Showing 393001 words to 396000 words out of 495987 words

Chapter 132 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

damu amman a gaskiya bana tunanin zata iya aikata haka ,
"zafa ta aikata cikin biyu zata yi daya kota aikata da kanta ko kuma tasa a aikata kaga bazan iya cewa ba ita bace ta aikata ba saboda bani da wanda zan tunhuma sai ita ,idan ma nace baita bace kai kasan abinda zai biyo baya kaga bani da mafuta dole dai itace din "yanzu haka soyayya tazama kenan kafin son abiodu da kuka hadu acikin shekara daya akan kisna da kuka shere shekara takwas tare?" babu irin wahalar da yarinyar nan bata ci ba akanka , a gaskiya idan ni ne bazan yi Shari'a daita ba komai za'a yi " ita ta cuci kanta ai domin ita ta furta cikin mutane ni yanzu bani da abinda zanyi duk abinda kotu ta zartar akanta shinkenan " fatai ya girgiza kai tare da juyawa ya barshi nan tsaye cikin jimami ."

*****
fadar  irin kalar tashin hankali da ahlin kisna suka shiga bata baki ne lawye musa ya bazama samo hujojimu kafin zama ya zagayo kuma  ya samu ana bukatar shedu uku ya samu shedu fiyye da hakan  , yayinda tsawon  lokacin nan lauyan kisna babu tattabin sheda a hannunsa aikuwa ana zama lauyan musa ya gabatar da sheidunsa da kuma furucin kisna na cewar zasuyi mutuwar wulakanci  nan  take aka yanke mata zaman gidan yari iya tsawon rayuwarta idan kuma hukunci bai mata ba tana iya daukaka qara ranar ma tayi kuka sosai ana ƙoƙarin turata cikin motar black maria ta hango yaranta tare da sadiq idanunsu kyam akanta hawaye suka shiga turereniyar zubo mata "na shiga uku aunty ummi ," Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un aunty zee " karku bari a tafi dani Allah bazan iya tafiya na bar yarana ba ina matukar qaunarsu ta k'arasa maganar tana ƙoƙarin durowa daga cikin motar gadiroba's  suka ririketa ,Kuka
kisna take rusawa da iyakacin karfinta irin wanda bata taɓa yi ba cikin fatan ina ma bai a halicceta ba ,tana kuka tana kiran "wayyyohhly Allah yarana ! wayyyohhly Allah ya'yana !! tun ba'a je ko'ina ba ta fara girban abinda ta dauki shekaru tana shukawa " lallai rashin imaninta da tausayin iyayenta ya Kaita ya rabo kallonta aunty ummi tayi duk da tsananin tausayinta dake dawainiya da zuciyarta amman hakan bai hana ce mata "abinda yafi dacewa dake kenan kisna ,idan Allah yasa kinga ma zaman prison kin dawo ku ci-gaba daga inda kuka tsaya keda Musa ,idan kuma shinkenan Allah ya hadamu a darussalam ba dai kin iya naci da hauka akan soyayya ba, kadan kika gani daga cikin bujirewa umarnin iyaye dama kin auresa da kin gane baki da hankali "tana gama fadar haka suka juya gbdynsu suna tafiya sai dai kowannensu cikin zuciyarsa babu dadi . "

mummunar tashin hankali ya shiga kisna tayi saurin zubewa kasa tana zaune dirshan tana kallon tafiyar yan'uwanta da yaranta dake kuka suna waigenta kamar sun san halin da take ciki yayinda direban motar ke kokarin tayar wa tana ji tana gani haka aka sake maidaita prison din dake ikoridu "Kaicona ni sakina na cuci kaina na cuci rayuwata bazan taba yafewa kaina ba yau ga sakamakon abinda na shuka *na cutar da kaina* "... fadar irin halin da mumy tashiga bazai misaltu ba dan Allah yasa ya badamasi ya hanata zuwa kotu daga karshe ta rungume jikokinta ta mikawa Allah komai sai dai tana nan  yau lafiya gobe babu twins ke qara daga wa mutane gidan hankali wata rana sai suki cin komai suyita kuka hakan ke saka kowa zubar da hawaye dan haka mumy ta shirya dan kaiwa kisna ziyara a lokacin da tayi sati biyu amman sai da tayi datasanin zuwa saboda ganin yadda ta koma acikin kwanaki shahudu , mumy ta tsura mata ido kawai ta kasa magana cikin matsanancin tashin hankali ,kisna tayi wata irin rama tayi baki bakinta ya bushe duk jikinta shashin bulala kallo daya idan kayi mata zuciyarka zatayi rauni "me ya samu jikinki haka kisna duk shashin bulala ?"cikin raunin murya tace bulala ake mana duk safiya mumy ta girgiza kai sannan ta cigaba da magana "kina addu'a kuwa kisna  ?"ina yi mumy cikin karfin hali mumy tace "ki ci-gaba da yi Allah ba azzalumi bawa bane sai dai bawa ya zalinci kansa sannan Allah na amsar addu'ar wanda aka zalunta ki dage kinji " ta gyada mata kai tare da kai hannu ta dauki yaranta daya bayan daya ta rungumesu ajikinta basu manta uwarsu ba ,cikin farinciki Aryan ya soma jan wuyan rigar  bursuna dake jikinta alamun zai sha nono ta tsuke karamin bakinta  zuciyarta na dokawa  sannan tace "babana babu komai da zaka samu daga gareni sai zubar hawayena ,ya ubangiji ka duba lamarina dana yarana da basu san komai ba aka zalincesu "mumy ta sanya wa jikinta dauriya dan idan ta biyewa zuciyarta babu inda zata sai dai a dauki gawarta a gurin "ki ci-gaba da addu'a mu zamu wuce dan babu wanda yasan nan muka zo inshallahu bazaki dagwama anan ba zaki fito nan kusa dan sai Allah ya bayyana gaskiya duk yadda zamuyi mu daukaka qara zamuyi ".

a fili kisna tace "Allah ya bada iko mumy  dady fa yaki saukowa har yanzu kou ? "mumy ki rokar min shi yafiya   yama barni da wannan qaddarar data sameni har ya Aliyu mumy ki rokar min shi ɗan wallahi har da hakinsa dana yaransa ke bibiyar rayuwata ,na gaji mumy na gaji da irin wannan rayuwar ina mutuwa take ta daukeni ya fiye min wannan wahalalliyar rayuwar mumy tana goge hawaye mumy ta sanya hannu tana goge mata hawaye tana cewa "ki daina ambaton mutuwa mamana ki dai cigaba da addu'a da rokon kyakkyawar rayuwa mai cike da albarka  kisani babu abinda yake da tabbass sai ikon Allah dan nasan yanzu da za'a bude zuciyarki babu komai acikinta illa tsanar musa da ahlinsa wannan ma wani baiwa ki sake godewa Allah "inshallahu
bazaki dangwama anan ba da yarda Allah zamuyi komai ki fita anan har mumy tayi mata sallama ta wuce  kisna na zubar da hawaye  ta dauki abubuwan da mumy ta kawo mata ta nufi hanyar koma ciki "lallai gurin yaci sunansa wato *jafojo* ma'ana  makabarta killa ma gara rayuwar kabari akan rayuwa cikinsa tunda wannan kasan ka mutu rayuwarka ta kare sai abinda ka shuka , da daddre ta fito daga dakinsu wanda duk kusan masu laifin kisan kai ne aciki tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah tana jin mutanen dakin na  kwashewa da wata irin dariya suna cewa" ko raka'a dari zakiyi zaki sallame batare da bukatarki ta biya na fita daga gurin nan ba bare wannan daki da duk wanda ya shigo ya shigo kenan babu mai iya rabashi da qaddarar mutuwa ."

a ranta tace "nayi imani ubangijina zai tallafawa rayuwata koda kuwa bai fiddani ba bare ina saka tsammani tunda ina tare da addu'ar mahaifiyata ta mike ta sake tayar da wani sallahr ita kanta batasan adadin da tayi ba har kusan Sallah asuba koda ta idar bata koma bacci  ba ta zauna tana lazimi babu abinda tasani byn istigifari , karatun sallahr ma iyakarta fatiha da kananan surori guda uku to ina ta tsaya tayi karatu,  ta karar da kuruciyarta gurin gujegujen bin musa  dan haka istigifari tayita tana kallon yan dakin addu'ar data durfafa cikin yan kwanakin nan tasan tabbas Allah maji rokon bawa ne baya ga tsananin tsanar musa da tsanar rayuwar da sukayi ada babu abinda take dan tun da gari ya waye tunaninta ya fara dawowa daidai har ta dinga tuhumar kanta akan batawa kanta lokaci datayi dashi alhalin ga wanda ya canci fiyye da haka ,anya ma kuwa kanta daya har ta iya rayuwa dashi na tsawon shekaru ?" shakka babu ta yarda ta amincewa zuciyarta ba'a banza ba akwai wani abu wanda Allah kadai ne ya sani kuma yanzu Allah ya yaye mata dan haka ita da musa har abada koda Allah yayi fitowarta ".

yadda kisna ke tsaye gurin kaiwa Allah kukanta haka mumy da yan'uwa tsawon wata biyar kisna na gidan yarin cikin kunci da wahalar aiki dan duk safiyar duniya sai anyi musu bulala dari sannan suje suyi aikin karfi  har ta gwamaci mutuwa da rayuwar dake take ,gashi kullum addu'a take amman har lokacin gaskiya bata bayyana ba ,a gidan dady ma komai ya tsaya babu wani labari mai daɗi sai na akasinsa  wato kwanciyar mumy rashin lafiya nan fa hankalin dady yayi matukar tashi baya son rasa matarsa  farinciki rayuwarsa uwar ya'yansa marayu dama masu uban, bai tsaya tambayarta damuwarta ba tunda yasan damuwarta bata wuce kisna ba, dan haka ya mike bisa kafafunsa gurin nemo manyan lauyayi daga cikin lauyoyin gwanati domin daukaka qara nan aka shiga bincike aka soma da mai gadin dake gadin gidan da Musa yake haya, juyin duniya yace bai san da komai ba ,dan haka aka kamashi aka tsaresa agurin hukuma babu bata lokaci gaskiyar da'ake nema ta fara fitowa acikin sati na uku gaskiya ta bayyana inda take aka koma zaman kotu da kwararan sheidu."

bayan dogon bayani lawyer ya bawa yansanda umarnin su shigo da amuda nan take gaban musa ya shiga dukan tara tara ya maida idanunsa ga inda lawyer ke kallo wacce aka kira da amuda ta soma kokarin shigowa cikin dakin Shari'a idanunta a kumbure alamun taci duka  zumbur musa ya mike tsaye yana kallonta cikin tsananin tashin hankali yayinda police ke biye daita da bindiga har ta isa inda masu laifi suke tsayuwa  "lawyer ya kira sunanta" amadu ko zamu iya sanin dalili da yasa kika kashe abiodu sharifat ?"Eh ! tayi maganar cikin dakiyar zuciya " ni tsohuwar budurwar musa ce mun hadu dashi ne a lokacin daya je ilori mun kulla halaka ta soyayya har ya sadu dani musa ne mutumin da yayi disvirging dina bayan mun saba dashi yayi min alkwarin zai aure bayan wasu wattani  ya tafi ya barni cikin kunci da tashin hankali abu na farko dana fara fuskanta shine barazana daga garesa duk wanda ya fito zai aureni da zarar yaji labari sai ya san yadda yayi aka  fasa auren sannan ya tura min text muddin ina son zama lafiya nazo Lagos na samesa a wanann zuwan danayi ya sadu dani  kuma ya  nuna min video daya taba min lokacin muna cikin soyayya a she shine makamin abinda yake firgita rayuwata data masu neman aurena  wannan video ya zama tamkar maka min musa na samun abinda yake so agurina idan nace  masa tunda baya son yaga wani ya aureni to ya aureni sai yace min shi me zai yi dani , shi da yake da mace kamar kisna shi bazai aureni ba nayi bakinciki sosai a lokacin har na qullaci kisna a raina da fari ita naso kashewa sai dai duk wata hanya nabi ban samu damar haduwa daita sai na hakura na samu wani sauri  saurayi mai suna salawudeeni dan kogi ne ban bari mutane sun sani ba har aka saka rana aure sai labarina aurenta ya samu musa nan take ya tura masa video aiko ya daina zuwa gurina a lokacin da hakan ta faru jikina ya bani akwai matsala dan haka tayita neman salawudeeni a waya ban samu  ba sai iyayenna ne suka samu ganisa suka tambayesa yace shi baya aure koda suka matsa matsa jin dalili bai tsaya wani boye boye ba ya nuna musu video tsirancinna da Musa ya tura masa nan na shiga tashin hankali na shiga neman hanyar da zan  tsaida musa kwansan naji batun aurensa ina cikin tunani yadda zan kashe musa sai ga kisna tazo gurin bikin duk abinda ya faru akan idanuna ne take na canza shirina ganin ga wata dama na samu tun daga lokacin na shiga neman hanyar da zan ga karshen musa na siye mai gadin gidan wanda shima gaskiya bai san abinda ke raina ba .
na dai ce masa ya barni na shiga ni budurwar musa ce duk na koro masa abinda ya hadamu da irin tozarci da yake min  hakuri  kawai zan bashi ya goge video yaji tausayina sannan na bashi numberta nace duk sanda musa yake gida da daddare ya kirani a  zahirin  gaskiya banzo da niyyar cutar da matar musa ba  amman ta arawa kanta mutuwa dan data barni shi zanyiwa kisan wulakanci baita ba ganin zata tara min mutane da kururuwa na  aiwatar da komai akanta na caccaka mata wuka a kahon zuciya shi din ma ban barsa ba dan hayar kashe shi nake nema ta kowani hali nan  take kotu ta haigitse da jimami wannan girman al'amarin."

majistrt ta dauke kanta akan amuda ta soma rubuce rubuce bayan kamar minti goma ta d'ago ta fara bayani kafin daga bisani ta zartar da hukunci akan amadu kisa ta hanyar rataya sannan ta bada umarnin a fito da kisna tare da wanketa wani irin kuka amadu ta rushe dashi tana kuruwa kotu tayi mata adalci abarta zata daukaka kara amman ina tuni aka mika ta hannun gandiroba sukayi waje daita tana kuka da turturjewar   bata zuwa aiko suka hau janta a kasa dan tausayi babu wanda bai yi kuka ba hatta jikin yan'uwan musa yayi sanyi musa ya kalli mumy tayi saurin kawar da idanunta dan bata son ko ganinsa ,a hankali yabi bayan mutane dake fita daga dakin yana isa haraban kotu wani mutum ya kalleshi "Gaskiya  kai dai mugu ne wallahi sannan ka cuci matar nan Yakamata kaji tsoron Allah domin mata ba bayi bane wallahi sai Allah ya tunhumeka akan abinda kayi mata kuma inshallahu sai kaga karshenka "karshensa ai yazo tunda gashi can  humanright zata shiga ciki za'a amsar mata hakinta Shima bazai tsira ba inji cewar wani mutumin "yauwa wallahi har naji sanyi araina "dan Allah kun dameni idan hukuncin da'aka yanke mata bai muku dadi ba ku  koma gaban alqali ko kuma ku taya daukaka qara yan iska kawai masu  saka kansu cikin abinda bai shafesu ba yana gama fadar haka ya juya ya isa inda yan'uwansa suke ya bude mota ya shiga suma suka shiga suka nufi gida yayinda yan'uwan kisna suka ci-gaba da jiran idan akai amadu a taho musu  da kisna ..."

Cikin sauri sauri ake kiran sunan kisna a prison "sakina realwan!sakina realwan!! domin ba'a son Kara daidai da second daya akan lokacin shigowarka  prison da lokacin fitar mutun  ,jikinta na rawa ta amsa tare da fitowa idanunta cike da kwalla umarnin sauya kaya aka bata sannan aka fito da file dinta aka shiga ciccke abubuwa karfe 4:00daidai aka fito daita  dan  zuwa kotu koda ba'a mata cikakken bayani ba tasan cewar ta fita daga wannan matsalar ai isar  motar ke da wuya yan'uwanta suka zagaye motar suna kukan farinciki da kyar ta fito saboda rashin nauyi da jikinta yake da  ,duk sukayi kanta suna kokarin rungumeta rashin kuzari yasa tayi kasa tana wani irin kuka wanda da gani na farinciki "alhamdulillah  Allah  na gode maka daka  nuna min wannan rana inji cewar mumy ."

Mumy tasa hannu tana goge mata hawaye idanunta sunyi ja haka jikinta  yayi  zafi ta d'ago idanunta tana kallon sauran yan'uwanta kafin daga baya ta mike tsaye ta rungume aunty zee Itama ta rungumeta haka aunty ummi  da mufeeda da zahra da ya badamasi  cikin tsananin  farinciki  suna murna ta d'ago ta kalli sadiq shima ya kalleta cikin murmushin jin dadin ganinta  yace "Barka  sakina Allah  kiyaye  gaba "."ameen ya  sadiq    suka dunguma zuwa  gida har suka kai  gida kuka take ,da yaranta yan shekara daya da wata  hudu ta fara cin karo a falo  suna wasa da mota suna ganin mumy  suka bar abinda suke suka rugo zuwa gurinta suka  rungumeta ta shafa kansu  tana turasu gurin uwarsu "kuje gurin mamanku " shiru sukayi suna kallon kisna  kafin daga baya suka  tafi da gudu suku  rungumeta  cikin  kuka  tace "a she baku  mantani  ba ? suka yi  murmushi   suna    goge  mata  hawaye" ta  yaya  zasu  mantaki  ke fa uwarsu ce inji cewar aunty zee  sake  rungumesu tayi  ajikinta tana sake jin qaunar yaranta , ranar gidan mumy tamkar Sallah kowa ka gani cikin murna yake, ranar kisna  ta saba jikinta  yafi sau goma kamar zata canza fatar jikinta kusan minti talatin tana bayi sannan ta fito zuwa falo inda aka shirya mata lafiyyayen  abinci  aunty zee ta matso kusa daita taja mata kujera "auta ki zauna kici  abinci  "to aunty  zee na gode da kokari ".  Aryan  da arif suka matso jikinta  suka makale kamar zata gudu ta barsu  tana cin abinci  tana basu suna  hira dasu mumy "kinga yaran nan  da shegen naci  bazasu barta ta  huta ba inji cewar aunty ummi "yaushe rabon su ganta gara suji dumin uwarsu bancin Allah ya takaita ai da  su daita sai labari Allah dai ya sake kiyaye wa suka amsa da "ameen. tana gama cin abinci mumy tace ta shiga dakinta ta  kwanta ta huta babu mutsu ta mike twins suka bita kamar wasu bindi  duk inda  tayi yaranta na binta  da zarar ta kallesu wani sanyi take ji lallai ya'ya  rahma ne  ,  yanzu data zubar dasu fa ?"  Allah Sarki aunty zee  bazata taba manta wa dake  ba a  rayuwarta  zan   dangwama ina miki  addu'a ."

washegari gidan  ya cika makil da jama'a  yan  taya  jaje har su Habib da jahid sun zo lokacin  bakaramin bugawa zuciyarsu tayi ba  da suka ga twins  ,dan rabonsu da gidan sun dade tun lokacin da kisna ta zubar da cikin yan'uku  Habib ya kasa hakuri yace "wadan  nan yaran fa  ya'yan waye  masu kama da muradi ?"har mumy zata fada musu sai  kuma ta tuna da maganar dady dan haka tace jikokina ne na gurin yayana bature suka zo min jaje uwarsu na ciki  dake sun san shi kuma sun san yana kama da muradi  sai kawai ya  gyada mata kai jahid yace "gaskiya suna kama da muradi sosai kamar an tsaga karya dan  idan  ba daga bakinki naji ba bazan yarda cewar ba ya'yansa  bane   "ai  dole   jini  ba karya ba mumy tayi mgnr a ranta , ta kwallawa kisna kira kisna ta fito sanye da hijab har kasa "gasu Habib nan sunzo miki jaje "ina yiniku ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login