Showing 120001 words to 123000 words out of 495987 words
Chapter 41 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
su ci ta basu ruwa ta sake kwantar dasu ta dan tsakuri sauran daya rage tana da numfashi ..."zaman me kike yi dicter? " ki tattara ki koma gurin danginki ko ki tafi gurin danginsa ko bakinsa garinsu bane ? Sala Tayi mata tambayar a jere "na soma tunanin haka zanyi duk abinda ya dace na gode sosai da kulawarki gareni bazan taba manta alkhairinki ba "babu komai kowani bawa da qaddararsa amman karki bari qaddararki ta zamo silar rasa rayuwarki sun dade suna tattaunawa akan rayuwa da yadda zata je ga danginta dan can zuciyarta tafi karkata tasan zuwa lokacin sun huce zasu iya amsarta sala ta mike ta wuce ita kuma ta sulale ta kwanta a bayan yaranta ta zagayesu a jikinta ranar dai kwana azaba tayi zuciyarta kunshe da bakinciki ."
washegari gari ya shigo gida yana taku da kyar da daga kafada wanda ya zame masa jiki wani kallon wulakanci yayi mata tana ganinsa jikinta ya kama rawa ta rakube ita da yaranta tana jiran taji abinda zai ce ,ko wace irin azabar zai sake mata ,hannu ya zira ciki aljihun wandonsa ya ciro key ya bude kofar ya shiga ya cire kayansa sannan ya fito ya shiga wanka bai ɗauki lokaci ba ya fito ya sake shiga dakin ya soma shiri yana zance zuci da mamakin karfin hali da naci irinata, dan ya dauka zai dawo ya iske ta wuce ,fitowa yayi sanye da shadda light green da hula wacce tabi da kayan jikinsa kamar wani mutumin arziki ya kalleta fuskarsa a yatsine yace " Sai ki shiga dakin ai tunda kin iya naci, na koreki kinki tafiya saboda nacin bala'i...muryarta na rawa tace " na gode ai bani da inda zani da yafi nan din ne shiyasa ka dawo kasaneni ,ni dai kayi hakuri dani ta fada tana mikewa tsaye wani haushi da bakinciki ya caki zuciyarsa a fusace yace " hakurin uwraki da ubanki zanyi , kika sake bani hakuri sai naci daurin uwarki jaka kawai Aliyu ya tsura masa ido yana kallonsa ita ma dicter shiru tayi tana kallonsa har ya gama balainsa ya sanya kai ya fita yana wani irin taku kamar dan wani shege a Nigeria nan ko dan asalin kauyen ilo ne garin da ko wutan lantarki basu dashi har wannan lokacin , yana fita ta soma taku cikin sanyi jiki sadiq ya soma shiga daki sannan ita Aliyu daya kasance karami sosai kin shiga yayi sai data sake fitowa ta daukeshi ta saba a kafadanta ta koma dakin
ta soma kokarin samawar yaranta abinda zasu ci .."
Haka dicter tayita rayuwar kunci da haroon ,kullum haroon cikin gargadi yake mata da azabtarwa iri iri , gashi Allah yayita da tsananin hakuri da biyayya komai tana yi masa wankin kayansa da guga da tsaftacce masa muhalinsa saboda tasan yana da tsananin tsafta amman har lokacin babu wani cigaba daga garesa dan halin damuwar da take ciki bai sa ya saurara mata ba duk matsalar da zata sameta ko ya'yanta babu ruwansa ,
lokacin da cikinta ya shiga wata bakwai ciwon mara yasata gaba ta rasa ganen kanta dan haka tayi tunanin zuwa gurin chairman wanda kusan yana taimaka mata a duk sanda wata matsala ta taso mata ya bata kudi taje asibiti , tana jin dumin kudi ta dawo daidai tace babu wani asibiti da zata ta koma gida ta shirya kayanta zuwa mahaifarta tana fitowa daga office din chairman bata sha wahala ba ta samu mota ta fada masa inda zai kaita kai tsaye tasha suka nufa ta shiga motar benue tun cikin mota take fargaban abinda zata tarar farinciki ko akasin haka tana sauka ta dauki drop din mota zuwa unguwar su tana kwatanta masa gidansu sunyi tafiya mai nisa sannan ya ajiyeta a inda ta kwatanta masa ,cike da sanyi jiki ta tsurawa babban din gidan nasu ido wanda kusan yafi kowani gida girma da tsaruwa acikin unguwar tura karamin get din gida tayi ta shiga hawayen na zubo mata a lokacin data tuna irin kyawawan rayuwar datai acikin gidan tare da mahaifiyarta da y'an'uwanta kafin ta tsunduma kanta cikin soyayyar haroon tana shiga parloun suka haɗu da daya daga cikin masu aikin gidansu zata fita "kai wa zan gani haka maraba da manya baki yau dicter CE a gidan nan "?
Ganin yanayin dicter yasa matar yin shiru tana kare mata kallo duk ta lalace idan ba wani kyakkywan saninn ka mata ba bazaka ganeta ba cikin Muryar kuka tace" mommy joy Ina mommy "?
"Mommy tana .......
Bata kai ga karasa maganar ba sai ga ema ya shigo ya dakatar daita yana kallon dicter a wulakance mommy joy ta dauki jakar kayanta zata shigar dashi ciki ema ya sake dakatar daita "ajiye mata jakar kayanta ki kama gabanki sannan ya sake fuskantar dicter " ke kuma me ya dawo dake gidan nan da waɗan yaran ? "dan Allah yaya kayi hakuri ka barni na rayu daku tare da yarana tayi maganar tana durkushewa a gabansa "kinsan Allah muddin kina son rayuwa damu sai kin maidasu gurin ubansu ko dangin ubansu sai ki dawo kiga yadda zan canza miki rayuwa zan miki komai zan baki kulawa fiyye da ta farkon rayuwarki ,amman idan kika nace lallai sai kin rayu da waɗan nan yaran wallahi sai dai ki mutu cikin wannan wahalar dan baki ga komai ba karki ɗauka bamu da labarin irin rayuwarki da kike muna sane ,"muddin kina son ingantaccen rayuwar ki mayar dasu ki dawo yana gama fadar haka ya nuna mata kofar fita , dicter ta fashe da wani marayan kuka haka mommy joy shi kanshi ema din hawaye ne cike da kwayar idanunsa da hanzari ta juya rike da hannu sadiq ga Aliyu goye a bayanta ga ciki tana wani irin matsanancin kuka hakan yasa hankalin mommy joy ya tashi ta dinga jin kamar ta nufi hospital din da'ake jinyar mommy ta sheida mata zuwan tillon 'yar'ta dan tasan duk saboda ita take wannan cutur ... A ranar dicter ta juya zuwa Abuja a galabaice ta shiga gida aiko da asuban fari ta haifi d'anta dan wata bakwai wannan karon sunan mahaifinta ta saka masa nanyak haka ta cigaba da rayuwa hakuri da haroon dan har bukkan yake kawo sabuwar budurwarsa Aysha da yayi duk ranar daya san zasu hadu da Aysha zai sanar ma dicter da sharadin ta gyara musu dakin kuma tayi waje da yaranta kafin aysha tazo kuma karta yarda ta bar duk abinda tasan nata ne dana yaranta babu mutsu zatayi masa abinda ya bukata ta tattara komai nata ta yiwa waje dashi ta ajiye a bayan dutse , haka tayi ta masa na tsawon lokacin ita kanta ayshar bata san yana tare da dicter ba bare tasan yana da wasu ya'yan ,Aysha na matukar burgeshi duk da bai jin zai iyabaurenta wannan kalmar kawai ya fadawa maimuna abokiyar halkallarsa ta hada shi da Aysha dan tasan ba iya burgewa kawai bane a ransa har da soyayya , ai kuwa saduwar farko yaji bazai iya rayuwa babu ita ba saboda wani yanayi daya tsinci kanshi bai taɓa jin dadin da yaji a jikinta ba itama haka taji ta dinga zuba masa ihun dadi tana kiran" babakarami zaka aureni? da yake sunan daya fada mata kenan " dan Allah ka aureni Allah bazan iya rayuwa babu kai ba haka tayita zuba masa sambatu iri iri ita kanta da fari bata so kulasa ba saboda sana'ar da yake amman tunda ta dandanashi taji bazata iya rayuwa da wani ba zata iya aurensa da business dinsa ,tayi mu'amala da maza dayawa amman babu wanda taji shi har tsakiyar kanta kamar shi ...."
******
Bayan shekara biyar
Hajiya kayi na zaune a tsakar gidanta tana ƙoƙarin d'aura sanwa taga shigowar dicter hajaran majaran rike da hannu yara biyu maza ga na uku a bayanta tana ganin yaran gabanta yayi wata irin mummunar faduwa saboda tsananin kamar da yaran suka mata da d'anta haroon barin farin wato Aliyu "sannu da zuwa, Ku karaso ciki barkan ku da zuwa ga guri ki zauna "dicter ta kwanto goyon bayanta ta sauke tana haki saboda gajiyar hanya data kwaso ta zauna tana haki, shima yaron sak haroun babu bambamci ko launin fata a tsakaninsu ta aika aka siyo mata sugar ta kawo mata ruwa mai gauraye da *komade* wanda ta zuba sugar a ciki ta mika mata sannan ta samu guri ta zauna akan tabarma kaba tare da kamo yaran ta zaunar dasu kusa daita tana shafa kansu tare basu kunu aiko tamkar suna jira suka dinga sha , a hankali dicter ta bude baki ta soma magana cikin rawar murya "Sunana Benedicter ni yar benue ce bata boyewa Hajiya kayi komai dangane da rayuwarta tare da haroon ba da irin matakin da y'an'uwanta suka ɗauka akanta har zuwa hukunci data yankewa kanta ta kawo mata yaran kuka Hajiya kayi ta fashe dashi ....."
Mmn Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
Page 21
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,
......Sun dade rungume da juna tsam suna kuka mai matukar cin rai da ban tausayi tana son ya'yanta tamkar ranta tana son y'an'uwanta da mahaifiyarta bata san wanda zata zaba ta bari ba a cikinsu ,a hankali numfashinta ya soma yin kasa ta dinga janyo sa da kyar tana fesarwa, ita kanta mommy tayi nadamar amincewa da tsarin ya'yanta data yi a tun farkon lamarin ,jin yadda numfashin dicter ke fita da kyar yasa mumy ta sausauta rungumar da tayi mata ta talla'bo bayan kanta tana Kallonta a matukar tsorace , sosai dicter ke kokuwa da numfashinta dake barazanar daukewa, take kukan momy ya soma tsayawa ta soma mata magana cikin tsananin tashin hankali tana girgizata da kiran sunanta "dicter ! dicter !! me nene ?" dan Allah ki natsu idan wani abu ya sameki bazan taba yafewa kaina ba ,ki duba rayuwar ya'yanki suna bukatarki a raye kada ki mutu kisa suyi rayuwar maraici nayi nadama abinda muka yi kiyi hakuri ta karasa maganar cikin tsananin kuka ......"
suna cikin haka momy joy mai aikinsu ta shigo d'akin saboda jin shiru yayi yawa har kusan mintuna ashiri da wani abu da madam ta shiga dakin dicter bata fito ba, idanunta na sauka akan dicter dake dafe da qirji tana jujjuya kai yayinda gabad'aya idanunta suka juye tayi saurin karasawa inda karamin fridge dinta yake ta bude ta dauko ruwa mai dan sanyi ta tsiyaya a cup ta mikawa madam "ki bata ruwa ta sha sannan mukai ta hospital a dubata , jikin momy na rawa ta amsa ta kafa cup a bakin dicter hawaye na zubo mata , da kyar ta kurbi kaɗan ta kawar da bakinta gefe tana sauke numfashi da kyar a hankali momy joy ta shiga kwantarwa momny da hankali dan ta lura tana cikin damuwa har zuciyarta ya samu natsuwa sannan suka tattara dicter zuwa asibiti domin duba lafiyarta dan yadda numfashinta keyi idan kagani sai kaji tsoro cikin gaugauwa likitoci suka rufa akanta da kyar aka samu numfashinta ya ɗan dawo daidai washegari y'an'uwanta gaba-daya suka hallara har matansu domin duba lafiyarta sai dai duk sannun da suke mata bata amsa musu ba hasalima ko kallon inda suke batayi ba fuskarta na wani bangare idanunta na tsiyayar hawaye ita kadai tasan yadda take jin kanta , satinta biyu asibiti aka sallamota ta cigaba da shan magani a gida .."
****
A can kauyen ilo kuwa
duk wata kulawar data dace hajiya kayi nayi akan yaran , tana sonsu tana ji dasu a cikin zuciyarta dan yadda take jinsu a ranta yafi yadda take jin sauran jikokinta duk abinda za'a dafa sai tambayesu abinda suke so sannan tabawa Jamila umarni , tun da dicter ta bar garin zuciyar aliyu ta kasa samun natsuwar zuciya duk da dare sai ya dauko diary data bashi ya rungume a qirjinsa yana kuka da bakinciki mahaifinsu wanda yasa kakkaifan alkamashin son zuciyarsa ya guntile masu duk wani jin dadin rayuwa ta hanyar rabasu da mahaifiyarsu farinciki su mai kaunarsu yana hawaye yana Kai karar mahaifinsu gurin Allah don ya zaluncesu ya rusa musu rayuwa ta silar abubuwa dayawa marasa dadi, ya kuntata musu ya hanasu jin dadin duniya ya azabtar dasu da yunwa da kishinruwa yanzu Kuma ya rabasu da mahaifiyarsu da suka fi so fiyye da kowa a duniya ta yaya zai iya yafe masa abinda yayi musu har abada bazai yafe masa ba zai girma ne da daukar fansa numfashi yake furzawa da karfin gaske ji yake kamar ya hadiye zuciya ya mutu wannan maseefar yayi musu yawa sadiq ya karaso inda yake ya kai hannu yana goge masa hawaye "ka daina kuka kaima da alamun baka son zaman kauyen nan kamar ni kazo mugudu kawai ai mumy tace a unguwar kankara suke a benue bazamu bata ba "bai ce masa komai ba ya juya masa baya tare da ajiye diary a karkashin pillow ya kwanta ya rungume nanyak yana cigaba da kukansa duk abinda suke akan idanun hajiya kayi bata musu magana ba ta wuce taje ta dauro alwala ta dawo a zaune ta zauna tana nafila saboda jirin dake dibanta,bayan ta gama ta dauki carbi tana tasbihi ga ubanginji tana rokon Ubangiji ya shirya mata haroon ya karkato mata da hankalinsa gida sannan allah yasa ƴaƴanta su fahimceta akan yaran tana son sheida musu amman tana jin tsoron suce bazaa amshesu ba .."
Yau tsawon satinsu uku kenan a kauyen ilo amman sadiq yaki sakin jikinsa da kowa kullum ya tashi burinsa yasan yadda zai bar garin ya koma zuwa gurin mahaifinsa ,
yayinda Aliyu burinsa ya girma ya cikawa mahaifiyarsa burinta ,ya bata kulawar data rasa agurin mahaifinsu bayan wata daya da kawo su Aliyu hajiya kayi tayi kokarin sanarwar ya'yanta maza dan su tayata shiga cikin lamarin dan rayuwar yaran ta inganta sai dai kalmar da suka faɗa mata ta bugar mata zuciya "wato babu ruwansu sannan babu hannunsu a cikin lamarin haroon bare wasu ya'yansa daya haifa a yawon duniya ,
wannan kalmar tayi matukar bakanta ran Hajiya kayi tamkar fadar mutuwa haka taji maganar a zuciyarta , duk yadda taso ta rinjayesu hakan ya faskaran sai salaha ce ta fahimceta kuma ta bata kwarin gwiwa akan ta rikesu zata dinga aiko mata da abinda Allah ya hore Mata dan kulawa da rayuwar yaran , ta kara da cewa ayi kokari a saka su a makaranta boko da islamiyya kafin ta shigo , hakan yayiwa Hajiya kayi dadi tayita saka mata albarka "shi yasa duk lalacewar ya mace wani lokacin tafi ya'ya maza tausayi da jinkai iyaye ai kuwa cikin satin aka saka su a makaranta boka da Arabic, bangaren boka basu da wata matsala tunda sun fara tun a Abuja islamic ne dai babu ..."
rashin dicter na dan lokacin nan yasa zazzaɓi mai zafi ya kama nanyak , acikin kwana biyu cakal da soma jinya yace ga garinku nan , wannan mutuwar ta taɓa zuciyar Aliyu yayi kuka sosai hankalinsa bai tashi ba sai daya ga an haka kabari an saka nanyak ciki, ranar kwana yayi zazzaɓi da firgita haka bangaren dicter jikinta yayi sanyi gabanta ya dinga faduwa zuciyarta ta dinga mata ciwo da tsinkewa ta mike tsaye tana tunani abun yi dan saisaita kanta ,momy ta shigo ta dafa kafadanta ta zauna jagwab akan gado jiki babu kwari tayi saurin kamota jikinta "take it easy dicter "mommy jikina na bani wani mummunar abu na faruwa da ya'yana "
"ba kin ce kakar yaran nada kirki ba? ta gydawa mommy Kai alamun "eh "
"to me yasa zakiyi iri wannan tunanin"? " i dont know mommy ni dai ina ji ajikina something is wrong "kiyi fatan alkhairi ne kinji, kwanta ki huta ta kwantar daita ta lullu'be mata jiki da bargo sannan ta fice daga d'akin tare da kullo mata kofar ."
Yadda dicter ta kasa runtsawa haka hajiya kayi tayi kwanan zaune tana tofa ma Aliyu addu'a ,cikin runtse ido Aliyu ya juyo ya rike hannu hajiya kayi gam cikin nasa jikinsa na sake daukar zafi ransa kamar zai bar gangar jikinsa yana kiran sunan mahaifiyarsa , sai dai cikin ikon Allah kafin wayewar gari jikinsa yayi dama ,shi kuwa sadiq kayansa ya haɗa yace bazai zauna ba tafiya zai yi ,a hankali Hajiya kayi ta riko hannunsa ,aiko ya haɗe rai ya fixge hannunsa yace "bazan zauna ba wajen babana zan koma , nanyak ya mutu ga Aliyu bashi da lafiya shima nasan mutuwa