Showing 270001 words to 273000 words out of 495987 words

Chapter 91 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

bayan bayanin malamin bai baku wani abu kunci ba "? "babu idan mun taba yi kinsan zan faɗa miki  ",to kun taba  shan jinin juna  ? Kisna tayi shiru tana tunani  dan tasan sun taɓa sha  "kun taba sha ko ? Kisna ta gyada mata alamun" eh "subuhanallahi  shiyasa kuka kasa rabuwa da juna wallahi " dan Allah  aunty afra ki taimaka min na auri musa sannan ki taimaka kije min gidansu ki duba min shi wannan azalumin  yayi masa dukan mutuwa ko  ina ruwansa da rayuwata ?

"Abinda Aliyu yayi masa daidai ne baki ga har kalazir musa ya watsawa mumy ba ke yanzu zaki  iya auran  mutumin da ya iya watsawa mahaifiyarki kalanzir har yana cewa a bashi a shana suka jiyo Muryar mufeeda  a bayansu ."Wallahi ban taba jin na tsani wani halitta a rayuwata ba kamar yadda na tsani ke da wannan yaron ,ke ko mu da ba mumy ce ta kawo mu duniya ba bazamu iya ganinta cikin damuwa ba bare ke wallahi ki guji fushin mahaifiyarki idan nan gaba duniya ta juya miki baya Allah yasa muna raye mu karar da abinda kika shuka da karanshin shekarunki yar banza yarinya kawai mara imani ta k'arasa maganar tana barin dakin ...

Kisna ta rushe da kuka "kowa ya tsaneni a gidan nan ,me yasa bazu fahimceni ba?  "Karki  damu ki kwantar da hankalinki zan  san abunyi afra na gama fadar haka  ta mike ta bar dakin tare da kullewa kamar yadda suka iske ta kaiwa mumy key ta nufi bangarenta a lokacin  ya badamasi na zaune akan kujera ya daura kafafunsa akan center table yana tunanin matsalar kisna da taki ci taki cinyewa , Afra ta karasa  shigowa  ta zauna  "baby Ina son magana mai mahimmanci  da kai ya waigo  ya dubeta tare da cewa "uhmmm ina jinki "daman akan maganar kisna ne da yaron nan ,yadda kuka ɗauki lamarin yarinyar nan ya wuce haka, mai zai hana ku hakura ku barta tayi soyayyarta da  yaron nan ya badamasi karkata kai yana Kallonta cike da mamaki jin maganarta "yadda kuke ganin aibunsa ita fa bata ganin hasalima bata ganin makusansa ku barta tayi soyayyarta har sanda zasu auri juna  idan Allah ya kaddaro  hakan shi  fa so babu ruwansa da wani kudi ko galihu ko yare ko addini  ko kankata tunda ta soma magana yaji wani abu ya tokare masa makoshi , ya jima yana mamakinta kafin daga baya ya soma magana cikin fushi "ke yanzu ina ruwanki  da matsalar gidanmu ? "Idan dai wannan ne gudumuwarki garemu to mun yafe dan Allah ki adana shawararki   ko zai miki amfani a wani guri  amman agurinmu bashi da wani amfani ,
kuma karki sake zuwa min da makamanciyar wannan  maganar   idan ke baki da hankali mu muna dashi mu rasa wanda zamu dauki kanwamrmu mu  bawa aure  sai wannan tantiri kuma dan shaye shaye wallahi gara ta mutu mu binne gawarta akan mu barta ta auri  yaron nan ,karma kiyi kuskuren faɗar wannan shawara taki a gaban Samir ko Aliyu Dan zasu miki abinda bakiyi expecting ba ,ya mike ya shige daki ya barta sake da baki  tana kallon kofar daya shiga " a she akwai sauran kallo a gidan nan  kenan tunda bazaku dauki shawara  ba ,kuma  kuna tare da aiki dan yanzu kuka fara ganin bala'in , ni  meye nawa daga bada shawara za'a nemi cinyeni  ? Kowa yaji da damuwarsa ni tawa damuwar ma ta isheni ta mike ta shige d'akinta ."

******

A daren wata ranar talata bayan dady ya idar da Sallah isha'i yana zaune yana addu'a kuka ya tsarkeshi ya kasa ci-gaba da addu'a yana cikin wannan halin aka turo kofar dakinsa aka shigo muradi ne a gaba sai Samir dady yayi hanzarin tashi zaune yana kokarin mayar da kukansa ciki tare da sanya hannu yana goge wanda ya bata masa fuska cikin dabara wai dan karsu gane amman ina tuni muradi ya fahimci kuka yake dan suna hada ido dashi sai jikinsa yayi sanyi kuzarin jikinsa ya sake yin kasa ya tsani yaga dady ko mumy suna zubar da hawaye akan matsalar kisna cikin tsanye jiki ya koma ya jingina bayansa da bangon dakin yana ma dady kallon tausayawa cikin tsananin damuwa Samir yace "plz dady me yasa kake hasarar hawayenka dan Allah ka bar komai a hannunmu zamu yi iyakar kokarinmu cikin kakalo murmushin dole dady ya fito muradi yana cewa "zo nan dana kai kuma wa ya fada maka kuka nake yi ?muradi ya karaso ya kai hannu a idanun dady yana goge masa guntun hawaye da bai rigada ya goge ba tare da cewa ",ga hawaye nan a idanunka sannan idanunka sunyi ja dan Allah dady kuyi hakuri wallahi kullum cikin tunanin mafuta nake akan matsalar nan banaso wani abu ya taba lafiyarku akan wannan matsalar Samir ya ja doguwar ya zauna suka tasa dady gaba suna kwantar masa da hankali dady ya sake kurawa yaransa ido da suka dawo kalar damuwa adalilin nashi damuwar "na fada muku ba kuka nake ba ......"


Manage not edit 👏🏼


Mmm Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
  CUTAR DA KAI
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 39

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.

......Idon   muradi  ya cicciko  da ruwan hawayen  tausayin  dady  saboda ganin  yadda  dady  yayi  shiru  tare da  tsura  musu   idanu  wanda yake nuni daya  cikin  tsanani damuwa  sai dai  yayi   dabara  ya  mayar  dasu  yana  cewa "ka   sani   dady   rayuwa na  tafe   ne  da  jarabawa kala kala  kuma  hakan  ba  yana  nufin  Allah  ya  manta  da  kai  ba  ko baya  sonka  bane   sai  Allah  na  sonka  ma sannan   zai   jarabeka  sannan  cikar  imaninka  zai   cika,  kowane  mumini ya   yarda   da qaddara  mai kyau da akasinsa   sannan   dady  zababbun mutane   ake  jarraba  kada  ka sanyawa  zuciyarka  damuwa  da  yin  Allah   damuwar   da  zai taba imaninka   kayi  hakuri inshallahu Allah  ba  zai bar  rayuwarta  haka ba muddin   muna duniya  baza  mu bari ka  cigaba da  kuka  akanta ba, ita kanta   nan  gaba zatayi ingantacciyar  rayuwa  a duniyarta  da izinin Ubangiji   amman  halin  da kuke   jefa  kanku kai da mumy  a sanadiyyarta   yana bala'i d'aga   hankalina   dana  Samir  ka taimakemu  dady   ka cire damuwar nan   koda   ba duka  ba  kaci  abinci  domin  ka samu  karfin jikin da zaka yi  addu'ar  nemammata  shiriya a gurin Allah  dady   ya daure  zuciyarsa   cikin  jinjinawa d'ansa   muradi  wanda samun  d'a  irinsa ke da matukar  wahala a wannan  lokacin  sai an tona  ma kafin a samu ,yana  matukar  son shi   gashi  dai  shi din daga  wani  tsatso ya fito wanda  har  lokacin  babu  tabbaci  akan mahaifiyarsa   sannan babu  nagartaccen  uba na  gari  sai shi daya dogara   dashi  wannan shine  matacce   ya  fitar da  rayayye   ina  ma  zai  amshi  auren kisna a wannan halin  da suke ciki  wallahi da babu abinda   zai  hana  bai aura  masa ita da  karancin  shekarunta dan yasan  shine   mutumin  da  zai  kula daita da rayuwarta   sannan zai   sota da irin  tawayarta    da lalurarta na rashin  jin  magana ,sai  dai  ina   kowani  rai yana  son  abu  mai kyau ko ɗan  iska  yana  son  natsatse   ba  dan iska dan'uwansa ba    kar  ta zo tana  bashi  ciwo   kai  , a hankali ya dinga  tunanin wanda  zai bawa auren kisna  ko  a cikin danginsa  ne , zai nemi alfarma   agurin ahlinsa su rufawa juna  asiri  sosai  dady yayi zurfi  cikin  tunani kafin daga bisani sautin muryar muradi ta dawo dashi  "Plz  dady   ka   daina   dogon tunani  haka  zai  iya  shafar lafiyarka "inshallahu  na  daina  d'ana   daga  yau  zan rage  muradi  yaji  dadi  sosai har  da murmushi  yace "na gode  dady sai ya janyo  kular abincin da'aka  kawo  masa mai cike  da lafiyayen abinci ya  bude cike da girmamawa  "Bismillah dady  ka daure kaci abinci  a hankali  shi da samir  suka  dinga lallaba  dady  har yaci abinci  yana ci yana kallonsu  tare da alfahari dasu ..."

Da  misalin  karfe  goma na daren ranar  afra na kwance   akan  makeken  royal bed dinta    ita kadai kasancewar  ya  badamasi na gurin aiki bai dawo ba sai zuwa shadaya , gabad'aya  ta  nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar  zuciyarta zai buga akan tsananin tunanin muradi juya kai kawai  take zuciyarta na sake harzuka  kamar ta daura hannu aka ta saka kuka ko taji sauƙin zafin da take mata
ta  tashi  ta zauna ta janyo  pillow  ta rungume a  qirjinta tana jin tamkar shi ne a qirjinta  tana cigabanani  da nazarin hanyar da  zata  shawo  kan muradi  cikin sauki batare daya bata matsala ba  sannu a  hankali  ta  yarda da  wasu  daga cikin shawarwarin  da  zuciyarta ta bata dan haka   a hankali ta  mike  ta  zira  silipas   dinta  ta fito cikin  sand'a ta shiga parlour'n mumy taci  sa'ar babu kowa sai karar tv dake aiki  dan haka ta sanyawa jikinta kuzari da jarumta  tayi hanyar step  ta karasa  jikin kofar dakinsu har zata yi knowcking  sai ta fasa  ta murda handle   din   kofar  ta shiga ta maida kofar  ta rufe har da  murda  key bata iske  kowa a parlour'n   ba dan haka ta kutsa  cikin uwar daka anan ta hango shi  kwance  tayi shiru na yan mintina   tana  kallonsa  kwance  sanye da farar  singlet  da farin wando iya  cinyarsa   kallon  kuralla  take masa kamar  zata  cinyesa  shi  kuwa gogan  da  bai san da shigowarta  ba sai  faman  aikin shafa qirjinsa yake yana lissafin  shafukan  rayuwarsa  data gabata  tamkar a mafarki  ya ganta tsaye  tana kallonsa ya zabura ya mike zaune  gabansa na wani irin faduwa "Me ya kuma  ya kawoki dakin nan maza  maza  ki kama hanya ki fita tun ban miki rashin mutunci ba kina son ki sani cikin bala'i ko me kuke nufi dani  ?"na rokeki  karki   yi sanadin da zamu samu matsala da dan'uwana  "I don't  care about that da ku samu matsala da karku samu wannan ba damuwar  afra bace damuwar afra ta samu gurbi a zuciyar Ali saboda soyayyar Ali ta rigada tayiwa  rayuwarta kamun kazar kuku idan babu  shi bazata iya cigaba da  rayuwa ba  "ai kuwa sai dai ki kare rayuwarki  a haka dan har abada nayi miki  nisa  ke ko matan duniya kaf sun  kare sauran ke afra  wallahil-azim  bazan  yi rayuwa  dake ba "ni  kuma gashi burina mu rayu tare ba har ma na haifa maka kyawawan baby's masu  matukar kama da kai ta  kara taku biyu zuwa inda  yake  batare da wani tsoro ko fargaba abinda zai faru ba  suna fuskantar  juna "ina sonka gadanga dan  nasan  you so different  daga cikin  tarin mazan duniya kana da kamalawa  da kamewa forget all the  ..... "Yayi  saurin katseta yana ja baya   saboda  kusancinsu yayi yawa dan har yana iya xukar numfashinta  a hankali ya  furta "azubillahi mina sheidanir  raji  saurin zaro ido waje  tayi "ni kakewa uziyya ?"tayi  maganar cikin tsananin fushi  tana nuna  qirjinta "fiyye da haka ma zanyi saboda  kin zama sheidaniya "tunda kace haka kuwa tabbas zan  tabbatar maka  da hasashenka wait lemme prove  it to you unexpected yaji  ta zubo  jikinsa  gabad'aya  ta rungumeshi  tana kokarin hade bakinsu guri daya yayinda  hannunta daya ke   daidai  gefen fuskarshi dake kwance  da  kwantaccen   suma sai sheki suke zubawa saboda gyara  saurin  kawar da bakinsa yayi yana  zaro  idanunsa  cike da matsacinan mamakinta  bai dauka isksncinta ya girmama  haka ba a hankali ta soma shafa  gefen  fuskarshi  tana tura masa brest   dinta   cikin  zafin nama ya hankadata   tayi  wani irin  juyi tayi baya  taga  taga  sannan ta tsaya bisa kafafunta  tana kamkame jikinta guri daya  idanunsa da suka sauya kala yake kallonta dasu  tana son ta sake matsowa garesa sai dai hakan ya faskara saboda tsoron daya ziyarceta,   numfasawa  yayi  cikin tsananin fushi ya nuna mata kofar fita  daga dakin batare  da yace  uffan ba dan ko yace zai yi magana bazai iya ba saboda zuciyarsa tazo wuya  ita kuwa afra tana  nan tsaye kamkame da jikinta tamkar gunki tana kallonsa tamkar mutum mutumi haka ta koma saboda tsananin tashin hankali kusan minti goma daya ɗauka yana nuna mata kofar fita sai dai ita din ta kasa kwakkwaran motsi wani irin ajiyar zuciya take sauke tana jin duniyar tayi mata zafi dame yake son taji da  shi  son dake azabtar daita ko kuma da wulakacinsa suna nan tsaye suka ji ana buga kofar dakin da  karfi  shiru dukkaninsu  sukayi kafin daga baya muradi ya kewayeta ya fito zuwa falon inda  Samir ke  sake kwankwasa kofar  yana cewa "muradi ka bude min  kofa me kake yi ne  ka kulle kofa ?  Yayi shiru haɗe da juyowa zai koma dakin sukayi karo da afra yayi saurin  ja  baya  yana kakkabe jikinsa da hannu muryarsa a fusace yace "sai ki san yadda zakiyi da kanki dan duk abinda kike nufina dashi da yarda Allah kanki zai koma bai yi shiru ba ta soma magana cikin sanyi murya ta yadda daga ita sai shi zasu ji  "bana  nufunka da komai Aliyu  sai alkhairi ka yarda dani sannan ka yarda zaka aureni  na kashe aurena ko kuma muyi soyayya  "wannan ne kuma bazaki  taba samu ba har duniya ta nade ko kinga nayi miki kama da irin wadan nan  yan iskan mutane  ?"tun wuri ki san  yadda zaki yi ki bar dakina   tun baki jefa kanki cikin matsala ba "I don't  care about that matsala  ko wani ya  ganni anan zai barni ya wuce babu inda zani ta karasa maganar tana sake jin wata irin zafafan soyayyarsa na taso mata tun daga cikin kasan zuciyarta tana jin kanta in har babu shi a rayuwarta tabbas mutuwa zatayi a hankali ya juya ya fara tafiya cikin zafin nama  domin  komawa  cikin dakin tamkar bashi da laka dan ya lura afra nemanshi  take da bala'i  yayinda Samir  ke cigaba da buga kofar ya zube  akan katifa idanunsa na ganin duhu  babu abinda zuciyarsa take sai faman  bugawa baya son wani tashin hankali a rayuwarsa a bar da yadda rayuwarsa ke tattare da cuwuka kala kala  har kusan shabiyun dare yana kwance  bai sanda  afra ta bar d'akin ba  da shigowar Samir   tun daga lokacin  muddin yasan shi kadai ne a dakin  zai  kulle ...."

******
Kullum   kisna  bata  da wani  aiki  sai na  tunani   yadda   zatayi  ta fito daga   d'akin   ta bar rayuwar   gidansu gaba-daya   ta  huta da takura
a  wani  shigowa  da ya badamasi   yayi  dakin ne  yace   suje  asibiti a duba  lafiyarta  saboda  ramarta  tayi  yawa  gashi duk abinda taci sai ta  amayar   da kyar  ta mike  tsaye  ta zira hijab dinta  ta   soma d'aga kafafunta   iska na dibarta  saboda   rashin kuzari   a bakin motarsa yace  ta  tsaya saboda ganin baba mai gadi zaune    ya shiga  bangaren mumy ya  sheida  mata , tayi masa  addu'a muradi dake zaune kusa daita  gaishesa yace  "yaya bari na mike  muje tare   "mumy tace "a'a  ka zauna ga breakfast  za'a kawo maka  bai  so karyawa mumy gwiwa ba  amman dole  ya bata hakuri dan sam hankalinsa bai kwanta  ba  dan yasan ya badamasi da sakaci za'a iya neman kisna  a rasa  muryarsa  a sarke yace "mumy  kiyi idan na dawo naci  nafi son nabisu Kinga idan ya gama daita  sai  mu dawo  tare ko a motar haya ne  basu tsaya  bata lokaci ba suka fito tare ya badamasi na gaba  muradi yana  biye dashi cikin jc  wando da riga  yellow mai  ratsin baki   Suna  fitowa  falo  ya bawa  masu aiki umarnin gyara dakin da kisna take  killace  sannan suka sa  kai  suka   fice tana nan tsaye a jikin motar rungume da hannuwanta kallo daya tayi musu ta dauke kanta tana tsinewa muradi dan babu ranar da bata tsine masa akan abinda yayi wa musa  wanda har lokacin bata san a wani matsayi  yake ciki ba yana raye ne ko ya mutu ya badamasi ya danna key din dake rike a  hannunsa sannan ya bude mazaunin direba ya shiga shiru tayi ta cigaba da tsayuwa har sai da yayi mata  magana a fusace "ki shiga mana kin wani tsaya dan rainin hankali kina kallon mutane jiki a sanyaye ta bude gidan baya ta shiga ta zauna tana daddaure fuska tare da shan kamshi  sannan ta  kawar da fuskarta gefe tana kallon glass din motar  ko shigarta mota  bai sa ya badamasi ya daina zazzaga mata ruwan  maseefa ba  kasa muradi yayi da murya yana cewa "haba ya badamasi ka bita a hankali  dan Allah ku daina nuna tsanarta hakan zai sake tunzura zuciyarta "zuciyartata ta dade bata tunzura ba itace zata kare rayuwarta cikin  wahala  har  suka karasa asibitin bata kalli inda suke ba haka zalika ya badamasi bai daina magana  mai kamanceceniya da nasiha  ba  ."
   
    bincike  farko ya  badamasi ya tabbatar  da  lafiyar kisna  lau tsabar  damuwa ce kawai tayi mata yawa da rashin cin abinci   tana  zaune akan daya daga cikin kujerun dake office din  yayinda muradi ke zaune  akan gadon duba marasa lafiya  rike da waya  yana danne danne wanda zaka ɗauka  wani abu mai mahimmanci  yake nan kuwa game yake bugawa sai dai gabad'aya hankalinsa na kan kisna duk motsinta yana hankalce  dashi  wanda zaka dauka sonta yake  dan a fili yake nuna kulawarsa gareta,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login