Showing 123001 words to 126000 words out of 495987 words

Chapter 42 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

zai  yi , idan ya mutu sai  ni Allah bazan zauna ba, ganin  haka yasa Aliyu sanyawa  jikinsa kuzari haɗe da  jarumta domin  baya son rasa d'an'uwansa daya sauran masa a duniya  , kuma baya son ya koma  gurin mahaifinsu da sunan neman taimakinsa duk da bashi da tabbacin zai taimaka masa din  , da kyar Hajiya kayi  ta  samu ta shawo kanshi  yace  ya hakura wanda  a zahiri ne ya hakura amman  a badini bai hakura ba  ,dan ya rigada ya  shiryawa   barin garin ta kowani hali  bayan  sati daya da mutuwar  nanyak  aka nemi sadiq  sama ko kasa aka rasa  daga zuwa gona hankalin  Hajiya kayi ya tashi  tayita nemansa daga  karshe ta samu labarin  ya bar garin, ranar  kam tayi kuka kamar  ranta zai bar gangar jikinta  har tayi data sanin haihuwar haroon  arayuwarta ta rungume Aliyu ajikinta "Karka barni Aliyu ina tsananin sonka Karka gujeni  "zaka rayu dani muddin rai ?  "bazan gujeki ba yayi maganar muryarsa a dashe "zakayi  hakurin zama dani acikin kauyen nan da babu wuta babu network  babu jin dadin rayuwa ? "zanyi bazanje ko'ina ba zan kasance tare  dake ta sake rushewa  da kuka rayuwar yaron tamkar ba daga tsatson haroon ya fito ba kama ce kawai zai sa a dangantasu "na  gode   saboda kai muradi ne a zuciyata    zan kula da kai da rayuwarka tana kuka yana goge mata hawaye   , bayan  kwana   biyu  ta  tattara  komai ta watsar ta  maida hankalinta gurin  kula da  rayuwar Aliyu   wanda a lokacin bai  wuce shekara shida   a  duniya  ba  ,amman Allah  yayi sa da kaifin  baseera  hankali natsuwa  uwa uba ilimi ta kowani bangare  ."

********
Cikin  fushi da tashin hankali take Kallonsu daya bayan daya hankalinsu kwance suke  bawa  likita umarnin dubata ,kullum idan ta Kallesu haushinsu take ji acikin zuciyarta  batasan lokacin da zasu qaunaci ya'yanta ba , ya'yan da bata da kamarsu a duk fadin  duniyar nan ,  kullum da karyar da suke mata bayan umarni kawai zasu bata taje ta dauko ya'yanta tunda tasan inda suke , abinda ya faru ya rigada ya faru ya kamata ace komai ya wuce  dan me bazasu hakura ba ,su barta ta rungumi yaranta  , taja numfashi tana cizan lip's d'inta ta ƙara jingina bayanta da abun gado ranta na mata kuna, jira kawai take su sake cewa wani abu ta sauke musu abinda ke cikin ranta , likita ya soma ƙoƙarin daura mata drip har ya haɗa komai  tana kallon wani gefe zuciyarta na zafi  yana gama aikinsa ta fixge allura  ta duro d'aga kan gadon tana huci kamar wata zautacciya , momy dake zaune a bakin gado  ta mike jikinta  na rawa ta kai hannu zata kamota ta zame "don't don't touch me momy  ,mutuwar tsaye momy tayi tana dubanta a tsorace , dicter  ta haɗe fuska  tamau babu annuri  acikinsa  huci kawai take   kafin ta fara magana  cikin fushi da  harshen yarensu "wallahi na tsaneku gabad'aya , kuma bana sonku acikin raina ,   ina mai  tabbatar muku  sai kunyi nadama mara amfani akan abinda kuka min  ,kun nuna isarku   kun   rabani da ya'yana,kun gwamaci suyi rayuwar kauye babu wuta babu network babu komai na jin dadin rayuwa  alhalin ina raye ,babu komai ta goge hawayen daya zubo mata "  nasan inda na kaisu kuma zan koma na d'aukosu , daman nice bakwaso ba yarana ba, ku din yan'uwana ne amman   kuka nuna bakwa son ya'yana wadan da nasha wahala reininsu , muddin baku lamunce min na daukosu ba, nayi muku alkwarin duk wani abu daya danganci jin dadin duniyarku sai na rabaku dashi koda kuwa ya'yan ku ne  "

"kina hauka ne waye sa'anki anan "? " ko dan kinga ana lalla'baki ,bari kiji kije kiyi duk abinda zakiyi gidan nan ne baki isa kiyi rayuwa da wadan nan  yaran ba sai dai ki koma ki karasa rayuwarki gurin wancan dillalin koken din ....."
   Wani irin zummmmmm taji a gabad'aya ilahirin jikinta ,take zuciyarta ta soma  bugawa da sauri sauri ta dinga Kallonsu daya bayan daya tana jin maganar eze  wata iri cike da mamakin yadda suka san sa'ar uban ya'yanta  "kin ɗauka bamu san aikinsa bane  "?"ana ƙoƙarin rabaki da wahala kina tura kanki lokaci nake jira da kaina zan tama masa akamashi yaje ya karasa rayuwarsa a jail ,har yanzu babu wanda ya hanaki koma masa ga hanya nan ki ....
Tasssss tasssss eze yaji yatsun mahaifiyarsu akan fuskarsa wanda yasa take bakinsa ya mutu ya dafe daidai inda marin ya sauka  "ka min shiru ,maganar dawo da yara ake ina ruwanmu da wani sana'ar ubansu , kar na sake jin ka faɗa mata kalmar da zata d'aga mata hankali ."
Wani mummunar ajiyar zuciya  dicter  ta sauke kana ta soma motsa bakinta alamun son yin magana amman ta kasa  sai tari  ta soma yi da karfi  duk sukayi kanta suna kiran sunanta ta saidasu da hannuta tana dafe daidai saitin zuciyarta ,  suka tsaya tamkar an dasasu suna Kallonta a matukar tsorace , likita ya  bukaci su matsa  sai dai babu wanda yayi kokarin matsawa ,har sai da  suka taimaka masa  ya kwantar daita ahankali tarin ya dawo  yana fita da numfashinta ,kafin kace me ta fara aman  jini  ,nan take sukayi asibiti daita ko cikkaken awa biyu basu yi ba likitoci suka fahimci  zuciyarta ta tashi aiki, gaba-daya  hankalin likitoci ya tashi dan sun  san da wuya ta rayu sai dai suka kasa fadawa y'an'uwanta aka kwantar daita a wani kebantaccen daki aka daura mata ruwa   ."
Bayan sati daya , tana kwance  akan gadon marasa lafiya duk ta rame sai idanuwa ,ta motsa bakinta a hankali alamun magana , momy ta kawo kunnenta daidai bakinta dan bukatar jin abinda take buƙata  "momy ki jingina bayana   ina son na dan zauna  tayi  mgnr da kyar mommy ta tayar daita tasa mata pillow a bayanta  suna kallon juna "sannu ya jikin "?
"Ai naji sauki anan asibin babana ya rasu ko momy  "?Tayi  tbmyr tana huci , mommy tace "Mai Kuma ya kawo  maganar mutuwa yanzu"?
"Saboda nima mutuwa zanyi  take momy ta  rushe mata da kuka" dan Allah karki min haka, karki mutu ki barni, ta riko hannuta cikin nata  tana kuka babu inda zaki tafi ki barni muna tare sai dai ni na tafi na barki ahankali dicter  ta shiga  shakuwa babu kaukautawa  mommy ta  mike da sauri  ta kawo mata ruwa ta bata tana mata sannu ,kamar kar ta sha ruwa sai shakuwar tafi ta farko ,da sauri mommy  ta nufi kofar fita dicter  ta d'aga hannu tana kiranta  alamun ta dawo , amman ina hankalinta baya jikinta burinta kawai ta isa ga likita  tare da likita suka dawo dakin   yana Kallonta yasan  numfashinta ya dauke a gangar jikinta ta zama gawa ,  amman  sai ya kwantar daita ya fara gwaje gwaje irin nasu na likitoci  har na tsawon minti goma sannan ya bukaci mommy ta biyo bayansa ,ta biyosa tana waiwayen dicter  dake kwance..."

Duk  yadda momy  taso jin wani abu daga bakin  likita  ya kasa  yiwa mommy bayani  komai illa ya kira number ema ya sheida masa halin da ake ciki ,a matukar haukace suka karaso asibinti , gabad'aya an rasa mai rarrashin wani sannan an rasa wanda zai fada wa mahaifiyarsu sai wata doctor ce ta sanar  mata , tana gama dogon nasiha da faɗa mata abinda ya faru mommy ta zube kasa tana birgima  tana kiran  sunanta  "shikenan komai ya kare min  ema eze James kun sa na rasa tilon diyata ,ta mutu ta barni  ,na tsaneku na tsaneku bazan taba yafe muku ba, ta mike a matukar haukace ta nufi dakin da dicter  take kwance ta kwanta ajikinta tana wani irin kuka mai taba zuciya tana kiran sunanta "ki tashi karki tafi ki barni am bad mother  ,mai yasa  nayi miki  haka "?
"Mai yasa ban tsaya miki ba  tunda nice responsibilty dinki ,Mai yasa ya nemi shawarar yanuwanki a tun farko am bad mother for you   tana gama fadar haka ta had'iye  zuciya ta zube kasa  shikenan bata sake motsi ba , take su ema suka yo kanta suna girgizata "mommy! mommy !! suna kiran sunanta da karfi plz mommy wake up don't do this to us we are really sorry mommy look at me eze ya fada yana haɗe fuskarshi da nata ,"mommy plz open your eyes ya fada yana sheshekan kuka ban da sautin kukansu baka jin komai acikin dakin likitoci suka yi cirko cirko suna Kallon irin haukan dasu ema suke yi tunda suke basu taba ganin mutuwa irin wannan ba ,a rana daya awa  daya   ne tsakaninsu ,  excuse me wani likita ya fada yana kokarin dagasu  akan gawar mommy "  plz live us like this "kuyi hakuri mahaifiyarku  ta rigada ta mutu ,haɗa baki sukayi gurin kiran "mommy wake up .........kamar wasu kananan yara "shikenan mommy kin tafi ki barmu why mommy Mai yasa kika mana haka alhalin kinsan muna tsananin sonki ? "mommy you can't just live us like this  Kafin kace me asibinti ya cika da yan'uwa da abokan arziki aka  dauki gawarsu zuwa gida ,a tare  aka kai  su kabari  kasancewar dicter  na ciki   ,da mommy ce  kadai  ta mutu sai an yi bikin mutuwarta  sannan a binneta ,ga kabarin  dicter  gana mommy zagaye da fulawas  kowa ya watse aka bar ema James da eze a gaban kabarin mommy da dicter  suna kuka  cikin bacci Aliyu  ya farka da misalin karfe biyar  na yamma bunkasa an binne mahaifiyarsa daman tun safe yake jin faduwar gaba sai dai rashin son magana yasa ya kasa fadawa Hajiya kayi  yayi shiru yana jin tsananin faduwar gaba  Hajiya kayi  ta kalleshi cike da tausayawa "duk taga yayi wani  irin ,duk sanda ta ga yayi irin wannan shirun to ya tuna da mahaifiyarsa ne  "sannu muradina ka tashi ....."? dake sunan dake kiransa kenan  ya gyada mata kai kawa "tashi kaje kayi sallah kaji ka kara  sakawa ranka hakuri wata sai labari inshallahu zaka sake daura idanunka akan rashida ai kana son ganinta ? da sauri ya gyada mata kai hawaye na zubo masa . bayan gigin mutuwar ya sake su  ema suka fara tunanin  inda zasu  nemo yaran dicter  dan sai lokacin sukayi  nadama, nadama mara  amfani  dan babu wata sheidar  inda zasu samesu, dan har inda haroon yake a garin Abuja sunje sai dai an tabbatar musu da tuni ya bar garin ya koma ibadan da zama  haka suka dawo benue jiki a sanyaye  ......."

*******

sannu a hankali  rayuwar Aliyu ta cigaba   a hannu Hajiya  kayi har  ya  cike  shekara  biyu agurinta  komai nata muradi   ne , komai ta samu tace  na muradina ne   ,duk abinda taci  sai ta rage masa wanda zuwa wannan lokacin salaha tazo yafi sau uku duba mahaifiyarta tun zuwanta na farko taji Aliyu  ya shiga ranta taso tafiya dashi amman yaki yarda  saboda Allah yayi sa da gudun mutane gashi bashi da saurin sabo da mutane, kowa dari dari yake dashi sai dai bashi da tsoro kana kallonsa kasan namijin duniya ne  ,kin amincewarsa yayiwa Hajiya kayi dadi dan itama bata son yin nesa dashi yana ɗebe mata kewa ta sanyawa zuciyarta mutuwace kawai zata rabata dashi  ,a hankali  tunani haroon yasa ciwo ya kama hajiya kayi tana son sake daura idanunta akanshi kafin ta koma ga Allah tun tana kirga shekarun datayi rabonta dashi har ta daina burinta dai ta gansa kullum cikin addu'a take masa akan Allah ya juyo mata da hankalinsa amman shiru  ciwo kamar wasa sai gashi ya zama gaske sai kwantar sai an tayar hakan yasa Hajiya salaha ta  tattaro ta dawo gurin mahaifiyarta ta ɗauke sai asibitin  sir yahya dake birnin Kebbi  gwajin farko likitoci suka tabbatar da ciwon zuciya ne nan aka daurata akan maganin ya'yanta na iyakar kokarinsu  haka surukinta Alhaji realwan  na turo kudi domin lafiyarta kullum hajiya kayi sai tacewa salaha " muradi ...."
"Karki damu zaki tashi ki cigaba da rikonsh watansu daya tace ga garinku    Allah ya amshi rayuwar   hajiya kayi a hannun tilon diyarta ,mutuwar data gigita Hajiya salaha tayi kuka kamar zata bita gbdy ta dawo abar tausayi , bayan an gama zaman makoki hajiya salaha ta nuna zata wuce da Aliyu  idan zata koma Lagos amman y'an'uwanta  suka hanata , garba yace" muddin ta kuskura ta dauki yaron babu shi babu ita har duniya ta nad'e  ,mai zatai da jinin haroon  mutumin da yayi sanadiyyar rasa iyayensu ina tabbatar miki yadda haroon yake haka ya'yansa zasu kasance ".
"kada ku manta jinin dake yawo ajinin haroon shi yake yawo ajinmu ,mutuwa kuma dole ce idan kwanan mutun ya kare ina da tabbacin kwanakin iyayenmu ne suka kare ba wai haroon  ne ya kashesu ba ,dan haka  babu abinda zai hanani d'aukarsa  dan babu wanda zai rikeshi anan  daya wuce mu ,"ki daukeshi amman babu saka hannuna aciki kuma duk abinda ya biyo baya babu ruwana wallahi". "naji zan sheidawa Alhaji muddin ya yarda zan daukeshi ta juya ta kalli Aliyu dake rakube ajikin kofar  dakin yana saurarensu daya bayan daya  tace "muradin Hajiya kayi zaka bini Lagos ?yayi shiru kawai yana Kallonta cike da tausayawa ta janyo hannunsa ta zaunar dashi saman cinyarta "zaka bini ko zaka zauna gurin Jamila ya ɗan gyada mata  kansa alamun zai bita dan ya ɗan saba daita kasancewar tana zuwa gurin Hajiya kayi akai akai saɓanin fuskarsu Garba  da tun zuwansa sau  daya kawai suka kawo  ziyara "yauwa muradi ta furta tana shafa kanshi," zaka zauna gurin jamila  idan an kwana biyu zan sa azo a tafi da kai kaji yarona ya sake  gyada mata kai watanta  daya ta bar garin  da  zumar zata sa a zo a dauki Aliyu  idan mijinta ya yarda .."

Koda Hajiya salaha ta tari mijinta da batun dauko Aliyu kin yarda yayi abun yayi matukar bata mamaki ,abinda batasani ba y'an'uwanta ne suka zuga shi kar yarda a daukosa ,wannan rashin amincewarwa ya tsaya mata arai har ta dinga masa wani irin kallo saboda a lokacin tana rike da zahra mufeda yaran  d'an'uwansa da ya rasu ya bari ,bata taɓa nuna gazawarta akan yaran ba yadda take kulawa da yaranta haka take kulawa da zahra da mufids amman shi dan d'an'uwana kwaya daya zai hanata daukowa tayi kukanta ta hakura ,sai dai ta dauki alwashin zata inganta rayuwar yaron cikin wannan lokacin ta samu labarin dawowar sadiq abun yayi mata dadi sosai tace shima ya zauna gurin jamila kafin tasan abun yi ,kullum sai tayiwa mijinta naci da rokon ya amince mata ta dauko Aliyu  har tsawon shekara biyu wanda a lokaci kauyen  ilo ya samu network din glo   , kuma sai a wannan lokacin  ya amince mata   yace a tawo har da sadiq  aiko  ranar yaga abun mamaki dan  har da sadakar wake da shinkafa  tayi  tsabar murna ya dinga mamaki irin farinciki da take da irin soyayyar da takewa yaran, hatta ya'yanta sunga sauyi atare daita, batare da bata lokaci ba ta kira  Jamila tace   ta biyo mota ta  kawo sadiq da Aliyu tunda ita tasan hanya dan kusan a Lagos tayi  rabin rayuwarta da mijinta kafin ya rasu   washegari gari alhaji realwan ya shirya zuwa  kano bikin wani yan'uwansa   ,Hajiya salaha ta  shirya masa kaya har gaban motarsa ta rakosa sai data ga ya shiga  sukayi sallama direba yaja motar zuwa airport sannan ta komai ciki tana masa addu'ar ta kira number Jamila tace su shirya zata tura musu da kudin mota ranar monday tazo da sadiq da muradi . "Suna gama waya ta sanarwa sadiq take yace mata bai zuwa ko'ina shi ta bashi kudin motarsa zai koma abuja ko zai samu labarin inda mahaifinsa take ita kuma tace sai dai ya zauna amman bazata bashi sisi ba yace "to bai zuwa kuma bazai zauna a ilo ba ta kira Hajiya salaha ta sheida mata tace a bashi waya tayi masa magana yaci yaji amman tun ranar Lahadi aka nemishi aka rasa .."

********
Zaune mutane suke a acikin mota kirar bus Mai cin mutun goma shabiyar Jamila ce zaune a gidan baya da Aliyu da bai wuce shekara goma da haihuwa ba ,tayi shiru tana tare da zabga uban tagumi a tun sanda suka taso daga kauyen bagudo dan suka samu mota mai zuwa lagos direct tun taso warsu babu abinda take sai tunani a cikin zuciyarta gabad'aya tunaninta ya yafi ne akan sadiq ɗaya ce bazai biyosu ba shi neman ubansa zashi   alokaci da bai wuce shekara 11 da wani abu ba wai bata son zuwan nasa bane aa bakunta a ko'ina yana da matukar wahala ,tafiya mai tsawo motarsu tayi Amman har lokacin basu ci rabin tafiyar ba a hankali ta janyo Aliyu ta kwantar ajikinta tana shafa laulausan sumar kanshi mai kama data ainihi zarma , tana  jin Aliyu aranta   tamkar dan data haifa dan akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu ,ko kwana uku kayi da Aliyu zai shiga ranka bare shekaru masu yawa ,a hankali bacci ya dinga fixgarta dan haka ta lumshe idanunta domin ta ɗan runtsa tunda zuwa birnin iko ba yanzu ba har sai garin Allah ya waye ......"

direba yayi saurin taka burki , sakamakon katon gungume daya tarar akan hanya an gicciye shi gaba-daya mutanen dake cikin motar suka fara salati da sallami tuni masu bacci suka wastake ciki kuwa har Jamila da Aliyu ta kwakwame Aliyu ajikinta tana furta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun cikin rawar jiki tsayawar motar ke da wuya sai kuwa suka ga wasu mutane sun fito daga cikin
dajin su goma sun kewaye motar .... "

Mmn Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 20

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login