Showing 87001 words to 90000 words out of 495987 words
Chapter 30 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
kuma tace "to tare da bin umarninsa daman yaso ya barta akan katifa dan yasan abinda ta tsana kenan kwanciyar kasa amman tunda ta tashi dan son jin gulma bazata koma saman gadon ba ,ta kasan idanunshi yake Kallonta kwance ranta a 'bace tana mutsumutsu da jikinta ya cigaba da aikinsa yana waya da nawal .."
******
Washegari
da safe tun karfe biyar ta tashi a barci duk da cewar bata samu isasshen barcin kirki ba saboda tunanin Aliyu da kwanciyar kasa da tayi , ta shiga Kitchen ta haɗa musu break fast, wata irin doguwar mika Aliyu yayi hade da salati yana gyara zaman jijiyarsa data mikewa sambal a hankali ya mike zaune yana yaye bargon daya lullu'ba dashi yayi hamma tare da runtse idanunsa yasa hannunsa a baki yana buɗe idanunshi aiko suka sauka akan calander ganin mark ajiki yayi mamaki, ya sauko yana taku a hankali ya tsaya gaban calander rike da kugunsa "waye yayi mark ajiki ya tambayi kanshi "waye zai yi banda wannan wawiyar yarinya wai ita nan tayi abin kirki shine har da rubutawa bayan totaly zero ce, abincin da mommy ce ta dafa kuma tasan dole zanci amman da yake dakikiyace tun ba'a aje ko'ina ta zuba min ruwa ajiki garin rawan kai yaja tsaki tare da ɗaukar biro yayi Cancel din mark din datayi ya shiga wanka .
Bayan ta gama hada breakfast ta dawo dakin domin gyarawa taci Sa'a yana bayi cikin sauri ta soma gyarawa ko'ina ya dawo tsab ta feshe dakin da turaren roomfreshiner da turarenta na jiki tazo bude wordrobe d'inta taga anyi cancel mark din ɗaya tayi jiya ta tsurawa calander ido ita dai tasan mark tayi ba Cancel ba tayi shiru tana daga kwayar idanunta sama alamun tunani "babu wanda zai yi wannan aiki sai ya Aliyu ta fada a ranta, tana cikin tunani ya fito jikinsa daure white towel yana goge jikinsa da karami ya kalleta tsaye a gaban calander ya dauke kanshi yana tabe baki , ta numfasa ta karaso gabansa ta tsaya muryarta a shagwa'be "me yasa ka goge min Please ?
"me kikayi da kwakwaluwarki ta fada shirme bakiyi abun arziki ba dan haka no need of mark ki dai yi wani abu amman na jiya da kikayi zero ne ya karasa maganar yana bude roban man shafawarsa ya soma shafawa "amman ni a ganina nayi kokari "
"agurin kenan ba , dan ki yaba da kanki yasa kikace a baki dama ? ta girgiza kai ya wuceta ya bude bangaren kayansa ya dauko deep blue t shirt da wonda baki ya shiga bayi tabi shi da ido kawai ,ya saka ya fito ya dauki cumb ya gyara suman kansa duk tana tsaye tana kallonsa komai a natse yaje cike da tsafta ,Yana gama shirinsa ya fita ya bar mata dakin babu yadda ta iya ta shiga bayi dan yin wanka ..."
aunty zee ta janyo daya daga cikin akwatinan mommy dake cike da tsaraba ta dubi kisna data tafka uban tagumi tayi murmushi "to ranki shi dade ki tashi ki dauki wancan akwati mukai parloun Kinga gobe ba sai mun tsaya bata lokaci ba ,kisna da idanunwanta suka yi jawur tana duba agogon dake daure da hannuta "ina jin kamar mommy ta cigaba da kasancewa damu "kin jiki da wata magana ta cigaba da zama mijinta fa? Kinga my friend idan zaki koyi rayuwa gidan miji ke kadai ki koya basu dade da saukowa ba direban nawal ya karaso mai gadi ya kwankwasa kofa aunty zee ta bashi umarnin shigowa ya fada mata anyi bako ta mike ta fita ko cikakken minti biyu bata yi ba ta dawo hannunta rike da wata ƙatuwar jaka Kisna ta bita da kallo "sakon nawal ne ba tace komai ba ta runtse idanunta ita kuma tayi sama domin sanarwa mumy .."
Washegari gari
mommy na taku a hankali Aliyu na bayanta rungume da aryan Samir na rungume da areef suka fice gabad'ayansu tunda daman a shirye suke ,suka dunguma zuwa filin jirgi a lokacin sauran minti talatin jirgin ya daga kisna ta dukar da kanta wai bata son ganin tafiyar mommy dan ba karamin so takewa mahaifiyarta ba, gashi bata san sanda zasu sake ganin juna ba,lokaci daya nawal da nasir da safy suka karaso nawal cikin fararen kaya komai fari ta saka hatta agogo da takalmi farare ne ta durkusa har kasa ta gaisheta da mommy "Ina kwana mommy ,mommy tayi saurin Kai hannu ta kamo kafad'unta "maza tashi karki bata kayanki ta mike ta koma kusa da Aliyu dake rike da waya ta gaisheshi tare da nasir da Samir ..
Mommy ta Mike a lokacin da zasu shiga jirgi aunty zeey ma ta mike ta rungume mommy" Allah ya tsare ya kai ku lafiya "ameen diyata Allah yayi muku albarka kuyita hakuri da juna kunji , ganin kisna taki d'agowa yasa mommy ta karaso inda take ta d'agota ta rungumeta "haba mamana meye haka kamar bazamu sake had'uwa ba hawayen idanunta da take kokarin maidawa suka silalo saman kuncinta tace" zanyi missing dinki mommy Ina Jin kamar karki tafi ki barni itama mommy hawaye take "na fiki shiga damuwa mamana Amman duka sauran wata nawa ne zaki zo bikin muradi tayi saurin runtse idaunshi tana jin zafi acikin ranta "nasan yadda kike ji mamana amman ki kara hakuri kiyi kokarin shawo kanshi kafin wata biyar din dana baku .."
A hankali mommy ta zareta saboda har mutane sun fara shiga jirgin aliyu na sauke aryan ya kwaso da gudu ya rungume Kisna shima areef dake rike hannu nawal mutsu mutsun sauka yake ta sauke shi ya karaso ya rungume kisna, ta rungumesu gaba-daya tana kissing dinsu tana zubar da hawaye nawal ta karaso inda suke "mai yasa kike kuka haka kamar bazaku sake haduwa ba ? zaki sa yara nan kuka fa .....shiru Kisna tayi batare da tace mata komai ba dan duk abinda zata faɗa baganewa zatai ba tunda bata san ya ake daukar cikin ba bare tasan mahimmanci ya'ya ga rayuwar iyaye ...."
Aliyu ya kalleta ya kawar da kanshi yana jan tsaki yace "kukan munafurci kawai "ya kukan munafurci tana kukan zata yi kewar ya'yanta kace munafurci "? Nasir ya fada yana jan tsaki "Ai nasan yanzu ka zama ɗan yankinta dole komai tayi bazaka ga laifinta ba "kai wallahi wani irin mutun ne to nayi yakinta sai kayi abinda zakayi ..da kyar mommy ta bambare yaran daga jikin kisna dan cewa sukayi bazasu bi mommy ba shi kansa Aliyu babu yadda zai yi ne amman da bazai bari a tafi dasu ba ,mommy ta sake kallon nawal "to nawal sai mun hadu a naija ko"?
"Sure ta fada tana gyada mata kai cike da girmamawa, mommy ta juya zuciyarta cike da kewar ya'yanta suna tsaye jirgi ya lula sararin samaniya suna binshi da kallo kisna ta share hawayen fuskarta ta juya da sauri ta faɗa mota zuciyarta na bugawa sosai sai yanzu take kara jin soyayyar mahaifiyarta "lallai qaunarsu acikin jini juna take itama mommy hawaye take goge wa a zaunen da take acikin jirgi ..."
Nawal ta matso kusa da Aliyu tana jujjuya masa jiki hannuta rike da jaka tana sakar masa murmushin "nur zan wuce gida muje ka rakani na shiga mota ko "ta fadi haka ne dan tasan halinsa zai iya barinta agurin ya kama gabansa "okay muje ko suka jera a tare suna magana kasa kasa a natse kisna ta d'ago idanunta karaf ya sauka akansu sunawa juna murmushi take qirjinta ya shiga luguden bugawa "yaushe ne zata samu irin wannan damar da nawal ta samu a zuciyar mijinta "?
"Ka yafe min mijina nayi kewar komai daya danganceka tana kallonsa ya bude ma nawal bayan motarta ta shiga ta zauna tana sake sakar masa murmushi "ko me yake ta fada mata haka yasa take ta faman murmushi "?ta tambayi kanta har sanda ya maida murfin kofar motar ya rufe direbanta yaja idanunta na kansu .."
Ko daya dawo gurin Samir bai gurin da gira ya tambayi nasir inda Samir yake shima da gira ya amsa masa alamar ya wuce ya kai hannu ya doki kadan nasir "kai fa nasir wani lokacin dan iska mutun ne ," yan iska dai taya zaka min tambaya da gira "?"Kaga muje har ya juya nasir ya kira sunansa ya juyo ya tsaya tare da zuba hannunwansa ciki aljihun wandonsa "ya'akayi Sarkin matsala"?
"Ai kai ne sarkin matsala wallahi daman akan yarinyar nan ce "wace yarinya kenan "?ya tambaye shi ,kisna mana dan Allah ka rarrashita idan kunje gida karka sa yarinyar mutane a gaba da bala'i bayan zuciyarta na cike da kewar mahaifiyarta da ya'yanta "kasan Allah bazan rarrasheta ba Allah yasa tayi ta kuka har ranar da zasu sake haduwa babu ruwana .
Nasir yace "dan iska kana wani nunawa kamar baka sonta bayan nasan kana bala'in sonta kamar ka mutu "na taɓa faɗa maka da bakina ina sonta "?Nasir yayi shiru yana mamakin hali irin na abokinsa "kayi shiru na taɓa faɗa maka ina sonta ko ka taba ganin wata alamar data nuna ina sonta "? "Baka sonta ya'akayi har ka mata ciki ? "Wannan tsautsayi da rabo ne ya bashi amsa yana ƙoƙarin juyawa nasir ya dakatar dashi " zaka san tsautsayi ne sai randa ka tsinci zuciyarka dumu dumu ta kamu da matsanacin soyyarta"babu wannan ranar nasir ba kuma na fatan zuwan wannan ranar a rayuwata, nawal kawai ta isheni rayuwa kasan wani abun farinciki "? Nasir ya girgiza masa kai "mommy ta bamu gud five month mu dawo daidai tamkar sauran ma'arata idan bamu dawo ba zata dauki mataki ka tayani addu'a Allah yasa mu cigaba a haka nasan karshe hukunci rabuwa ne zai biyo baya na huta da jaraba .."
zaro ido waje nasir yayi tare da cewa "ba ameen ba dan iskan Allah yasa wani tsautsayin ya sake shiga tsakani mu sake samun yan shida dan da alamun spam din abokina baya bada kwai daya "ba ameen ba dan iska kawai mai mugun baki yana gama fadar haka ya juya escort d'insa suka zagaye motar da yake kokarin shiga kowannensu na rige rigen buɗe masa kofar gidan baya inda kisna da safy suke zaune tana rarrashinta , ko kallon inda take zaune bai yi ba,
Ya juyar da idanunshi yana kallon wani bangaren , ganin tsayuwarsa yasa safy tayi ma Kisna sallama ta fito ya shiga direbansa yaja motar
*******
Har suka karaso haraban gidan bai waigo ya kalleta ba direba na gama parking escort dinsa suka fito daga cikin nasu motar suka bude masa ya fito yana ciccin magani sannan ya soma daga zara zaran yatsun kafafunsa cikin isa da takama ,a hankali ta yunkura ta fito jiki a sanyayye ta shiga ciki , tun byn dawowar su Daga airport Aliyu ya shiga part dinsa ya kwanta bai sake yunkurin fitowa ba sai zuwa sanda yaji kira sallah sannan ya motsa ya shiga wanka ya fito ya sauya kaya riga dark blue da wando ligth blue ya nufi masjid bayan ya dawo a parloun kasa ya zauna ya kunna tv.."
Da misalin karfe tara na dare ta sauko a natse cikin hadaddiyar rigar bacci wanda ta bayyana komai na jikinta ta sameshi yana danne danne a system dinsa ta zauna a gefensa gabanta na faduwa muryarta a raunane tace "ummmmm ammmmm Sai kuma tayi shiru ta kasa magana shima yana jinta yayi mata banza sake motsa lip's d'inta tayi cikin in ina "kunyi waya da mommy na nemi layinta ban samu ba "uhmmm kawai yace atakaice ya cigaba da aikinsa , can ta kirkiro murmushin dole ta sanyawa fuskarta
"yayana ka bar aikin nan haka ka huta ya d'ago da niyyar yayi mata Banza kallo qirjinshi ya buga da matsanancin karfi sakamakon ganin Brest dint tsaye suna kallonsa yana kallonsu dogon tsaki yaja , idan ban yi aiki ba uban me zan miki da zakice na bar aiki? Yayi magana a zafafe cike da jin haushi "Allah ya baka hakuri ka mayar da wukar na kawo maka abinci nan ne ",?
"Bana ci kar kuma ki dameni plz. "dan Allah kaci wani ........
"oh my goodness Kisna kin fiyye damuwa wallahi idan zanci zanci bana jin yunwa ne ya mike yana kashe system dinsa ,ya bar mata parloun shiru tayi tana zance zuci har kusan minti talatin sannan ta mike ta nufi sama koda ta shiga dakin har yayi bacci dan kwance ta hangoshi daga shi sai boxcer da singlet yana fidda numfashi ta kai hannunta gefen kyakkywar fuskarsa tana shafawa a hankali tana lumshe idanunta a hankali taji saukar hannunsa kan hannunta ya fixgota yana ƙoƙarin bude idanunshi ......."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Second to the last free page 15
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰
........ Saurin maida idanunshi yayi ya runtse gam saboda jin saukar tsayayyun dukiyar fulaninta dake cike bammmm , yayinda ita kuma tayi saurin ɗauke numfashinta cikin tsananin firgita da tsinkewar zuciya mai tattare da tsananin tsoro, qirjinta sai faman bugawa yake da matsanancin karfi kamar zai fito daga qirjinta gabadaya ta kasa kwakkwaran motsi a kwance da take a faffad'an qirjinshi jikinta sai kyarma yake gaba-daya ta sadaukar jira kawai take yaji saukar duka ta ko'ina ajikinta ....."
ajiyar zuciya Aliyu ya sauke tare da sake runtse idanunshi yana jin wani irin yanayi a sansar jikinsa har sai da yayi daya sanin fixgota jikinsa , gaba-daya tsigar jikinsa sun mike tsaye , ji yake kamar ya hau sarrafa albarkatun qirjinta da yake jin duminsu a qirjinshi amman jin kai da isa tattare da miskilanci ba zai barsa ya iya murza brest dinta ba ,dan a gurinsa ci baya ne gara ya danne ya hakura har zuwa sanda nawal zata zo gidansa "."
a hankali ta fuskanceshi
tana kallon kyakkyawar fuskarsa mai cike da annuri da tsantsar kyau taga idanunsa a runtse numafsshinsa na sauka a hankali alamun ya koma bacci ta lumshe idanunta sannan tayi control din jikinta tare da daidaita natsuwarta ta daure ta cije lip's dinta da karfi ta soma kokarin tashi daga jikinsa wanda zuwa lokacin tunin hawayen tausayin kanta ya fara gangaro mata hankalinta bai kwanta ba sai da taji ta d'auke hannunsa ajikinta ya cigaba da sauke numfashi sannan ta sauke wani wahalallen numfashi tana cigaba da kallonsa , wani iri ta dinga a gaba-daya ilahirin jikinta kamar ana jonata da wutar lantarki , yayinda kowani part na jikinta ke sake bud'ewa soyayyarsa na sake gudana a cikinta , gabad'aya wani irin son shi da fellings dinsa ke d'awainiyya da ruhinta da gangar jikinta ,wani irin sanyi ta dinga ji yana ratsata tun daga tsakiyar kanta har zuwa kasanta ,ta tasa bayan hannunta ta goge hawayenta tana jin digar sanyi ruwan sha'awa na diga a pent d'inta bayan kamar minti goma ya juya ya kwanta ruf da ciki yana cigaba da sauke numfashi , zara zaran yatsun hannunta ta d'aura a gadon bayansa tana shafawa a hankali tana lumshe idanuwanta tana jin wani irin sanyin dadi na sake ratsa sansar jikinta da zuciyarta, rayuwar hakuri ta rigada ta aureta tunda zuciyarta ta kamo da tsananin son mutumin da bai kaunarta bai sonta sannan baya kaunar ya bude idanunshi ya ganta a rayuwarsa, "amman ai kece kika jawowa kanki komai zuciyarta ta aiko mata da wannan tambayar "tabbas na tafkawa kaina kuskure da babban hasara dan gara ace duk abinda na mallaka zan rasa dana rasa Aliyu yanzu a rayuwarta , garzon namiji, jarumi wajen iya sarrafa mace damka daya idan yayiwa mutun dole