Showing 99001 words to 102000 words out of 495987 words
Chapter 34 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
wacce taji kayan hadi bayan ya gama ya koma sama , a daren ya hada kayansa da kanshi cikin qaramar jaka dake dauke da zanen kwallo da tambarin sunan club dinsu , bawasu kaya ya diba ba saboda kowani kasa da yake buga wasa yana wadatattun kaya wanda ba tsiya yake ba kamfani ke bashi ."
har 11 :00 ta buga bai runtsa ba sannan bai ga shigowar kisna ba bai damu ba yayi kwanciyarsa bayan yayi waya da mumy da dady kafin bacci ya daukeshi wayar nawal ce ta shigo ya ɗauka ya duba da kamar bazai amsa ba sai kuma ya ɗauka saboda ba lallai ne ta sameshi a waya ba idan ya tafi , har bacci ya daukesa nawal na zuba masa surutu akan yadda take son shi jin shiru baya magana ta katsen kiran itama ta kwanta dan ta fahimci yayi bacci , karfe hudu daidai ya farka yana mika haɗe da salati ya fada bayi domin yin wanka tare da dauro alwala ya fito ya shiya cikin hadadden sult ya daura agogon dioman a tsintsiyar hannunsa tare da fesa turare a jikinsa da bayan kunnensa ya rataya jakarsa ya fito daga dakin har ya wuce dakin mumy ya dawo da baya da baya ya tsaya a bakin kofar saboda zuciyarsa ta tabbatar masa da kisna na ciki , yasa kafarsa ɗaya ya buga kofar da karfi kamar zai balla ....."ya Allah ta furta tana farkawa daga baccinta tare da kamkame jikinta guri daya a hankali ta fara karanto addu'ar neman tsari daga bala'in sa , a zafafe yace "ki bude kofa ".
"nayi maka me ? ta fada cikin karfin hali ,nifa banason tashin hankali da sanyi safiyar nan , tafiya zakayi ka tafi Allah ya tsare ya bada Sa'a "ko baki min addu'a ba zan yi nasara tunda uwata tayi min kuma wallahi kin taimaki kanki da kika boye kanki da jikinki ya gaya miki "tun da kana jin karfi ai sai ka balla kofar ka shigo ka kasheni ta fada masa a tsorace "da kyau ai ina son haka ki jira dawowata sai dai idan ban iske ki a gidan ba amman wallahi sai na .... ƙarar sautin wayarsa ce ta katse shi ya ciro yana duba screen din wayar tare da manna wayar a kunneshi ya barin kofar dakin ..."
Ba ita ta fito daga d'akin ba sai da taji sautin muryar aunty zee ta dawo da natsuwarta jikinta "ya naganki a firgice ? Numfashi ta sauke tace "nida ya Aliyu ne tun jiya dana shiga dakin nan na kulle kaina sai yanzu na fito ke ina ganin kwaso kayana ma zanyi na dawo nan wallahi bazan iya da balainsa b "me kuma ya faru da zaki raba daki da mijinki ke da kike cikin sharadi ? A hankali ta fara zayyanowa aunty zee duk abinda ya faro ,aiko ta dinga dariya har da rike ciki "wallahi kisna baki da kirki amman kuma kin yi daidai gara da kika masa haka "ai ina ganin zan fara nuna masa ajina na nan bai je ko'ina ba dan sakar masa da nake yasa gabadaya ya rainani wai har da cewa sai dai bai dawo ya sameni a gidan nan ba kamar wata yarsa ke wallahi na ma fasa dawowa dakin nan a can zan cigaba da zama ya dawo ayi burouban da za'a yi ..."
"ke ban son cika baki kiyi kokari dai komai ya daidai tunda dan rainin hankalin ya fara shan baki ina ganin ya Kusan zuwa hannu "tab wannan mai shegen taurin kan abinda ma shan bakin yana sha yana cika yana batsewa kamar nace dole ya sha "kai ya Aliyu sai a hankali zuciya kamar da karfe aka ginata yana magana cike da izza da nuna mutun ba kowa bane mutun kamar dan gidan saurata koda yake a duk jirgi ɗaya ya kwaso ku ke dashi "a'a wallahi muna da bambanci kisna ta fada da sauri nan dai cigaba da magana akan muradi ..."
Karfe daya suka tashi suka shiga kitchen kasancewar kayan abinci a bangaren kisna yake jollof rice suka dafa anan suka wuni suna hira wanda rabin hirar duk ta muradi ce tsawon kwanakin uku suna zaune a bangaren kisna ranar da su muradi zasu buga wasa kuwa kisna manta komai tayi ta tare agaban tv , muradi kawai take kallo sanye da wonda da riga dark blue Wanda aka rubuta muradi a bayansa yayi maseefar kyau sai ya saje da fararen fata , sai kwace kwallo yake a kafar abokan karawarsu yana bugawa yadda ransa ke yaso ,idan aka dauke fuskarshi kisna taji wani mugun haushi , idan aka haskoshi ta dinga murmushin kenan tamkar wacce aka yiwa bushara da gidan aljanna duk aunty zee na lura daita tayi murmushin tana dafata "muradi fa ya tafi da rabin rayuwarki autar mumy " bata kalli inda aunty zee ke zaune ba ta maida mata amsa da "ba rabin rayuwata ya wuce dashi ba gabadaya rayuwata ya tafi dashi shi yasa na kasa ciresa araina ,sai dai duk da haka bazan sake daukar wulakaci daga garesa ba wallahi duk yayi min sai na rama saurin mikewa tayi haɗe yin tsalle cikin jin dadi sakamakon muradi ya wulla kwallo cikin raga ba ita dake tsallen murar ba hatta abokansa murna suke gabadayansu suka rungumeshi , bayan wani lokaci aka cigaba da wasa sun dauki tsawon lokaci suna fafatawa babu wanda yayi nasara sosai muradi yake kokarin jefa kwallo cikin raga wani abokin buga wasansu messi na tauyesa babu zato yasa masa kafa tare da dukan qirjinsa take muradi yayi kasa rike da qirjinsa kisna ta dafe kirjinta da duka hannuwanta taji kamar qirjinta aka taba gabadayan zuciyarta ta jagule kamar ta dora hannu aka ta sa kuka ganin an rufesa har reaf .
ta fashe da kuka tana kamo hannu zeey cikin nata tare da tsine wa wanda ya hardeshi take aka sake hasko yadda abun ya kasance tabbas mugunta abokin wasansa yayi masa, reaf dake tsakiya ya janyo mesi gefe yana bashi warning tare da yi masa magana kasa kasa "ka daina buga wasa haka sai kayi lossing tun ba'a je ko'ina ba ko da yake na lura ka sakawa muradi ido da yawa, cikin tsananin jin haushin maganarsa messi ya soma magana yana daga murya reaf ya juya ya barshi ya karasa gurin muradi dan tuni likitansu ya karaso da wata karamar akwati ya tsugunna a gabansa ya soma duba lafiyar ,muradi dake kwance ya damki sumar kanshi dake kwance luf luf gwanin ban sha'awa da hannunsa daya, yayinda dayan hannun ke dafe da qirjinsa ya runtse idanuwansu kisna kamar ta fasa tv ta shiga dan dawowa tayi gaban tv ta zauna tana kuka , cikin kankanin lokaci aka masa abinda ya dace ya dawo daidai aka ce ya fita a canza wani a madadinsa amman yaki dan haka aka sake komawa wasa dashi , har kusan sau uku ana bawa messi warning akan muradi dan zuwa yake yayi atttakig dinsa har sai da aka bashi yellow card, hankalinsa bai dawo jikinsa ba sai da aka ciresa gabad'aya aka bashi read card , ranar cikin sa'a team dinsu muradi suka lashe su 3-0 .
washegari ma aka sake hadasu da wasu team din still suka cinye har aka je final still dai sune suka cinye
Ranar cike da fara'a kisna ta yini daga karshe ta shige daki tayi kwamciyarta zuciyarta na tunanin muskilin mijinta ...
Satinsu biyu suka soma shirin dawo wa kasar cairo ,Samir yayiwa aunty zee tsaraba sosai yayinda muradi yayi fuska duk da yaga abubuwan da zasu dace da kisna amman yaki siya ,ganin haka yasa Samir daukar mata yana zolayarsa , misalin takwas saura na dare tana kwance a falo ta runtse idanunta sai dai ba bacci take ba ta dukufa ne gurin nazari da tunani , sam bata ji motsin shigowarsa ba ,yayinda shi kuma yayi tsaye akanta yana kare mata kallo da kallon falon komai tsaf tsaf very neat kamar yadda yake bukata ga kamshin airfreshner na tashi gauyare dana turarenta ita kanta a tsaftace take tayi kyau sosai cikin doguwar riga kamar an tsinkareta ta motsa haɗe da bude idanunta taga mutun tsaye a gabanta wani irin mummunar faduwar gaba taji sai dai bata nuna masa ba tayi masa kallon sama da kasa tace "sannu da zuwa ta dauke kanta akanshi ya ajiye jakar hannusa yana cigaba da kallonta cike da takaicinta "wato ma dan samun dama taci ta koshi ta hau bacci ganin yadda yake kallonta kuma bata manta da yadda suka rabu dashi ba ta mike tsam tana kokarin bawa kafarta iska sautin muryarsa taji "tunda nake ban taba ganin wawiyar yarinya irinki ba....."
da hanzari ta tsaya tana dubansa da idanuwanta da suka kada zai sake magana ta katseshi ta hanyar daga masa hannu "enough muradi ya kamata zuwa yanzu kana sanin irin maganar da zaka dinga fada min, karka manta nifa ba yarka bace matakar ce ita kuma mata ba kowace magana zaa dinga fada mata ba, ka lura ka hankalta kuma gane kisna tafi ƙarfin wannan tozarci dan haka kayi ka dawo taitayinka , idan ba haka nan kusa zaka tantance tsakanin aya da tsakuwa taja tsaki tana sakar masa harara tayi gaba abinta tana rausaya abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa ayi masa tsaki a wuce shi ji yake kamar ya mutu ya gwamaci shi yayi da ayi masa , biyota yayi cikin zafin nama aiko ta kara sauri sai dai akan step ya cafkota ya damki naman cikinta zuciyarta ta soma sarewa da lamarinsa daga dawowarsa abin nasa yafi karfinta hawaye suka gangaro mata "wannan wace irin tsana ce haka" ?
Da kyar ta fixge jikinta tana masa harararsa da yi masa Allah ya isa ta shige dakin mumy tun kafin ta saka key ya banko dakin ya ɗauketa da mari "bayan tsaki har da Allah ya isa ni sa'anki ne dukan tsiya mata ,sai da yayi mata lilis sannan ya samu guri akan kujera ya kallonta tana kuka "muddin zai fada ta fada bazai raga mata ba ya dinga gallazawa rayuwarta kenan har sai ta shiga hankalinta" zaki yiwa mutane shiru ko sai na an kawo min kyankyasai ?tana jin haka tayi shiru ta daina zubar da hawaye sai shesheka "shima sheshekan kuka bana son jinsa dan kin cika min kunne kuma na sake jin kin kirani da muradi sai zubar miki da haƙora wawiya kawai ". tashi tayi gbdy ta shige bayi , tunda ya dawo bata sake bari sun hadu dashi ba ,shima bai fiyye zama a gida ba kullum sai ya fita acikin kwananki harkoki sun masa yawa training da office saboda zasu sake fita German buga wasa yadda ya fita tsabgarta haka itama ta sharesa babu mai shiga tsabgar wani sai ya wuce ta wuce .."
*********
da wani yammaci da misalin karfe hudu tana zaune akan doguwar kujerar hannunta rike da waya tana magana da mommy yayinda idanunta ke lumshe ,kamshi turarensa ne yasa ta bude idanunta suka sauka akan shi yana saukowa daga mattatakala sanye da gajeren wando baki da karamar riga fara irin ta yan kwallon hannusa rike da kwallo yana bugawa har ya sauko daga step ya fita zuwa wajen idanunta na kanshi , sake lumshe kyawawan idanunta tayi" Aliyu ba dai kyau ba komai kyau yake masa cigaba da waya sukayi da mommy daga karshe ta hadata dasu areef ..
Shi kuwa aliyu kai tsaye field din gidan ya nufa inda Samir ke jiransa shima sanye cikin irin kayan dake jikinsa tun kafin ya karaso zee ta hura husir tana karfafawa mijinta gwiwa "karka yarda ya cinyeka kamar sauran lokuta "Kima daina bata bakinki yarinya dan kamar na cinyesa na gama idan dai wannan mijin naki ne da bashi da momora sai aiki cin tsiya Samir yayi dariya yana tafa hannu yace " sharesa baby duk ya gama cika bakinsa daga karshe Allah ya bani Sa'a akanshi ba". Aliyu ya saki kwallo aunty zee ta sake hura husir suka fara wasa da kwallo.."
Ganin har kusan minti goma suna fafatawa a tsakaninsu kuma har lokacin babu wanda yayi nasara cinye d'an'uwansa, sai dariya take ita kadai, idan taga Aliyu zai cinye mijinta da sauri zata sa ihu kamar zatayi kuka haɗe da daura hannuwanta saman kanta ,idan kuma mijinta ke kokarin cinye Aliyu sai tayi ta bashi kwarin gwiwa tana kiran "Samir !Samir !!Samir !!!
Haka nan tayi tunanin taje ta fito da kisna itama tayi kallo koda aunty zee ta shiga parloun ta isketa zaune ta tallafe gwiwar hannuta da filo data daura a saman cinyarta ta tallafe kumatunta da tafukan hannuwanta tana tunanin mijinta da auren da zai yi "kisna stop overthinking "me ke damunki mai yasa kike wannan dogon tunanin"? "Idan kika kashe kanki da tunanin ya Aliyu babu ruwansa ya'yanki zakiyiwa hasara ".
Taja numfashi ta fesar tana