Showing 207001 words to 210000 words out of 495987 words

Chapter 70 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

bugawa ,cikin sauri ya badamasi ya dawo ya fara bashi taimakon gaggawa bayan yasa shi dole yaci abinci , yayi masa allura yace "ya kwanta ya hutu ,duk suka bar d'akin banda mumy dake zaune tana shafa sumar kanshi cike da tausayawa , qaunar Aliyu ta musamman ce a zuciyar mumy ta mamaye zuciyata da komai nata cikin tautausan murya mumuy ke masa sannu tana kwantar masa da hankali sosai zuciyar Aliyu ta sake yin sanyi hawayen farincikin samu kanwar mahaifi ne ke zariya akan kuncinsa ,baya alfahari da mahaifinsa amman yana alfahari da yar'uwarsa tamkar mahaifiyarsa yake jinta ,yanayinta yana yawon tuno masa da mahaifiyarsa ya kasa manta kamanin mahaifiyarsa da komai nata saboda samun kyawawan mazauni da yayi a zuciyarsa ."
Duk motsinsa sai momy tayi masa sannu tare da karfafa masa zuciya , "mumy me yasa Afra ta tsane ni ?
"Me nayi mata momy ?





Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗


Page 32

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.



"Baka mata komai ba muradina kawai mugun hali irin nata ta bashi amsa cike da tausayawa " mumy zuciyata na zafi sosai saboda ina jin tsoron kar wata rana Afra tayi nasarar rabamu , banaso rabuwa dake mumy sai dai mutuwa ta rabamu amman ina ganin lokaci yayi kusa da zan gudu na barki da kaina duk da ina tsananin qaunar zama dake ya karashe maganar hawaye na gangaro masa "kar na sake jin ka furta kalmar rabuwa ko guduwa tayi maganar a zafafe ranta a matukar bace "yadda bazan iya rabuwa da É—an cikinna ba haka zalika Bazan Iya rabuwa da kai ba kai ba kuma kar naji kar na gani kai dana ne halak malak ni mahaifiyarka ce ," na soma jin tsoron sharrin Afra tana son shiga tsakanin uwa da danta ya k'arasa maganar wasu zafafan hawaye masu zafi na gangaro masa."
numfashi mumy ta sauke tare da fadin "hakika abinda take so kenan muradi sai dai kafin lokacin zan yakiceta daga rayuwarmu ta zauna iya matsayinta dan ko dan cikina yace zai shiga tsakaninmu zan taka masa burki bare ita "rayuwata ce kai muradi kuma ina tausaya wa rayuwarka da me zakaji babu tsayayen uba babu mahaifiya babu dangin mahaifiya a dangin uban ma ni kadai na yarda da kai nake sonka tamkar numfashina na shaku da kai matuƙa muradi karka sake cewa zaka bar rayuwata muna tare muddin rai sai na aurar da kai da kaina sai na ga ya'yanka ta karasa maganar tare da sauke numfashi take ya haɗe rai ya zame kanshi akan cinyarta "mumy nifa babu wani aure da zanyi "murmushi kawai mumy tayi ta sake ɗaukar kanshi ta mayar saman cinyarta"Allah ya shiryeka muradi muna nan da kanka zaka furta zakayi wata rana " ya sake haɗe rai a hankali mumy ta dinga lalla'bashi
har bacci ya d'aukeshi , Aliyu yayi kwana biyu yana jinya kafin ya dawo daidai .."

zuciyar mumy ta kasa yin sanyi da Afra duk abinda take mata baya burgeta , gabad'aya ta fita ranta bata son ko Kallon inda take ,ita kanta Afra ta fahimci sauyi daga mumy amman ta nuna ko ajikinta a ranta tace "na rigada na zama karfen kafa a gidan nan ko babu halaka ta aure tsakaninta da badamasi gidan nan gidan yayan mahaifina ne ba'a isa a rabani dashi ba zama dole .
bangaren kisna kuwa cikin kankanin lokaci suka sake dinkewa da uwar d'akinta afra suka dawo fiyye da da suka ci-gaba da cin kare su babu babbaka , sharri kuwa babu wanda Afra bata kawo wa Aliyu hari sai dai Allah na kubutar da dashi daga sharrinta dan a lokacin har hada baki tayi da wata makwafciyarsu maman Abba cewar tazo da yarinyarta sadiqa tace Aliyu na sa mata hannu ajikinta saboda yana son yara ƙanana sosai kuma yana daukarsu sannan suka koyar da yarinyar yadda idan an tambayeta zata ce Aliyu ne, lokacin da ta dawo gida ta samo kyankyasai guda uku murd'a murd'a saboda shirinta akan kisna tana shigowa bangarenta kisna ta fado tana haki "ke kuma daga ina haka?" daga gida ke na hango shine nazo "yauwa gara ma da kika zo "akwai abinda zai faru a gidan nan gobe akan wannan kinibabban Aliyu da zarar kinji an fara maganar kema kice yana miki ".
Kisna ta girgiza kai "dan Allah aunty Afra Ki daina hadani da wannan mutumin wallahi zuciyata bata kaunarsa bana son duk abinda zai hadani dashi da sauri Afra ta bude roban data saka kyankyasai ai kisna na daura idanunta akansu "tace Kiyi hakuri zanyi duk abinda kike so". "better dan wallahi idan bakayi ba a cikin wandonki zan saka miki kisna ta mike jikinta na rawa ta soma ƙoƙarin gudu Afra ta biyota tana kokarin kamota dan ta kara tsoratata da kyankyaso ."

lokacin da zance ya fito Aliyu ya rude ya shiga damuwa mai tsanani maganar maman Abba bai daga masa hankali ba kamar na kisna aiko tana gama magana mumy ta dauketa da wani gigitaccen mari Wanda yasa take ta fadi ta sume ta daga kafa zata taka mata ruwan ciki Muradi yayi saurin durkusawa ya rike kafar mumy "ka barni na kashe shegiyar yarinyar nan wato kina zuwa ana koya miki makirci kou "? "Dan Allah mumy Karki mata illa ya karasa maganar yana mikewa tsaye rungume da kisna ajikinsa ya kwantar daita akan doguwar kujera ya dauki ruwa ya shafa mata saboda yaga alamun suma tayi a firgice ta bude idanunta "Karki kasheni mumy zan fadi gaskiya tayi maganar tana wuri wuri da ido shiru duka mutanen parlou'n sukai yi Aliyu ya riko hannunta batare da yayi magana ba sai numfashi da yake fitarwa da kyar Samir ya kafeta da ido "muna jinki faÉ—a mana gaskiya waye ya sakaki fadar karya "? Tayi shiru tana kallon Afra dake tsaye rungume da hannuwanta ta bala'in tsareta da manya idanunta mai tattare da gargadin , a hankali Samir ya kalli inda take kallo Afra take kallo jikinta na rawa take jinin jikinsa ya bashi akwai wata a kasa mumy ta kalli maman Abba jikinta na tsuma tace " ki É—auki yarinyarki ki bar min gidana kuma duk ranar da kika sake zuwar min da makamanciyar wannan maganar sai nayi Shari'a dake kuma ko yanzu bazan bar maganar ba ki shirya gobe zamuje muga likita wallahi muddin aka tabbatar da babu abinda ya samu yarinyar ki zaki sha mamakina tsim tsim maman Abba ta dauki yarinyarta sadiqa ta bar gidan sannan mumy ta maida hankalinta kan kisna "wallahi idan baki faÉ—a min wanda ya sakaki fadar maganar nan ba sai na ..."
Samir yace "bari mumy ai zata faÉ—a dan kisna bata yin karya saboda tasan mai karya dan wuta ne, idan mutun yayi karya me kika ce min hukuncinsa shekaranjiya "Allah zai hukunta shi da azabar wuta mai rad'ad'i ta fada cikin rawar murya "to ki faÉ—a mana gaskiya waye yace ki faÉ—a abinda kika ce ?"Ta sake kallon inda Afra take tsaye shima Samir ya kalli Afra na second biyu sannan ya dawo da hankalinsa kan kisna "itace sakaki ko "?Kamar tace masa " eh" amman data tuna murd'a murd'a kyankyasai data gani agurinta sai tayi saurin girgiza masa kai "a'a ba ita tasani ba "to waye ya sakaki ?
"Babu kowa kawai na faɗa ne gaba-daya parlour'n yayi shiru a matukar fusace mumy tayo kanta Aliyu ya ɗauketa cak ya boyeta a bayansa zuciyarsa na wani irin zafi "miko ita nan kafin na gaugaura maka mari".Samir yace "Karki ɗauki hakinta mumy bata da laifi ,ni nasan bata da wayon da zata shirya wannan makircin sakata akayi kuma ba kowa bace ila Afra ....."Bakin Afra na rawa tace "me kake nufi Samir dan Allah karka sakani cikin wannan shirmen saboda ka tsaneni komai kace nice "babu wani tsana illa gaskiya maman Abba kowa yasan kuna shiri daita an samu matsala daga gurinta an kuma samu a gidan nan kinga kuwa duk inda aka je aka dawo da saka hannunki ciki "Allah mumy ki yarda babu hanuna kisna ni na saki ? Ta tambayi Kisna a tude" Ki fad'awa mumy gaskiya "kinga afra duk bana bukatar jin komai ada can kin zauna a hanuna har sanda na aurar dake ,a yanzu kuma kina karkashin mijinki ko ba haka ba ? Afra ta gyada mata kai alamun "eh " to abinda nake son dake daga yau banason na sake ganin kafafunki a bangarena nan gidan mijina ne kema ki zauna a gidan mijinki na miki iyaka da gidan nan har abada , ke ko ciwo nake komai zai sameni bance kizo ba na yafe kowa ya zauna inda Allah ya ajiyeshi , ke kuma mumy ta kalli kisna " ki bari naga kafafunki a gidanta sai na yankaki yanka rago ta karasa maganar zata kai mata duka Aliyu yayi saurin tarewa "hukunci mai kyau mumy baki taɓa burgeni ba irin na yau Malama sai a wuce ko ".inji cewar Samir ..

Cikin sanyin jiki Afra ta nufi kofar fita dukkaninsu idanunsu na kanta cike da takaicinta ,numfashi mumy ta sauke tare da barin falon "sam zuciyarta bata mata dadi da hukuncin data yanke akan Afra ba ,ko babu komai mahaifinta mutumin kirki ne kuma ya sadaukar da rayuwar afra da komai nata gareta har ila yau idan yazo gidan amanarta yake bata gashi akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu tun kafin ya auri mahaifiyar afra tasan yarda da amana ne yasa ya bar mata afra har aurenta ,"shin ita kanta afra bazatace ta goyawa muradi baya ne saboda yana jininta? sosai jikin mumy yayi sanyi shima dady daya dawo ya iske zance bai ji dadi ba sai dai bai ji dadin hukuncin mumy akan Afra ba ,dan haka ya cire dokar hana Afra shigowa gidan da dokar hana kisna zuwa gurinta "tunda kowa yasan halinta sai a san yadda za'a zauna daita "ita kuwa kisna a hankali zaki dinga fahimtar daita dan bazaki iya rabasu ba saboda kece kika bari shakuwa mai karfi ya shiga tsakaninsu ina tabbatar miki koda ban janye wannan hukunci ba kisna zata je gareta ."

Tunda wannan lamari ya faru Afra ta É—auke kafarta a gidan mumy sai dai abu daya tayi tayi kokarin sa ya badamasi ya kawo mata Kisna tun Kisna na jin tsoron karta saka mata kyankyaso a wando har ta ware suka sake dinkewa sai dai mumy bata san kisna na zuwa ba dan satar hanya take ,cikin haka takardun karatun su Aliyu zuwa kasar cairo ya fito suka fara shirin barin kasar kisna sanye da Kayan makarata kamar abun arziki ta shirya ta kama hanya ta fice daga gidan tana fita muradi ya shigo yana daura agogo a tsintsiyar hannunsa sanye da je c da bakin dogon wando wanda kasanshi ke tsuke da rabo "muradi fita zakayi ne yanzu ? ya gyada ma mumy kai alamun "eh."dan ka bi min bayan yarinyar nan zainab bata nan bare su tafi tare yace "to haÉ—e da bin bayan Kisna shida jahid har zata karya kwanar gidan Afra sai ta ga aliyu shi da jahid dan haka ta mike zuwa hanyar makaranta shi kuwa ganin haka yasa suka dauki hanyar inda zasu .."

A hankali ta juyo taga babu su a bayanta ta dawo ta shige gidan Afra tana ganinta ta saki murmushin jin dadi "oyoyo autar mumy nayi kewarki kwana biyu shiru nace kila baki samu hanya bane k'araso muniyassss suka rungume juna suka zube kan kujera ," on 12 ne fa birthday dina me zaki bani gift ? Afra ta fada duban kisna . "me kike so my aunty ?"Ke dai kiyi tunani mana". kisna ta daga idanunta sama alamun tunani abinda zata bata, can tace "yauwa my aunty kawo kunnenki kiji tsadadden abinda zan baki , take Afra ta matso ai tana gama ji ta saki wani ihun murna sannan ta rungumeta "Kai gift mai kyau baby gaskiya kwakwaluwarki naja fa nan suka zauna suna hirar makirci kafin daga baya ta mike ta wuce gida kamar taje islamiyya ,ana sauran sati Aliyu da Samir su wuce cairo aka nemi passport din Aliyu sama ko kasa aka rasa wannan karon babu wanda yayi zargin Afra saboda ta daina shigowa bangaren mumy, haka kisna babu wanda yayi tunanin tana zuwa gurinta , neman duniya anyi wa passport ba'a gani ba .,har lokacin tafiyarsu yayi ba'a gani ba, dole aka daga tafiyar Aliyu Samir ya wuce ya barshi , aiko kisna da Afra suka kulle kansu a bangaren Afra sukayi ta dariya ranar har da karamin party suka shirya shi kansa ya badamasi sai daya tambayi dalilin wannan murnar suka ce" babu komai murna taya birthday ne sai da'aka yi report gurin ma'aikata akan cewar passport din ya bace ne sannan aka bashi damar yin wani ,cikin kankanin lokaci komai ya kammala ya tattara ya bar kasar bayan barin Aliyu kasar Afra ta shiga damuwa da tashin hankali hakan ta dinga jin kewarsa a cikin zuciyarta ..
Tana kwance akan ƙatuwar katifarta tana karewa dakin kallo da tunanin ƙaddara data sameta zuciyarta nata aikin lissafe lissafe halin da take ciki a dalilin barin muradi kasar sai yanzu take jin matukar damuwa kewa da rashin muradi anya kuwa zuciyarta ta kyauta mata kuwa ita da take da burin tabarbare rayuwarsa tayi nufi wargaza shi ta hanyar yaudara ta sha karantawa kanta abubuwa akan shi anya zata yafewa zuciyarta kuwa data tsunduma cikin tafkin tunaninsa babu shiri wasu zafafan hawaye suka fara kwaranyowa a kuncinta ,tayi juyi kukan nada karuwa har ya fara fitowa fili datasanin abubuwan da tayi masa take ,shiru tayi tana tunanin ya zatayi da rayuwata ? " me zatayi yanzu ta daina tunaninsa sannan ta daidaita komai kafin dawowarsa ? ina afra bakin alkalami ya rigada ya bushe zuciyarki ta rigada ta debeki ta kaiki ta baro kinyi sabadiyyar datse duk wani halaka ta arziki a tsakaninki da muradi kece matar da wargaza masa farinciki na rayuwarsa to yanzu wa gari ya waya gashi kin tsinci kanki a tsakiyar dogon dajin da kika rasa ta inda zaki iya , mugunta ta kinkimi kaddararta ta sauya ,yaya zata yi da rayuwarta ? " rayuwa babu tunanin muradi bashi da wani amfani tasan har a nade duniya bazata ji dadin tunanin wani halitta ba kamar yadda take jin dadin tunaninsa ..."

"a shekara duk abinda ta shuka kanta take shukawa mugunta bata san ana haduwa da ukuba tunani irin wannan a dalilin kiyayya ba tun daga lokacin da Allah ya wurga mata tunanin muradi cikin rayuwarta gaba-daya ta sauya walwala kuzarinta nishadi da annashuwa duk suka ragu sai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login