Showing 159001 words to 162000 words out of 495987 words
Chapter 54 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
kice ya saukeni Allah bazan bata hakuri ba ai itace tace na daureta kamar rago "ai kuwa ko itace tace ki daure ta sai kin bata hakuri ko na zaneki yau " dan Allah kayi hakuri karka dakeni banaso bulala ka sauke bazan sake ba cikin tsananin tashin hankali take ihun bai sauketa ba sai da suka karaso falo inda ya iske zinnira da jahid sun shigo tana rike da wuyata mumy ta kamo zinnira tana duba wuyanta "muradi a she d'aure wuyan 'yar mutane Kisna tayi shine na tambayeka kace babu komai ? zo nan sai na zaneki yau mumy ta matsar da zinnira dake gabanta ta kai hannu zata damko Kisna muradi ya matsa baya kadan "Karki daketa mumy bari dai ta bata hakuri sannan tayi alkawarin bazata sake ba gaba-daya mutanen dake falon suka zuba masa ido suna kallonsa shi daya shigo tamkar mayunwacin zaki zaka dauka dukan mutuwa zai mata amman ya buge da iya hakuri zata bayar mumy kuwa wani irin tashin hankali da bakinciki ne ya dirar mata a lokaci daya saboda bata samu damar hukunta Kisna ba, muradi ya saki hannun Kisna tare da cewa "ki bata hakuri sannan kiyi alkwarin bazaki sake ba ya faɗa yana kallonta shiru tayi taki yin magana tana shesheka duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali amman shegen taurin zuciya ya hanata bude baki a tsawace madu yace "ba dake ake magana ba kika tsaya kina kallon mutane ki bata hakuri mana ? ya kai hannu zai mareta muradi yace "no madu karka mareta mana zata bata hakuri "dan Allah yaya ka bari na dan mareta yarinyar nan ko na shake mata wuya taji yadda yarinyar mutane taji "muradi ya girgiza masa kai "matsalata daku kenan saurin hannu wallahi "kai da baka da saurin hannun ai gashi nan taki yin abinda kace saboda ta rainaka Samir ya faɗa yana shigowa falon " muradi ya rage tsawonsa daidai na Kisna tare da cewa "ki bata hakuri Allah baya son mutun azzalumi kuma mai mugunta idan bakya son Allah ya sakaki a wutan daya tanadarwa azzalumai tare da azaba mai radadi ki bata hakuri ita kuma ta yafe miki shinkenan kin huta da azabar Allah magana yake mata amman tamkar bada ita take ba gashi duk yadda yan'uwanta suka so hukuntata ya hana gabadayansu suka zubawa sarautar Allah ido suna kallon muradi dake rike da hannuwanta yana rarrashita da kyar Kisna ta bawa zinnira hakuri tana jan tsaki shima dan taji madu yace idan bata bayar ba zai dauko mata kyankyaso ...
muradi yaji tsakin da kisna tayi amman ya share ya mike a natse ya riko hannun zinnira suka fito waje jahid ya biyo bayansa yana cewa "kai wannan yarinyar da gani zatayi taurin kan bala'in da zuciya common hakuri sai datayi kusan minti shabiyar Allah ku tashi tsaye akanta "muradi na fita Samir ya waskawa Kisna mari "dan ubanki wa kika yiwa tsaki idan na sake jin kinyi tsaki sai na karyaki maza ki wuce dakin mumy ki kwanta a karshen gado ta kwasa da gudu ta shige dakin mumy tana kuka ta faɗa kan gado ta rufe idanunta da hannuwanta duka ....
A can waje ma bayan muradi ya sallami zinnira da sweet cigaba da magana Kisna jahid yake masa wanda har lokacin bai ce masa komai ba "Sai naga kamar kana biyawa Kisna wallahi ka bari a hukunta yarinya tunda kai baka iya hukuntata amman ka tsaya kana wani lalla'bata kamar kwai " "ka kasa fahimtata ne ni dukan mace ne banaso wallahi ina mugun jin tausayi mata bare Kisna yarinya ce karama idan ta saba da duka zuciyarta zata kangare har tazo ta daina jin tsoron duka "ai shinkenan Allah ya kyauta sai dai kasani wani dukan yana gyara mutun jahid ya karasa maganar yana masa sallama ya wuce da misalin karfe takwas na dare gaba-dayansu suna zaune akan dinnig table suna cin abinci ,yayinda da kisna ke zaune akan cinyar afra tana bata abinci tana ci tana zuba mata shagwa'ba ,can ta kalli Aliyu dake zaune ya gama cin abinci yana kallon sama tace "dady d'azu da bakya nan wannan ya kai ni islamiyya bayan nace bazani ba "waye wannan din "?mumy ta fada a matukar fusace yayinda kisna bata fahimci fushi mummy tayi ba ta sake narke fuska ta nuna muradi da yatsan hannunta "na sake jin kince masa wannan sai na cire wannan ɗan iskan bakin naki yayanki ne ba wannan ba ta karasa maganar tana buge mata baki aiko ta bare baki ta sauka daga kan cinyar afra ta soma birgima a kasa tana jiran dady yayi magana sai dai gani tayi ya mike ya nufi waje yana waya "au Dan ban miki duka ba shine kike birgima bari kigani mummy ta yunkura da sauri afra ta mike ta ɗauketa tayi daki daita tana cewa "ba yayyanki bane wannan bawa ne kuma ɗan tsintuwa shege ne karki dauke shi matsayin yayanki kinji baby na kisna ta d'aga mata kai .."
A parlour kuwa muradi bai d'ago ya kalli abinda ya faru ba duk da kunnuwansa sun jiyo masa komai tunanin abubuwa kawai yake , haka nan wani lokaci kwakwalurwasa zatayi ta tunanin mahaifiyarsa ,
yana mamakin yadda ta dauki tsawon shekaru bata kawo kanta garesu ba , sau tari idan sun yi waya da anyarsa jamila yana tambayarta ko akwai wani sako daga mahaifiyarsa sai tace" a'a sai dai su kan gaisa da sadiq wanda shima zuwa lokacin babu abinda yafi bukata da gani kamar daura kwayar idanunsa akan mahaifiyarsu ,yana son zuwa inda take sai dai rashin takamaiman sanin full address din inda take ke hanashi zuwa, ya dai san ita din yar benue ce a unguwar kankara amman a wani gida ?" Bai sani ba mahaifinsu ne kawai zai iya danganasu da inda mahaifiyarsu take , shi kuma har lokacin ba'a sanda inda yake ba ..
Mummy ta Kai hannu ta shafa sumar kanshi tana sauke numfashi sannan ta tsura masa idanu tace "ya'akayi muradi meke damunka tunanin me kake yi ?muradi ya dawo da kanshi daidai yana sakar mata murmushin karfin hali batare da yace komai ba ,sake tsareshi tayi da idanu "tambayarka nake kayi min shiru ko bazaka gaya min bane ?"Still shiru yayi mata tare da zuba mata idanu dan bai san abinda zai faɗa mata ba ,a ganinsa idan yace mata tunanin mahaifiyarsa yake zata dauka ko ya raina kulawar da take bashi ne shi yasa yaga gara kawai yayi shiru ,ganin har lokacin shi take jira ya fada mata damuwarsa ya ɗan kalli Samir yana lumshe idanunsa da suka dan canza tashi Samir yayi ya fice daga falon gabad'aya tashin Samir ya bawa mufeeda da zahra har ma da madu tashi suka koma kan kujera tare da maida hankalinsu kan tv naunauyen ajiyar zuciya ta sauke kana yace "mummy karki damu fa babu abinda ke damuna illa......."mummy Bata bari ya karasa maganarsa ba ta katse shi ta hanyar cewa "muradi ka saurareni da kyau bana son wannan dogon tunanin dake iya haddasa wa mutun ciwo idan wani abu aka maka ka fito ka faɗa min ina tabbatar maka akanka zan iya batawa da kowa dan haka ba zan rokeka ba umarni zan baka ya zamo dole ka faɗa min damuwarka ta karasa maganar a fusace ganin ran mummy ya ɓaci yasa jiki muradi yayi sanyi , zuciyarsa tayi rauni domin kuwa babu abinda ya tsana a duniya kamar yaga ɓacin ranta haka zalika babu abinda yafi so fiye da farincikinta sannan ya tsani ya bata mata rai yanayinsa kadai ta kalla ta fahimci yadda damuwarsa ta qara muradi ya kamo hannun mumy cikin nasa yayinda idanunwansa tuni sun canza launi cike da rashin kuzari cikin tautausan muryarsa mai sanyi da shiga jiki "kiyi hakuri mumy banason ganin ɓacin ranki abinda ke damuna ba wani abu bane wani lokaci ina jin rashin mahaifiyata a kusa dani karki ɗauka wai ko ban yabawa kokarinki bane a'a hakan nan dai nake kwadayin sake daura idanuna akanta "mumy ta sausauta murya tace "karka damu ina da tabbacin zata zo gareku ni kaina babu abinda nafi bukata kamar ku sake sanyata a idanunku da kuma nasan inda take da tuni na kaiku "Nasani mumy nasan ke din uwa ce mai daraja a gareni ya karasa maganar idanunsa na ciccikowa kamar zai yi kuka "kiyi hakuri mummy ban raina kulawarki garemu ba sai dai bansan dalilin da wannan tunanin yaki barin zuciyata da tunanina ba "...
Mumy ta saki naunayen ajiyar zuciya tace " ka kwantar da hankalinka wannan ba wani abu bane tunanin mahaifiyarka dole gareka ko ni idan kace min ka manta daita zan ji babu dadi a raina ka cigaba da addu'a idan da rabon zaku sake haduwa Allah zai yi dalili sai lokacin ne ya saki jikinsa sosai "Allah yayiwa rayuwarka albarka a kasan makoshi yace "ameen ."..Cike da kulawa mumy tace "da fatan dai tunbin dan kwallo ya cika da abinci muradi ya da'ura kansa akan kafad'an mumy yace "mumnynah na koshi babu sauran space daga bayanta taji Muryar Alhaji realwan "idan an gama da dan lale sai azo a Bani abinci mummy tayi kayataccen murmushi tace "Allah ya bawa ranshi ya dade hakuri muradi ya tashi ya nufi bangarensu a daidai lokacin dady ya karaso mummy taja Masa kunne "zauna ka ɗauki siriki amman har yanzu baka canza ba "ta yaya kike tunanin zan canza tunda kema baki canza ba kullum kina cikin salon jan hankali , mummy tayi murmushi wanda ya bayyana kyawawa hakuranta masu haske irin na muradi ta tsaida idanunta akan shi tace "wannan gaskiya ne zan cigaba da murza zuciyar abokin rayuwata ,
"kina da matukar kyau salaha gaskiya nayi sa'ar samun kyakkyawar mace mai kyawun hali da zuciya ga tsabata da yawon ado cike da jin dadin yabon da yayi mata ta saki dariya mara sauti tace "kai kar fa kasa kaina ya kara girma "tunda dai ba rabewa gida biyu zai yi ba ai na auna arziki ta bude kular abinnsa ta zuba masa a cikin plet ta ajiye a gabansa tana dubansa ta dibo abinci "bude baki na baka abaki kaji rabin raina ya bude baki ya amshi abincin yana lumshe idanunsa "gaskiya ke macece ta gari da samun irinku ke da matukar wuya acikin gidan aure shiyasa babu babban riba a rayuwar namiji kamar ya auri kyakkywar mace ta gari mai kyawun hali Allah yayi miki albarka tayi murmushi tace "ameen sai data tabbatar da ya koshi sannan ta barshi yana sakace ta shige daki domin shirin bacci"
******
Washegari gari bayan mummy ta taya dady ya shirya kanshi ta kai shi dining area domin yaci abinci ,a lokacin Gabadaya yaran gidan suna kan table suna cin abinci ,bayan ya kammala ya mike yace "mu zamu office"Ta biyosa a baya rike da jakarsa,suna dan tautaunawa ,
"Dady sai ka dawo inji cewar mufeeda ,afra tace "Allah ya taimaka dady ya bada kasuwa mai albarka ka siyowa kisna kayan dadi yayi dariya yace "ke zan siyowa dan ko na siyo mata ai kece zaki cinye dariya ta kwashe dashi tace "ai babu komai dady kai da kaya duk mallakar wuya ne,sai da suka gama barkwancinsu sannan ya sa kai ya fice har jikin motarsa ta takashi suna barkwancinsu ya shiga direbansa yaja tana daga masa hannu..."
Mmn sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 24
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
......Tun lokacin da muradi ya kasance a gidan hajiya aysha tunanin bai dauke masa ba duk daren duniya sai ya zubar da hawayen bakinciki abinda mahaifinsa yayiwa mahaifiyarsa da sadiq da shi kansa , zuciyarsa na tsananin kewar mutane hudu da suke da matukar muhimmanci a rayuwarsa mahaifiyarsa, kakarsa hajiya kayi , inna jimila da bai san a wani hali take ciki ba da hajiya sallah wacce tayi kokarin bawa rayuwarsa gudunmawa, zuwan da samir keyi ke ɗan ɗauke masa kewa wani lokacin ,duk sanda ya wuce gidansu sai tunani ya tsarkafi zuciyarsa a lokacin babu abinda ya fi bukata kamar d'aura idanunsa akan mahaifiyarsa , soyayyar mahaifiyarsa na makale da zuciyarsa duk runtsi duk wuya, haka duk saukar numfashinsa da soyayyarta yake sauka ya kasa manta komai nata ya kasa manta irin rayuwar da suka yi kullum gani yake tamkar a lokacin komai yake faruwa daidai da rana daya bai taba jin qaunar mahaifinsa a zuciyarsa ba illa muguwar tsanarsa da yake ji ,babu abinda yafi daga masa hankali kamar yadda ya nemi diary din data bashi ya rasa a lokacin da zasu taho babu abinda ya mallaka nata sai wannan diary din mai dauke da wasu kudi a cikinsa , kudin da yake ji ba zai iya rabuwa dashi ba duk runtsi duk wuya komai tsananin yunwa da kishinruwan da riski kansa aciki bazai tabasu ba domin tunawa da wani abu daya fito daga hannun mahaifiyarsa sai gashi ya nema ya rasa wanda yake da yakinin sadiq ne ya dauka a dalilin kudin dake cikinsu dan ya sha takura masa akan ya bashi kudin ya rasa me yasa sadiq yaki kwantar da hankalinsa ya zauna guri daya domin bin umarnin mahaifiyarsu shi a halin yanzu da yake a wannan lokacin yafi bukatar kudin tarihin mahaifiyarsa akan kudin duk shima yana ganin abu ne mai daraja da tattalawa agurinsa ."
duk da hajiya aysha na matukar kokarin sosai akanshi a dan kwanakin da yayi amman still zuciyarsa ta kasa samun natsuwa , zuciyarsa tayi nisa akan hukuncin da zai dauka akan azzalumi mahaifinsa wanda shi ya ciresa a wannan matsayin , ya yarda ya amince zai cigaba da zama a gurin hajiya aysha ya karasa rayuwarsa ta data yi masa saura baya jin zai tsaya ko agurin dangin mahaifinsa ne gara yayi nesa da rayuwar mahaifinsa da danginsa, wani lokaci kuma sai yaji kamar ya tattara ya shiga duniya kamar yadda sadiq yayi yaje duk inda Allah zai kai shi yayi rayuwarsa ya bar rayuwar mahaifiyarsa a hannun Allah a duk inda take daman kuma rayuwarta ba'a hannunsa take ba amman idan ya tuna mahaifiyarsa na bukatar