Showing 219001 words to 222000 words out of 495987 words
Chapter 74 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
har cikin dare tunaninsa ya tsananta a zuciyarta ta kasa runtsawa ,idan ta runtsa idanunta shi take gani ,ta tashi zaune ta zubawa celling dakinsu Ido tana lissafi ta yaya ita yar shekara goma zuwa sha daya a duniya zata damu kanta akan dan shekara shabiyar ? ",ita dashi duk kallon yara take musu dan yanayin jikinsa ma bazaka taɓa cewa ya girmeta ba zaka ɗauka sa'anin juna ne .
abu kamar wasa har gari Allah ya waye musa da kisna basu samu isasshen bacci ba , mikewa tayi ta shiga bayi tayi wanka da alwala tayi sallah bata tsaya cin abinci ba ta nufi dakin momy tayi sallama tare da tsayawa a bakin kofar domin jiran umarni daga mumy ,mumy ta bata umarnin shigowa , ta shigo cikin filin dakin bakinta dauke da sallama tana lumlumshe idanunta saboda rashin wadataccen bacci da bata samu ba, muryarta cike da shagwa'ba tace" mumy kudin school "yau wata rana mamana anyi abun arziki za'a tafi school da wuri kuma batare da anyi tsokanor gado ba ".? kisna ta yatsina fuska batare da tace komai ba, mumy ta shafa kanta cike da tsananin qaunar diyarta wacce kallo ɗaya tayi mata ta fahimci kamar tana cikin damuwa "har kin karya ne ?" Kisna ta daga mata kai alamun "eh "Meke damunki mamana naga idanunki sun yi wani iri ko bakya jin dadi ne ?"Lafiyata lau mumy "Are You sure ? ta sake gyada mata kai , mumy ta janyo jakarta ta ciro 200 ta mika mata dan kaidar abinda take bata kenan idan ta karya ,idan suka makara har 500 tana basu ita da zainab ,kisna ta amsa tayi mata sallama ta fito zuwa haraban gidan tana ihun kiran direbansu , shi kanshi idi direba sai da yayi mamaki ganinta a daidai wannan lokaci saboda kullum shine ke jiranta wani lokaci ma har sai yaje ya sauke zainab ya dawo bata gama shirinta ba ,hatta Principal yasan da zamanta gurin latti bata taɓa shiga school 7:30 dot ba , kullum sai an kusan gama assembly zata shiga school , bai ce daita uffan ba ya soma ƙoƙarin juya kan mota a daidai lokacin da zainab ta fito rataye da jaka a bayanta ta tsaya kusa daita "ya'akayi autan mumy kece yau da wuri haka lallai za'a yi ruwa ? murmushi gefen baki kisna tayi sannan ta bude gidan bayan ta shiga ta zauna itama zainba ta shiga suka bar gidan ,yau ma kamar jiya a bakin get ta iskeshi yana rungume da hannuwansa duka a kirji yana ganinta ya sauke naunauyen ajiyar zuciya idanunsa na kanta har ta wuce shi bai ce umh ba bare uhmmm haka itama illa qirjinta da ke wani irin bugawa da karfi .."
******
Abun duniya ya taru ya damu zuciyar Afra sam ta rasa gane kanta , kullum kokari take ta tayakice soyayyar muradi a zuciyarta abun yaci tura a yanzu tafi kowa matsuwa Ali ya dawo gida sabanin da data fi kowa damuwar ya bar gida ya tafi koma ina ne sai gashi ya tafi sai dai ya tafi da rayuwarta da dukkanin farincikinta ne ,yau kimanin shekaru uku kenan da barinsa kasar kuma har lokacin basu waiwayo Nigeria ba ,a yadda take ji a bakin ya badamasi sunce sai sun haɗa digree dinsu na farko zasu dawo wannan maganar ba karamin daga mata hankali yayi ba kullum da tunaninsa take kwanta take wuni jikinta yayi bala'in sanyi ,idan kuwa ta runtse idanunta babu abinda take hangowa sai kyakkyawar fuskarsa mai ɗauke da miskilanci mai nuni da babu ruwansa da duk wani halitta dake cikin duniya ,ta tuna yadda yake haɗe rai a duk sanda ya ganta ,wani irin bugu zuciyarta ke yi akanshi hankalinta gabad'aya yana gurinsa ,shi kansa ya badamasi ya rasa gane inda hankalinta da natsuwarta take dan kulawar da take bashi ma ta zubar gaba-daya ta dawo shiru shiru ,idan kisna tana zagin muradi yanzu bata tsoma baki haka zata gama zaginsa ta wuce bazatace mata uffan ba tambayar duniya mumy da dady har ma da mahaifinta sun mata sai dai amsa daya take bawa Kowa babu komai gaba-daya ta kauracewa shimfidar mijinta ada ma can bata wani jin dadin auratayya dashi bare yanzu da zuciyarta ke shawagi a kasar cairo babu abinda take son da kwadayin gani kamar Ali gadanga so take ta sake daura kwayar idanunta akanshi koda kuwa zai mata kallon kaskanci daya saba mata ne ..."
******
akwai mata dayawa acikin school din dinsu Kisna sai dai lokacin kankani kisna ta shafe farinjinin waɗan da suke takama da kyau da ilimi a matakinsu na yan aji daya daga js 1 a, js 1 b, har zuwa c kisna ta zarcesu a komai , kowani matashi mai ji da kansa in ya motsa kisna zai kawowa hari saboda ita din mutunce wacce bazaka taɓa gajiya da Kallonta ba ,duk abinda zaka kalla a jikin diyaace ya burgeka kisna tana dashi cikar qirji ne kawai basu gama bayyana a jikinta ba ,
kasancewar brest d'inta irin mai gindin tasan nan ne ba suka dauko alamar fitowa , mata ma y'an'uwanta satar Kallonta suke ballantana namiji hakan kuma ya samo asali ne saboda tsananin kyaun da take dashi da jin kai mai tattare da miskilanci ,zai wahala ka ganta tana hayaniya ko yawon murmushi ,da yar uwarta mace ma bata yi ballantana namiji ko tsokanarta ta rage iya gida take yin kayanta ,tun shigowarta makaranta samarin da suka isa yammata na rubibin su so su su kuma kisna suke so, sai dai babu wanda ta yarda ta kula acikinsu ,
hakan yasa ko fita break ta daina yi saboda duk ranar data fita kuwa haka mazan zasu yita mata layi kamar zasu cinyeta dan ma wasu daga cikin daliban sun san cewar musa na mutuwar sonta sanin ko waye musa a makarantar yasa suke yi suna kaucewa bancin haka da bakaramin gurmi za'a yi ba ,kawarta kwaya daya ce zinnira muhd bandi tare suka kare primary school kuma har lokacin islamiyyarsu guda shakuwarsu ce tasa suka zabi makaranta ɗaya, kisna ta yarda daita sosai kasancewar itama bata da hayaniya sai dai bata kai kisna rashin son magana ba , dan ita wani lokaci tana ta'bawa ."
wannan yanayi na kisna yasa matan ajinsu suka dauki karan tsana suka daura mata musamman idan sukaji yadda samari basu da zance sai nata ita kuma kyalesu kawai take tana tarasu jira take dubunsu ya cika ta nuna musu wacece ita , kyawun kisns na bala'in daga musu hankali matuka basa kallon wulakanci da takewa samarin dake mutuwar sonta , har shi Musa daya ɗan kwanta mata a rai bai tsira daga wulakancinta ba, duk nacin irin na musa kisna taki sauraransa ,hatta Ugo dan Principal yace yana son kisna Bata kula shi ba bayan shi din matashi ne mai daraja da kyau ya nika Musa sau dubu bambamcisu shi Musa muslimi ne shi kuma kafuri ne , gashi dan gata ga tari ilimi boko ga tsananin kyau babu wanda yayi tsanmnin zai ce yana son kisna a yadda yake tsananin ji da kanshi da takama shi wani ne a makarantar sai gashi yana bin kisna ta so shi tana gudunsa ,duk sanda yayi mata magana sai ta wulakantashi hakan yasa aka ƙara tsanar kisna a makarantar, zinnira ce kawai ke tare daita ita kanta zinnira bata tsira akan kisna ba .."
Abu kamar wasa tunanin musa ya sha kan kisna ta fara daina fahimtar komai a aji dan har class teacher dinsu sai daya fahimci haka , ya rubuta letter ya bata yace ta kai wa babanta ta amsa batare da wata damuwa ba , tana zuwa gida ta mikawa mumy farar envelope ta shige daki domin cire uniform sai dai kiran da mumy tayi mata yasa ta fito daga sauri batare data cire uniform din jikinta ba "meke damunki kinsa yau kusan wata shida kenan ina binki akan kina tattare da damuwa kice min a'a ,yanzu gashi har ta kai malamai sun fara fahimtar kina da damuwa har ta fara shafan karatunki " uban me kike tunani as age d'inki ?" Shiru Kisna tayi ta kasa magana tana wasa da yatsun hannunta faɗa sosai mumy tayi mata ta korata daki hankalin mumy bai sake tashi ba sai lokacin da sukayi exam , madadin kisna tazo na daya kamar yadda tazo a first time da second time sai tazo na uku har kusan dukanta mumy tayi kuma ta shedawa Samir da Aliyu kar su kuskura su sake aiko mata da komai daga cairo ,kuma idan zasu dawo karsu zo mata da komai , tabe baki kisna tayi a ranta tace "kar su kawo gara ma tsaraban samir tana amfani dashi na Ali kuwa bayarwa take ko ta zuba a shara ."
naci irin na musa da karfin matsayin daya samu a zuciyar kisna yasa ya shawo kanta suka fara gudanar da soyayyarsu a boye , wanda lokacin ne komai ya sake tabarbarewa sakamakon kisna ya dawo na biyar tun mumy na faɗa har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido sai dai ta sanya ido sosai akanta ."
A hankali soyayya mai karfi ta shiga tsakanin kisna da Musa har ta kai idan basu ga juna ba basa jin dadi dan haka ta cire lokaci cikin lokaci zuwanta islamiyya asabar da lahadi suna haduwa a unguwarsu musa , soyayyarsu ta kai har sun tsotsi jini juna da zumar babu rabuwa a tsakaninsu tare da d'aukarwa kansu alkwari kasancewa da juna muddin rai babu wanda zai kula wani da sunan soyayya ,musa ya shaidawa mahaifiyarsa batun kisna tayi murmushi tare da ɗaukar abun wasa ."
Wannan shekarar samir suka kare karatunsu suka tarkato suka dawo gida ,ranar murna agurin Afra ba'a magana a fili take bayyana tsantsar murnarta da farincikinta babu wanda bai yi mamakin haka ba ,
abinci kuwa ta shiryawa Aliyu yafi kala biyar cikin tsananin kulawa ta kawo abincin parlour'n ,kisna ta bita da kallon mamaki sai dai acikin zuciyarta tasan wannan rawar jikin da aunty afra ke yi ba na Allah ba ne akwai makircin data shirya dan haka ta kawo ido ta zuba tana jiran tashin bom din , muradi yayi kowa tsaraba a gidan hatta yan aikin da mumy ta dauka yayi musu tsaraba ban da Afra ,kisna kuwa kallon banza tayi masa dashi da kayan tace "kaga alamun butarsu a tare dani ko ance maka talaucina ya kai nan banaso , karka sake bani wani abu daga hannunka wanda kake aikowa ma zubar dashi nake bana sawa ,yayi shiru yana Kallonta yana mamakinta karamar yarinya daita ta har iya kallonsa tana faɗa masa magana haka, shi da yake dauki yazo ya ganta yaga yadda ta kara girma shine zata zuba masa kasa a ido , miskilancinsa bai barsa yayi mata magana ya tattara kayan ya karawa zainab ,ita kuwa Afra babu kunya ta kalleshi tace " ina tsarabarta naga ka bawa Kowa ban dani "?
Wani irin kallon rainin hankali yayi mata mai tattare da mugun kallo sannan ya ɗauke kanshi ya wuce daki mikewa tayi tana waige waige ganin babu kowa a parlour'n tayi wuf ta fada dakinsu muradi cikin zuciyarta take addu'a Allah yasa babu wanda ya ganta a kwance ta ganshi a dakin idanunsa na kallon celling d'akin maganganu kisna ne suke dawo masa kamar daga sama ya ganta akanshi yayi wata irin zabura ya mike yana Kallonta tunda suka girma bata taɓa kuskuren shigowa inda suke ba sai yau , cigaba da Kallonta yayi "nasan zakayi mamakin ganina Aliyu sai idan idan kayi la'akari da yanayin canji da yanayina ya samu akan dawowarka ba abun mamaki ba ,Aliyu tun barinka kasar nan na tsinci kaina cikin tsananin tashin hankali ban jima cikin dogon tunani ba na fahimci zuciyata ta kamu da matsanancin sonka tunda ta soma magana ya karkata kai yana Kallonta hankalinsa a matukar tashe yana ganin kamar abun yana faruwa ne acikin mafarki "wallahi har ga Allah nake jin sonka kuma zan kashe aurena saboda kai" still shiru yayi mata ya dauki wayarsa ya koma kan kujera ya zauna ya soma danne danne dan gaba-daya mahaukaciya ya ɗauketa bai ma yarda Afra ce a gabansa ba idan kuwa itace lallai wani tuggu take son hada masa shi yasa ya danna record yana ɗaukar maganarta yana mata dariya a zuciyarsa "muradina ....."Ta kirasa da sunan da mumy take kiransa dashi baka ce komai ba ? Cikin kaukausar muryarsa mai razanarwa yace me zance miki ? " Kinga dan girman Allah banason damuwa bana son abinda kike min ki tashi ki bar dakin nan ta matso kusa dashi tana ƙoƙarin kamo hannunsa wata razananniyar tsawa ya buga mata muryarsa a fusace yace "ke fita a dakin nan dan ubanki cike da razana ta mike ta buɗe bakinta zatai magana "idan kika sake wata magana anan sai ba tona miki asiri kowa yasan abinda kika furta min a yanzu,"wallahi da gaske nake karka dauka wani makirci ne kaga ko bazaka aureni ba zan mallaka jikina ya girgiza kawai yana kallonta a dage kafin daga baya ya fara magana a dake "Kinga ikon Allah ko ,kinga kin nufe da irin wannan halin batare dana aikata ba sai gashi yau da aurenki kike furta kalmar na amshi tayin soyayyarki idan ban amsa ba na kusanceki ,kadan kika gani afra daga cikin sakkayar da Allah zai min akanki ,dan na rigada na kai kakarki zuwa garesa kuma nasan ubangijina ya amsa ki fita yanzu ko na tara miki mutane ".
murmushin gefe baki tayi tana kallonsa" sai me dan ka tara min mutane ka ɗauka soyayarta karya ce ko yaudara nake maka kasani soyayyata gareka gaskiya ce , kuma sai yanzu na fahimci duk abubuwan da nayi maka a baya so ne ,ko ka fadawa mutane cewar ina sonka hakan bazai sa nayi nadamar furucina ba ,sai ma dadi da zanji zan rabu da igiyar dake kaina wanda zai bani damar mallakar ka a rayuwa ...."
"wa zaki mallaka ?"Yayi mata tambayar yana watsa mata wani mugun harara "kai muradin zuciyata ,zuciyata ta makance akan......"dogon tsaki ya ja tare da juyawa da sauri domin barin dakin gbdy hakan yasa ta katse abinda tayi niyyar furta masa ta tsaya shiru tana cizon yatsa "mai yasa ban rungumeshi ajikina na saka ƙara mutane su fito su samemu haka ?"
Ai kuma laifinki za'a fi gani tunda kice a dakinsa fito wa tayi tana nazarin yadda zata bullo masa .
tun daga ranar kullum da iskancin da Afra take ma muradi baya sauratonta hasali ma ko kallon inda take bayayi cikin haka wani club dinsu na Nigeria suka bukacesu da kyar mumy ta yarda suka tafi tare da Samir da mujahid cikin lokaci kankani sunan Aliyu ya daga a duniya a dalilin wannan wasan daya buga acikin lokacin ya