Showing 189001 words to 192000 words out of 495987 words

Chapter 64 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

akwai labari " zama yayi kusa da ya badamasi itama ta zauna gefensa tana zolayarsa suna barkwancinsu da suka saba "eh yau din dai nasan hirar duk akan surukarki zai min suka sa dariya gbdy har dasu Afra da bata fahimcesu ba shi kam badamasi sai murmushin jin dadi yake dan rayuwar iyayensa na matukar burgeshi"

Gabad'aya hayaniyarsu ta karad'e parlour'n ya badamasi na ci abinci yana zuba santi Afra ta mike ta jingina bayanta a bayansa "ga taimakon gaugauwa dan karka rushe a kasa, ya kai hannunsa zai zuba mata dundu tayi saurin janye bayanta "yanzu ya badamasi sai ka zuba min wannan hannunka ?"Da dai kin tsaya yarinya kiga aiki da cikawa suka tuntsire dariya ...""Assalamu alaikum" sallamar abokan muradi da Samir ne ya karad'e parlour'n jahid khalifa da yasir Habib suka ƙarasa shigowa , gabadaya mutanen dake zaune a parlour'n suka amsa musu ban da afra data yatsina fuska dan sam bata qaunar masu zuwa neman muradi kusan duk wanda yake tare dashi haushi yake bata suma kuma sun san da wannan tsanar , su jahid suka k'arasa shigowa falon haɗe da gaishe da mummy sannan suka wa ya badamasi sannu da zuwa sannan suka samu guri kan doguwar kujera suka zauna kowanensu hannunsa rike da iPhone, muradi da Samir suka mike daga inda suke zaune akan kujerar dining table suka zauna kusa dasu ,nan hayaniyarsu ta karad'e parlour'n ban da hirar kwallo da yahoo babu abinda suke suna tsaka da hira jahid yace" ku tsaya na baka wani labarin ban dariya ya badamasi da yayi niyyar mikewa dan ya huta jin abinda jahid ya fada yasa ya gyara zama dan Allah yayisa da son jin labarun ban dariya musamman yake zuwa gurin hajiya kayi ta dinga bashi a lokacin da take zaune a Lagos jahid ya soma magana yana dariya "wani mahaukaci ne ya iske wata mahaukaciya a bakin rafi tana kuka sai wannan mahaukacin yace "ke mahaukaciya me yasa kike kuka ?".
Sai tace "sugar na zuba a cikin rafi kuma bai yi zaki ba ".Sai mahaukacin yace "cokali yakamata ki samu ki gauraya zai yi zaki ya karasa maganar yana kwashewa da dariya duk parlour'n babu wanda bai yi dariya ba har afra sai datai dariya ,jahid ya saida dariyarsa yana numfasawa "yanzu cikin su wa yafi wani hauka nan wata hayaniyar ta sake kaurewa wannan yace mahaukaciyar wannan yace mahaukacin ganin sun soma mutsu a tsakaninsu yasa ya badamasi ya mike ya nufi bangarensa yaso Afra ta biyosa amman mummy tayi dabara ta aiketa d'akinta dan ita dai idan tace tana qaunar hadin nan tayi karya saboda wasu daga cikin halaiyen afra din da bata so ,duk yadda ya badamadi yaso kebe wa da Afra mummy taki yarda ,hatta tsarabansu shi da kansa ya kawo musu sai dai na afra dana kisna yafi na kowa yawa, har zahra da mufeeda suka saka ayar tambaya amman ta sharesu".

Daren washegari ranar badamasi ya dade a d'akin dady suna tautaunawa akan rayuwar duniya a hankali suka gangaro kan maganarsa da Afra sun jima suna tautaunawa har sai da mummy ta shigo ta koresa tace "maza tashi ka bar min miji ya huta haka nan wai ma me kuke ta faman tautaunawa akai ?"ya Badamasin yayi murmushi ya tashi yayi musu sallama ya wuce part d'insa .
Bayan wata da dawowar ya badamasi yana tsaye a tsakiyar dakinsa yana shirya kansa cikin wasu ratsatsun kanana kaya , ya gama ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi , kai tsaye part din mummuy ya nufa ya tsaya yayi breakfast sannan ya nufi kofar d'akinta yana isa yayi sallama ya ɗan tsaya domin ta bashi damar shigowa, mummy dake tsaye cikin wani had'ad'd'en volyal lace Mai kyau da tsada sai kamshi turaruka take ,ta waigo zuwa kofar shigowa d'akin tare da bashi umarnin shigowa, Ya badamasi ya shigo dakin fuskarsa dauke da annuri da tsantsar farinciki ,a natse ya karaso inda mahaifiyarsa take tsaye tana saka abun hannu ya amsa ya k'arasa saka mata yana yabawa da yadda mahaifiyarsa ke da tsananin tsafta da kula da kanta a zuciyarsa , ta kowani bangare baka isa kaci gyaranta ba, dan kusan dukkaninsu yanayinta suka d'auko gurin tsafta da iya tsara kwaliya son kamshi cike da girmsmawa ya durkusa har kasa ya gaisheta "ina kwana mummuy ?".
Mummy ta shafa sumar kanshi cikin farinciki tace "lafiya lau son ka tashi lafiya ya gajiyar aiki fatan komai na tafiya yadda ya dace "alhamdulillah mummuy komai na tafiya daidai sai godiyar Allah ,dan hira suka soma tabawa kafin daga baya ya yunkura ya mike "bari naga dady kafin ya fita office ."Wani dadyn mutumin da yayi sammakon fita ,ai tun bakwai ya bar gidan nan ko breakfast bai tsaya yayi ba, shiyasa yaso ace kasuwanci ka karanta amman ka nacewa wannan aiki ,gashi ka bar min miji yana faman shan wahala shi kadai ta karasa maganar tana haɗe rai tare da kawar da fuskarta gefe alamun fushi".Ya kamo hannuwanta duka cikin nashi "kiyi hakuri mummuy wallahi koni yanzu nayi nadamar za'bar aikin karatun likintanci da nayi akan kasuwanci ,sai dai babu yadda zamuyi da qaddara, inshallahu nan gaba dady zai zauna ya huta tunda ga Samir Aliyu da madu nan , mummy ta juyo a hankali ta tsura masa idanunta "naso ace kaine ka gaji mahaifinka tunda kai ne babba "ya sakar mata murmushi cikin tautausan lafazi yace "maganarki gaskiya mummuy Amman Shima wannan aikin dana yi karatu akanshi yana da nashi amfani kuma zai taimaka sosai, mummuy ta saki fuskarta "shikenna Allah ya taimaka sai ka maida hankalinka sosai akan aikinka kafin batun aureko?". ya badamasi yayi shiru na wani lokaci sannan yace "nifa mummuy nan kusa nake son ajiye iyali". mummuy ta girgiza masa kai alamun rashin yarda "bazan taɓa yarda ba duka Afra ma guda nawa take da za'a ce aure yanzu kai amatsayinka na likita kaga dacewar haka ace ka auri yarinyar yar shashida ?"ya badamasi yayi raurau da idanu kamar zai fashe mata da kuka yace "mummuy a ra'ayina banason auren yarinya sama da shashida zuwa sha takwas kuma wa zai dubi Afra yace bata zarta 16 ba dady ma yace suna kare secondary school zai aurar dasu gabad'ayansu, kinga kuma wannan shekarar zasu kare tunda ya soma magana mummy ta tsura masa idanuwanta masu haske irin nasa domin tabbatar da abinda yake faɗa mata ita ba auren bane bata so afra dince bata son ya aura nannauyen ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "to da kake ta rawar jiki ita yarinyar ka faɗa mata ne ?ya girgiza mata kai "cikin satin nan dai nake son faɗa mata , nasan inshallahu bazan wani samu matsala daita ba tunda akwai shakuwa mai karfi a tsakaninmu ,tana son cusa masa ra'ayin kin aurenta amman sai wani bangare na zuciyarta ke kwabarta muryarta a raunane tace "shikenna Allah yasanya alkhairi , Allah yayi maka albarka cike da farinciki ya amsa da "Ameen ".
"Tashi muje kaci abinci "sai dana ci mummuy kafin na shigo " .
ya mike tare da yi mata sallama ya wuce office .

daddare ya badamasi da afra na zaune akan dinnig table yana faman zuba santin abinci da afra ta girka masa ya dubeta yace ."girkinki yayi dadi sosai har yasa na kusan mantawa da kunnena ".Tana jinsa tayi shiru haɗe da maida idanunta a kan Aliyu dake zaune akan kujera yana duba takardun makarantarsa dan suna da text gobe , sai daya zungureta sannan ta dawo da hankalinta gareshi tace "daman ai kwadayi ne da kai ".ya ajiye spoon din hannunsa ya ɗauki ruwa ya sha kaɗan ya mike tsaye ya kamo hannunta " tashi muje dakina akwai maganar da nake son muyi dake mai matukar mahimmanci". ta girgiza masa kai alamun bazata ba "ka faɗa min anan mana "Bazaki fahimta a nan ba zai fi kyau mu kebance kanmu "karka damu yaya zan fahimceka yayi murmushi ya koma ya zauna yana murza yatsun hannunta ",ina son na dinga ganinki a kusa dani hakan yana matukar sakani farinciki" ta sakar masa murmushi ta sake maida idanunta akan muradi wanda ita kanta ta rasa dalilin kallon da take masa a yau din nan , gabad'aya ya badamasi ya tattara natsuwarsa da hankalinsa akanta yayinda ita kuma ta tattara hankalinta da natsuwarta akan muradi .

ya badamasi yayi kasa da muryarsa sosai sannan ya fara magana a natse "Afra akwai wanda kike so ne "?.
Onexpecting ya jeho mata tambayar ,
duk da shi yasan bai zama lallai ace tana soyayya da wani ba , duba da yanayin gidan nasu , ba'a bada wannan chance din, ko ummi dady ne da kanshi ya had'ata da yaronsa har ta kai su ga aure ,Afra ta tsaida idanunta sosai a kan muradi tana cigaba da kallonsa tayi tamkar bata ji abinda ya badamasi ya fada ba , tun daga kan yatsun kafafunsa har zuwa yatsun hannunsa take bi da ido , haka nan yau ta tsinci kanta da kallonsa abinda bata taɓa yi ba kenan a tun sanda suke rayuwa a gidan ,duk inda yayi idanunta na kanshi haka matsonsa ."ya badamasi ya kai hannu ya dawo da fuskarta garesa "abokin fadanki kike kallo haka ko da matsala ne ? "ta furzar da wani numfashi mai zafi tana hura hanci cike da takaicin kanta dan me zata zauna tana kallonsa kamar wani shahararre , ko ɗan wani attajiri bayan ubansa ma yana can yawon duniya ya manta da rayuwarsu sam wannan kallon da take masa bai dace da mace kamarta ba , ta sake jan dogon tsaki "Afra ina sonki ......."
Taji maganarsa tamkar saukar aradu a tsakiyar qirjinta ,ta sake kawar da kanta daga dubansa ta maida kan zara zaran yatsun kafafun muradi masu matukar kyau tamkar baya taka kasa gefen kafarsa fari sol abun sha'awa , kullum kyawunsa sake fitowa yake , uwa uba ilimi tsafta natsuwa da kamewa .a hankali ta dinga jin bakincikin kalmar ya badamasi gareta domin abinda ta tsana kenan a rayuwarta namiji yace yana sonta, ita tafi son ta cigaba da rayuwarta haka babu wanda zai ce yana sonta har sanda ita da kanta zata ga wanda yayi daidai da rayuwarta sannan ta amince masa kuma ta furta masa da bakinta "Afra ina sonki tun lokacin dana fara daura idanuna akanki na fara sonki ko kuma nace tun zuwanki duniya, sonki da tunaninki ya hananin komai ya hanani kwanciyar hankali har zuwa yanzu da nake zaune gabanki rayuwata fansa ne a gareki".
"Nifa yarinya ce har yanzu yaya me zanyi da wata soyayya har da kake faɗa min yadda kake jina a ranka ?" "kawai ka nemi wata dan Ni karatu ne a rayuwata ba wani aure ba ". ta ya ma za'a yiwa karamar yarinya kamata aure impossible ?" tana gama faɗar haka ta mike zata bar gurin yayi saurin damko tsintsiyar hannunta ta tsura masa ido tana kallonsa "ya kamata kisan ke ba yarinya bace kamar yadda kike ɗaukar kanki , jikin masu shekaru a shirin aka baki dan haka babu inda zaki har sai nasan matsayina acikin zuciyarki "....

Mmn Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 29

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096..


....Magana ta gaskia shine mu kara hakuri sai Allah ya kawo mana Anty Aisha mu huta lahiya.......
.....Yana shigowa unguwar yaji gabansa ya fadi daga nan yayita jin faduwar gaba har ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da matsanancin karfin gaske , Samir ya dubesa tare da cewa "lafiya muradi ka dafe qirji ? jiki a sanyaye yace "wallahi haka nan naji zuciyata na rawa da matsanancin bugawa "kayi addu'a zaka daina ji ya gyada masa kai yana sake dafe da qirjinsa suka shigo gidan Samir ya wuce bangarensu har muradi zai bi bayansa sai ya juya ya nufi bangaren mumy tun kafin ya karaso yake jin sautin murya kasa kasa hakan ya kara masa jin faduwar gaba fiyye da wanda yake ji "Allah Akbar mumy ta fada da dan karfi Allah sarki rayuwa kenan a she duk burin da muka ci na neman rashida a she bata raye a duniya na tsawon shekaru ? Mumy tayi maganar cikin tsananin tashin hankali tana juya wasikar da mutumin dake zaune a gabanta ya bata sako ne daga haroon gabad'aya muradi ya rude sakamakon sunan daya ji mumy ta furta da kalmar mutuwa take jikinsa ya kama rawa ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu zuciyarsa na cigaba da bugawa tamkar wanda ake bugawa guduma .
zuciyarta mumy duk a jagule ta cigaba da magana "ta ya zan sanarwa ya'yanta wannan mummunar labari daka zo min dashi ? tayi shiru hawaye na zubo mata "me yasa haroon bazai yiwa kanshi fada ba yayi rashin abubuwa dayawa a duniya mahaifi mahaifiya mata amman duk hakan bai sa zuciyarsa ta natsu ta karkato zuwa gida ba? " yanzu meye amfani wannan wasikar daya baka k kawo min sannan hakurin me yake bawa mutane ? mu bai yi mana laifin komai ba ya dawo ya rungumi rayuwar ya'yansa kada maraici yayi musu yawa wallahi naji mutuwar rashida sosai koda ban taba sanyata acikin idanuna ba ........"
tashin da ba'a sa masa rana ai muradi na gama jin maganar mumy ya saki wani gigitaccen kara wanda ya dawo da hankalinsu mumy ga kofar ya kife kasa babu numfashi mumy tayi wurgi da wasikar hannunta ta kwalla kara da ihun neman dauki tayi kan muradi tana kiran sunansa ina numfashi ya tsaya baya ko motsi kafin kace me parlour'n ya cika da jamar gidan aka daukeshi domin ceton rayuwarsa Samir da mumy da sauran yaran gidan suka dinga kuka yayinda mumy ke furta kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un muradi kuwa wuni biyu yayi a sume sannan ya farfaɗo cikin mayunwanci hali yana kiran sunan mahaifinsa "mamana bamuyi haka dake ba me yasa kika tafi kika barmu ?" bakice mana zaki mutu ki barmu ba cewa kikayi zaki dawo garemu mu cigaba da rayuwa na dade ina jin wani abu makamamcin haka sai dai na kasa gasgata mutuwa kikayi ," Allah sarki ya Allah kajikan mahaifiyata rashida Allah ka saka miki ga duk wanda ya zalinceki duk wanda yake da saka hannun cikin musguna rayuwarki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login