Showing 66001 words to 69000 words out of 495987 words

Chapter 23 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

bazasu bi mommy ba shi kansa Aliyu babu yadda zai yi ne amman da bazai bari a tafi dasu ba ,mommy ta sake kallon nawal "to nawal sai  mun hadu a naija ko"?
"Sure  ta fada  tana gyada  mata kai cike da girmamawa, mommy ta juya zuciyarta cike da kewar ya'yanta   suna  tsaye jirgi ya lula sararin samaniya suna binshi da kallo kisna ta share hawayen fuskarta ta juya da sauri ta faɗa mota  zuciyarta na bugawa  sosai sai yanzu take kara jin soyayyar mahaifiyarta "lallai qaunarsu acikin jini juna take itama mommy hawaye take goge wa a zaunen da take acikin jirgi  ..."

Nawal ta matso kusa da Aliyu tana jujjuya masa jiki hannuta rike da jaka tana sakar masa murmushin "nur zan wuce gida muje ka rakani na shiga mota ko "ta fadi haka ne dan tasan halinsa zai  iya barinta agurin ya kama gabansa "okay muje ko suka jera a tare suna magana kasa kasa a natse kisna ta d'ago idanunta karaf ya sauka akansu sunawa juna murmushi  take qirjinta ya shiga luguden bugawa "yaushe ne zata samu irin wannan damar da nawal ta samu a zuciyar mijinta "?
  "Ka yafe min mijina nayi kewar komai daya danganceka tana kallonsa ya bude ma nawal  bayan motarta ta shiga ta zauna tana sake sakar masa murmushi "ko me yake ta fada mata haka yasa take ta faman murmushi "?ta tambayi kanta har sanda ya maida murfin kofar motar ya rufe direbanta yaja  idanunta na kansu .."

  Ko daya dawo gurin Samir bai gurin da gira ya tambayi nasir inda Samir yake shima da gira ya amsa masa alamar ya wuce ya kai hannu ya doki kadan nasir "kai fa nasir wani lokacin  dan iska mutun  ne ," yan iska dai taya zaka min tambaya da gira "?"Kaga muje har ya juya nasir ya kira sunansa ya juyo ya tsaya tare da zuba hannunwansa ciki aljihun wandonsa "ya'akayi Sarkin matsala"?

"Ai kai ne sarkin matsala wallahi daman akan yarinyar nan ce "wace yarinya kenan "?ya tambaye shi ,kisna mana dan Allah ka rarrashita idan kunje gida  karka sa   yarinyar mutane a gaba da bala'i bayan zuciyarta na cike da kewar mahaifiyarta da ya'yanta "kasan Allah bazan rarrasheta ba  Allah yasa tayi ta kuka har ranar da zasu sake haduwa babu ruwana .

Nasir yace  "dan iska  kana wani nunawa kamar baka sonta bayan nasan kana bala'in sonta  kamar ka mutu "na taɓa faɗa maka da bakina ina sonta "?Nasir yayi shiru yana mamakin hali irin na abokinsa "kayi shiru na taɓa faɗa maka ina sonta ko ka taba ganin wata alamar data nuna ina sonta "? "Baka sonta ya'akayi har ka mata ciki ? "Wannan tsautsayi da rabo ne   ya bashi amsa yana ƙoƙarin juyawa   nasir  ya dakatar dashi " zaka san tsautsayi ne sai randa ka tsinci  zuciyarka dumu dumu ta kamu da matsanacin soyyarta"babu wannan ranar nasir ba kuma na fatan zuwan wannan ranar a rayuwata, nawal kawai ta isheni rayuwa kasan wani abun farinciki  "? Nasir ya girgiza masa kai "mommy ta bamu gud five month mu dawo daidai tamkar sauran ma'arata   idan bamu dawo ba zata dauki mataki ka tayani addu'a Allah yasa mu cigaba a haka nasan karshe hukunci rabuwa ne zai biyo baya  na huta da jaraba  .."

zaro ido waje nasir yayi tare da cewa "ba ameen ba dan iskan  Allah yasa wani tsautsayin ya sake shiga tsakani mu sake samun yan shida dan da alamun spam din abokina baya bada kwai daya "ba ameen ba dan iska kawai mai mugun baki yana gama fadar haka ya juya  escort   d'insa suka zagaye motar da yake kokarin shiga kowannensu na rige rigen buɗe masa kofar   gidan baya inda kisna  da safy suke  zaune tana rarrashinta , ko kallon inda take zaune bai yi ba,
Ya juyar da idanunshi yana kallon wani bangaren , ganin tsayuwarsa yasa safy tayi ma Kisna sallama ta fito ya shiga direbansa yaja motar

*******
Har suka karaso haraban gidan bai waigo ya kalleta ba direba na gama parking escort dinsa suka fito daga cikin nasu motar suka bude masa ya fito yana ciccin magani sannan ya soma daga zara zaran yatsun kafafunsa cikin isa da takama ,a hankali ta yunkura ta fito jiki a sanyayye ta shiga ciki , tun byn dawowar su Daga airport Aliyu ya shiga part dinsa ya kwanta  bai sake yunkurin fitowa ba sai zuwa  sanda yaji kira sallah sannan ya motsa ya shiga wanka ya fito ya sauya kaya riga dark blue da wando ligth blue ya nufi masjid bayan ya dawo a parloun kasa ya zauna ya kunna tv.."

Da misalin karfe tara na dare   ta sauko a natse cikin hadaddiyar rigar bacci wanda ta bayyana komai na jikinta   ta sameshi  yana danne danne a system dinsa ta  zauna a gefensa gabanta na faduwa   muryarta a raunane tace "ummmmm ammmmm Sai kuma tayi shiru ta kasa magana shima yana jinta yayi mata banza sake motsa lip's d'inta tayi cikin in ina "kunyi waya da mommy na nemi layinta ban samu ba "uhmmm kawai yace atakaice ya cigaba da aikinsa , can ta kirkiro murmushin dole ta sanyawa fuskarta
"yayana  ka bar aikin nan haka ka huta ya d'ago da niyyar yayi mata Banza kallo qirjinshi ya buga da matsanancin karfi sakamakon ganin Brest dint tsaye suna kallonsa yana kallonsu dogon tsaki yaja , idan ban yi aiki ba  uban me zan miki  da zakice na bar aiki? Yayi magana a zafafe cike da jin haushi "Allah ya baka hakuri ka mayar da wukar na kawo maka abinci nan ne ",?
  "Bana ci  kar kuma ki dameni plz. "dan Allah kaci wani ........
"oh my goodness Kisna kin fiyye damuwa wallahi   idan zanci zanci bana jin yunwa ne ya mike yana  kashe  system dinsa ,ya bar mata parloun shiru tayi tana zance zuci har kusan minti talatin sannan ta mike ta nufi sama koda ta shiga dakin har yayi bacci dan kwance ta hangoshi daga shi sai  boxcer da singlet yana fidda numfashi ta kai hannunta gefen kyakkywar fuskarsa tana shafawa a hankali tana lumshe idanunta a hankali taji saukar hannunsa kan hannunta ya fixgota yana ƙoƙarin bude idanunshi ......."

  Mmn sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

Free page 12

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number08059623096,
yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰

Shiru yayi yana kallonsu suna kuka zuciyarsa cike da matsanancin takaici , haka kawai tana neman d'agawa yaransa hankali a karon banza da kukanta ,qirjinsa sai faman tafasa yake , babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar yaga uwa da ya'yanta suna kuka rungume da juna wannan abu na bala'in d'aga masa hankali .. "wannan wacce irin tarbiyya ce yayi maganar a zafafe zuciyarsa na kuna "? "kin wani rungume yara kina ƙoƙarin gur'bata musu tunanin da wannan dakikancin naki "kina son nuna musu zalintarki nake saboda su tsane kou me "? yayi maganar a tsawa ce gaba-daya yaran suka sake makalewa jikinta suna kyarma
"kiyi kokarin yin duk abinda zai sa su tsane a cikin zuciyarsu wallahi kece zaki kwana a ciki dan nan kusa zan samu wasu ya'yan da zasu maye min gurbinsu aikin banza kawai komai kuka kamar wata matar mamaci ,da yarda Allah sai Allah ya maida miki mugun nufinki akanki ni bazan ga kuka a rayuwata ba ". ya k'arasa maganar tare d'aura hannunsa ɗaya akan sumar kansa dake kwance luf luf gwanin ban sha'awa kamar irin na areef da aryan ."

D'akin ya dauki shiru bata sake yunkurin yin kuka ba bare yaranta su tayata ,shima kuma bai sake cewa komai ba sai aikin jan tsakin da yake aika aika zuciyarsa na bugawa da karfi , a hankali ya runtse idanunshi da sukai jawur yana Allah wadai da irin halayyar wasu matan , ya furzar da iska sannan ya gyara kwanciyarsa cike da takaicinta yayi rigingine yana ƙara jin tsanarta a cikin zuciyarsa , ai muddin bai nika abinda tayi masa ba to bai kyautawa rayuwarsa ba, tamkar ya rako maza duniya ne , gara ya rama itama ta d'and'ani irin abinda yaji ."

Har goshin asuba kisna bata runtsa ba tana tsaye bisa kafafunta ta dukufa gurin kaiwa Allah kukanta , tasan abinda tayi masa yayi muni da yawa ,amman abinda yake mata a yanzu har duniya ta nad'e bazata taɓa mantawa ba, ta d'aga hannuwanta duka sama tana rokan Allah akan ya sanyaya zuciyarsa ,"Allah Kasanyawa Aliyu hakuri a cikin zuciyarsa , Allah kasan ina cikin tsananin damuwa akanshi , kasan yadda nake sonsa a halin yanzu karka bari zafin zuciyarsa ya rabamu alhalin ina tsananin son shi , Allah na tuba bazan sake aikata abinda nayi masa ba , Allah ka yafe min bisa kuskuren dana aikata ya Allah Aliyu bawanka ne kai kake da karfin ikon akansa ka gaugauta sanyaya zuciyarsa akaina ,Allah na rokeka da sunayenka tsarkaka ka sanyaya zuciyar aliyu yayi min afuwa Allah kasan ina son aliyu saboda kai ,Allah ka tausaya min saboda darajan fiyyayen halitta ,Allah kafi kowa sanin zuciyata nada rauni a kan bawanka Aliyu , Allah idan soyayyar da nake wa Aliyu alkhairi ne a rayuwata da addinina kasa Aliyu ya hakura ya dauki al'amarinmu da sauki idan babu alkhairi Allah ka cire min son ka raba tsakaninmu cikin sauki batare da tashin hankali ba sannan ka k'arawa mahaifiyata lafiya dan tayi namijin kokari akaina dan ganin rayuwarta ta inganta ba kowace uwa ce zatayi irin abinda mahaifiyata tayi min ba a ganiyar kuruciyata ta karashe addurta tare da haɗawa da yiwa yaranta akan Allah ya albarkaci rayuwar su sannan ta shafa addu'ar tare da shafawa akan yaranta da bacci yayi awon gaba dasu tuni ,bata tashi ba har sai data ji ana ƙoƙarin gabatar da sallar asuba sannan ta mike ta shiga bayi ta d'auro sabon alwala ta fito ta gabatar da sallah tayi azkar din safe sannan ta kwanta a kasa kusa da yaranta ta rungumesu ajikinta ..."

Washegari sai gurin karfe tara na safe ta tashi shima sautin zazzakar muryarsa ce ta dinga shiga kunnuwanta yana waya da coch dinsu , ta yunkura da kyar ta mike cikin sanyin jiki tana kallonsa suka hada ido shine yayi saurin janye kwayar idanunsa akanta yana yatsina fuska kamar yaga mugun abu , yaranta ta kamo ta soma yiwa wanka ta shiryasu cikin kananan kaya ta kai su dakin mumy sannan ta faɗa wanka ta jima acikin bayi tana saɓa jikinta da turarukan wanka masu kamshi sannan ta fito ta shirya cikin wata had'add'iyar doguwar riga wacce take da adon fulawa tun daga kasa har sama cikin kayan da mommy ta siyo mata ne jiya tayi tunanin ta saka ta gani kafin su bar kasar , ƙaramin gyale tasa ta nad'e kanta dashi kafarta na sanye da takalmi kalar kayan tayi matukar kyau kwarai babu wanda zai ganta bai sake Kallonta ba, gashi daman jikinta akwai shi da daukar kaya ,babu kayan da zata saka basu amshi jikinta ba , ta shafa hoda kadai a fuskarta dan bata damu da yin fente fenten a fuskarta ba sannan ta feshe duk ilahirin jikinta da ruwan turare .."

Aliyu dake tsaye sanye da kananan kaya wanda daka Kallesu kaga kalar kudi bama sai an faɗa maka adadin kudin kayan ba zaka fahimci iya tsadarsu ,ga tsabar kyau da kwarjini sai kace shi yayi kanshi ga siffarsa kamar dan larabawa , Allah dai yayi a kasar Nigeria za'a haifosa kuma acikin jinsin *zarma* amman idan ba faɗa maka aka yi ba bazakace asalinsa dan nigeria bane ."
kallon kasa da sama yayi mata hakan yasa tayi saurin durkushewa kasa a gabansa dan tasan ma'anar kallon cikin rawar murya tace "ina..ina kwana"? yaja dogon tsaki yana kawar da fuskarshi a ranshi yace "mai zan yi da ina kwananki "? jiki a sanyaye ta mike tana ƙoƙarin barin d'akin ba dai ta gaishesa ba kar ya amsa ita dai tayi , dan gaisuwar na cikin dokokin daya kafa mata ko ta sha mahaukacin mari , tana daf da barin d'akin tana rausaya taji sautin muryarsa mai shegen dadi da tsuma zuciya wanda tsautsayi yasa ya faɗa kunnuwansa koda kuwa bakar magana zai faɗa sai mutun yaji tasirinsa ajikinsa "tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mace mai tsananin muni irin ki ba ......"
cak ta ja ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya sannan ta kasa juyowa , sai dai take jikinta ya ɗauki rawa kamar mazari ta dinga bin jikinta da kallo gabanta na faduwa "ban taba ganin mace mara kyan fasali irinki ba yanzu ke nan har wani kyau kika yi da kike wani tafiya kina rausaya kamar wata gurguwa ..... "?

wannan karon da hanzarinta ta juyo gaba-daya ta zuba masa narkakkun idanunta tana kallonsa, ido cikin ido suke kallon juna zuciyarta na rawa cike da tsananin mamaki jin furucinsa " ya rabbi mai kuma nayi masa da safiyar nan yake aibantani haka ? ta yiwa kanta tambayar har lokacin idanunta na cikin nashi , take idanunta suka kad'a suka yi ja tsabar ɓacin rai da yake son haddasa mata . "me ke laifinna da sassafen nan da zai muzani haka wato dai Aliyu ba zai bar rayuwarta ta huta ba duk yadda zai yi ya dagula mata lissafi sai yayi daga wannan balain sai wannan
Allah ma yasa daga ita sai shi ne a dakin dan tasan ko agaban mutane haka zai mata dan ya kuntatawa rayuwarta ,bafa tsoronsa take ji ba kawai dai tana son gyara kuskurenta ne yasa take had'iye abubuwansa "
Ranta yayi bala'in 'bace akan abinda yayi mata yanzu a cikin ranta tace "lokaci ya kusa da zan taka maka burki akan abubuwan da yake mata ,a zahiri kuwa cewa tayi "wannan shine lokacin da zangargadeka matukar kana son zaman lafiya a gidan nan to ka fita hanyata kamar yadda kace na fita naka , idan ba haka ba zan rikeka a matsayin gawurtaccen makiyina da yake son kassara min rayuwa ,wai dole ne sai ka min magana ma tunda kace baka bukatar hakan a tsakaninmu " ai kace baka bukatar zama dani to ka sawwake min saboda nima yanzu ba bukatar zama nake da kai ba ka bani takardata dan Allah kaga aiki da cikawa ta k'arasa maganar tana sakar masa harara gabanta na faduwa dan karfin hali tayi kawai amman zuciyarta a matukar tsorace take da kalmar ya bata takardanta cikin sanyi jiki ta dinga daga kafafunta zuciyarta na zafi tana data sanin furta masa haka dan tasan halin zuciyarsa kadan da halinsa ya maka saki .."

Murmushin mugunta yayi dan abinda yafi bukatar gani kenan akan fuskarta damuwa da tashin hankali sannan ta bukaci rabuwa dashi da kanta kuma duk yayi nasarar haifar mata ,bai barta iya haka ba yace "ayi gaba dai zuciyata ta huta da tashi saboda ganin wannan mumnunar banzar fuskartaki mai mugun hali kawai ai nasan duk abinda kike faɗa akan kin canza karya ne dan ba zaki taɓa canzawa ba maganar zaki rikeni a matsayin gawurtaccen makiyinki ai nafi son haka , ke na ma fi makiyinki tasiri a rayuwarki idan baki manta ba ni dake makiyan juna ne baza mu taɓa sauyawa daga matakin da muke ba saki kuma tunda kin bukata sha kuruminki sa ido kiyi kallo kina zaune zai sameki saboda zama dake bashi da wani amfani dan bana sonki i really hate you ..........." abinda kunnuwanta suka jiyo mata kenan a lokacin da zata karasa ficewa daga d'akin kafafunta kawai take dagawa zuciyarta na zafi da rad'ad'i idan shi bai sonta ai ita tana son shi , dole ne sai ya furta baya sonta ko sai ya saketa ya barwa zuciyarsa mana har sanda zai aiwatar da niyyarsa akanta, Allah kaga bawanka Aliyu ko allah ka kawo min ɗauki ,kasa min dauriya amsar duk abinda zai zo daga garesa zama dashi ko rabuwa dashi "

Tsayawa tayi ta daidai natsuwarta tare da goge hawayenta sannan ta cigaba da tafiya a kan step ta hango aryan da areef suna rige rigen Isa gurin mommy gabad'aya suka faɗa kan cinyar mommy dake zaune saman doguwar kujera tana ware musu hannuwanta alamun su taho gareta Hajiya mommy ta dubi jikokinta cike da farincikin ganinsu cikin koshin lafiya, yayinda qaunarsu ke cigaba da ratsa kowani sashi na zuciyarta ,ta shafi kansu daya bayan daya tana yiwa Allah godiya daya azurta Aliyu da kisna da samun kyawawan ya'ya wanda take qauna fiyye da komai a duniya , mikewa tayi tare dasu suka isa dining table inda Samir da aunty zee ke zaune suna murmushin jin dadi ganin areef ya tashi lafiya babu wata matsala kisna ta karaso jikinta a matukar sanyaye ta durkusa har kasa tana gaishe da mommy "Ina kwana mommy .."? "Lafiya lau mamana kin tashi lafiya ya karfin jikin"?"Alhamdulillah naji sauki sosai ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi dan kwantar da hankalin mahaifiyarta , ta juya inda samir yake ta gaishe dashi da aunty zee.

aliyu ya sauko yana ciccin magani kamar wanda aka yiwa wani laifi ya gaishe da mommy cike da girmamawa ta amsa masa cikin sakin fuska ita dai tana son Aliyu arayuwarta a natse yaja kujera ya zauna kusa da Samir aunty zee ta kalleshi fuskata dauke da murmushi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login