Showing 489001 words to 492000 words out of 495987 words

Chapter 164 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

da jikinsa "wato ke kinsan ta kan mugunta kou ai kuwa zaki jiki wallahi "am really sorry daman gobe nake cewa zamu dawo, kinsan Allah daga nan bazaki ko'ina ba sai gida dan na gaji da zaman kadaici ni kadai a gidan kamar wani maye ko'ina yayi min shiru babu dadi ko kaɗan ,ta kwashe da dariya" to ka bari na shiga na dauko mayafi na ya kalli kan kujera inda hijab din mumy yake ya nuna mata da baki "to bari nayi wa mumy sallama "shi kuma rantsuwar da nayi fa babu yadda ta iya ta dauki hijabi din mumy ta zira shi kuma ya saba mother a kafad'ansa ya kwashi iyalinsa sai gidan suka bar mumy dasu aryan dan suma yanzu basu qaunar barinta suje wani guri ko sunje kuwa basa iya bacci sun fi so sujisu a karkashin kakannensu kamar yadda ta sabar musu ."

gida daga su sai mother hakan yake basu damar cin karensu babu babbaka dan kullum ganin junansu suke tamkar sabon ango da sabuwar amarya Allah yayi musu kyakkyawar turba, a yanzu kisna ta zama mudubin gidan muradi baya ganin kowa a gabansa sai ita bama gidan ba hatta family dinsu kowa cikin qaunarta yake daman ita ce damuwarsu , yanzu kwanciyar hankalinta ya kwantar da nasu ,
kullum cikin sa albarkar iyaye take musamman mahaifinta ji yake kamar ya bata rayuwarsa a dalilin farinciki da take bawa muradnsa mahaifin nawal ya kira muradi yafi sau babu adadi amman bai daukan  kiransa  nawal ta fashe masa da kuka dady "nace maka ka nemi iyayen goyonsa wallahi nasan zai maidani nifa da shi kadai zan iya rayuwa idan babu shi mutuwa zanyi tunda mahaifinta ya runtse Idanunshi bai buɗe ba yana taya diyarsa bakinciki da jimami  yana matukar son nawal a rayuwarsa  kasamcewar ita  kadai ce lafiyayyen acikin yaransa babban dansa nakasashene komai sai an yi masa diyarsa ta biyu halima ta dade da mutuwa gurin haihuwarta ta biyu sai nawal shiyasa ya dauki dan duniya ya daura mata sam baya son damuwarta yaso ta hakura da muradi ne ta samu wani ta amman tunda ta nace babu yadda zai yi dole ya nemi alhj realwan ."

a lokacin mahaifin nawal ya nemi dady domin ayi sulhu yace babu komai komai ya wuce ta shirya dawowa d'akinta cikin satin waya kawai dady yayi wa muradi yace babu komai ya amince amman yace ya tainakesa   ya fadawa  kisna da kanshi  dan shi bazai iya  fada mata ba "kenan tsoronta kake ji ?"a'a dady bana dai son ganin bacin ranta ne to shinkenan kazo min daita yau da daddare suna gama waya ya kira afra yace tazo itama  yana son ganinta ."da misalin karfe takwas  suka kamo hanyar zuwa gidan dady ,kisna ta kalli muradi taga duk baya cikin farinciki ransa a hade "wai lafiya kuwa tun d'azu nake kallon yanayinka wani iri ?,babu komai ya fada yana damke hannunta cikin nashi  ya ɗan waigo inda take ya sakar mata laulausan murmushi suna zuwa suka iske ya badamasi zaune yana jiran fitowar dady hannu muradi ya bashi suka gaisa cike da girmamawa haka ma kisna ta gaishe dashi suka zauna byn kmr minti biyar sai ga dady ya fito sanye da jallabiya gbdy suka hada baki gurin gaidashi ya amshi mother yana mata wasa ko cikakken minti goma dady bai yi da zama  ba sai ga afra duk ta rame tsufa ma  ya fara  bayyana ajikinta ,nan take ta sha jinin jikinta ta durkusa har kasa ta gaishe  da dady suka gaisa da kisna batare da sun gaisa da ya badamasi da muradi ba a ganinta tunda basa sonta meye amfanin gaisawa dasu ? ."

Falon ya dauki shiru can dady ya kalli afra "kenan har yanzu bakwa gaisawa da yanuwanki?shiru tayi ta kasa cewa komai numfasawa yayi kana ya kwantar da mother akan kujera a nan kusa dashi saboda bacci ya soma ɗaukarta ya kalli ya badamasi da muradi sannan ya fara magana a natse cike ban tausayi " hakuri dai da  kuke ganinsa wani abu ne da yake da falala a addinin musulunci , kusan babu abinda ya kai shi falala saboda Allah subhanahu wata'ala da kansa yana cewa "

إِنَّما يُوفَّى الصَّابِرون أجْرََهُمّ بِغيْرِ حِسابٍ

Lalle masu haquri za'ayi tacika musu ladansu acikin mizanin batare da hisabi ba, duk lokacin da wani bala'i ya fado wa mutun ko kuma a kayiwa mutun wani abu mara dadi amman ya mallaki zuciyarsa yayi hakuri kuma yayi hakurin nan saboda Allah to zaayita rubuta masa lada har iyaka yadda Allah yaso shine abinda Allah subhanahu wata'ala yake nufi me hakuri kadai yake samun irin wannan ladan babu wani aiki da mutun zai yi da za'a yita bata shi lada batare da lisafawa ba ,badamasi ka duba kaga muradi bani na kawo shi duniya  ba yau an wayi gari na kiransa  umarni na bashi na  ya maida matarsa nawal kuma kai tsaye babu ja inja babu jayayya yace min to amman Kai dana haifa yau tsawon shekaru huɗu kenan ina binka tun daka saki afra amman daidai da rana daya baka taba amsa min da zaka mayar daita shin byn laifin data maka akwai wani laifi ne ?yayi shiru yayi  kasa magana " kisna ta kalli muradi da sauri fuskarta da alamar  tambaya da kwayar Idanunshi yayi mata magana ta zagmasa harara tana kawar da fuskarta "ko kisna da tayi  mana laifi ta 'bata mana rai  ta musguna mana ta nuna mu din ba komai bane,  ta wulakanta mijinta ta tozartashi yau gata a karkashin mijinta sun cigaba da rayuwa me yasa bazaka yafe mata ka dawo daita ba ?dady ya karasa maganar yana ƙoƙarin zubar da hawaye atare suka dawo gabansa gbdy suna kuka har afra "kayi hakuri dady ka daina masa maganata wallahi na dade da cire zan sake zaman aure da ya badamasi ,dady ya shiga girgiza masa kai "yana tausayinta yana tausayawa iyayenta shekarunta na tafiya duk sauran yan'uwanta suna gidan  mazajensu "ni dai nafi qaunar ganinki a karkashin ikonsa idan har zai iya min wannan alfarma" zai mayar daita a gobe nan  tunda haka shine farincikinka numfashi dady ya sauke sannan ya mike yana cewa kisna ta biyosa , ta shiga d'akinsa ta gansa zaune a bakin gado ta samu guri ta zauna a kasa qirjinta na luguden bugawa  "kisna mijinki zai dawo  da nawal sai dai yace yana gudun damuwarki to karki yarda ki nuna masa bai isa ba a gidansa, kada ki kawo masa hayaniya ko tashin hankali ki zauna lafiya da abokiyar zamanki ,idan ma bata biki ba ke ki bita ku zauna lfy ba wani abu bane duniyar ma guda nawa take nasiha sosai yayi mata mai ratsa jiki tana kuka har da shesheka ita ba dawowar nawal din ne bata so ba tashin hankali take gudu dan sam bata ga ta inda take son su zauna lafiya ba , gashi ita yanzu ta saba da rayuwa ita kadai da mijinta .."

acan falon ma muradi tashi tayi ya shiga dakin mumy ya bar afra tana kuka ,ya  badamasi ya  tsira mata ido yana kallonta  tana kuka ",kin cire rai da zaki sake zaman aure dani saboda  bakya sona ?'ta d'ago idanunta a hankali ta tsura masa sai dai ta kasa bashi amsa illa ta mike ta juya ta fice a falon yana zaune yana kallon bayanta dan dole zai maidaita ko babu darajan Iyaye shi kansa danne zuciyarsa kawai yake amman akwai soyayyarta  me karfi  a cikin zuciyarsa ."akan hanyarsu kisna ta komawa gida kuka kawai take muradi na rarrashinta tace"  taji amman kafin nawal ta dawo ya gyara mata saman gidan ta koma yace an gama ranki shi dade duk abinda kika ce shi za'a yi ko cewa kika yi baza'a dawo da nawal ba dole ne  a bi dokar uwargida sarautar mata  "ka jika kamar idan nace zakayi  ne ?,zan yi mana me zai hana da a min rikicin gangan gara nabi doka da oda   cikin satin yasa aka gyara mata sabon bangarenta itama nawal ya gyara mata part dinta na da ranar lahadi aka tsara zaa mayar da  auren nawal da muradi ya bada da afra amman sam afra taki sai na nawal da muradi aka mayar   kuma  a ranar ta tare da Ahmed dan yayarta  sai  dai ta dawo gidan ne da shirin zama na dindindin babu tashin hankali har gida mahaifin nawal yazo yayiwa  dady  godiya bisa karamcin da yayi masa dady yace ",babu komai ai an zama daya nawal diyata ce har abada Allah ne ya hadasu da dana dana fi so kuma take qaunarsa kaga dole ne nima na sota." Haka ne Allah ya sake haɗe  kansu sai abu na gaba   Ina neman wata alfarma mahaifin nawal ya fada dady ya fuskancesa ,
akan maganar aikin nawal kayiwa yaron magana domin itace ke kula da wasu daga cikin kasuwancina na kasashen duniya  shiru dady yayi har sanda  ya dasa aya sam baya jin muradi zai amince dan ko kisna da take gabansa a yanzu  bai ji yana maganar zatayi aiki da takardunta ba bare aikin kasa da kasa ,bari dai  na kirasa inji cewar dady  nan take dady ya kirasa yayi masa bayanin komai shima muradin shiru yayi yana mamakin hauka  irin na mutumin sai daya numfasa sannan yace "dady zamuyi magana da nawal din abinda ake ciki zata masa bayani ya tsaya sai dady  ya  kashe  wayar  tukuna  yana jinsa yana yiwa mahaifin nawal bayani  a hankali ya  shiga part  din  nawal   jikinsa sanye da wando jeans baki da riga dark green yayinda kafafunsa ke sanye da takalmin canvers baki haka ma kansa facing cap ne baki  tana  ganinsa ta soma bare baren neman gindin zama ya zauna yana  dubanta  ta tsiyaya masa  ruwa acikin glas cup ta mika masa bai ki amsa ba,  ya  sha  kaɗan  ya  mika mata  "da zamuyi aure a tun farko  munyi  alkwari dake cewar zaki ci gaba da yawo kasashen duniya ?tayi saurin cewa a'a ,to me yasa yanzu mahaifinki yazo wa dady da batun ?gaskiya ban sani ba amman zan kirasa ,well wanan ya rage naki idan zaman aure zakiyi idan yawon kasashen duniya sai ki zabawar kanki   yana gama fadar haka ya mike ya fita ta sauke naunayen ajiyar zuciya gara tayi zaman aurenta ya fiyye mata alkhairi dan babu komai acikin yawon zuwa kasa da kasa sai zubar da mutunci ka dinga cudanya cikin maza zuciya kuma bata da kashi  nan take ta kira mahaifinta ta sheida masa ita zaman  aure  zatayi  ga lawan idan ya qara tasawa ya maye gurbinta lawan dan farin yayarta halima ne yana daf da karasa karatunsa a London ."

****
Babu  laifi kisna ta dan sakarwa  nawal  fuska, nawal na zuwa saman kisna itama tana zuwa nata sai dai ita kisna bata fiyye zuwa ba gaskiya sannu a hankali suka ci-gaba da rayuwarsu tana jan su aryan ajiki sosai a duk sanda suka zo gidan zata dinga haba haba dasu tana nuna tana bala'in son su din nan, barin ma idan akwai idanun mahaifinsu haka ne yasa muradi ya fahimci sauyawarta kuma yayi farinciki , duk kuma lokacin daya shigo da mother zata amshi yarinya tana mata wasa idan yana bangarenta tare zasu wuni itace komai nata muradi ya cigaba da daukar nauyin karatun  Ahmed dan shekara bakwai yana  mata fatan samun nata , tafiya tayi tafiya shekarar  mother biyu  kisna ta samu ciki wanda ita kusan bata so haka ba sai dai tayiwa kanta alkwarin bazata sake cire ciki ba haka zalika bazatayi planing ba zata haifi abinda Allah ya qaddaro mata dan tasan mutuwa da rayuwa duk na Allah ne , ai  nawal na  fahimci tana dauke da ciki nan kishinta ya motsa ta soma shan kamshi , ta daina zuwa bangaren kisna  a lokacin data fi buƙatar taimakonta   ko haduwa sukayi sai tana jiran  kisna ta gaisheta ita kuma idan tayi yau tayi gobe sai tayi mata ba sai hakan na neman ya kawo gaba a tsakaninsu amman hakan kisna ta  dauke kanta ta cigaba da tsagoginta dana mijinta dan gbdy ta gano abinda yasa ta sauya har ma akan yaranta idan sun so idan babu idanun ubansu ko kallo basu isheta ba Amman da zarar ta gansa zata fara rawar jiki ."

akwana a tashi babu wuya har cikin kisna ya kai wata  shida alokacin ta dan  samu lafiya ,ya fito  abin sha'awa sai yayi mata mugun kyau yayinda nawal kullum idan ta kalli kisna da ciki sai zuciyarta ta motsa  tayi  kukan zahiri dana bani di, cikin take so ta kowani hali  amman yaki zuwa wata kanwar mahaifinta ce ta samo labarin me magani haihuwa a Sudan ta hanyar wata kawarta dan haka ta sanar da mahaifiyarta nan fa suka sheidawa muradi bai hanasu ba dan shima yana son Itama tasamu nata  , sun isa lafiya ta sha magani iri iri an basu wani da alkwarin tana dawowa sai ciki satinsu biyu suka dawo da takamar nan da wani lokaci zata haihu sai dai har wata uku wanda yayi daidai cikin wata tara  bata samu  Cikin ba ,cikin kisna ya tsufa  sosai suna jiran edd dinta sai dai a daren wata laraba ta tashi ciwon nakuda daman tun magrib tana jin ciwo sai dai tunaninta ai lokacin da'aka bata bai yi ba shima gogan yana lura daita idan yaga ta cije sai yace "yaya dai baby love kodai zamu hospital ne ?sai ta yatsina fuska tace babu komai fa ta tashi da kyar ta sauko daga kan gadon ya tashi shima ya taimaka mata ta sauko yace ",ina zuwa ?fitsari zanyi ya riketa suka shi ga toilet tana tsugunawa taji kamar an sauko mata da ciwon duniya ta hau nishi nan muradi ya rikice ya fita aguje ya kira aunty ummi  ya shiga ya taso nawal  ta tashi  Itama a rikice ta biyosa yaje ya fito da mota shida nawal suka riketa  suka sata a mota duk dauriyarta sai da hawaye ya zubo mata tana salati tana cewa akira mata mumy da dady shima idanunsa ya fara cikowa da hawaye sai zabga gudu yake yana mata sannu gudu yayi sosai atare  suka isa asibitin da aunty aummi  ai yana gama parking ya fito  sai ɗaukarta yayi dan kasa tafiyar tayi dan kafafunta sun rike sai ciki a gaba daya sauko kasa aka shiga daita labor room   mintina Kadan doctor ta fito dake sun san aiki za'a yi mata suka fara shirin aiki ana aka mata shirin aiki ai ana shirin shiga dakin tiyata daita tayi wani nishi sai ga kan da karasa shiga daita akayi ta haihu da kanta likitoci kansu sun jinjina wannan  girman al'amarin na  Ubangiji  murna kuwa agurin muradi kamar ranar aka fara haihuwa a gidansa kudi masu yawa ya dauko ya bawa nurse din data masa wannan albishir nan ya zaro waya yana fadawa mumy , madala mumy tayi a waya tana wa Allah kirari tace gata nan zuwa yace mumy shabiyu  dare yayi tace" kai gafara can in samu jika kace min inyi jinkirin zuwa cikin minti talatin direba ya kawo mumy alokacin har an gyara kisna tana dakin hutu ita da kyakkyawar diyarta sannu da kokari baby love Allah yayi miki albarka abinda muradi yake fada kenan ita dai sai murmushi take ita kanta cikin tsananin murna take ta haihu da kanta "..

washegari gari aka sallameta byn an tabbatar da babu wata matsala da sassafe sai ga su aunty  mufeeda  ta zo tare da aunty Zahra har ma da afra  kafin yamma gida ya cika makil  da dangi ranar suna kowa yayi tunanin sunan mahaifiyarsa zai sa wa baby sai kawai sukaji sunan aunty ummi Aisha murna har da rafka buda tayi ,suna na kece raini akayi kuma me kayartawa  kaya iri daya muradi yayi musu ita da nawal byn suna kowa ya watse aka bar aunty ummi sai da tayi sati sannan ta koma gidanta  haka da rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi da kwanciyar hankali agurin kisna ,kisna ta gina gidanta cike da ni'imar qauna soyayya da kwamciyar hankali wanda kula da junansu da kulawa da soyayya shine ya haifar musu da haka kowannensu na kokarin sauke hakin dan'uwansa tare da kyautatawa , duk abinda kisna tagani na maza muddin yayi mata kyau zata siya ma muradi  tunda yanzu da kudinta wanda kasuwanci ke kawo mata ga gidan mai ga supermarket da mijin kwarai ya mallaka mata  har karshen rayuwarta babu shakka mijinta kyautar Allah ne  shekarar Aysha daya da rabi ta sake haihuwar namiji shima da kanta yaci sunan Aliyu suke kiransa da papi nawal ta dauki soyayarsa papi ta saka aranta komai ta samu papi ne ita kuwa kisna ido ne nata duk har cikin ranta bata son nawal din na shiga tsabgar ƴaƴanta tunda ta lura soyayyar bata Allah bace ta ganin ido ce ."

Bayan shekara shida a lokacin kisna nada ya'ya biyar aryan arif ,mother da aisha mai sunan aunty ummi papi mai sunan muradi ga wani sabon ciki ajikinta yayinda har lokacin ko batan wata nawal bata taɓa yi ba kullum dai tana kan yawon neman maganin haihuwa bata hospital bata ga na gargajiya  muradi ya tabbatar mata lokacin ne ta kwantar da hankalinta muddin tana da lafiya kuma spam dinsa ke dinga ya'ya a cikin kisna itama zata haifi nata duk sanda ya fada mata haka jinsa kawai take dan gani take bai damu da rashin haihuwarta ba tunda yana da wasu ya'yan .

Ranar wata laraba aunty zee tazo duba jikin kisna dan laulayi ya fara sakata gaba suna zaune tace "ke dai kisna abun yayi miki yawa ga laulayi ga wahalar nakuda ,to ya zanyi aunty zee?  qaddarata kenan Allah dai yasa muci amfanin ya'ya ameen aunty zee ta amsa ya kuwa zamanku da nawal babu wata matsala ko ?,to gaskiya dai matsalar da sauki sai dai ta iya makirci ni kuwa bana ma son na iya ,ai makirci bai yi ba a zaman aure ace sai da makirci ai mugun abu ne kowa dai ya zauna da halinsa ,ato zan zauna da halina bazan koyi halin banza ba sbd wata  kishiya yanzu ko bako mukayi zai dauka nice mara kirki ni

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login