na fara  kwallo dake ?
zumbur  ta  mike  jikinta na  kyarma  tana mamakin  jin furuncisa sam  batayi zaton haka halinsa  yake ba asanin data  masa shi mutun shiru  shiru , bata taɓa jin furucin  zagi daga bakinsa  bare  kalmar kwalmashashshiya .
"yar iska  yarinya kawai  kin  ɗauka nima ɗan iska ne irinki? " maza ki  kama gabanki  mara zuciya "

Tafiya ta soma yi a hankali  tana waigensa har  ta karaso  bakin kago  ta  hau  kan katifa  ta  kwanta lamo   tana mamakinsa  yaja tsaki tare  da komawa ya kwanta  ruf da ciki  .."

Da misalin  ƙarfe biyar na asuba  ya  tashi domin gabatar  da  sallar , bai tasheta  ba  yaje yayi alwala  ya  fito, motsinsa ya  tayar daita  ta tashi ta shiga bayi  ta d'auro alwala  ta fito   ta gabatar da sallah  "bayan  ya idar yayi  addu'oinsa  wanda ya zame  masa jiki ,ita kan  duk  adduarta akan shi  ne ,  ya  koma ya kwanta  akan doguwar kujera   itama  gado ta haye  ta koma bacci , gari na  wayewa  ta  rigashi  tashi  ta shiga bayi tayi wanka  ta  shirya  sannan ta  haɗa masa ruwan   wanka  ta  fito ta tsuguna a  gabansa  ta  kai bakinta daidai saitin   kunneshi  tana   hura masa  iskar bakinta, a hankali  ya buɗe idanunshi  tana durkushe  kusa da  jikinsa  , wannan abu ya 'bata masa rai "jaraba......"  ya furta a fili  sam  taki  zuciya  ,ya mike  tsaye batare da yayi  mata  magana ba, itama  mikewa tayi ta tsaya  a gefensa tana wasa  da zara zaran yatsun  hannunta "uhmm na  haɗa  maka ruwan wanka  ka shiga kayi wanka  "na saki ?  yayi mata  tambayar  yana jefanta da wani mugun kallo , ta girgiza masa kai  tace "uhmm naga hakina ne  ba sai  ka sani ba "to karki  sake bana so okay"
  ya    wuce ya barta tsaye   ya  shiga bayin , yana  shiga ya zubar da ruwan  data  haɗa  masa  ya  haɗa wani yayi wanka ya  fito kugunsa d'aure da farin  towel  tana ganin fitowarsa  ta  juya masa baya  sakamakon ganin qirjinshi  a  buɗe  dan hakan nasata jin wani iri ajikinta , tsaki ja a ranshi yace  "munafuka  kawai  kalleta  kamar ta Allah nan  kuwa kasurgumar yar  ta'adda ce "
Lotion  ya  mulka a tafukan  hannunsa ya soma  bin   jikinsa yana shafawa , ya  fesa turare, cumb  ya ɗauka  ya gyara  sumar  kansh   ya karasa   jikin  wordrobe  gefen daya ga ta jera kayansa ya  buɗe  ya dauki  suit ash  colour  da vest fari da  boxcer fari  ya karaso   gaban  mirrow  ya tsaya ya ajiye kayan akan ƙaramin  stood   yana  sanya   boxcer da vest ,  ta  ɗan juyo ta gani ko ya gama  shirin , ganin ya saka  vest  da boxcer yasa   ta juyo gabadaya ta  tsura masa ido kawai batare  da  tace komai ba  .

a natse  ta soma takowa zuwa  inda yake  tsaye yana  ƙoƙarin saka dogon  wandon suit ta ɗauki farar   rigar suit  zata  saka masa, a hankali  taji  sautin muryarsa  ta  doki kunneta  wanda ya haddasa mata  jin mummunar faduwar gaba  "ajiye  min riga wai ke  wata irin jarababbiyar yarinya  ce mara zuciya ?  Ta  numfasa kana  tace  "ta ya zanyi zuciya da lamarin  mijina ? "aljannata  nake  so kaga kuwa   samunta  da wuya da  wahala ,wata uwar  harara  ya watsa mata  ya  fixge  rigar  daga hannunta  ya saka ya tura  cikin wandonsa   ya soke  belt  ,ya da'ura yar saman  suit d'insa   ya sakawa  kafafunsa safa tare  da takalmi ash , ganin ya gama shirinsa tsaf   jaka  aikinsa  kawai ya  rage  ya  ɗauka   ta karasa   da  sauri inda taga  ya ajiye
ta  dauko,  wani  kallon raini  yayi mata yana kallonta  a wulakance , sai  lokaci  yayi mata kallon  tsaf  tun daga samanta  har kasa  sanye   take  cikin   jar riga  doguwa wacce bata kai  kasa ba mai kama jiki  sosai  dan sunyi bushing  brest  d'inta kasancewarta  mai wadatattun dukiyar fulanin  ,kanta  sanye da hula  mai kalar riga, kafarta  sanye da jan takalmi  silifas, fuskatar kwance   da murmushi wanda bai san ko na meye ba  amman yafi kama  dana  iskanci ."

"ka  barni na rike  jakar dan  Allah  iya kasan gida nan   kawai  zan  rakaka fa  "ki fita hanyata  ance miki  barinki  zanyi a d'akin  nan ai  wucewa zakiyi  ki komai parlour'n  kasa  na kulle d'akina  " ya  fixge  jakarsa  da karfi  tare  da  juyawa , hannusa  rike  da jaka  ya buɗe  kofa  ya tsaya a bakin  kofa yana jiran fitowarta .."

Da sauri  ta shege bayi ta danna  key "wallahi bazan  zauna a parlou'n kasa    irin  na jiya ba  , tayi  maganar  muryarta cike da shagwa'ba , cike da sanyi jiki   ya dawo cikin  d'akin ya  k'arasa bakin  kofar bayi  "a she zaki  sha wahalar data fi na  jiya  dan kulleki zanyi a bayi kuma na kulle d'akin sannan na kulle ko'ina a gidan nan ,  tunda  kika  zabi rayuwa dani  kin zabarwar kanki tashin  hankali da matsalar  rayuwa iri iri, bazan taɓa saurara miki ba  , dan  kece mace ta farko  dana tsana a rayuwata   yana gama fadar  haka ya juya zai bar  d'akin  da niyyar kulleta  ciki  ta bude kofar  bayin  ta fito da gudu   ta  matso kusa dashi  fuskarta a shagwa'be  ta tsaya tana kallonsa  cike da matsanancin  sonshi  "ina sonka  ya Aliyu me yasa  bazaka soni  ko dan  darajan su  ar.......?
" Shot   up    bazaki   taɓa  cin wannan darajan  ba har abada   yayi saurin katseta ta hanyar fadar haka ,sake  matsoshi  tayi kamar zata shige jikinsa  tana busa masa iskar  bakinta,  yayi saurin  matsawa baya yana  watsa mata wani banza kallo "kina son shige  min  ,okay nasan dalili   saboda  yanzu idanunki  sun  buɗe  kin gane  wanene  aliyu , Kinga aliyu  ya  dawo  had'ad'd'en  gaye  fiyye da yadda  kika sanshi  ga kyau  ga  kudi   ga ilimi ko " ?

tayi tsam da ranta tana cigaba  da kallonsa qirjinta  na dokawa da karfin  gaske a hankali ta shiga  girgiza  masa kai alamun  ba haka bane  "karki  'bata min  lokaci da  iskanciki na banza da wofi  fitar min a d'aki  na kulle   "zuciyarta  na cigaba da bugawa da karfi  ta ra'ba  ta gefensa ta  fita daga d'akin tafiya take  kamar wacce bata da  isasshen lafiya tana zance  zuci har ta karaso parlou'n  kasa taja ta tsaya  tana jiran fitowarsa,  ta gabanta ya wuce  ya hau wani ƙaramin  table  zai kashe wutar  gidan  "dan girman Allah  karka kashe wutan ka  barshi  karka barni cikin  duhu "wannan ne kuma  baki isa ba yarinya da  yunwa da rayuwar duhu  zan miki izaya har sai  kin mutu   ta turo masa ƙaramin  bakinta a ranta  tace "ya cika taurin  kai  da shegen jaraba kamar  mutanen farko ai sai  ka kashe tunda kayi niyya  "
"me  kika ce? ya juyo yana  kallonta  , tayi saurin  daidaita natsuwarta  tana girgiza masa  kai alamun babu komai" na ɗauka wata maganar  banza kika yi na  sauko  na ci ubanki na kara miki  da dukan mutuwa , tasan  tunda ya furta , zai  aika dan haka ta  shiga hankalinta ya sauko  ya  juya yana taku daya  bayan  daya  ,sautin takun takalminsa  ne kawai ke tashi  a parlou'n ta zubawa  bayansa ido har bata  son kiftawa ya  fice daga  parlou'n ya kulle kamar  jiya ....

Naunayen  ajiyar zuciya ta  sauke  ta zauna a hannu kujera tana mamakinsa  a hankali ta mike  ta nufi gurin changeover  ta hau kan   kujera  daya hau dan canza  abun wuta amman tsawonta  bai kai ba  "wato dan yasan tsawonta bazai kai ba ne  yake  kashe  wutar gidan saukowa  tayi tana tunanin  yadda zatayi    idanunta  ya sauka abakin  kofar kitchen wani  irin  tsalle tayi sakamakon  ganinsa a buɗe  da tayi  ,sauri  lekawa tayi  ko'ina duhu bata  iya hango komai saboda  kofafin window a rufe suke parlou'n ta sake  dawo ta tsaya can ta  matso  gurin  center  table ta durkusa ta soma turawa , wani  irin karfi taji  har sai da tafin hannunta  yayi zafi ta kalli  hannunta  tana yarfewa  sannan ta kara kai wa jikin table ta dinga turawa har ta kawo gurin abun  canza wuta  ta d'aura  kujerar daya hau akan  Center table ta hau da  kyar kamar zata fadi tana  girgidi har ta samu nasarar  canzawa take gidan  yayi haske  ta sauko  tana sauke numfashi   ta shiga kitchen  ta kunna wutar kitchen  ta kunne ac sannan  ta soma bubbude  kitchen cabinet, babu  komai acikin ta bude frizer shima babu komai  dan  akashe ma  yake , kawai  ta daura hannuwanta duka aka ta  rushe da kuka "shike nan ya  aliyu  zai kasheni da yunwa  " jikin  window kitchen  din  ta koma ta bude  hawaye  shabe Shabe  a kwance a fuskarta mai  gadi ta hango  zaune ta sauke numfashi  tana kallonsa ta  rasa abinda zata faɗa, masa  ita ba yaren garin take ji ba bare ta kirashi, hakan  jikin mai gadi ya bashi  ana kallonsa , ya waigo  idanunsa ya sauka akanta  yayi shiru yana  kallonta har sanda tayi  masa alamar yazo da hannuta da sauri ya karaso  ta lumshe idanunta  na second daya sannan tayi masa alamar  tana bukatar abinci .

hannu ya kai bakinsa shima tayi saurin gyada masa  kai, da hannu yayi mata alamar  yana zuwa ta juya da sauri ko cikakken  minti goma bai ɗauka  ba ya dawo hannusa rike da takeway ya  mika mata ta amsa tana  godiya  ta zauna akan  kujera data gani a kitchen  din  ta bude soyayyiyar  shikafa ce da soyayyiyar   kaza da ruwa  ta  soma  cin abinci kafin kace me ta tashi da abinci tas  har wani gumi ne ya rufeta ,  ta rufe takeway  ta maida cikin ladar  ta sake dawowa bakin  window bata ganshi ba dan haka ta tura  tasan idan ya dawo zai  gani ya ɗauke , ta nufi sama da niyyar  gyaranwa  sai  tunawa datai  ya rufe dakin , ta  dawo kasa    ta soma gyarawa sai data gyara ko'ina tsaf sannan ta  mike a  saman doguwar kujera ta kwanta tana tunanin rayuwa "wai  ita ta  Aliyu yake wulakanta ? wannan  abu ya tsaya mata a rai  lallai duniya juyi juyi ne abinda kafi karfi wata rana shi zai fi karfinka "

Misalin karfe uku na rana ya  shigo parlou'n gidan  bayan ya bude cike da matsanancin mamaki yake bin parlou'n da kallo kafin idanunsa ya sauka akanta kwance akan doguwar kujera tana sauke numfashi a hankali  iskar parlou'n sai faman kada  gashin kanta  yake  a saman kafad'unta yana neman rufe mata fuska take wata  irin tsanarta ta kuma  sakko masa cike da  takaici yake dubanta .a hankali ya dinga takowa har ya karaso inda take kwance bai tsaya wata wata ba ya sauke mata mari har biyu  a fuska.....

*Domin bukatar karanta novel dina kyauta a sauke manhajar Aysha a bagudo ta hanyar shiga wannan link din dake kasa* 👇🏻
https://play.google.com/store/apps/details?id=aysha.a.bagudo.all.books.pro

Mmn Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
  💖💖💖💖
💗💗💗💗💗

Free page 3

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number   +234 803 238 4602  alert  domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalmi, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰

...A  matukar  firgice  ta farka  daga  nannauyen baccinta  tana  zaro idanuwa  dafe  da gefen fuskarta  inda  taji  saukar  mari "are  you mad  what are you doing  ? "  yayi  maganar a  fusace  yana  zaro mata kyawawan idanunshi   , take  jikinta ya  ɗauki  rawa  "uban wa yace  kiyi  changeover ?"

   "inna  lillahi  wa  inna ilaihi  rajiun  ta shiga furtawa  a zuciyarta  tana  maimaitawa  kafin a hankali  ta yunkura ta  mike tsaye  tana duban inda  yake  tsaye  kikam hannunsa  rike da yar saman  suit  d'insa,  Kana kallonta  zaka   gane  irin tashin  hankalin  da take ciki  a lokacin, dan gabadaya  fuskarta cike take  da  matsanancin tsoronsa , babu  abinda take  ganewa  a tun sanda  ta buɗe  idanunta akanshi    baya ga fuskarsa  da  kayan dake

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login