Showing 468001 words to 471000 words out of 495987 words

Chapter 157 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

kuma bawan Allah baya kin ci ,dan kara mata karfin gwiwa ma ko abinci bai yi dadi ba cewa yake yayi ita kuma tayita murna tana sake shige masa da bashi kanta yayi duk yadda yake so sam bata masa rowa jikinta ,haka bata nuna gajiyawarta duk sanda yazo tana maraba dashi , sai dai duk da haka baya jinta kamar yadda yake jin kisna , ita kisna kan kaciyarsa na shiga jikinta yake jin wani sauyi Na daban a gbdy ilahirin jikinsa , akwai wani sirri dake tattare daita amman haka cigaba da bawa nawal kulawa yana danne abinda yake ji akan kisna ,yayi Google din maganin kiba saboda baya bukatar ramarta aka nuna masa dynwel dan haka yaje ya siyo ya kawo mata, aiko dadi kamar ya kasheta sai kuma bare bare ya tashi ta dinga masa godiya ta sake shige masa kamar zata yi masa numfashi dan tuni ta lura akwai matsala a tsakaninsu da gimbiyar tasa , tunda direct motarsa yake shiga idan ya fita daga part dinta ko kallon part din kisna ba yayi ai kuwa farincikinta ya nunku ta dinga addaur Allah yasa daga haka ya karasa mata sakinta tayi gaba ta huta ."

wata sabuwar rayuwa suka soma shifidawa da nawal cikin kankanin lokaci kisna tazamo sanadiyyar farinciki nawal dan babu laifi maganin daya siyo mata ya ɗan amsheta dan ta murmure acikin sati biyu cakal tafi da sosai sai dai duk da haka bazai taba hadata da kisna ba ai kisna daban ce akwai diri mai kyau da daukar hankali duk abinda yake ya rasa dalili kisna na nan makale a zuciyarsa taki barinsa ya huta duk inda juya tana makale dashi idan runtse Idanunshi ita yake gani ,gida da office bashi da hutu tunaninta ya hanashi sakat."

Bangaren kisna kuwa tuni ta dawo daidai zafin da kasanta yake mata ya daina , ta daina kulle kofar falon har sai taga goma ta buga bai shigo ba take kulle ko'ina ta kwanta nan fa shirun da dauke mata kafar da yayi ya soma damunta hankalinta ya tashi dan zuciyarta har wani tuttuki take mata bayan zazzafar soyayyarsa har da matsananciyar sha'awarsa ke damunta tana kwance lamo hawaye na gangaro mata can ta mike zumbur ta mike tana hawaye da kallon boobs dinta "wayyyohhly Allah nah me yasa nayi masa abinda nayi gashi ya ɗauki fushi dani ? ta shiga zariya a d'akin tana kuka a ranar batayi isasshen bacci ga tsananin tunani da bakinciki mijinta ya juya mata baya ga kewarsa daya addabeta har safiya bata runtsa ba sai juyi take tana kuka ."
cikin wannan yanayin tafiya ta kamashi zuwa Abuja zai yi sati biyu zuwa uku kafin ya dawo a daren ranar yake sheidawa nawal tana kwance a jikinsa bata san sanda ta mike zaune ba tana dubansa ita fa bata qaunar abinda zai sa yayi mata nisa tafi son su dangwama tare cike da so da kulawarsa ya sauko daga kan gadon zai isa gaban wordrobe dinsa muryarta na rawa cike da kuka tace "ni dai dan Allah ka tafi dani waiwayowa yayi yana kallonta "kiyi zamanki kamar yau ne fa zan dawo kuma idan naje ba zama zanyi guri daya ba kullum zan fita "ba dai zaka dawo ka kwana tare dani ba to zan zauna zaman jiranka ? yayi shiru ya d'auko jakarsa ya soma haɗa kayansa kuka tasa masa tana cewa " ita lallai zata bishi jakar da yake hada kayansa ta amsa tana dubansa "ka tafi dani , girgiza mata kai yayi tana kokari sosai gurin nuna masa kulawa shiyasa ma yake ta kokarin danne kishin bai sameta a yadda yake so ba dan zamansu ya daure , magiyar da ta dinga yi masa ne yasa yace ta shirya su tafi .

washegari sai da suka je gidan mumy suka mata sallama sannan suka wuce airport mumy tayi mamaki yadda ba da kisna zai tafi ba amman datayi tunanin kisna zata iya kin binsa yasa ta share ,yayinda a lokacin kisna na can cikin damuwa da tashin hankali tana cikin wannan halin kiran aunty zee ya shigo wayarta tana dauka tasa mata kuka aunty zee tace" lallai ba lafiya ba zargina ya tabbata tun da naji abban Junior yace min da nawal muradi ya tafi Abuja.

"Tafiya yayi zuwa abuja kuma da nawal ?eh ! meke faruwa ne "am...dama daman akan wai nan ta shiga koro mata abinda ya faru "amman dai ke muguwar sakarya ce shine zaki dauki wannan matakin ai shinkenan gashi kin jawo yayi fushi dake "nayi nadama aunty zee dan Allah ki kira min shi ki bashi hakuri "hmmmmm aunty zee ta sauke naunayen ajiyar zuciya n sannan ta cigaba da magana"wallahi kin aikata babban laifi wanda ni kaina raina ya ɓaci sosai amman babu ki daina kuka gobe inshaallahu zan kirasa yadda mukayi zan kiraki "na gode aunty zee washegari aunty zee ta kirasa ya ɗauka lokacin nawal na kwance a saman qirjinsa tana shafa gashin dake kwance a qirjinsa shima yana shafata nan aunty zee ta soma bashi hakuri da farko nunawa yayi bai san komai ba, ya zare nawal ajikinsa ya fita daga d'akin ya koma baya gurin swiminpool dan kar nawal taji halin da'ake ciki "hakuri dai aunty zee take bashi "wai zainab me akayi ne nifa ban fahimceki ba? ce miki tayi nayi mata wani abu ko tayi min ? ni bata min komai ba idan kina da abun yi kije kiyi zai fiyye miki yana gama fadar haka ya disconnecting din Kira".

"Inna lillahi ta furta sannan tayi shiru tayi rike da waya kafin daga baya ta kirab kisna tana ɗauka ta shiga mata fada sosai daga baya ta dawo nasiha akan yadda zata shawo kansa idan ya dawo ",hakuri zakiyi da yanayinsa dayawa daga cikin mata suna facing din wannan problems din , kin dai ga ishara ke kina gudunsa gashi ita abokiyar zamanki ta bishi idan ma mutuwa zatayi ta sadaukar masa da rayuwarta ,kiyi hakuri ki jure sannu zaki saba gashi akwai lada da falala acikin ribar zaman aure kiyiwa mijinki biyayya ,sosai ta dinga mata nasiha tana kwantar mata da hankali a karshe suka yi sallama wata irin kulawa da soyayya muradi yake nunawa nawal wanda yasa gbdy ta manta da su biyu ne agurin garzon mijin nasu ."

Satinsu biyu suka tattaro suka dawo tunda muradi ya shigo gidan kamar ya shiga ya ganta amman ya share kai tsaye part dinsa ya nufa tare da nawal wacce ta zame masa kamar chingum , ita kuwa kisna tunda aunty zee ta sheida mata ya dawo take son zuwa inda yake amman tsoro da fargaba sun hanata,bama haka ba bata son taje ya disgata a gaban nawal dan tasan zai aikata a yadda yake jin haushinta duk wuni ranar a tsorace tayi sa sai tayi kamar taje garesa sai ta fasa, ta dawo falo ta zauna tana kallon hotonsa tana jin zazzafan qaunarsa na kara huda zuciyarta "wayyyohhly Allah kazo gareni na tuba bazan sake ba da daddare tun takwas ya rufe kofarsa ya kwana yana juyi cike da matsanancin sha'awar kisna gbdy nawal ta gundiresa dumin jikin kisnarsa kawai yake son ji ,tayi knowcking yafi sau biyar amman yaki tashi ya bude ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa ya jima ruwa na sauka ajikinsa sannan ya dauro alwala yazo ya saka kaya ya fara nafila dan yasan koya kwanta ma bazai yi bacci ."

Washegari nawal na tsaye a d'akinsa tana maida kayansa ciki wordrobe dinsa , sakon kudi ya shigo cikin account din kasuwancinsu , ta bar abinda take ta ɗauki wayarta tana dubawa can sakon taya murnar ranar haihuwarta ya shigo wayarta daga bank tana kallon sakon tana murmushin jin dadi a lokacin daya ta tuna sauran kwana biyu muradi yayi nashi birthday din "lallai kuwa zanyi suprise dinka ta faɗa a fili domin ya taba fada mata bai taba celebreting din birthday dinsa ba , dan haka zatayi kokarin tayi masa koda baya ra'ayi tasan bazai karya mata gwiwa ba ".

nan da nan ta kira wayar masu decoretoin din guri kasancewar tana da contact dinsu tana gama wayar muradi ya fito daga bayi yana goge jikinsa da towel yaga sai murmushi take shi dai kallonta kawai yayi bai ce mata komai ba , har ya shirya kansa cikin kayan shan iska dan baya jin fita ko'ina yana bukatar hutu babu ya kwanta flat akan katifa dan ya huta nawal ta hau kan gadon tana massaging din jikinsa a hankali har bacci yayi awon gaba dashi ta fita daga d'akin tana kiran wata cousing sister dinta fedy maganar mintuna goma sukayi ta ajiye wayar ta shiga wasu tsabgogin."

washegari masu decoretoin suka k'araso lokacin muradi bai gida yana office
kai tsaye flat din baya ta kai su suka shirya gurin byn sun gama tayi musu transfer suka kama gabansu ta shiga motarta suka hadu da fedy suka je suka siyo gift kala dabam dabam wanda zata bawa muradi ,tayi order cake da snaks kala kala donut fishpie, samosa da abinci da za'a ci tare da kayan da take buƙatar ya saka a gobe ."
washegari aka kawo mata cake din har gida fedy da wasu daga cikin yan gidansu ne suka fara zuwa ..

karfe takwas daidai na safiya ranar ta lallaba ta kashe wayoyinsa sai a lokacin tayi event din mutane masu mahimanci a rayuwar muradi da wasu abokansa guda uku data sansu tare , masu busa ne suka farkar dashi daga naunayen baccinsa ya tashi a natse yana mamaki from where ake masa busa a gida ? a hankali yaji an turo kofar d'akinsa idanunsa suka sauka akan nawal sanye cikin wasu hadaddun kayan shi bana bacci ba shi bana sakawa a fita ba zai da fi kyau a saka shi a gida muryarta a sanyaye tace "happy birthday my norr .
_You may be the apple of your parents' eye, but for me, you're as sweet as the most exotic blueberry in the world! Wishing you a very Happy Birthday my norr_

"Ya rabbi ya furta yana janyota jikinsa ya rungumeta tsam yana mai jin dadi abinda tayi masa ,duk da ba dabiyarsa bace celebrate din ranar haihuwarsa , ya sha ganin abokansa tun daga fararen fata har zuwa kan bakake suna yi amman shi bai taba sha'awar yi ba amman yanzu yaji dadi sosai."

zare jikinta tayi ta riko hannuwansa duka cikin nata ta fito dashi zuwa makeken palonta inda ya iske mutane har da samir ciki ga masu busa na aikin yi , suna ganinsa suka shiga masa happy birthday ya rungume samir "thank you samir ya'akayi kasani dan ko ni na manta "nawal ce ta tunarta dani ta karaso ta tsaya gefensa tana murmushi "muje kayi wanka zafa ka yanka cake ya sakar mata tsadaddan murmushinsa yana jinjina girman soyayyar da take masa gbdy ya kasa boye farincikinsa hannunsa ta kamo zuwa ɗakinta anan yayi wanka ta dauko masa sababbin kaya riga ja da wondo army green takalmi green da ratsin fari ta mika masa ya janyota tare da kayan ya zaunar daita akan cinyarsa "nawal kina son muradin nan dayawa "sosai zan iya mallaka masa rayuwata saboda son da nake masa sun bata lokaci sannan suka fito tare alokacin mutane sun taru a inda za'a yanka cake shi kawai ake jira kowane cikin shiga ta alfarma tuni labari ya iske kisna tace bata zuwa aunty tayita fama daita "karki yi haka kisna wallahi kice zaki kwana cikin matsala , matar da wayo da siyasa take son kwace miji idan kuma kince fushi zakiyi wallahi zakiyi nadamar da tafi ta farko kuma karki nemeni."


nawal sanye da doguwar riga puppy hannunta daya tsarkefe cikin na muradi yayinda dayan hannun ke rike da flowers suka shigo gurin "ya salam ya furta a kasan makoshinsa yana kallon nawal tare kallon yadda aka tsara gurin kamar bashi ba " gaskiya nawal tana mugun son shi fiyye da tunaninsa nan take yan'uwa da abokansa suka shiga tayasa murna ta kai shi har gurin cafke mai hawa biyar ta tsaida shi fedy taje ta dauko gift data tanada dominsa ta dan rage tsawonta ta bashi mutane nata daukarsu hoto har da video ta bashi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login