Showing 126001 words to 129000 words out of 495987 words

Chapter 43 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,



....Kuka hajiya kayi ta fashe dashi tana furta kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun tana sake maimaitawa  jikinta na wani irin rawa  , gabad'aya   tsigar jikinta suka mike tsaye kanta  kamar zai tsage gida biyu , wani ya dinga  wani irin bugawar da bata  taɓa jin irinsa ba saboda tsananin  tashin  hankali da kyar tasanyawa jikinta jarumta  tace "yanzu ina shi  baban   yake "? Ta tambayi dicter hawayen tausayinta na zubo mata dan duk rashin imaninka sai ka tausaya mata muryarta cike da tashin hankali tace "Yana  garin Abuja tare da wata yarinya   Aysha data zo daga  Lagos , gbdy   idanunsa sun rufe akanta  ba yaji baya gani sai abinda tace ni ba sonta da yake yi mata yafi damuna ba kamar yadda yaki amsar yaran ya'yan cikinsa "meye laifinsu da zai dinga nuna musu kiyayya ? "Idan ni baya sona su fa jininsa ne ta karasa maganar tana zubar da hawaye .
Hajiya kayi  tayi shiru kawai  tana  sauraronta tana  nazarinta cike da tsananin tausayawa    yayinda dicter ke kuka sosai tana tausayawa yaranta dan sune abun tausayi yanzu "Allah ya  kyauta Allah ya shirya  mana zuri'a shiri na addinin musulunci ,Allah yasa ya gane ,Allah ya  karkato min da hankalinsa zuwa gida  murmushin  takaici dicter   tayi mai idanunta na zubar hawaye  dan  tasan wannan ɗan nata da take yiwa addu'a  yayi nisan da bai jin kira, rayuwar duniya ce kawai a gabansa babu wani zancen dawowa gida dan tunda take dashi bata taɓa jin ya bukaci ganin iyayensa ko yan'uwansa ba shi dai rayuwa   .."

    Mike kafafu hajiya kayi tayi zuciyar sam babu dadi gaba-daya ta nemi natsuwarta ta rasa kawai zaune take amman ita kadai tasan Yadda take jin a zuciyarta "wai dan cikinta ya dawo haka "? Allah ya shirya ta sake furta wa a fili tana kwallawa Jamila kira "Jamila wai har yanzu bacci kike ? " Ki tashi munyi baki  kusan kira uku tayi mata tana shafa kan aliyu sannan ta amsa tare da fitowa ta bi dicter da kallo da yaran kafin daga baya tayi musu sannu ta durkusa a gaban hajiya kayi dake cigaba da shafa Aliyu tunda ta daura idanunta akan yaran taji sun shiga ranta amman soyayyar Aliyu dabam taji a zuciyarta kwatankwacin wacce takewa ubansa ne saboda shine ya dauko komai na haroon dinta babu abinda ya bari " d'aura  musu abinci  Jamila tayi magana zuciyarta cunkushe  da bakinciki saukinta  ma mijinta baya raye da tasan tashin hankali da za'a fuskanta sai yafi wannan, dan bazai yarda da yaran  ba , tunda ubansu ma ya haramta masa zuwa  garesa bare wasu ya'yansa  cikin sauri Jamila ta daura abinci dan ko ba'a fada mata su waye ba tasan suna da matsayi a gurin hajiya kayi bayan ta daura ta dawo ta tsaya tana jiran karin bayani kafin tace wani abu hajiya kayi tace "Kaita tayi wanka sannan kiyiwa yaran wanka kafin abinci ya nuna ta juya ta dauki botiki ta isa bakin rijiya ta cika botiki da ruwa ta nufi hanyar bayi "tashi rashida ki wasa ruwa kinji Allah zai kawo mana sauƙin lamarin ta mike tsaye ta bi inda Jamila ta shiga tana maganar zuci "wannan sunan ya zamo tarihi a rayuwata domin na bar muslinci har abada duk da ina tsananin son addinin musulunci amman dangina bazasu yarda ba ".

Jamila ta gama  abinci  ta zubo musu ta bar kwano  a bude da miya ta kawo gabansu inda suke  zaune akan tabarma kaba "ga abinci amman  ku bari ya  dan sha  iska kunji ta fada tana kallon fuskar  sadiq da Aliyu  gyada mata kai suka  yi  sannan ta nufi gurin randar kasa ta zuba ruwa a buta  tayi alwala ta soma ƙoƙarin  gabatar da sallah itama Hajiya kayi mikewa tayi tayi alwala
Tana yiwa haroon addu'a a zuciyarta
  bayan ta idar ta dade zaune tana addu'a da tunanin duniya   .."

Bayan sun gama cin abinci sun huta   Hajiya kayi da kanta ta sake yi musu wanka ta  sauya musu kaya  sannan  tayi musu shimfida  tare da kulla musu  gidan sauro suka kwanta  amman ita  da dicter suka  kasa kwanciya  suna zaune yayinda  hannu hajiya kayi ke rike da mafici tana su Aliyu fifita dan su samu damar runtsawa , shiru gidan baka jin motsin komai sai na tsuntsaye a hankali zuciyarta ke  aiyana mata abubuwa da yawa , da akwai  network a garin da babu abinda zai hana ta kira tillon diyarta ta sanar mata da halin da danuwanta yake ciki ,ta dinga  jin  kamar ta fice a daren  taje inda suke samu network  ta fara sheidawa yaranta maza  sai dai wani bangaren na zuciyarta na gargadinta akan aikata hakan domin komai zai iya faruwa gara  ita salaha  zata fahimceta akan mazan  dan matsalar mace sai mace ita zata kawo hanyar gyara saɓanin mazan , ranar dai bata samu isasshen bacci ba har gari Allah ya waye da safe  itace da kanta tayiwa yaran wanka dicter da Jamila nacewa ta barsu  zasu yi musu  amman sam hajiya kayi taki sosai ta dinga basu kulawa da jikinta da aljihunta har sukayi kwana biyu suka saba daita sosai tana nuna musu kauna da kulawa fiyye da tunanin mai karatu    har zuwa   lokacin babu wanda ya san da zuwan dicter   acikin ya'yanta sai Jamila hatta mutane gari basu san takamaiman abinda ya kawo dicter   ba sai dai duk wanda yaga yaran sai ya dasa ayar tambaya akansu ".

Abunka ga kauye kafin kace me tuni  an soma gutsiri  tsoma cewar haroon yayiwa yarinyar ciki shege ne bata hanyar auren ba  aka kawo wa hajiya kayi shegu yaran  da aka haifar masa wannan kalmar itace  tafi komai  konawa Hajiya kayi   rai ta dinga ji haushi mutane bisa rashin dalili   sai dai babu yadda ta iya tunda tasan gaskiya suka fada , duk wanda ya tare da maganar kuwa cewa take karya ne ya'yan sunah ne ba shegu ba "..

Ranar da  dicter ta cike sati  biyu a kauyen ilo  ta soma  shirin tafiya benue  sai dai zuciyarta tayi rauni sosai  dan haka ta sanya  yaranta gaba  dake kwance akan gadon hajiya kayi  tayi tagumi  tana Kallonsu daya bayan daya, tsawon lokaci ta dauka tana Kallonsu cike da tausayawa  sannan ta mike ta fito hannuta  rike da jakar kayanta inda ta iske  Hajiya kayi tsaye a tsakar gida  zaune akan kujera ta karasa ta durkusa a gabanta muryarta a raunane ta soma magana  "a yau zan  bar garin amman ban san me zan ce akan zaman yarana agurinki ba ,sai dai na bar komai a hannun allah da  hannunki dan nasan zakiyi abinda ya dace akansu ,a ɗan zaman da nayi dake  na fahimci yadda kike son haroon  Kuma hakan yasa kike jin qaunar yaran nan  ina da tabbacin  zaki so jininsa fiyye  dashi da kika haifa  amman duk da haka zuciyata na cike da rauni da  alhinin rabuwa da yarana  ta goge hawayen da suka gangaro bisa kuncinta sannan tasa hannu ta ciro farar envelope wanda tayi tanadinsa domin  bata  ,ta mika mata a matukar tsorace Hajiya kayi tace  "menene haka kikeyi  bazan amsa  komai daga hannunki ba  waɗan nan yaran dole na ne na dauki nauyin su, karki damu  zan kula dasu kamar yadda zan kula da kaina, nayi na wasu ma     da bansansu ba bare waɗan nan da suka kasance jinina  kuma daga dan dana fi so a rayuwata, karki wulakantani ta hanyar bani waɗan nan kudaden da babu abinda zasu min sai karin bakinciki  ".
"ba haka nake nufi ba Hajiya  na fahimci yadda kike jinsu a zuciyarki , bana  baki kudin nan dan kulawa da rayuwarsu bane , a'a  wannan kudin nasu sadiq ne saboda zasu bukace siyan sweet da wasu abubuwan yara ki siyan musu abinda suke so daga hannun mahaifiyarsu dan allah ki amsa ki ajiye musu  agurinki bani da wani abinda zan basu tayi maganar cikin zubar da hawaye ......"

"bafa zan amsa ba duk abinda suke so zan siya musu da kudina na faɗa miki zan yi musu komai muddin ina raye bai kamata ki damu ba tunda kema kinyi iyakar kokarinki akansu zai fi kyau ki ɗauki hanyar komawa saboda nisan dake tsakaninmu da inda zaki  "shikenan na gode bari na shiga na sake dubasu  ta ajiye jakarta ta bude ta dauko kyakkyawan diary dinta ta rike tana tunanin wa zata bawa acikin ya'yanta domin adanawa idan sun girma su fahimci halin rayuwar da tayi dasu a hankali ta   juya  ta soma tafiya zuciyarta na karfafa mata gwiwa akan ta bawa Aliyu har ta   koma ciki  d'akin zuciyarta na rawa da bugawa wanda zuwa lokacin tuni  sadiq ya farka yana zaune a tsakiyar gadon yana tunani  inda ta shiga ta barsu "kar dai mommy ta wuce ta bar mu anan ne  "? ya fadi a haka fili hankalinsa a tashe dan shi sam baya qaunar zaman kauyen gara Abuja sau dubu agurinsa .."shigowarta yasa shi   sauke numfashi yana dubanta, ta zauna a gefen gadon idanunta na kansa  a hankali ya sauko  daga kan gadon ya tsaya a gabanta yana yatsina fuskar   ta kamoshi  jikinta ta rungume  tsam "fatan kayi bacci mai dadi yarona "?Shiru yayi yana jin wani iri ajikinsa " mommy kamar akwai abinda kike son faɗa min tun jiya   "Yes I do my son  naso na faɗa maka tun jiya sai dai fargaban halin da zaka shiga kai da kannenka ya hanani furtawa amman yanzu ya zama dole kasani  ina son komawa gurin yan'uwana da mahaifiyata  domin karasa rayuwata   tare dasu zan yi haka ne saboda bani da wata damar data sauranmu baya ga komawa garesu tana cikin magana idanunta ya  sauka akan Aliyu  a she Shima  ya Dade da tashi miskilanci ne ya hanashi mikewa  ta kai  hannu ta riko hannunsa cikin nata  ta mikar  dashi tare da kwantar  dashi ajikinta tana shafa kwantaccen sumar kanshi mai taushi " sadiq  kaine babba ka kula da kanka da  kannenka ka dai ga irin rayuwar da mahaifinku yake yi da irin wahalar da muka sha a hannunsa, ka jajurce domin inganta rayuwarku  zan dinga kawo muku ziyara lokaci zuwa  lokaci zan so   ka karfafa zuciyarka ta bambamta data mahaifinka , zaku cigaba da rayuwa anan  tare da kakarku kuyi hakuri  da rayuwa yarana ,zan barku anan ne  ba dan bana sonku ba sai dan babu yadda zanyi  amman zuciyata na cike da matsanancin damuwa akan nisan da zanyi  daku abinda nake so  daku ku cigaba da zama  anan tare da kakarku zata kula daku zata soku fiyye da babanku  ta karasa maganar tana rungunesu ajikinta tana jin kamar numfashinta zai bar gangar jikinta "mommy ni dai gaskiya karki barni anan  gara ki maidani gurin  babana ni ina son zama tare dashi tayi shiru tare da sausauta rungumar data masu ta tsura  musu ido na wani lokaci  sannan tace "kaima Aliyu kafin son zama da babanka akan grandma "?Yayi sauri  girgiza mata kai  alamun baya  so "nafi son zama anan karki damu mommy  kiyi tafiyarki  kawai idan muka  girma zamu zo har inda  kike a kankara    ya furta muryarsa a raunane " really  my boy  zaka zo gurina "?ya gyada mata kai alamun "eh  "Idanunshi suka yi raurau alamun yana son yi kuka kawar da fuskarsa gefe yayi yana ƙoƙarin danne kuka     ta juyo da fuskar gareta "tsaya haka yarona karka boye min damuwarka  da kukanka "no mother karki damu dani I really want to you to go zan cigaba da rayuwa anan shiru tayi cike da tausaya masa dan  tasan ya faɗa ne kawai dan karfafa mata gwiwar tafiya   amman yana da kulafucinta sosai ba kamar sadiq ba wanda daman shi  tana kallon tsantsar qaunar da yakewa mahaifinsa  "ka gani ko sadiq kaninka ya fika wayo  da hankali kuyi zamanku anan kunji yarana Allah yayiwa  rayuwarku albarka karku damu zakuyi farinciki anan nima zan dawo gareku  nan bada jimawa ba da zarar na koma bakin aikina   alamura suka daidaita zan zo na maidaku inda nake   ta karasa  maganar tana fashewa  da  wani sabon  kuka, suka soma rige rigen goge mata  hawaye cikin tsananin soyayarta suna cikin wannan yanayin Hajiya kayi tayi sallama ta  shigo ta ɗauki Nuhu dake bacci ta goya a bayanta tace "tashi ga mota can zata kwantagora sai kibita  zai fi miki sauki ,babu mutsu ta mike tsaye jikinta na rawa suma jikinsu duk rawa yake ,hawaye na sake gangaro mata suka nufi waje da baya da baya ta dinga tafiya har ta bar dakin   idanunta na zubar da hawaye kewar yaranta  jikin yaran yayi mugun  sanyi barin ma Aliyu da kana kallonsa zaka fahimci irin tashin hankali da yake ciki duk da ƙarancin shekarunsa  suna kuka dicter na Kuka   har da shesheka , Hajiya kayi ta rungumesu a  jikinta tana rarrashinsu cikin harshen zarma dan tunda suka zo shi take musu yayinda mahaifiyarsu ke musu turanci , suka kamkame Hajiya kayi  suna  ganin mamansu zata shiga mota  suka zare jikinsu da sauri  suna Kallonta Aliyu kam kana kallon yadda yake janyo numfashi da ajiyar zuciya da kyar  dan har kana iya hango tashin hankalinsa a makoshinsa dake lobawa yana tashi, hawaye na gangaro masa zuciyarsa cike da bakinciki kuma tun a wannan ranar ya dasawa zuciyarsa tsananin tsanar  mahaifinsa a zuciyarsa   bancin mugun hali irin nasa da zasu  rayu tare da mahaifinyarsu koda kuwa bazasu ci bazasu sha ba kasancewarsu tare zaifi dacewa akan nesanta juna...

Dicter ta kamo hannu Aliyu ta saka diary aciki "kayi masa adani tamkar yadda kasan zaka adana mamanka duk runtsi Karka yi kuskuren rabuwa dashi domin shine rayuwar mahaifiyarka tana gama fadar haka ta juya ta shiga mota bayan ta zauna ta waigo tana kallon Aliyu dake zubar da hawaye ta daga masa hannu " gud bye  ta furta masa a hankali  "mommy zanyi kewarki sai dai  zan yi kokarin  ganin na girma da burin daukar miki fansar abinda mahaifinmu yayi miki kinyi hakuri matuka, kinyi komai dan ki rayu tare damu amman mahaifinmu yaki baki wannan  dama "karka damu yarona just take care of yourself  wasu zafafan  hawaye suka gangaro mata ka girma da zuciya mai kyau da ƙoƙarin inganta rayuwarku  kai da yanuwanka kada kazama loser  irin mahaifinka I will try mommy  karki damu zan zame miki yadda kike buri tana hawaye tana d'aga masu hannu suma suna d'aga mata hannu a hankali motar ta soma tafiya suka biyo motar da gudu suna kuka ta juyo tana Kallonsu tana sheshekar kuka "bazan taba yafe maka ba haroon tunda kayi sanadin rabani da farincikina  tana kuka tana   tsine masa ,na dinga tsine maka kenan a dukkanin shafukan rayuwarka nadama da danasani zaka yisa a lokacin da nadamar bashi da amfani , sai rayuwarka ta kaskanta a duniya sai kaga kudi kace kashi da yarda Allah sai kazama abun tausayi a idanun duniya  har ta isa benue hawaye bai daina zuba daga idanunta ba tana shiga gidansu da mahaifiyarta ta soma cin karo a parloun zaune tana ganinta ta mike jikin ta na rawa ta rungumota jikinta tare da zaunar daita "daman zan sake ganinki dicter?" A she idanuna zasu sake ganin sanyin idaniyanta ? Ina yaranki suke ? kuka take sosai a jikin mahaifiyarta batare da bata amsa ba "taso muje ciki diyata mai ya faru da dake haka ina yaranki suke ta sake jeho mata tambayar zaunar daita tayi a bakin gado har lokacin kukanta yaki tsayawa "hankalin mumy ya tashi " ki faɗa min idan wani abu ya samesu ne ......"?Cike da Muryar kuka tace babu abinda ya samesu na maidasu gurin dangin ubansu na dawo gareku kamar yadda kuka bukata naunayen ajiyar zuciya mommy ta sauke ta sake rungumeta duk da bata ji dadin hakan ba ,cikin kankanin lokaci y'an'uwanta suka samu labari ta maida yaran sunyi murna kamar waɗan da akayiwa albishir da rabin duniya washegari gari aka gyara mata d'akinta komai sabo aka saka mata ema ya amshi takardunta "kina son cigaba da aiki a inda kika fara ko a canza miki "?
"Duk yadda kukayi ta fada zuciyarta na tsinkewa cike da jin haushinsu a ranta dan duk abinda zasuyi mata ba zai saka zuciyarta farinciki ba kuma baya gabanta kuma bazai burgeta ba ."

******

Tunda dicter ta komai gidansu bata samu kwanciyar hankalin da take bukata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login