Showing 201001 words to 204000 words out of 495987 words

Chapter 68 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

iya rashin ji ".

*****
Da yammacin ranar wata juma'a afra ta lalla'ba ta shiga dakin mummy ta sato sakar zinarin mummy wanda akalla kudinsa zai yi nara dubu dari tara , Kisna ce zaune a gabanta , yayinda afra ta kamo hannunta ta damka mata karamin akwatin sarka a tafin hannunta cike da kauna ,cikin tausasan murya kisna tace " me zanyi dashi aunty ?"so nake ki saka a jakar kayan Aliyu amman karki bari kowa ya ganki ki lalla'ba ki saka masa , so nake a kamashi dumu dumu da laifin sata kafin musan yadda zamu koreshi daga gidan nan ko bakya son ya bar gidan nan ?".
"Ina so mana aunty shi da yake takura min sai naje islamiyya gashi yana sa mutane punishment akan dole na tsanashi sosai banason shi "yauwa baby nah Kinga idan ya tafi kin huta zaki sakata ki wala ko ?
Kisna ta gyada mata kai alamun" eh , "assalamu alaikum sallamar ya badamasi ta karad'e falon "me kuke tautaunawa haka kun wani haɗe kanku guri daya ?".Afra tayi saurin boye sarka hannunta tace "wa'alaikas Salam Barka da dawowa hirar ce kawai muke yi "Kisna ta mike tsaye "nima so nake na tafi zanje na shirya zuwa islamiyya "okay bari to na rakaki "a'a ba sai kin rakani ba kisna ta faɗa a matukar tsorace sai an jima ! sai an jima!! dan a wautatan ya badamasi ya fahimci abinda suke kullawa ,afra bata daga hankalinta kan dole sai ta biyota ba saboda ganin hankalin mijinta yana kansu ta dawo kusa dashi cikin sakin fuska "ranar yau akwai zafi kou? ta fada tana amsar jakar hannunsa "haka ne a dan kwanakin nan ranar yayi zafi sosai mutane na shan wahala".annu ta amshi jakarsa ta ajiye ta tsiyaya ruwa a glas cup ta mika masa "ka sha kaji sanyi .Ya amsa ya sha tare da ajiye cup "ya kamota ya zaunar daita akan cinyarsa " idan rana tayi sanyi mu dan fita mu shakata , " me zai hana mu samu yanayin mai dadi ba irin wannan lokacin ba dan lokacin zafi fita yawon shakatawa babu dadi ."
"Ni zan shiga nayi aikina ta mike tsam batare data tsaya jin abinda zai sake cewa ba , ya bita da ido kawai saboda ya lura har lokacin bata ta tashi , sannan ya rasa inda zuciyarta da hankalinta yake ,kwata kwata abinda ya lura dashi tana dai zaune dashi ne ba dan tana son shi ba , wayarsa ya ɗauki ƙara ya dauki wayar "hello
akace masa a can bangaren "okay na gane shikenan gani nan zuwa .."
Tashi yayi ya shiga ciki yayi wanka ya fito cikin wasu kananan kaya "zan dan fita amman ba dadewa zanyi ba akwai magana mai mahimmanci da nake son muyi sai dai yanzu bazan samu damar yi ba sai na dawo zuwa anjima ya fita ya barta tsaye cikin jimamin maganarsa .

"Magana kuma wace irin magana ce zai yi dani har da cewa tana da mahimmanci ?" .Tayi shiru tana tunani ,kai tsaye ya badamasi part din mummy ya shiga dan da safe yana sauri bai shiga sun gaisa ba "ina kuma zaka daga dawowarka son ?" Mummuy ta fada tana dubansa "Akwai aikin da zanje nayi ne yanzu amman ba dadewa zanyi ba zanje na dawo "to shikenna Allah ya bada Sa'a "ameen ya fada sannan ya fita.

"kai muradi ina Samir ne?
"Nima ban gashi ba mumy "to ina yaje haka"? " tun safe daya fita ban sake ganinsa ba ?"Me yasa zai dinga fita batare daya sanar dani ba ?"Kaga bambamcinku dashi kenan baza'a taɓa nemanka a rasa ba, zai dawo ya sameni ne inji cewar mummuy "kiyi hakuri mummuy bari naje na dubo shi yanzu , jikina yana bani ko yaje neman kudi da zamu biya kudin club ne "
Neman kudi kuma ?Yanzu danace a hakura baza'a yi ba sai da kuka takura kanku ?"Wallahi ni mummuy na hakura shima ina ta fama dashi akan ya hakura , bari dai naje na nemo shi Ya juya cikin sauri zai fita .."

"Kaga dawo karka wahalar da kanka zai dawo kana jina ko muradi yau tsawon kwana biyu kenan ina neman akwatin sarkarta dubai ban gani ba, gashi ita nake son na bawa hajiya asabe ta canzo min idan taje Kano kuma d'azu da safe ta kirani wai gobe zata wuce ."Kuma kin duba inda kika ajiye ?"na duba sosai a tsakiyar kayana na sakata sai dai babu inda ban duba ba amman bangani ba ,"okay bari naje na sake duba miki ya shiga d'akinta ,babu inda muradi bai duba ba har inda mummuy bata ajiye sarka ba ya duba amman bai gani ba ya gyara mata kayanta kamar yadda ya tarar yaje ya fada mata bai gani ba mummuy ta cika da mamaki tayi shiru tana tunani babu abinda zuciyarta bata saka mata ba "to yaushe aka fara sata a gidan nan ?"To waye ma zai ɗaukar mata sarka gida daga ita sai Samir ,madu Aliyu sai kuwa zainab da duka satinta daya to ko zainab ce ?
"Kai guda nawa zainab take da zata dauki sarka kamar wannan to waya shigo ya daukar mata sarka..?
Da daddare har dady mummuy sai data tambaya yace "bai gani ba har washegari neman sarka ake amman babu ita babu alamunta yayinda duk sanda mummuy tayi maganar sarka sai gaban kisna ya fadi saboda sanin inda sarkar take ,mummuy ta kalli kisna dake zaune kusa daita tace "zo nan mammana jiki a sanyaye ta karaso ta tsaya a matukar tsorace "ko kin ɗauki sarkata kinje wasa dashi ?
Kisna tayi saurin girgiza mata kai "ki faɗa min gaskiya ? Allah ban ɗauka ba mummuy tayi shiru tana nazarin yadda ta nemi sarka aka rasa ."

" Akwai abinda kake bukata ne ?
Ya badamasi dake zaune yana bin afra da kallo yace "a'a yanzu na tambayeki zaki iya fita shakatawa tare dani ? Tayi shiru tana kallonsa tare da lulawa duniyar tunani " koda da adaddare ne hakan zai samu ?nan ma shiru tayi ta kasa cewa komai har sai daya tabota tayi firgigib "kayi hakuri banji abinda kace ba ka sake maimaitawa ."bance komai ba ya fada cikin dakiyar zuciya, ganin yanayinsa ya canza ta fahimci bai ji dadi abinda tayi ba , dan haka ta matso ta shige jikinsa taji zafi sosai "anya kuwa ma ba zazzaɓi kake yi ba amman kake maganar fita gurin shakatawa ?"Karki damu dani , akwai abinda nake son na tambayeki ?"Ina da tamtamar zamana dake akan bakya sona kawai dai kin aureni ne dan babu yadda zakiyi ko ba haka ba ? "amman me yasa ka tambaya ?"kawai dai Ina son sani gaskiya ne saboda nasan matsayin zuciyata agurinki zan cigaba da sonki ne ko kuma zan takaita daga yadda nake ."Me zuciyarka take shiryawa akaina "ke zanwa wannan tambayar tunda na aureki dai-dai da rana ɗaya banga wata alamar ta soyayya daga gareki ba ko aurattaya muke bakya nuna kina jin dadi ,kuma idan zanyi sati biyu zuwa wata daya ban nemiki a shimfidata ba bazaki damu ba bare ki nemi ..."

"kai ya badamasi ka daina fadar haka kowace zuciya da yadda take daukar nata soyayya "kunji ba maganata dai tana kan hanya ya fadi haka yana zareta ajikinsa "kuma kullum za'a kirani sai dai yaya badamasi har zuwa yanzu ban samu matsayin da za'a kirani da honey ko darling da dai sauransu ba ."to kayi hakuri inshallahu zan canza "Allah yasa ya fada yana ƙoƙarin shiga dakinsa tare da zare agogon hannunsa "Ni dai har ga Allah ina matukar sonki kuma bana jin zan daina sonki ya sake kamota ya haɗeta da jikinsa ya zagaye hannuwansa duka a kugunta ya manna mata kiss a gefen wuyanta "kice kina sona babu love Ina son jin wannan kalmar daga bakinki .."Shiru tayi yayinda
a zuciyarta tace "wannan kalmar ce bazaka taɓa samu ba daga gareni saboda har ga Allah bana sonka , da laifi na mallaka maka zuciyata ko furta maka kalmar so alhalin baka cancanta ba duk yadda yaso ta furta masa ki tayi ta shige jikinsa tare da mantar dashi komai akan batun soyayya ..."


Cike da dabara afra ta sanya akwatin sarka mummuy cikin kayan Aliyu ,yau kusan wata biyu kenan mummuy na neman akwatin sarkarta ta tattara yaran gidan kaf ,mummuy ta kalli Samir "cikin kai da madu ku fito min da sarkata dan bazan saka muradi da zee ciki ba "mummy nifa ban ɗauki akwatin sarkarki ba ,nima ban ɗauka ba samir da madu suka fadi haka kisna najin haka jikinta ya kama rawa "kenan akwatin sarkata yana da kafa ko shi ya dauki kanshi da kanshi to shikenna duk inda ma ya shiga zai fito ne ,amman zan so ka faɗa min gaskiya, kai Samir ance ka biya kudin club ina ka samu kudi idan ba sarkata ka ɗauka ka siyar ka biya muku ba ?"Wallahi mummuy ki tambayi mujahid wani cleat dina ne ya biyani shine na biya mana amman me zai sa na dauki sarkarki mummuy ? Muradi yayi saurin cewa "gaskiya ne mummy wallahi bai ɗaukar miki ba," kai ma ka min shiru anan wato ka fara biye masa ko ? ta karasa maganar tana kokarin shiga Kitchen ,afra dake la'be tana jin abinda suke faɗa sai data bari sun gama tayi wuf ta fito ta biyo bayan mummuy "lafiya mummuy ke dawa haka kike ta fada ?"Wallahi akwatin sarkata nake nema ina tunanin Samir ne ya ɗauka ya siyar ya biya musu kudin club "anya mummuy Samir din zai yi haka ? "Ke dai ki duba da kyau ko kuma ki bincika cikin kayansu idan ma ɗauka yayi ya siyar dole za'a samu wasu kudi a hannunsa bare ina da ja akai wannan ba halinsa bane " , mumy tace "ya dauka ya siyar fa "gaskiya mummuy Samir baya da wannan halin Samir baya sata ,Samir na jinta ya sauke numfashi "ya biyo mummuy kitchen "haba mummuy wai me yasa kike min haka ne ? wallahi ni ba barawo bane ,me zanyi da sarkanki ? yayi maganar hawaye na zubo masa Aliyu ya kamoshi shima hawaye sun cicciko idanunshi gashi magana yake son yi masa amman bakinsa ya kasa furta komai , haka dai sukai ta magana akan batar sarka har satin ya wuce ba'a gani ba ,ganin hankalin mummuy bai kai ta duba dakinsu ba yasa afra ta sake satar jiki ta dauko sarka a wata safiyar asabar su Aliyu suna makarantar islamiyya ta saka cikin jakar kwallonsa tasan dole zai dauko jakar zuwa da yamma ko kuma washegari ranar Lahadi fatan ta dai idan ya zazzage jakar ya zamo akwai idanun mutane ,ai kuwa da yammacin ranar Aliyu da Samir suka shigo falo kowannensu hannusa rike da jaka , yayinda mummuy da dady da yaya badamasi da afra har ma da aunty wacce tazo gidan , suna zaune a parloun suna hira. "kaga mazajen mummuy, Allah mummuy bakaramin Fama zaki yi da yammata akan wannan ɗan naki ba ,kalleshi fa kullum sai ƙara kyau yake da kwarjini ranar daya zo gidana rasa yadda zanyi da yammata gidanmu nayi kowa tana so kinsa har kanwar sha'aban ruky da bata magana tsabar miskilancin sai datayi data ganshi da alamun son shi take dan ko yau sai data ce min na gaishe mata da mai kyau, bata san ba'a yi masa gwaninta ba ta karasa maganar tana dariya ...."
Aliyu kuwa tun data fara magana ya haɗe rai tamkar wanda aka aikowa sakon mutuwa dan ya tsani ana yi masa zance yammata , ya samu guri opposite din mummuy ya zauna yana ciro takalminsa wanda ka'ida ne idan zasu fita buga kwallo shi a parloun yake karasa shirinsa .
mummuy tace "gashi shi kuma a duniyarsa babu abinda ya tsani ji kamar zance yammata da aure ba ? "Ai kuwa yin aure dole , kai nice ma zan haifa maka matar gabad'aya kowa ta huta ...... "Wannan karo kowa yayi dariya banda afra dataji ranta ya soso sai dai Allah Allah ta dinga yi mugun nufinta ya hau kan Aliyu mutuncinsa da darajansa su wargaje a gaban ahlin da suka fi kaunarsa akan komai "babu uwar da bazata so baka auren diyarta ba muradi natsuwa kamewa kwarjini ilimi komai Allah dai ya bani haihuwar diya mace na baka daga yanzu ma ka zama surukina "Kai aunty ummi Wai me yasa kike min haka ne ?inji cewar muradi "Kai ma me yasa baka son maganar aure ?"Rabu min da yaro ummi , aure kuma inshallahu zai yi bazan mutu ba sai naga aurensa da ya'yansa ,ke kuma ki rike yarinyarki dan bazai zauna har sai kin haifi mace ta girma sannan yayi aure ba suka sake kwashewa da dariya har dady , afra ta yatsina fuska ita dai burinta ya zazzage jakar tunda kowa yana gurin "dan Allah Aliyu kayi sauri kasan fa mu kadai ake jira "sorry samir duk laifin aunty ummi ne ya fada yana jan tsaki , Samir ya karaso zai dauki jakar Aliyu da niyyar dauko masa dayar safarsa , Aliyu ya rike jakar "karka damu zanyi komai da kaina dan'uwa Samir ya fixge jakar "dan Allah ka cika sanyi jiki wallahi ya zazzage jakar sai ga sarkan mummuy a kasan tayis sai walkiya take zubawa , dake idanun kowa na kansu ana barkwancin yasa suka ga sarka, wata irin zabura afra tayi tace "mummuy wannan kamar sarkar da kike nema me take a jakar Aliyu ? ta dauko sarkar tana nunawa mumy ,take kan Aliyu ya sara , zuciyarsa ta shiga rawa da shiga tashin hankalin da bai taba haduwa dashi ba a dalilin ganin sarka acikin jakarsa ......."









Mmn sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 31

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.


"Gabadaya kallo ya koma kan Aliyu dake zaune cikin tsananin tashin hankali da fargaba zuciyarsa cike da mamakin abinda ya kawo sarkar mumy cikin jakarsa , bai gama mamaki ba yaji sautin Muryar Afra ta karad'e parlour'n cike da isa da izza "me sarka momy take a cikin jakarka Aliyu ?"Shiru yayi ya kasa bata amsa tambayar da tayi masa sannan ya kasa d'ago kanshi ya kalleta illa zuciyarsa da gangar jikinsa da suka ɗauki rawa " ..
"Mummy dady aunty ummi duk kunyi shiru kuna kallonsa ba zaku kuyi magana ba ? " ku tambayeshi dalilin zuwan sarkan cikin jakarsa mana ? " Shiru sukayi mata gabad'aya zuciyar kowannensu cike take da rashin yarda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login