Showing 72001 words to 75000 words out of 495987 words

Chapter 25 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

cewa" ku shigo muje wannan sarkin zuciyar ya hau sama ko wa ya kunnosa oho?.
jiki kisna a sanyaye ta shiga gidan baya idan aunty zee ke zaune hira Samir yake masa amman yayi masa banza aunty zeey tace "ranka shi dade dan allah ina son siyan wasu dogayen riguna .Aliyu bai ce mata komai ba sai gani tayi ya faka a bakin *kaafor mall* batare da yace uffan ba .
"muje kisna bani da abinda zan siya aunty " tayi magana muryarta can kasa "Ke dai muje ta bude bangaren da take ta fito suka shiga rike da hannun aryan ."

Samir yace Aliyu tun d'azu ina maka magana amman ka shareni me yasa kake takurawa rayuwarka ne kana son kisna me yasa bazaka manta komai kuyi rayuwarku ba tsaki yaja "dan Allah karka daga min hankali banason damuwa " malam ka bada kai bori ya hau kaima ka dinga shiga sawun ........
"Please Samir mai yasa har yanzu ka kasa fahimtata ne ?sanin kanka ne soyayya bata gabana ko nawal daka ga zan aura tausayi ne yasa zan aureta ba wai soyayya ba, idan kuma soyayyar zanyi kisna bata cikin jerin matan da zan iya so kayi hakuri idan maganata ta maka ciwo "

Tsaki Samir ya ja "dadina da kai wallahi taurin kai kamar mutanen farko yarinya tana sonka yanzu ka bata dama kaki " takaici ya rufewa Aliyu zuciya ya bude murfin kofa da karfi ya fito a kufule tare da saba areef a kafad'ansa Samir ya biyo bayansa yana cewa "gaskiya lamarinka akwai gyara ana gabas kana yamma kana bukatar addu'a Allah zan fadawa momy ta mike tsaye a samu ka soma soyayya "dan Allah ka rabani da batun soyayyar nan bani da lokacinta ...."

Cikin mall din suka shiga kai tsaye Aliyu yayi layin takalman yara suna tafiya suna hira da Samir har suka karaso kusa dasu aunty zee, muryarsa tasa ta jujowa idanunta ya sauka akan Samir "baby ta kira sunansa ya waigo da hannu tayi masa alamar yazo ya karaso ya tsaya a bayanta tare da daura kanshi a kafadanta "ta yani zabar kanana kaya kema kisna Ki zabi wanda kike so yayanki ya biya ,kananan kaya masu yawan gaske da dogayen riguna masu kyau ta dinga ɗauka ,duk abinda ta gani indai ya burgeta sai ta ɗauka ganin kisna ta ki ɗaukar komai ,yasa ta dinga zabar mata bom short da riguna masu kyau wanda zasu dauki hankalin mijinta sannan suka kara gaba suka bar kisna dake tsaye rike da hannun aryan kamar ance ta juya bayanta idanunta ya sauka akan mutumin d'azu yana tsaye rungume da hannuwansa duka a qirji ,tsura masa ido tayi tana kallonsa mutun kamar aljani har zata bar gurin taga gara kawai ta tsaya ta fada masa gaskiyar ita din matar aure ce ya daina binta a hankali ya karaso ya tsaya a gabanta yana kare mata Kallon tsab irin typing din matar da yake so ce ya dade yana neman irinta bai samu ba sai yau sautin muryarsa taji ta doki kunneta "tunda nake arayuwata ban taba ganin halittar data ɗauki hankali ba irinki dan Allah kibani dama na zamo abokin rayuwarki, farinciki da bakinciki ne suka hade mata a lokaci daya ,ga mijinta na tsananin nuna mata kiyayya ,ga wani na mata naci ta so shi wanda a yan sakonin da suka gabata ya daura idonsa akanta batare da yasan ko ita din wacece ba ."
Ta tsuke karamin bakinta gashi dai magana take son yi amman ta kasa sarrafa harshenta kawai ta juya zata wuce yayi saurin shan gabanta " ki tsaya ki faɗa min sunanki da address din inda kike kafin ki wuce dan bazan bari ki subuce min ba saboda na dade ina nema irinki ...."😳

Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: .💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Free page 11
~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰


A  matukar  harzuke  ta shiga dakin zuciyarta  kamar  ta kama da wuta , tana k'arasa  shiga  cikin filin d'akin   idanunta  ya  sauka  akanshi  tsaye a tsakiyar  d'akin  ya zuba hannunwansa  duka  a cikin  aljihun wandonsa  yayinda idanunshi  ke runtse yana ciza gefen lip's dinsa na kasa  a hankali  , duk  da  bai  bude  idanunsa ba yasan  itace ta shigo dakin duba   ga  yanayin  da  yaji bugun  zuciyarsa  ya  qaru."

  kallon  second  biyu  tayi masa ta ɗauke  idanunta akan shi    ta k'arasa  da sauri  ta  bude wardrobe   ta dauko akwatin kayanta  data  zo  dashi kasar  ta ajiye akan  gado  ta bude  ta soma dibo  kayanta ɗaya bayan ɗaya   tana zuba  aciki  ,still  bai bude idanunshi ya kalleta  ba  bare ya  dakatar  daita daga   abinda take  ƙoƙarin yi  ya cigaba da ciza lip's dinsa , hakan  yasa taji  sabon ɓacin rai ya mamaye zuciyarta  taji  muddin  bata bar masa  gidan   a lokacin ba zata iya mutuwa.."

Aunty  zee  ta shigo dakin   cikin tsananin tashin hankali ta k'arasa  gareta   ta rike hannuta batare da ta kalli inda Aliyu ke tsaye ba  hankalinta a matukar  tashe ta soma magana   "mai kike ƙoƙarin yin   saboda  Allah ? "Kiyi hakuri mana
duk  fa abun bai kai   haka  ba, idan fa rai ya ɓaci hankali baya bata kisna  , ki   dawo  hankali    ki natsu  dan  girman Allah Karki yi abinda zai janyo bacin rai  fiyye da wanda muke ciki yanzu ".Tun da aunty zee ta soma magana kisan bata furta komai ba  ta cigaba  da zuba kayanta cikin akwati zuciyar na wani irin zafi da ciwo , haka  shima Aliyu bai ce komai ba sai sake  juya musu  bayansa yayi yana furzar  da iska mai tattare da bakin ciki ".

Kisna na  shirya kaya  aunty  zee na dauka tana  maida wa cikin wordrobe  tana  bata  hakuri , wani  sabon kuka ne ya kufce  mata , hawaye sai turereniyar zubowa suke daga cikin kwarnin idanunta "mai   kike son nayi aunty  zee   shine fa  da kanshi yace na bar masa gida  "? Tayi maganar cikin tsananin  kuka wanda da kyar muryarta  ta fito  "nasani  amman  dan  girman Allah  kiyi  hakuri ko zaki tafi ba yanzu  ba  saboda tashin hankalin da mommy  zata  shiga  Sam Sam mommy  ba zataji dadi  faruwar haka ba.  tayi maganar tare da juyowa  ta kalli  inda  Aliyu  ke tsaye har lokacin tamkar  babu wani halitta dake motsi agurin, ya aliyu  ka bata  hakuri dan Allah  sannan  ka dakatar  daita dan gaskiya   kayi  kuskure abinda kayi sam   bai dace ". Bazan yayi  daita  qirjinshi na wani irin dokawa da  karfin gaske  "saboda me zai  bata hakuri bayan bai ga abinda yayi  mata  ba  ,idan  zata zauna ta zauna  idan  zata  tafi ta dade   shi  dai bazai  wani  dakatar daita  ba  yayi maganar  aransa yana furzar da iska mai zafi ....

   kisna ta sake  rushewa  da wani sabon  kuka  mai matukar cin rai ganin  ko  kallonsu Aliyu  bai yi ba bare  ya  kula aunty zee dake masa magana   ,ta  d'aura  kanta  a kafad'arta   aunty zee numfashinta na barazanar  daukewa saboda kukan da yaci  karfinta   "kisna  !kisna!!  Aunty zee  ta ta kira sunanta  a rude  tare  da rungumeta  a  jikinta  suka zauna a bakin gado  tana cigaba da kiran sunanta , da kyar kisna ta janyo numfashi ta sauke zuciyar na mata wani  irin  azababben  zafi  da  ciwo ,   aunty zee ta mike ta tsiyaya mata ruwa  a  glass  cup  ta mika mata "ki sha ruwa kisna ko  zaki  ji  sanyi  babu mutsu kisna  ta amsa cup din ta kai bakinta ta  kurbi  kadan  ta mikawa aunty zee  sauran ,aunty zee ta amsa ta ajiye ta  cigaba da bata  baki  .
cikin  haka  aryan  ya shigo dakin yana  kuka aliyu  ya juyo  a hankali yayi taku daya  yana  ƙoƙarin kamoshi  zuwa garesa , amman  tuni   yaron ya  karasa gurin uwarsa dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta , ya haura saman  gadon ya rungumeta  ta baya yana  furta mata  kalmar  "sori  mommy , papa ne ya saki kuka kou  ?" Ki yi shiru Ki daina kuka zan rama miki  kinji  ".
kukanta ne  ya  qara  akan wanda take tabbas ya'ya  rahma  ta  juyo  ta rungumeshi  ajikinsa tana sheshekan kuka  tamkar ranta zai fita,hawaye  tausayinsu ne  ya shiga gangarowa  aunty zee  Aryan ya soma ƙoƙarin raba jikinsa dana kisna ",mumy bari naje na rama miki "a hankali ta shiga girgiza masa kai tana kuka gumi na tsatsafo mata ta ko'ina ajikinka matse aryan tayi gam saboda kokarin fixgewa da yake kokarin yi ajikinta yadda take kuka haka arayan da aunty zee ke kuka gaba-daya an rasa wanda zai rarashi wani   ."

Sautin kukansu ne ya soma damun Aliyu a   natse  ya  fita daga d'akin  yana jan dogon tsaki ya shiga  d'akin da areef  yake  kwance  ya  zauna  a  gefensa tare da tsura masa  idanunshi  yana kallonsa, ganin yadda  numafashinsa ke sauka a hankali yasa shi  sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare ya  d'aura  hannunsa akan sumar  yaron yana shafawa a hankali  yana  jin wani irin sanyi mara misaltuwa a zuciyarsa , dan da wani abu ya samu d'ansa da sai yayi distroye rayuwarta  ,sai  yayi mata abinda har ta  koma ga Allah bazata mantawa  dashi ba taimakonta daya d'ansa yana numfashi kuma ko yanzu bazai barta ba har sai yaga mikewar d'ansa tukunan zai saurara mata    ..."

"Idan   kika ji  ancewa  mutun yayi  hakuri   bisa wani abu daya faru to an cucesa  ne ,ki qara hakuri kisna  idan kika  bar gidan Aliyu da sunan yaji ko rabuwa  dashi  ina zaki "?"kin san dai baki  da inda zaki sannan baki da masauki  a gidan dady  idan  kin  manta  abinda  dady  yace bari  na tuna  miki "cewa yayi matukar ba ziyarar arziki ce  zata kowaki  gidansa ba  baya son  ganinki da suna matsala dan   baki a masauki a gidansa, kuma duk  ranar da kika kashe aurenki da Aliyu  sai  dai  ki  nemi wani uban amman  ba shi ba, zan rokeki  da ki kara  hakuri kisna  ki zauna a d'akinki  kada ki ɗauki maganar Aliyu  da  mahimmcin  da zai sa ki  bar gidan nan ". wani sabon kuka ta rushe mata  dashi  tare da zubewa kasa bisa gwiwowinta ta kamkame Aryan dake rungume ajikinta  "shikenan  haka  zan kare rayuwata cikin  kunci da maseefa da tashin hankali "? "mai yasa  dady da mommy suka  kasa fahimtata akan  ya Aliyu "?
"Mai yasa suka fi son shi akan ni da suka yi silar zuwana  duniya "?
  aunty zee ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali ta amshi aryan a hannunta sannan kamota ta zaunar daita tace   "  wannan soyayya daga Allah ce kisna  da kuma  kyautatawar  da yayi musu, kin sani na sani kowa ma ya sani a cikin yan'uwa  Aliyu mutumin kirki ne   ,ni yanzu babu abinda zan ce miki daya wuce  kiyi  hakuri sannan kiyi  ƙoƙarin ki  adana damuwarki  kafin mommy  ta dawo gidan nan  ta fahimci  wani abu , sannan waɗan nan kayan suma ki karasa  maidasu cikin  wardrobe  zanje muyi magana da  ya Aliyu  ta k'arasa maganar tana fita daga."

   kai  tsaye parlou'n kasa ta  zarce  domin yin magana da Aliyu sai dai bata  samesa anan  ba  sai nasir da Samir  da Safiyya ta  samu   zaune shiru  tamkar  waɗan da aka turo musu  da sakon   mutuwa , ta Kallesu daya bayan daya sannan tace "ina ya  Aliyu ko ya fita ne "?Safiyya da nasir ne  suka hada baki gurin   ta bata amsa da  bai sauko ba yana sama ,
yayinda   har lokacin samir  ya kasa furta komai  sannan  ya kasa aiwatar da komai dan jin zuciyarsa yake kamar zata kama da wuta yau da wani ne ba Aliyu ba yayiwa kisna irin wannan wulakanci Allah ne kadai zai rabusu  amman akan Aliyu babu abinda zai  iya yi ko dady yaji yayi magana akan   lamarin sai ya bata masa rai bare matsayin Aliyu ya zarta komai a zuciyarsa ..."

Har aunty zee ta juya zata   koma sama  ta  tsaya batare data juyo ba tace  "dan Allah  abban  Junior  ka dawo  daidai  kar mommy ta dawo ta fahimci  wani abu  ,wannan matsalar tsakaninsu  ne kuma  inshallahu komai  zai  dawo normal yanzu batare da bata lokaci ba , tsakanin miji da mata  sai  Allah ko mutun ya shiga faɗansu  kunya zai ji tayi masa hannunka  mai  sanda saboda lura da tayi gaba-daya yanayinsa ya sauya  tana gama fadar haka  ta hau sama da sauri  ta   shiga dakin mommy ,nan ta samesa zaune ya tasa areef gaba yana kallonsa hawaye na tsiyayo wa daga idanunshi  jin  motsin shigowar mutun  yasa yayi saurin ɗauke hawayensa da hannunsa , sai dai  ya makaro dan  ta  rigada ta gani  .
    girgiza  kai aunty zee tayi sannan  ta  samu  guri  ta zauna akan  kujera tana kallonsa sai data numfasa sannan ta kira sunansa a natse " ya  Aliyu  .... Bai amsa mata ba haka zalika bai waigo inda take ba ,sanin datayi yana sauraranta yasa ta cigaba da magana "dan Allah ya Aliyu ka canza ,a zahirin gaskiya  ban ji dadin  abinda  kayi wa kisna ba , kuma  nasan ko mommy tana nan kai zata bawa rashin gaskiya akan abinda ya faru "."ina  dalilina  nayi  haka , barinta gidan nan shine  abinda zuciyata ta yanke akanta  idan taga zata iya ta cigaba da zama a gidan   idan bazata iya  ba ga hanya nan dan Allah Karki sake bata hakuri  akan lallai sai ta zauna  ki bari ta wuce duk inda zata dan nima nafi bukatar haka  "."Uhmmm  Aliyu ka kuwa masan abinda kake faɗa kama ajiye  batun aurattayar  dake tsakaninku     kai da kisna yan'uwa ne na na jini kasawa ranka  kisna Aliyu suna tare muddin rai mutuwa ce kawai zata rabasu  "stop saying that zainab I don't like what you are doing Ina nugun ganin girma da mutuncinki saboda ke din mai mutunci ce kowa ya sani ...... ".

  "bazan  daina  fadar  haka ba ya  aliyu  saboda bayan jinin na y'an'uwanta akwai wani jini na musamman  dake gauraye acikin jininku   ko kaki ko kaso kisna da Aliyu  abu guda ne  "dan Allah ki daina  faɗar haka kina maseefar  taba min  rai  wallahi "",Babu wani ɓacin rai   hakuri ma  ya kamata  kaje ka  bata saboda kayi mata ba dade ba .  "wannan maganar ma  ba mai yiwa ba ne dan Allah  ki daina fadar haka banaso ina ganin girmanki  zainab  saboda me zan bata hakuri "? "Laifin mai  nayi   da zan bada wani hakuri  "?  yayi mata tambayar ajere ransa na sake ɓaci  sannan ya cigaba da magana cikin zafin zuciya "bana tunanin abinda nayi ya sa'bawa Shari'a   to saboda me kike tunanin  zan bata hakuri "? yayi maganar yana rike hannun areef yana jin yadda hannunsa  yayi sanyi  "yanzu kana son fahimtar dani cewar ba kayi kuskure ba Kenan "?"Yes of course ban yi komai ba wallahi ,kin kasa dai  fahimtata ne kawai saboda kina ganin kamar nayi kuskure alhalin ni Kuma  nasan babu kuskure dana akan za'a kashe min da.... .....".....
yayi  shiru ya kasa karasa maganarsa  yana  kallon kofar d'akin ,itama aunty zee  kofar  tabi da kallo ganin kisna ta gani tsaye  idanunta na tsiyayar da  ruwan hawaye muryarta cikin kuka tace  "ki yarda aunty zee  bai yi min  laifin komai ba ,ni kuma daman na ɗauki laifina  ya dai kasa min uzuri ne amman nasan nice da laifi wallahi tunda nasan halinsu aryan basa zama guri daya ". ta runtse idanunta wasu hawaye masu zafi da ciwo suka sake gangaro mata .
"ni  kaina a yanzu zanso rabuwa dashi
sai  dai bazan iya kallon idanunshi nace na tsaneshi   ko nace  bana bukatar rayuwata dashi ba   saboda darajan  ya'yana, bazan  iya kallon idanun uban ya'yana nace banason shi bana bukatarsa arayuwata  ko bana bukatar had'uwa dashi a lahira ba kamar yadda ya fada min   ".

A matukar fusace yace "kinji ba kinji abinda wannan wawiyar take  cewa ko zainab  wato ma  darajan ƴaƴanta takewa komai ?  "ai daman  nasan abinda ke zuciyarki kenan shi yasa nake son rabaki da su gaba-daya na canza musu wa.........."tayi saurin katse masa hanzari ta hanyar cewa " duk abinda zaka faɗa ya  Aliyu  ka fada amman bazaka  taba canzani agurinsu arayan ba  saboda nice nan na dauki cikinsu na tsawon   wata tara da kwanaki kuma nayi na kudarsu  ...." Ni yanzu   Abinda zaka min   tunda baka bukatar zamana  da kai  ka taimaka ka wankeni  agurin mahaifina   tunda nayi iyakar ƙoƙarina naga mun sasantar kanmu muyi   zaman lafiya da juna   amman kaki ," ba dai baka son zama  da kisna ba ? yayi shiru tare da jan tsaki "to  ka taimakawa rayuwata ka  wankeni agurin iyayena kafin ka sawakemin aurenka dake kaina  wallahil azim ina bukatar takardar saki daga gareka ,ka sake ni ka huta rayuwarka nima na huta " .

tunda ta fara magana ya dauke kanshi akanta sai dai  jin maganarta ta karshe   yasa Ya  d'agowa idanunshi  a hankali yayi mata wani    kallon banza sannan  ya  ɗauke kanshi ya cigaba da kallon areef zuciyarsa na masa wani irin tuttukin bakincikin, sosai aunty zee ta tausayawa halin da kisna  take ciki gashi dai a shirye take data sadaukar masa da rayuwarta amman ya kasa fahimtar kisnar  da data yanzu akwai bambamci  "ya Aliyu karka biyewa zuciyarka kayi hakuri dan Allah,  karka biyewa maganar kisna tana cikin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login