Showing 372001 words to 375000 words out of 495987 words
Chapter 125 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
gidan suka iske mutane suna zaman jiran karasowarsu shiru tayi tsaye tana kallonsu daya bayan daya zuciyarta na bugawa granny ta kamota tana kokarin zaunar daita dan jikinta babu kwari ta zauna cike da ɗari dari zuciyarta na cigaba da bugawar da yake da matsanancin karfin gaske ."
Falon shiru har lokacin babu wanda yayi kwakwaran motsi yayinda idanun dady dana mumy har ma dana sauran mutanen dake zaune a falon suke kanta tare da rafka tagumi itama cikin tsananin faduwar gaba take cigaba da kallonsu, byn kamar minti shabiyar "dady yayi gyaran murya ya fara magana a tsanake "sakina me yasa kika iya cin amana da yaudara da ha'incin da cazawa mutane zukata ? " yayi mata tambayar a jere yana kallon cikin kwayar idanunta da suka jeme sukayo waje "kullum zuciyarki na sake bushewa babu digon imani acikinta idan har baki yarda Allah daya bane sai yaushe kisna ?" lokaci yayi daya kamata ki buɗe dodaddiyar kwakwaluwarki ki san abinda duniya take ciki , kina nunawa mutumin da bai ji ba bai gani ba kiyayya mara dalili wanda har kiyayarsa tasa kika kashe masa ya'ya har uku a rana daya sai kuma ga wani sakkayar Allah ya sake nuna ishararsa akanki ya nuna karfin iko da mulkinsa akanki kika sake ɗaukar cikinsa na wata hudu da sati daya a karo na biyu ,me zaki cewa Allah akan wannan ? " akan kujera take amman bata san lokacin data zubo kasa bisa gwiwowinta tare da dafe qirjinta da duka hannuwanta tana zaro ido tare da girgiza kai sannan ta bude baki da kyar muryarta na rawa "wa wai dady ni ke dauke da ciki har na wata hudu da sati daya ? ya gyada mata kai alamun" eh"" kenan cikin na nan bai fita ba ?
"Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un gbdy Jamar dake zaune a gurin suka hada baki gurin furta hakan , wannan kalmar da suka furta yasa ta fahimci lallai ta gama tonawa kanta asiri a fili tayi maganar "kenan shima wannan cikin kinyi kokarin zubarwa ? sautin muryar mumy ta karad'e falon cikin tashin hankali "kisna tayi shiru tana zazzare idanu qirjinta na faduwa "lallai kisna baki da imani sam zuciyar kafirai ne dake inji cewar mumy wacce ta mike a zuciye ta hau zuba ma kisna maruka "walllahi da kinyi gangancin cire cikin nan da ni da kaina zan kasheki mara imani kawai babu wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba haka babu wanda bai yi Allah wadai daita ba "maganar daurin auren babu " inji cewar alhj Nuhu wanda ya kasance yaya ga alhji realwan alhji marwan yace "babu mana yaya tunda babu yadda za'a daura mata aure da ciki sai ta haihu zan nemi yaron idan yana sonta ya jira har ta haifa mana abinda ke cikinta sai suyi aure wata irin zufa ce ta shiga karyo mata ta ko'ina a sansar jikinta tamkar wacce akayi wanka da ruwa dan kuka ma kasa yi tayi ta dawo tamkar gunki a durkushe "daga yau ta dawo gidan nan kenan da zama har ta haihu dan zamanta agurina bazan samu natsuwa ba inji cewar granny ban da ma mugun hali irin na kisna kinsan kina da ciki zakiyi aure da ciki saboda Allah "ba jahilci da haukan kiyayyar na damunta ba ai dole tayi ai nan dai suka yita tautaunawa akan batun cikin ."
kusan kisna ta daina fahimtar abinda suke fada har sai data dawo dakinta sannan tunaninta ya dawo jikinta ta tashi ta zauna tare da daura hannuwanta duka akanta tana tunanin maganganun 'yan'uwanta tana kokarin tantace gaskiya daga karya kawai taji zuciyarta ta yarda cikin da tayi kokarin zubarwa na nan bai girgiza ba babu wani karya a ciki maganar su , toshewar baseera ce kawai irin nata ta kasa fahimtar cewar cikin bai fita ba yana nan tunda tun dan jinin da ta gani bata sake gani ba aiko ta rusa kuka da kururuwa tamkar wacce uwarta da ubanta suka mutu "wannan cikin gaskiya ne amman duk halin da zan ciresa sai na ciresa ko sama da kasa zasu haɗe bazan haifi cikin nan ba wallahi bazan yi hakuri zaman gidan nan ba wallahi , bazan zauna ba gbdy na gaji na gaji da zaman gidan nan duk ta burkice acikin dakin tana sambatu zuciyarta ba bugawa da karfi , haka ne yasa kafin gari ya waye jinita ya hau ta sume da kyar aka samu ta dawo haiyacinta babu wanda ya tsaya rarrashinta tunda kowa yasan yadda zuciyarta take da kafiyar tsiya sanda ake rarrashinta da ban hakuri lokacin zuciyarta ke sake hautsinewa tun daga lokacin kacokam 'yan gidan suka maida hankalinsu gareta suna bata kulawa bata cass bare ass sai a girka akawo mata amman yadda aka kawo mata haka za'a dauke bata ci a tunaninta yunwa zai sa cikin ya wahala ya zube".
******
Bangaren musa kuwa sanda yaji tabbas cikin muradi ne ajikinta ciki tashin hankali da rudewa ya zube kasa daga tsaye yana furta "kisna ta cucesa ta yaudaresa taci amanarsa gbdy mahaifiyarsa ta rasa gane kansa da gindinsa ɗan sai zuba sambatu yake wani irin kuka da qara yake yi mai ban tausayi kamkameshi mahaifiyarsa tayi tana fashewa da kuka domin tasan dole zai ji abun a zuciyarsa a yadda ya kwallafa rai akanta zuciya sai tafasa yake jikinsa yayi zafi sai kuka yake yana kiran sunan kisna ta cucesa har sai daya kai ga kwanciyar a asibiti laida ruwa biyar ya sha sannan ya dan dawo daidai sai dai har lokacin zuciyarsa na cikin kuncin abinda kisna tayi masa dan idan wani ne ya fada masa zata iya bawa wani namiji kanta bashi ba zai mutsa sai ga sheida wacce babu karya sai zallar gaskiya tunda ba'a shan ciki a ruwa yayi bakinciki sosai da wannan cikin gidansu cike da mutane ana jajantawa mahaifiyarsa abinda ya faru shi kuwa musa duk abinda suke hankalinsa baya jikinsa kallon kowa kawai yake ..."
Yadda musa ya daga hankalinsa haka kisna ta daga hankalinta aunty ummi ta kalleta tace" kina ta faman kuka da kin cin abinci ko mutuwa aka miki sai haka "ai dama mutuwar nayi wallahi na huta da wannan bakinciki Allah ya sani ni bana son cikin nan yadda bana kaunar wanda yayi cikin haka cikin bana son shi mufeeda ta kalleta cikin jin haushi maganarta tace " to kada Allah yasa ki soshi din ai tunda Allah nason shi sai kin haifeshi da izininsa muguwa kawai mai muguwar zuciya ta Allah ba taki ba wallahi koda wasa wani abu ya samu cikin nan sai munyi Shari'a dake " zahra ta karɓe maganar"wallahi ki ma shiga hankalinki tun wuri dan akan wannan cikin zaki jawowa kanki matsala da kowa a gidan nan dan zaki karawa kanki sabon tsana ne kawai , idan kika hakura kika kwantar da hankalinki ke kanki zaki yi mamaki yadda zaki samu farinciki maganar bakya son Wanda yayi cikin shima ai baya sonki dole tasa ya amshi aurenki, yanzu haka ma ya manta dake a rayuwarsa dan ko sunanki baya qaunar ji "to yazo ya kashe ni mana tunda baya qaunar yaji sunana mugu kawai Allah ya isa cutar da yayi min "yadda bazaki iya kashesa ba haka shima bazai kasheki ba kuma kika sake zaginsa sai kin gwamaci baki da wayo a tare suka bar dakin zuwa falo suna huci suka zauna har aunty ummi zata zauna ta fasa ta koma dakin da kisna take "bani wayarki "ki bar min wayata aunty ummi "a'a bazan bar miki ba jikina na bani za'a iya kulla makirci daita tana kuka ta rike wayar gam hannu aunty ummi ta Kamo hannunta ta bude da iyakacin karfinta ta amshe wayar ta sake ficewa ."
yau tsawon kwana uku kenan mumy tana neman layin muradi da samir bata samu ba domin fada musu abun farincikin daya samesu yanzu ma da take zaune a falonta layinsa take kokarin kira cikin tsananin farinciki ai kuwa taci sa'ar number ta shiga yana dauka ya gaisheta cike da girmama wa bata amsa masa gaisuwarsa ba tace "kana jina muradi "...take dady daya shigo falon ya kwace wayar a hannunta tun kafin ta ida maganarta yace " yarona kana jina ?" ykk ya ayyukan fatan dai kuna cikin koshin lafiya ? "mumynka ta dan tashi yanzu amman dai tana lafiya okay to shikenan ya katse kiran ya fuskanci gabadayansu har su aunty ummi da yanzu kullum suna gidan tunda abun ya faru "banason muradi yasan komai akan labarin cikin nan dan zai iya d'aga hankalinsa bayan da kyar aka samu zuciyarsa ta samu natsuwa , abarsa ya huta ko samir banason ya sani" har kusan sati biyu kisna bata warware ba tana kwance a daki tana aikin kuka ta rasa wanda zata zanta da matsalar data sake kunno kai rayuwarta a karshe ta tashi ta shiga dakin mumy ta dauki wayarta ta kira zee tana kuka ta fada mata abinda ya faru abun mamaki da takaici sai jitayi ta hau kyakyale mata dariya domin taji dadi ,cikin muryar kuka tace "shikenan aunty zee tunda dariya matsalata ta baki" Ni kisna na zama abar tausayi ni ba marainiya ba ina fama da maraici ta kowani bangare babu farinciki "bazaki gane bane kisna wallahi dadi naji sosai kuma wannan shine soyayyar da muke miki duk wani mai kaunarki zai so ki haifawa ya Aliyu ya'ya Kinga wannan cikin wallahi wata rana zakiyi alfahari da abinda ke cikinki , Allah yasa su zamo 'yan uku irin na wancan karon "ba ameen ba Allah ya isa abinda yayi min mutun kamar akuya daga yi daya sai ciki ". aunty zee ta sake yin dariya tace "namijin kenan ai kuwa yau ba sai gobe ba zan masa albashi "wallahi kar kiyi masa dan wannan cikin ma rariya zai bi kamar wancan bata tsaya taji abinda aunty zee zatace ba ta katse kiran ta soma neman layin musa kira uku tayi masa bai dauka ba a karo na hudu ne ya dauka yana jin muryarta ya kashe dan shi tuni ya fara dawowa daga rakiyarta ,tarraya daita babu alkhairi sannan babu abinda yake janyo masa sai tashin hankali da bala'i iri iri kullum shikenan cikin tashin hankali da guje guje uws uba yaudararsa datayi na kin fada masa gaskiyar ta bawa muradi kanta tayi shiru tana mamaki ta sake kira amman wayar na ringing yaki dauka a karshe ma ya kashe wayar gabadaya jikinta yayi sanyi tare da daukar zafi
ta goge number dan kar mumy tazo ta gani tabi number zata kira layin aunty afra kenan mumy ta shigo dakin tace "bani wayata kar na sake ganin kin daukar min waya ta mika mata ta fice daga dakin zuciyarta na ta fasa mumy ta duba dialled bata ga sunan kowa ba sai na zee ta sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare tana kokarin ajiye wayar kira ya shigo sunan zee ta gani har zata kira kisna ta bata wayar sai ta dauka daga can bangare aka fara magana "kina jina kisna dan girman Allah karki taba lafiyar cikin nan zan fadawa muradi nasan zai yi farinciki "karki fada masa sautin Muryar mumy ya doki kunnen zee "mumy Ina yini ?"lafiya kin dai ji abinda nace "to shikenan mumy amman ki kara sanya idanu akan kisna dan tace zata zubar da cikin "inshallahu ina wannan sarkin kukan yake ?"yana nan lafiya mumy yanzu ya gama kukan nashi na gado yayi bacci sai da suka dauki minti shabiyar suna hira sannan sukayi sallama ".
Da daddare muradi na zaune shi da Samir suna cin abinci zee tayi murmushi tana cewa "ya Aliyu ka gama cin abinci akwai abinda zan fada maka " ya d'ago yana kallonta yana cin abinci "uhmm ina jinki menene shi ?"no ka gama tukunan a hankali ya cigaba da cin abinci har ya kammala ya sake tsura mata ido "uhmm ina jinki zee ".kisna na......."
saurin d'aga mata hannu yayi tare da haɗe fuska tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa "banason damuwa zee sannan ban yi tunanin akwai wata rana da zaki dawo min da wannan sunan ba "ka tsaya kaji ko akan me zanyi maganar " bana bukatar komai daya danganceta kinga ni na wuce gurin nawal yanzu haka tana can tana jirana "ni wallahi banason nawal din nan mai siffa kaguwa "fada min dalilinki na kinta bayan ba soyayya muke ba ?" karki manta yadda ta taimakawa dan'uwanki ya dawo rayuwa kamar ta sauran mutane " . ta karya da kai tana dubansa sannan tace "na sani but ita ai da alamun sonka take "kin cika shirme zee haka ake soyayya ?" ya karasa maganar tare da ficewa daga falon ta maida idanunta kan Samir "abinda zan fada masa mai mahimmanci ne fa amman kalli yadda ya watsa min kasa a ido "to yace baya so ko dole ne ?" to kai bari na fada maka Allah nasan har albishir sai ka bata ni " nima banason ji dan haka ki kama kanki sosai ya karasa maganar a zuciye shiru tayi har sanda shima ya mike ya nufi d'akinsa ta zaro ido waje sakamakon tuno abinda mumy ta fada mata Allah ma ya taimaketa da basu saueareta ba da me kenan tayi ?"
*******
Da misalin karfe hudu na yamma muradi na kwance a bangarensa a gidan da dady a gina musu a unguwar rehab wayarsa tayi qara alamar shigowar sako ya dan mirgina ya kai hannunsa ya dauki wayar yana duba screen din wayar ganin sunan nawal dauke da sako yasashi mikewa ya zauna rigingine ya fara karanta sakon hankin kwance .
_"ya kai mai rike da zuciyata bazan iya tsayawa gabanka da bukatar da bansan yadda amsar zata zo min ba, haka nan bazan iya cigaba da rike abun acikin zuciyata ba , Aliyu muradi sonka nake ,qaunarka nake, na tabbatar da haka ne tun a lokacin da ban tsamaci zan hadu da kai ba,yanzu kuma dana zo na hadu da kai muka shaku sai soyayyar ta qara fiyye da lokutan baya , a lokaci na dauka burgeni kake daga baya na fahimci zallar qauna ce , "gbdy a halin yanzu na nemi zuciyata a fadin qirjina na rasa ,zuciyata babu namijin data kamu kuma ta yarda ko mafarkin qauna sai kai , zuciyata na dauke da qaunarka da alkwarin zata tsaya tare da kai a kowani hali, zata sadaukar maka da komai nata muradi kai ne ka mallaki zuciya nawal ba zabi nake baka ba shawara nake baka ka soni da gaskiya hakika zakaji dadin zama dani, bazan damu da ko mata nawa gareka ba muddin zan kasance a karkashin ikonka zanyi farinciki da wannan alfarmar zuciyata ta makalewa sonka muradi irin son da bazai sa ta kasa fahimtarka ba , kota sabawa umarninka ,ko yi maka karya, zuciyata bazata saba alkwarin data ɗauka ba sannan bazata taba son waninka ba dan ban fara sonka dan na daina ba , ban taba son wani namiji yadda nake sonka ba akanka nasan soyayya gaskiya ce ba irin ta yaudarata da maza uku suka min ba kamar yadda na sheida maka abinda bani da tabbacin akai shine ingantacciyar rayuwa a yayinda na kasa samun amincewarka mai kake jira norr da wannan ceton ran ka ceci zuciyata ka soni muradi na tabbatar bazakayi nadama ba ,ka soma daukata a matsayin masoyiya kuma wacce zata zamo uwa ga ƴaƴanka_
Ya dade yana karanta text dinta yana sauke numfashi da ajiyar zuciya , sai daya baya jin zai yarda ya fada motar sonta , kusan kwana biyu suna haduwa daita agurin shakatawa da yamma kamar yadda suka saba haduwa duk karshen sati , sun dade suna hira sai dai ko da wasa bai nuna mata yaga sakonta ba dan shi a tsarinsa baya son mace mai iya fallasa abinda ke zuciyarta barin ma a bangaren soyayya, dan kwantawa nawal ta kwanta masa illar dai hanzarin fito da maitarta fili da tayi.
Ranar asabar da yamma suna zaune nawal ta tsura masa idanu tana kallonsa duk burin wata diya mace muradi ya cika a dan muamular da sukayi ta fahimci mutun ne shi mai kirki , hakuri ,addini ,gaskiya ga ilimin Arabic dana boko sannan kuma kyau gashi d'anuwanta mai arziki mai daukaka wanda duniya tasan dashi , ya dan bata tahirinsa sai dai abu guda ya tsaya mata arai inda yace mata yana da mata a hankali ta dinga jansa da hira kamar koda yaushe kasancewarsa mara son magana har ta sanyo maganar soyayyarta kamar zatayi kuka "ko matarka bazata iya zama dani bane ?"yayi mata shiru kawai yana kallonta " wallahi bazan bata matsala ba , zan bita yadda kake so ta karasa maganar tana riko tafin hannunsa cikin nashi tana murzawa take jikinsa yayi sanyi sai dai bai ji komai akanta ba "wallahi ko mata uku gareka ba daya ba zan iya zama dasu, zanyiwa mahaifiyarka bibbiya ,
zan kular maka da yanuwanka ta karasa maganar tana kokarin zubar da kwalla naunauyen ajiyar zuciya ya sauke muryarsa a sanyaye yace "kada ki bari hawayen nan su zo "tayi saurin goge su da bayan hannunta tana sauke numfashi , idanunta akanshi "wasa nake miki dana fada miki inada mata,sai dai a zahirin gaskiya na taba aure wanda ya kasance na zumunci ne har ma nayi missing triple sai dai mun rabu daita " wani sanyin dadi ne ya mamaye zuciyar nawal ta sake riƙe hannunsa gam tana murzawa "ka amince min muradi "na amince miki sai dai da sharadin idan na aureki zaki zauna tare da mahaifiyata na tsawon wata shida har sai naga yanayin zamanki da mahaifiyata saboda rayuwar waje data gida akwai banbanci , bana wasa da mahaifiyata da yanuwana zasu soki dan suna son duk wani abinda nake so ".kenan kana sona ?ta fada tana bayyana tsantsar farincikinta ya dage mata girarsa daya yana ciza lip's dinsa "zan zauna tare