Showing 81001 words to 84000 words out of 495987 words

Chapter 28 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

bawa  aryan abinci , kasa zama kisna tayi ta biyo byn mumuy domin son aiwatar da kudirin ta .."

A tsakiyar dakin mommy   ta iskeshi yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa  jin motsin shigowa dakin yasa ya juyo yana zare rigarsa ya saura daga shi sai farar vest da dogon wando a hankali ya shiga fifita da rigarsa  yana furzar  da iska mai zafi daga bakinsa  yayinda hannunsa daya ke rike da kugunsa sai zufa yake yi ,jijiyon kanshi duk sun mika sun yi rudu rudu   tamkar wanda ya shiga  fagen  yaki   " bana ce kabi komai a hankali ba me yasa zaka ........."shigowar kisna ya katsewa mumy   hanzari ,kisna  ta karasa  shigowa  jikinta a sanyaye idanunta na kanshi a kallon da take masa ta fahimci yana cikin  tsananin damuwa "to me kuma  ya sameshi"? tayi  Maganar akasan ranta tana takowa  inda jug din ruwa yake ta tsiyaya a glass cup ta karaso inda yake yana fidda numfashi ta mika masa kin amsa yayi sai da mommy tasa baki sannan ya amsa sai dai ya kasa  kai cup din bakinsa yana jin tamkar ya saki  cup  din kasa   ,babu  zato babu  tsammani  suka ga ya  matse   glass  cup din a hannunsa take cup din ya  soma tarwatsewa ruwa da fasassasun glss suka yi kasa kisna da momy suka tsura masa ido hankalinsu a tashe cikin tsananin tashin hankali mumy ta rike hannunsa tana furta  "menene haka muradi zaka kashe min kanka ne kalli yadda ...ai ganin jini ya fara diga  yasa mumy yin shiru tare da rudewa cikin tsananin soyayya ta tsinka  masa marin da sai data ji saukansa a zuciyarta kana da sauri ta yaga gefen zaninta,  kisna ta matso kusa dashi tana  kokarin taba hannunsa ya dakatar daita da hannunsa   sannan  ya runtse  idanunshi gam dan baya son ganinta   bai ji zafin marin  da momy tayi masa ba illa gyara tsayuwarsa da yayi  cike da jarumta,  ahankali  ya dinga motsa labbansa yana furta kalmar  "kiyi hakuri  momy kiyi hakuri  ...."   "karka   sake  cewa zakayi wani  abu kaji na faɗa  maka ka manta da  komai    "no mommy  "no I  can't  ",wallahi  mommy abinda  Kika  faɗa min nayi  banyi wani abu dana san ba daidai ba ".muryarta a raunane tace  "mommy me yasa mesa  dan Allah kice masa  ya dinga sawa zuciyarsa salama  ya dinga bin komai a hankali idan wani abu ya sameshi ban san yadda su aryan zasu ji ba  ......."
"har  ke kanki zakiji babu dadi dan duk abinda ya samu uban ya'yanki ya sameki "a hakan da bai daukeni da daraja ba , bai san mahimmancina  ba ,sannan bai  damu  da damuwata ba tayi  zance a zuci "shima  kuma bazai so wani mummunar abu ya sameki ba amatsayinki na matarsa kuma uwar ya'yansa inji cewar mumy , aliyu ya sake runtse idaunshi yana ciza gefen lip's d'insa da karfi mumy ta kamo sa ta zaunar dashi akan kujera "karka sake min  irin wannan ganganci dan rayuwarka nada matukar muhimmancin gareni ta kalli inda kisna ke tsaye "kin wani  tsaya kina kallon mu ki  je dakina ki dauko   min akwatin first aid  ,juyawa tayi a sanyaye ta bar d'akin ko cikakken second biyar bata yi ba ta dawo ta ajiye ta sake fita dan dauko tsinyaya ta gyara gurin ta cigaba da tsayuwa tana kallonsu dan ko tace zata taimaka masa bazai yarda ba
mumy  ta bude laulausan  tafin hannunsa gabanta na wani irin  faduwa  ,shiru tayi tana kallon raunin daya ji ,tausayinta ya kamata  taji kamar ta cire ciwon ta dawo dashi jikinta  wanke  masa hannu tayi da  hydroxy da  auduga, tana wanke raunin tana duba ko kwalba ya shiga naman hannunsa .
Bayan ta gama ta rufe akwatin ta janyo kisna tare da zaunar daita gefenta  bayan kamar minti goma " kisna taga gara ta aiwatar da nufinta tunda gasu tare , ta kira sunan mumy a hankali "mumy   ina neman  wani alfarma agurinki saboda kece mutun ta farko a duniya da kike son zamana  da ya Aliyu tun ada can baya har zuwa yanzu ,sai  gashi har yanzu babu wani cigaba a rayuwar aurenmu.
"da cigaba mana me yasa zaki ce  haka "? Mumy  tayi mata tambayar a dan kufule dan yaji haushin maganarta "allah babu wani cigaba mommy saboda har yanzu ya  Aliyu bai daukeni a matsayin matarsa ba me zai hana mu saukakawa juna ya sawakemin idan zaki wuce na biki mu koma tare dan wallahi zuciyata ta gaji da wannan zaman idan kuma hakan bai samu ba wata rana labarin mutuwa zai riskeku a lokacin da kuke tsananin bukatata ta karasa maganar hawaye na gangaro mata mumy ta damki tsintsiyar hannunta jikinta na rawa numfashinta na barazanar daukewa "ki kwantar da hankali mumy Allah rabuwar mu zai fi kwantar miki da hankali zucoyoyinmu zasu fi samun natsuwa Allah ya raya mana su Aryan "abinda ta faɗa   gaskiya ne mumy nima ina iyakacin kokarina naga cewar na manta baya na inganta relationship din sake tsakaninmu  amman na kasa idan dai har zai yiwu mu sawakewa juna ......."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un " mumy ta shiga furtawa jikinta na tsananta rawa ..."


Inshallahu ku saurari 14 zuwa an jima

Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Free page 14

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰

....Wani   irin  kyarma   jikin mumy   yake   batare   da  sun  fahimci  haka ba   saboda   idanuwansu   daya  rufe,  sai  faman    ya'bawa   juna  bak'ar  magana  suke   cikin kunar rai  ,
A matukar  fusace  Aliyu  ya  katsewa kisna   hanzarin  "na  fiki  son  rabuwa  dake    mumy  nima  na amince da tsarinta   mu  rabu  kawai  kowa ya huta  ,  dan Allah  mommy  ki  sanyawa  zuciyarki  salama  kiyi   hakuri   ki   bari mu  bar    rayuwar  juna  mu  cigaba  da zumuncinmu   shima   idan  zai  yiwu idan  kuma  bazai   yiwu ba kowa ya kama   kansa  ya fada yana  furzar da iska  mai  zafi  daga  bakinsa , wannan maganar  data  sake dokan kunnuwan mumy  yasa  taji wani  mummunar faduwar  gaba  ya sake ziyartar jikinta , qirjin  mumy  ya  dinga  baguwa  da  tsananin karfi , duk wani tashin  hankalin  da take kokarin dannewa  acikin zuciyarta sai daya fito  fili  saboda  babu abinda ta tsana a rayuwarta  kamar taji  maganar   rabuwa  a  bakin   Aliyu  dan na  kisna mai  sauki  ne  tunda sakin  ba a hannunta   yake  ba ...."

Aliyu  ne  ya fara  lura  da  yadda  jikin mumy   ke   karkarwa  kamar  mazari   yayi   saurin   rikota cikin tsansnin  tashin  hankali  yana kiran sunanta   "mumy !mumy!!! dan  girman  Allah  mumy  ki kwantar  da hankalinki  ".a  hankali   ta kai  hannu  ta dafe daidai  qirjinta  da taji yana mata  wani  irin  zafi  da  bugawa  " Please Karki   min  haka  wallahi bana son na rasaki  bana  son  wani abu ya sameki a dalilin  rabuwata   da kisna  idanunta   suka   fara  rufewa  sakamakon kalmar rabuwar daya sake maimaitawa  "mumy  Please  ki tamaineni ki  bude  idanuki me kike so  ayi  yanzu ? " duk abinda kike so a shirye  nake  zan  miki matukar zai sakaki  farinciki  cikin tsananin tashin  hankali  kisna  take furta mata haka kafin  daga  baya  Aliyu ya kwantar daita  akan katifa  ya  mike cikin sauri  gaba-daya ya  rud'e ya  gigice hawaye sun cika masa kwarnin idanunshi    tamkar  ba wannan  Aliyu   mai karkarfar zuciya ba  ya fita daga d'akin  , itama kisna hankalinta  yayi  matukar tashi dan  kusan  tafi  shi shiga  tashin  hankali,   take  ta fara data sani maganarta da bata furta kalmar su rabu da mumy bata shiga damuwa ba  ,wani  sabon  hawayen   ne  yazo   idanunta ya  fara zuba  akan  kuncinta tamkar an bude fanfo , a  hankali ta  fara rera kuka mai ban tausayi  ,ta sake riƙe hannun mumy  dake  cikin nata gam yayinda hawayenta  yaki tsayawa sai faman kuka  take da  kiran  kalmar  "na shiga uku     cikin  tsananin tashin hankali "mumy  na tuba  bazan sake ba, bazan sake furta kalmar rabuwa da ya Aliyu ba  tunda  bakya  son rabuwarmu , " ki  taimakeni  dan Allah  karki  mutu  ki  barni a gurinki  kawai nake samun farinciki da kwanciyar hankali   idan kika  mutu   kika barni rayuwa  zata min  muni,  sosai take kuka tana rike da hannun mumy itama mumy ta rike hannunta gam hawaye na gangaro mata ... ....."

Zuciyar  Aliyu   na matukar zafi ya dawo   d'akin    hannunsa  rike da goran  ruwa   bai  tsaya tsiyaya  ruwan a cikin cup ba ,ya ɓalle murfin goran da karfi wani zafi yaji ya   ratsa tafin hannunsa inda yaji ciwo  sai dai bai tsaya  kallon tafin hannunsa ba ,ya soma   shafa   ruwa  a fuska mumy  yana kiran sunanta , naunayen  ajiyar zuciya   ta  sauke  sannan ta  dinga sauke  numfashi  a hankali a hankali  "sannu  mumy   suka hada baki gurin furta mata haka da kyar ta gyada musu kai  idanunta  na  runtse   ,Aliyu ya  kamo  kanta  ya  kai goran ruwa bakinta   "ki  sha ruwa mumy  " .
Ta girgiza  masa kai  alamun  bazata sha ba  "dan  Allah mumy  ki rufa  min asiri  ki kwantar da hankalinki  ya kalli  kisna da idanunsa da suka rikice suka canza kala tamkar garwashin wuta  ya soma magana cikin zafin rai  "wallahi   Idan  wani  abu ya same mumy  a  dalilin furucinki bazan taba  yafe miki ba , kuma wallahi  bazan cigaba da zama  dake ba  dole  na yakiceki   ta  karfin tsiya daga jikina  domin nafi bukatar  rayuwa mahaifiyata  akanki  ya karashe maganar yana wurgi da rabon ruwa  ......."
kuka  kisna take sosai tamkar ranta zai  bar gangar jikinta  tana rike da  hannun mumy  Sun yi   matukar  tausayawa   halin da mumy  take ciki  , bazasu iya daukar halin  da zata shiga    a dalilin cikar burinsu  ba .......
Aliyu  ya  mike  da  hanzarin  zai  fita daga  dakin  domin kiran Samir dan sukai mumy asibiti  ta rike  hannunsa ya  dawo da sauri   ya   daura hannunsa  akan nata tare da zubawa mata  idanunshi kamar zai yi kuka  "mumy zanje na kira Samir ne mu kai ki asibiti"  sake  girgiza masa kai tayi    ta  zuba masa ido  cikin sarewa tace "karku  wani  kai ni asibiti alhalin   magani na gida , kune  damuwata muradi , idan zanganku cikin farimciki  da kwamciyar hankali wallahi  nima zan kasance haka"bazan  taɓa   yarda da   tsarinaku  ba  ,rabuwarku  wani babban  tashin  hankali ne  gareni bansan  me yasa nake son kasancewarku   tare da  juna  ba amma kafin na cigaba da magana ku amsa  min wannan tambayar  "?
ta soma yunkurin  mikewa zaune daga   kwance  da take jikinta na daukar zafi  Aliyu da kisna suka kai hannuwansu  da sauri  domin taimaka mata hannun Aliyu  ne  ya riga na Kisna  sauka a gadon bayan mumy sannan  hannunta  ya sauka akan nashi   saurin kallon kwayar  idanun  juna suka  tare da jin    faduwar gaba  mai tsanani zuciyarsu ta dinga bugawa a tare , zuwa wannan lokacin ko'ina ajikin Aliyu rawa  yake  yayinda zuciyarsa ke dokawa  da sauri  sauri fiyye dana Kisna , gabad'aya gabobin jikinsa sun yi sanyi, a hankali Aliyu yayi  saurin janye  kwayar idanunsa  a kanta  itama tayi kokarin dauke hannunta dake  kan nashi    suka  yi shiru  a tare suna  satar  kallon kwayar idanun   juna ,karamin bakinta ta turo masa   tana  kashe  masa idonta  d'aya  ..

abinda tayi ya bala'i  bashi  haushi sosai  and he don't want any dilemma with  her  ko sake kallon inda take bai yi  ba dan gani yake bata damu da halin da mumy take ciki  ba kukan munafurcinta data saba ne  ...
Cikin sanyin  jiki  ya kamo hannu  mommy cikin laulausan tafin hannunsa    tare da matsowa  gefenta sosai  itama  kisna ta  sake matsota  suka sakata a tsakiya  ya d'ago kanshi a hankali ya watsa mata harara itama batayi  sanya a gwiwa ba ta mayar masa  tana murgud'a masa baki yaji  tamkar ya  buge mata  baki ko janyo ta ya  yaryarfa mata maruka masu rai da lafiya   sai dai  ya kasa aiwatar da ko daya  saboda shi a  yanzu babu abinda yafi bukata kamar samun natsuwar mumy muryarsa a ƙausashe yace "malama ki dan matsa can mumy ta  samu wadataccen   iskaa  kin  wani manne  mata kina kokarin ....." 
      "kai ma ka matsa mana cikin ni da kai wa ya hanata shaƙar wadataccen numfashi ?  ta kasheshi tana zabga masa harara  " nifa bana son damuwa dan Allah  kowa yayi lamarin gabansa kawai    zai yi magana mumuy  tayi saurin d'aga masa  hannu alamun yayi shiru umarninta yabi bai sake cewa komai ba ,mommy ta numfasa sannan ta cigaba da magana a tsanake"  banason jin wata magana bayan amsar tambayar da zan muku yanzu  "tsakanin  kai  da  kisna idan  kun rabu  zaku iya  manta   junanku  har duniya  ta nad'e"?shiru  ne ya sake  biyowa  baya , hatra d'akin ya sake  daukar shiru tamkar babu wasu halitta acikinsa  kisna ta d'ago idanunta  a hankali ta kalleshi  dan ganin yanayinsa  wani kallo ya watsa  mata wanda yasa  take hantar cikinta kadawa , ta tabe masa baki  qirjinta  ya  bugawa  da karfin gaske .
"ina  tambayarku kun min  shiru  zaku iya manta  junanku  har abada  ?  Still shiru suka yi suna kallon mommy "Ni nasan bazaku iya manta  junanku  ba  har duniya ta nade da tunanin juna zaku mutu  amman idan amsarku   ta  kasance "eh  zaku iya manta  juna  sai  nasan  abun  yi  ........"

Jin yadda suka yi shiru yasa ta waigo  gefen da Aliyu  yake da gefen da kisna take makale daita tamkar zata mata numfashi  taga  suna kallon juna  tayi murmushi irin nasu na manya   "mai yasa  kuke kallon  juna ku bani amsar  tambayata mana kun  min  shiru  suka sake  yin shiru kowanensu na jiran yaji abinda  d'an'uwansa zai furta  "nasan baza ku iya amsa  min  wannan tambayar  ba bari na faɗa  muku abinda zai sa ku shiga  hankalinku wallahi  muddin kukayi kuskuren barin juna karshenku wahala mai tsanani ,kuma sai ta shafi rayuwar ya'yanku  saboda zaku raba musu hankula , saboda kai  Aliyu wata matar zaka aura kema Kisna  wani mijin zaki aura kuma duk wanda zaki aura bazai kai uban ya'yanki ba ,hakazalika kai ma nawal bazata zama tamkar Kisna agurin su Aryan ba ,da zaran ta samu nata  zata manta dasu  ba kowace matar uba ke rike masa yaya tsakani da Allah ba ta karashe maganar tana sauke numfashi da kyar Aliyu ya sake tashi ya dauki goran ruwan da yayi wurgi dashi yaga da sauran ruwa aciki ya mika  kai bakinta ta kurba tana lumshe ido "na gode muradi Allah yayiwa rayuwa albarka Allah ya yaye maka zafin zuciya ".
"gara kan kina yi kina masa addu'a, wannan zuciya kamar ta mutanen farko ,zuciya a wuya kamar kuturu ba'a  jin rarrashi  bare hakuri  kallonta kawai yayi ya furzar da iska   tare da jan tsaki ,ta watsa masa harara tana hura masa hanci dan ta sake tunzura shi ,a ranshi yace kiyi duk iskanci da kika ga dama ganin idon mumy ne  zamu hadu ne  .."
"Kana magana ne ? tayi maganar cikin jan hankali ."

"ke kisna ban son iskanci sa'anki  ne"? tayi shiru  "ki shiga hankalinki   dan kice  kika fara kawo zance rabuwa a tsakaninku  da muradi    bayan kuma kece za   kiyi   hakuri   dashi domin   kin zo gyara kuskurenki ne a gurin mutumin da  yake tsananin fushi dake dan iskanci sai kina fada masa magana "kiyi hakuri mumy  , "bani zaki bawa hakuri ga wanda zaki sake bawa hakuri nan kuma  yanzu a gabana saboda ko babu aure a tsakanin ki dashi d'anuwanki ne bai cancanci wasu abubuwa daga gareki ba , muryarta a raunana tace "to ..to kayi  hakuri  ".
"haka   ake  bada  hakuri  ki hada kalamanki  guri daya ki bashi hakuri ta  shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace  "kayi hakuri ".. shiru yayi yaki magana dan zafin da zuciyarsa keyi  ba zai bar shi ya amsa mata ba .."Kisna na kiraki da babban murya karki sake zance rabuwa tsakaninki da muradi  saboda ina matukar sonku tare bana son ku rabu, rabuwarku daidai yake da shigata damuwa "Ni kuma zafin da zuciyata take akan shi fa  mumy ni kadai fa nasan abinda nake ji kar a waye gari a iske bana numfa........" Da ikon Allah babu abinda zai sameki  idan kika zauna dashi  tsakani da Allah zaki samu lada mai dimbin yawa   sannan  zaki jiyar da mahaifiyarki  dadin da bata bata  jin irinsa ba ,zata sake magana mumy ta dakatar daita kana ta maida hankalinta kan Aliyu .....
    "aliyu  wacece ni agurinka "? da kyar ya iya bude bakinsa muryarsa can kasa yace  "Mother " yana riko hannunta cikin nashi "tabbas ni uwarka ce shiyasa ma nafika jin haushi   akan  abinda kisna ta maka ,abinda tayi  ya balain  tsaya min a rai ya dameni ya daga min hankali saboda na fahimci halin daka shiga a lokacin  amman duk da haka yana da kyau  ka yafe mata  a karo na biyu  dan Allah ku fahimci mahaifiyarku ina son  ganinku cikin farinciki dan Allah ku zauna lafiya dan kwanciyar hankalina shiru suka yi zuciyarsu na dokawa da sauri  iska ya furzar yana Kallon Kisna  itama  shi  take kallo "mai yasa mommy zata masa haka akan kisna "? "Mai yasa zata sa igiya ta  daureshi akanta ? "Aliyu ta sake kiran sunansa  muryarta a sanyaye  kamar zata zubar da kwalla ," ka saki ranka  nasan  halinka  kana da tsananin  fushi da riko a cikin zuciyarka 

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login