Showing 213001 words to 216000 words out of 495987 words

Chapter 72 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

cikin damuwa gaskiya bazan zauna ba tafiya zanyi idan kaga zaka iya kazo mu tafi tare idan bazaka iya ba ni zan wuce Samir ya kamoshi suna fuskantar juna cikin tsananin tashin hankali yace "ka kwantar da hankali muradi komai zai zo da sauki tunda ga dady ga ya badamasi nasan duk zasu yi komai dan gano inda take , shiru yayi kawai dan bashi da abun da zai sake cewa sai dai baya ji zai iya cigaba da zama alhalin mumy na cikin damuwa ..."

bangaren kisna da musa kuwa kasancewarsu guri ɗaya acikin kwanaki yasa wata muguwar shakuwa da soyayya ta sake shiga tsakaninsu wacce tafi ta da , har ta kai idan ya fita yawonsa sai ta dinga jin kamar ta rasa wani abu daya danganci rayuwarta ,sosai musa yake bata kulawa da matar yayansa har ma da mahaifiyarsa abunka da kuruciya sai kisna take ganin kamar sun ma fi sonta akan yan gidansu duk halin da 'yan gidansu suke ciki musa na kawo mata labari saboda shi yana fita ko'ina yaje yawonsa cikin abokansa ya dawo wasu daga cikin abokansa kamar fatai marly sun san kisna na gurinsa dan haka idan yan gidansu sunzo unguwar sai suyi kamar zasu faɗa musu amman tsoron musa olegele yasa basa iya faɗa sai dai suyita Kallonsu yayinda hakan ke sake bawa yan'uwa kisna haske akan lallai kisna na tare da musa .
yau ma daga massalaci dady ya wuce neman kisna yana furta "laila a illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumi zuciyarsa cike da faduwar gaba "ya Allah kasan ban taba lalata diyar kowa ba da sunan zina Allah ka tsare min da mutunci kisna ka karkato min da hankalinta garemu tafiya kawai yake yana karanta duk wata addu'a da tazo bakinsa har gari yayi haske ya koma gida batare daya ganta ba .."

musa ya siyo wa kisna kanana kaya wando legis dogo da t shirt, kullum zata shirya su fita yawo inda suka san idanun 'yan gidansu ba zai kai garesu ba ,kwasam madu ya jiyo labarin inda suke , jikinsa na rawa ya zo gida ya faɗa aiko gabad'aya yan gidan suka nufi gidansu musa zasu shiga da hayaniya , dady ya hana ya nemi iso a gurin mahaifin musa Alhaji abdulganiyu olegele ,dattijon ya dingiso ya fito waje sanye da gajeren wando da singlet ya mikawa dady hannu amman bakinciki yasa dady ya kasa mika masa nasa hannun ya fara magana cikin ɓacin rai akan abinda ya kawoshi bayan mahaifin musa ya gama jin komai ya shiga gidan ya tambayi alaja mutia , kai tsaye tace masa "ita batasan komai ba amman bari ta Kira musa taji ko da gaske ne ,ta shiga daki ta kirasa ta kora masa bayanin komai ,hankalinsa bai tashi ba kamar yadda na kisna ya tashi saboda za'a rabata dashi , Kuka tasa masa tare da cewa bazata ko'ina ba ya rabu dasu idan sun gaji da wahala zasu koma gida "ki kwantar da hankali ni kaina bazan so Ki koma hannunsu ba amman alaja tace lallai nazo yanzu dan haka kema ki wuce gida ta yadda ba'a fahimci muna tare ba dan alaja bata son ansan muna tare dake ."


tare suka fito ta kowannensu ya kama gabansa ta nufi hanyar gida shi kuma ya nufi gidansu ,koda ya iso unguwarsu ya tarar da dangin kisna tsaye cirko cirko a kofar gidansu ,ko kallon inda suke bai yi ba ,zai shige gida madu yayi taku biyu zai cafko bayan wuyansa dady ya hanashi cikin tsananin bakinciki yace "ba wannan bane a gabanmu ganin kisna shine abinda muka fi buƙata a halin yanzu ko cikakken minti goma Musa bai yi a cikin gidan ba , sai ga Alhaji abdulganiyu ya fito"Alhaji ga yaron da'ake magana akan shi sai dai yace baya tare da yarinyar da'ake nema dan haka kuyi hakuri ku je ku nemi diyarmu a gaba , dady yayi shiru yana saurarensa yana kallon Musa har ya dasa aya sannan yace "ina da karfin da ikon da zan fito da yarinyata a cikin kankanin lokaci amman banason damuwa da tashin hankali ,minti talatin kacal na baku naga yarinyata a cikin gidana idan ba haka ba rayuka zasu ɓaci musa dake tsaye a zauren gidansu ya karasa fitowa waje sosai yana ciccci magani "a fito maka da yarinyarka fa kace to wa kake tunanin ya ɗaukar maka yarinya? kaje kayi duk abinda zakayi tun da yarinyarka bata gurina me zai dameni kuje can Ku nemanta bai gama rufe bakinsa ba yaji saukar naushi a bakinsa aikin madu kenan "dan iskan makaryaci ,wa kake fadawa maganar banza ?" zan maka duka mutuwa yanzu kuma na doki banza , Khalid zai maka karya ne?" to shine ya tabbatar min da kisna tana gurinka , wallahi idan wani abu ya samu kanwata ka mutu kafin kace me dambe ne ya kaure a tsakaninsu da kyar aka rabusu musa na zagin Madu, madu nawa musa gargadin akan ya fito da kisna .

a matukar jikace suka karaso gida mumy na ganinsu empty hand's babu kisna ta rushe da wani kuka tana salati "ina yarinyata take karku ce min baku ganta ba "?Dady bai ce mata komai ba dan bakinciki gani yake duk itace silar wannan matsalar da tabi abun cikin sauki da wata killa basu tsinci kansu cikin wannan damuwar ba , ya shige d'akin shi ya zauna a kasan tayis ya tallabe kanshi da hannuwsnsa duka shi kadai yasan yadda yake jin zuciyarsa .."

Misalin karfe goma shabiyu daidai na daren ranar mai gadi gidan yaji ana buga karamin get ya tashi da sauri ya fito daga dakinsa yana tamabayar "waye ?"Alhj Hamza ne ka bude tare nake da kisna jin ya ambaci sunan kisna ya bude masa karamin get da sauri ,ya shigo rike da tsintsiyar hannun kisna mai gadi ya maida kofar ya rufe yayi gaba alhj hamza na biye dashi da kisna wacce ke dar-dar din abinda zai faru .

cikin daga murya mai gadi yayi magana a lokacin da gabad'aya mutanen gidan ke zaune a parloun cikin jimami kowane na fadar irin bala'in da za'a yi gobe idan ba'a fito da kisna ba yayinda mumy ke ɗakinta a kan sallaya rike da carbi tana ja hawaye shabe shabe akan fuskarta . Alhaji hamza ya tsaya a bakin parlou'n tare da yin sallama shi kuma mai gadi yana cewa ga kisna sallamarsu aka amsa suka shigo a hankali jikin madu ke rawa saboda jin sunan kisna dan shi kasa amsa sallamar yayi idanun madu na sauka a kan kisna ya nufi dakin mumy cikin sauri yace " mumy ga kisna nan ya juya da sauri ya fito wata irin zabura tayi ta mike tsaye jikinta na rawa ta fito hannunta rike da gefen zaninta alhj hamza ya samu guri ya zauna kisna ta ruku'be a jikin bango cikin tsananin tsoro da matsanancin firgici a hankali zuciyarta ke bugawa da karfi , mai gadi ya kama gabansa yana mai jin dadi an ga kisna "ina alhj realwan ? Alhj hamza ya tambaya
"Gani dady ya amsa yana ƙoƙarin fitowa saboda sunan kisna daya ji an ambata ne ya fito dashi " ita din ce kuwa dady ya furta ya soma taku zai isa gareta tayi wuf ta boye a bayan Alhaji hamza tana Kuka a tunaninta dukanta zai yi."

"karka taɓa alhj sha'anin dan yau sai hakuri tunda ga yarinyarka ta dawo shikenan "ai ba dukanta zanyi ba "."Yauwa yanzu dai babu abinda zamu ce sai godiya ga Allah da yasa aka ganta tabbas tana gurin yaron nan dan ko ni na samu labari amman rashin kaukauran sheida yasa nayi shiru gata nan yanzu naganta tana la'be labe na cafkota ayi ta addu'a kuma ana kula daita Allah ya shirya mana zuri'a shiri na addinin muslinci dan Allah kar wanda ya doketa a bata abinci taci tayi wanka ya mike tare yi musu sallama , dady ya biyo bayansa yana masa godiya ...."

Afra ta karasa ta rungumeta tana kuka gaba-daya damuwar rashin kisna yasa ta nemi damuwarta ta rasa "me yasa kisna ?"Mai yasa kika tafi kika barmu Karki sake barin gida akan namiji zuciyarmu bazata iya daukar rashinki ba ,kalleni ko abinci bana iya ci kalli kowa ki gani dan Allah Karki sake kinji ta k'arasa maganar tana kuka itama Kisna kukan take ,mumy ta tsura mata ido kawai tana kallonta tana kuka duk ta rame farinta ya dusashe alamun bata samun kulawar data dace gabad'aya ta zube kamar ba kisna ba cikin tsananin tashin hankali mumy ta fara magana "yanzu kisna daga dukanki kika sa kafa kika bar gida batare da kinyi tunanin halin da zamu shiga ba ,sannan kika rasa inda zaki sai gurin wannan dan iska yaro guda nawa kike kisna da zaki zabarwa kanki irin wannan rayuwa ?
" me zaki yi da wannan dan iskan ya.....""Abar magana kowa yaje ya kwanta Allah ya tashemu lafiya ya badamasi da ya kasa magana saboda tsananin bakinciki ya nufi kofar fita Afra na biye dashi a baya tana masa magana yayi mata banza .."

Mumuy ta zuba mata abinci ta ci sosai sannan ta shiga dakinsu ta shige bayi ko kallon inda Zainab take batayi ba Dan har lokacin tana jin haushinta,a cikin daren mumy ta kira Aliyu ta sheida masa an ga kisna naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da furta" alhamdulillah a fili mumy dan Allah kar a sake dukanta ayi mata duk abinda take so muma inshallahu karshen shekarar nan zamu shigo sukayi sallama sai ranar Aliyu ya samu wadataccen bacci dan kullum da tunanin kisna yake kwana yake tashi shi kansa ya rasa dalilin dayasa yaji ya damu daita sosai a lokacin daya ji ta bar gida .."
washegari mutanen da suka san an neme kisna an rasa suka yita zuwa suna jajanta wa mumy tare da bata shawara akan yadda zata bullowa abun ,matar Alhaji hamza tace " sai fa kin tashi tsaye da rokon Allah dan wannan yaro da yan'uwansa ba mutanen kirki bane bare ayi tunanin hada zuri'a dasu mumy tayi mata godiya .

tun daga lokacin bacci ya kauracewa idanun mumy kullum cikin addu'a da nasiha takewa kisna da sake janta a jiki duk abinda tace tana so shi take mata haka duk abinda za'a girka a gidan sai an tambayeta haka ma dady duk zai fita office sai ya shigo dakinsu ya tambaye ta ko akwai abinda take so idan zai dawo yazo mata dashi sannan zai bata kudin kashewa dan duk hankalinta ya kwanta ta manta da musa yayinda ita kuma duk abinda mumy da dady suke mata baya gabanta burinta taga sanyi idanunta a sati biyun datayi a gida duk a takure take jikinta babu abinda take buƙata kamar ta sanya musa a idanunta ,hanyar fita kawai take nema ta sha gwada fita sai dai mai gadi na tsaye kyam ko sallah zashi sai ya samu wanda ya tsaya masa bisa dokar dady kar abarta taje ko'ina har sai ya nemo mafuta dan ko maganar cigaba da zuwa school dinta ba'a yi an barta a gida har aka cinye zango karatu tana zaune gida ,saboda ita mumy ta daina fita ko'ina sannan ko compand din gidan bata aikenta komai masu aiki ke yi ko dan gyara d'akin da take sakata ta daina ,
lokacin da za'a koma school aka canza mata mkaranta zuwa Grange college hakan kuwa yayi bala'in d'agawa kisna hankali har kuka tayi a boye saboda tasan bazata samu damar ganin musa yadda ya kamata ba , washegari ranar farkon data fara zuwa school direba na sauketa ta fito ta nemi musa a business center har ya shirya zuwa school ya fasa ya fada mata inda zasu haɗu ...
Zuciyarsu kamar zata buga cikin tsananin farinciki suka rungume juna numafashinsu na barazanar ɗaukewa "i miss You ta furta masa tana kamkameshi ajikinta yace "me too ajiyar zuciya ya sauke tare da zareta ajikinsa ya kafa mata ido ",kin ƙara kyau fa ifemi rashina ma bai sa kin canza ba ,ta narke fuska kamar zata saka masa kuka "bazaka gane halin da rashinka ya sakani ba ta k'arasa maganar tare da kai hannu ta shafi gefen fuskarshi kai ma kayi kyau yayi murmushi "ni ina naga wani kyau ?
"No karka ce haka kana da kyau fa sosai "dan kina sona ne shiyasa kike ganin kyauna , hannu juna suka rike suna jin kamar karsu rabu , nan ta wuni a gurinsa sai lokacin tashi ta wuce gida kullum idan aka sauketa Ko cikakken minti biyar bata yi take fitowa su jone da musa, sai ta wuni a d'akinsa suna romancing din juna sannan ta koma nesa kaɗan da bakin get din school ta jira zuwan direba .

haka nan jikin mumy ya bata kisna tana tare da Musa dan haka ta kirata d'akinta ta nuna mata gurin zama "kisna har yanzu bazaki fita harka yaron nan ba ko jikina fa na bani kina tare dashi ."wallahi mumuy bama tare haka kisna tayita rantsuwa akan basa tare da musa sai dai zuciyar mumy bata amince daita ba ", yi min shiru munafukar Allah kawai bayan duk sanda kika je school kika dawo sai naji jikinki na warin maza kuma irin warin yoroba , yanzu bazaki yiwa kanki faɗa ba kisna , ki ma rasa wanda zakiyi soyayya dashi sai wannan yaron da baki yayiwa yan gidansu myawa kowa ya bude baki babu alkhairi wallahi ace wannan yaron bahaushe ne ni da kaina zan bari a miki aure a shekarunki na 12 a duniya "nifa mumy bana tare dashi "Allah yasa haka ne mumy ta hakura ta bar maganar ne dan babu yadda zatayi ."

wani abu daya ƙara d'agawa mumy hankali bai wuce duk sanda kisna zata dawo daga school ba sai taga idanunta sunyi ja alamun tayi faɗa ,"idan ta tambayeta sai tace mata babu komai nan kuwa dambe ta sha da yammata musa dan lokacin ko tsayuwa taga kinyi da musa ko kalmar gaisuwa ce zata dauka son shi kike yi , itama wani bai isa ya nuna yana sonta ba yanzu za'a yi yaki dashi ,abun har ya kai su da sun fara yin dambe a tsakaninsu kamar dai yadda al'adar yoroba take saboda yawon yammatansa ,zuwa gidansu kuwa kai tsaye take zuwa ta ma daina jin kunyar 'yan unguwar su, yanzu gashi kusan dangin musa kowa yasanta cikin haka yan gidansu suka samu labari dady yasa aka kama musa da mahaifiyarsa ,da yaso a haɗe har da mahaifinsa ne sai aka ci rashin Sa'a uban bashi da lafiya yana kwance har an saka masa roban fitsari Dan haka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login