Showing 171001 words to 174000 words out of 495987 words

Chapter 58 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

sai hakuri naga wata kamar nayi miki kanwa daita , kawar da maganarsa tayi ta hanyar cewa "dady dan Allah na tambayeka wata magana mana ".?
ya gyada mata kai "wai irin son da nake maka kana yi min kwatankwacinsa iri sa kuwa ?"
ya zabga mata harara sannan yace "bana miki kwantakwacinsa zan aureki har mu kai tsawon wannan shekaru ko kin mata irin wahalar dana sha kafin na samu aurenki? " ko dan kinga ina cewa zan miki kishiya shine zaki yi wani tunani ?"
"Ina dai zance kishiya ne a cikin barkwanci ,duk da an san aure nufi ne na Allah idan Allah yayi dake kadai zan zauna har kashen rayuwata haka zan mutu da mata daya, idan kuma da rabon zan kara zan kara
ke irin wannan kwalisan da kike min da kulawar da kike bani ina zai bar ni na ga wata nace ina so ? idan na shigo bani da damar sake lekawa ko'ina, amman dai zaki sani ne allah dai ya kai damo ga harawa yarinyar karama sa'ar su mufeeda zan dauko nayi wasan sallah daita ".mummy ta kasa cewa komai sai murmushi take dan tasan wasa yake a ranta take aiyana irin soyayyar da dady yake mata ita tasan biyayyar da take masa ko yayi aure bai zama lalle ya samu ba ,cikin kwantar da murya tace "wallahi irin son da nake maka araina ko nace a zuciyata ya wuce misaltuwa, ina mai alfahari da kai a rayuwata ," nima ina alfahari dake kuma babu wata mace da zata sha gabanki, kina da kyau uwar marayu ga ladabi da biyayya kwaliya da kamshi dukan ba kya tsallakesu, shi yasa nake kara sonki Allah ya dangwamar damu cikin farinciki har karshen rayuwarmu a natse take bashi abinci har ta gama ta janyo kular farfesu kifi daya sha kayan hadi ta zuba a farantin tangaran yaci suna ta hira har ya gama can ya d'ago ya kalli agogon bango dake manne da parlour'n karfe goma daidai ya mike ya fita zuwa gurin baba Mai gadi ."bayan wasu mintina ya dawo parlour'n ya isketa tayi shiru tana jiran dawowarsa cikin kwantacciyar murya tace "ka dawo nima na gaji muje mu kwanta nan suka tashi suka nufi daki suka kwanta cikin aminci da nuna kulawa ga junansu .."

Daren ranar kasa runtsawa muradi yayi duk inda ya juya tunani kashi da kashi ya addabeshi , tashi yayi ya mike yaje ya dauko kundin tarihin mahaifiyarsa ya dawo ya zauna akan kujera mai zaman mutun daya karo na farko da yayi tunanin dubawa a tun sanda ya dawo hannunsa ya soma buɗe shafin farko mai dauke da kyakkyawan rubutun mahaifiyarsa a hankali ya dinga bin rubutun yana karanta rayuwar jin dadin da mahaifiyarsa ta gudanar tare da ahlinta har zuwa kan had'uwarta da mahaifinsu da irin rayuwar da sukayi cikin kankanin lokaci kwakwaluwarsa ta soma yamutsewa babu abinda yake ambata a cikin ranshi sai kalmar" Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un gumi ya haɗa sharkaf manya lamura guda biyu suka shiga yawo a cikin kwakwaluwarsa kuma kowanne yana bukatar nazari sosai yana matukar bukatar sake ganin mahaifiyarsa da bukatar sanin yadda zai yi da afra wacce take kokarin zame masa karfe kafa da yiwa rayuwarsa karan tsaye ,gaba-daya ta gama yad'awa kowa a school da unguwa matsayin rayuwarsa a gidan duk hanyar da zata aibantashi tasani wanda ya rasa dalinta na yin haka amman duk laifin waye ? Sannan kuma aikin waye ? ya shiga tambayar brain dinsa "duk laifin azzalumi mahaifinsa ne daya tsaya ya rungumi rayuwarsu da wata killa yanzu suna tare da mahaifiyarsu cikin soyayya da farinciki da shi kansa bai danganta kanshi da kalmar shege ba bare ta samu damar musguna masa cikin kankanin lokaci idanunsa suka kada suka yi ja ya dinga huci kamar kumurcin maciji wani bala'in tausayin mahaifiyarsa ya mamayeshi "me ye laifinta da yan'uwanta suka mata haka ? "Ko yanzu a wani hali take ciki ? "me yasa suka aikata mata abinda suka mata ? Yana son sani inda take da halin da take ciki Muradi ya rushe da wani irin kuka dan a ganinsa shine ya kamacesa " Allah sarki mamana ya furta a fili "kin tsinci kanki cikin matsalar rayuwa ne a dalilin azzalumi mahaifinmu "shi kuwa me zai yi dashi a rayuwa har kullum adduarsa Allah ya haɗa shi da mummunar bala'in da zai kawo kanshi garesu shi kuma a lokacin ne zai tabbatar masa da bashi da wasu ya'ya a duniya, sosai yayi nisa cikin kuka yana tunani "me yasa kake masa mugun fatan ? wani ɓangare na zuciyarsa ya tambayesa "shine mutumin da zai sadaka da inda mahaifiyarka take domin shi yasan inda suka dauko rayuwarsu "no no bazan bukaci komai daga garesa ba zan nemeta da kaina idan lokaci yayi bana neman taimakonsa ya mike a fusace yana yarfe hannu tamkar wanda yaji ciwo kafin daga baya ya soma Zariya a dakin duk runtsi duk wuya bazan bukaceka ba nasan duk inda mahaifiyata take hankalinta na kanmu ba karamin dalili ne ya riketa na tsawon shekaru batare da nemi inda muke ba "ya Allah ka tsare min rayuwarta da lafiya a duk inda take kasa ta dawo garemu muna tsananin bukatarta a hankali ya tsurawa diary din hannunsa rinannnun idanunsa wadan da suke shatatar da hawaye gani yake kamar fuskarta zata bayyana ajikin bangon diary ransa gurin baccinsa ya koma ya kwanta rungume diary ....."

Bayan kwana biyu

da wuri mumy ta tashi ta nufi kitchen domin haɗawa dady da yaranta breakfast shi kuma dady ya shiga wanka ta shirya dinnig table ita da kisna tana wasa da dariya da tsalle tsalle,dayan bayan daya yaran suka dinga shigowa sanye da uniform ajikinsu suna durkusa wa har kasa domin gaishe da mummy a daidai lokacin da dady ya fito cikin manya kaya shadda fara sol da babbar riga da hula kalar kayan kasancewar ranar juma'a ce , nan suka juya zuwa gurinsa har kasa suka durkusa kan muradi na kasa ya gaishe dashi cikin sakin fuska ya dinga amsa musu tare da saka musu albarka yayinda kisna ta makale ajikinsa tace "dady ina kwana dady yace "lafiya lau sarkin rigima "me ka siyo min jiya daka dawo"? "na siyo miki fura "to ai Ni bana son fura nafi son sweet "ai itama furar dana siya miki tana mota na manta daita "muradi ungo key kaje ka daukowa iya rigimar nan fura ya amshi key kansa na kasa cike da girmamawa ya fice ta kalli dady tace "idan ya dauko bazan ba yajita amman yayi kamar bai ji ba har muradi yaje ya d'auko ya dawo ya mikawa Kisna taki amsa tare da turo baki tasa hannu ta buge goron fura tana furta "bana sha tunda ya taɓa haushi ya kama mumy ta kai hannu zata ɗauketa da mari muradi ya ɗauketa cak ya dagata sama "mumy wannan daga hannu kamar zaki mari babba mamanki ce fa ?" Wallahi idan kana biyewa Kisna zan bata maka rai ,muradi zan ajiye matsayinka a gefe naci mutuncinka fa "kiyi hakuri afuwa mumy "ni ka saukeni banaso ta soma mutsu mutsun sauka ajikinsa aiko Samir da madu suka kama masa da dariya tare da cewa "Allah shi kara ai maganin mai tausayi irinka kenan da kabari an nada mata duka da yanzu ta shiga hankalinta "bazan bari a daki Hajiya kayi ba yayi maganar yana sauketa "ai ba asalin ita bace suna ci dan haka duk tayi ba daidai ba sai an hukuntata dady ma dungure Kisna kai yayi "idan kina yiwa muradi haka zan daina siyo miki komai har suka karasa breakfast dady fada yake yiwa Kisna yayinda afra dan haushi kasa cin abinci tayi ta tsani ana nuna wa muradi kulawa ."

"aliyu dauko min takalmina ka goge min cewar dady har Aliyu ya mike da sauri mummy tace "yi zamanka muradi na goge masa , dady yace " Allah yayi miki albarka taje ta d'auko ta ajiye masa takalmin kusa da ƙafafunsa , a hankali yayi magana a daidai kunnenta "duk wani launi na soyayya kin iya kama namiji dashi salaha ". tayi dariya batare da tace koma ba saboda idanun yara, amman a ranta cewa tayi ai mata ne ke janyowa kansu kishiya , idan mace zata kama mijinta ai babu zance kishiya ,Amman sai kaga amare acikin gidansu kamar wasu jakuna wata ma sai ta kwana biyu jikinta bai ga ruwa ba kayan da kaganta dashi yau gobe shi zaka ganta dashi ,idan kuma ta dade da aure sai ta bari yaya su hanata yiwa miji kwaliya da kulawa da lamirinsa, ta kalli kyakkyawar fuskarsa "dady tashi muje na rakaka dan tasan idan tayi wasa zai bata lokaci , ya mike suka jero "ka ta sani gaba baka son zuwa kasuwa ko ?
"au korata ma kike yi "haba Ni na isa idan kuma zama zakayi muje sitroom nan idanu yara na kanmu "bari na wuce yau juma'a kuraren lokacin ne da wuri zan dawo na soma shirin barin kasar gaba-daya ki huta
Tayi murmushin gefen baki suka ci-gaba da tafiya tana rike da jakarsa da wayoyinsa , ta rakashi har bakin motarsa ya shiga direbansa ya karaso da sauri ya gaisheta cike da girmamawa suka bar gidan ,ita kuma ta dawo ciki dan ta sallame yaranta ,bayan ta sallemusu ta sake kintsa ko'ina ta dafa musu taliya ta zuba a kula sannan ta shige d'akinta ta yi wanka ta kwanta dan ta huta .

*******

Washegarin ranar asabar tun karfe tara muradi da Samir suka shirya zuwa gurin wasan kwallo ,koda suka isa abokansu gaba-daya sun hallara kusan su kadai ake jira ,suna gama k'arasowa kowanensu ya sha ruwa kadan kadan sannan suka fara gaisawa a tsakaninsu suna hirar yadda wasan zai kasance "karka damu jahid yau mune zamuyi nasara inji cewar habib shi dai muradi yana tsaye rungume da hannuwansa a qirji batare da yace komai ba har sanda aka tara su gabadaya acikinsu aka zabi leder guda biyu muradi da Samir domin duk sunfi sauran kwarewa agurin iya buga kwallo aka ajiye takalmi a tsakiya "muradi ina kake so "? Cochi ya tamabaye muradi yana kallonsa cike da farinciki muradi ya nuna inda yake so shima Samir ya nuna inda muradi ya nuna ,ya jefa takalman guda biyu sama suka dawo kasa daya ya kifi daya ya bude wanda ya bude shine na muradi Dan haka muradi ne ya dauki bangaren dama ,daman kuma koda yaushe nan yake ɗauka cochi ya fara cirowa muradi mutanensa ya bar wasu a waje haka ya dinga jerasu har aka fara wasa karon farko muradi ya lashe ,aka cigaba da wasa wasa muradi da members dinsa suka lashe su Samir kamar koda yaushe ,cike da fara suke gaisawa a tsakaninsu muradi ya rungume Samir ajikinsa "kafa yi kokari sosai kawai dai kasan aliyun naka ne sai hankali shima murmushi yayi yana shafa bayansa a hankali ya zare jikinsa jahid ya bashi hannnu "gaskiya ka buga kwallo yau sosai sai dai ban ji dadi yadda kasa min kafa ba "karka ji dadi bayan ka cinyemu da me kake son naji ai ina sane nasa maka kafa jahid ya fada yana dariya suka fara saka kayansu habib yace "ai next time mune zamu cinyeku "."Ku shirya da kyau kafin ku fito Aliyu ya fada yana takunsa cikin isa da izza ."

Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 25
~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.

Tsuke   karamin   bakinta tayi  tana  kallonsa ,  ganin  yaki  ɗauke  idanunsa  akanta  yasa  ta ajiye ice cream   din  dake rike  a  hannunta   tasa  masa kukan  shagwa'ba  ,a rud'e  ya   kamo  tafin  hannunta cikin nashi yana   murzawa a hankali  yace "menene  my  queen "? "Me  ya saki kuka "?"Ba   kai  bane  kake kallona   nifa  bana  son  yawon  kallo ......."
dariya  ya badamasi  yake  tayi   a  cikin   zuciyarsa  a  tun  sanda ta motsa  karamin  bakinta dan  yasan muddin  yayi a fili zai ballowa kansa ruwa  dan sake birkice masa zatayi  "my  eshat kin  cika  shagwa'ba  da yawa   ban  da abunki  meye  abun  kuka  akan na  kalleki  bayan nan gaba  kaɗan  ma zaki za.. ....
Saurin   katse abinda yake son fada yayi  cikin tsarkewar  murya ," kallo ma  tayi  masa  kuka  ina ga  ya  fadi  abinda ke ransa  ,ai sai ihu kenan zata  saka  da  kururuwa neman  ɗauki , ya cigaba da  murza  yatsun hannunta yana kallonta  "kaga  ya  badamasi banason  abinda  kake min  ta zare hannunta cikin  nashi  tana sake rushewa  da  wani sabon  kuka "

"ya Salam  meye kuma abun  kuka anan daga taɓa  hannu,"ni ka daina ummana  tace kada na yarda na bari maza suna taɓa  min hannu , idan ba haka ba   zanyi ciki   gashi  ni  bana son  nayi ciki  ina  yar yarinyata " da  kuka  ta karasa maganar.."
  kuka  take  sosai kamar wacce  ake   zarar  ranta  ganin  haka  yasa hankalinsa  ya  tashi matuka  "kinga nifa  ba  wani abu zan miki  ba  wasa nake miki , kuma  rikon hannunki   da nayi   bazai  sa  kiyi  ciki ba oya kiyi  shiru  karbi  wannan , wani  kyawawan hankchif   fari  sol ya mika  mata  yana sake  tsareta da idanunsa  "plz wipe  ur tears my queen  I don't  want  to see ur tears  Karki min hasarar  hawaye ..."
Shiru  tayi  tana sauraronsa  dan  bata  da   niyyar  amsa hankchif din , ganin haka yasa  ya aje mata akan  cinyarta  yana  rarrashinta "kiyi shiru ki  goge hawayenki  kukan ya isa haka  bazan sake ta'baki ba  shikenan ".Cikin  sheshekan  kuka tace  "Allah ya badamasi bana  son ana taɓani  "to naji na daina  sarkin rigima  da shagwa'ba dauki  ice cream din ki  sha".murmushi  ta sakar masa  yayinda take kokarin  share hawayenta  "shiru yayi  yana  Kallonta  kasa kasa yana jin yadda zuciyarsa ke sake narkewa akanta  saboda kyawun  data sake yi masa  a lokacin da  take  kuka , a hankali yace  "kinga  kyan da kika qara kuwa lokacin da kike kuka?  "ni ka daina ganin  kyauna  banaso  tayi  magana tana turo masa karamin  bakinta   saurin   zaro   ido yayi waje  "ai  kuwa baki isa ba  yarinya ya furta acikin zuciyarsa tare da   gyara  zamansa   "kallo kam  yanzu  na fara  afra  har zuwa lokacin da zan mallakeki ,"kana magana ne "?Ta tambaye sa tana shan ice cream  ya girgiza mata kai alamun "a'a"har  ta  gama  shan ice cream  din yana kallonta yana  zolayarta  , wani abun  tayi  dariya,  wani ta  saka  masa kukan shagwa'ba  har  karfe shida  ta buga  suna tare sannan ya jata  zuwa inda  su  aunty ummi    Zahra, mufida  madu da Samir suke  daukar  hoto  rungume da kisna da tuni  tayi  bacci a kafad'an aunty ummi    "  idan kun gama  muje ko "?

"Mun   gama " gabad'aya  suka haɗa baki   "kun gama a ina to ni ban gama wallahi   afra   ta faɗa  tana  turo karamin  bakinta  gaba duk suka zuba  mata 

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login