Showing 135001 words to 138000 words out of 495987 words
Chapter 46 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
akan kujera mai zaman mutun ɗaya" "kowa yana lafiya marwan ya mutanen ilori an yi taron biki lafiya"? ya amsa da lafiya ta karasa ta bude fridge ta d'auko ruwa mai sanyi ta tsiyaya masa a glass cup ta mika masa "ka sha kaji sanyi "na gode hajiya yayi maganar yana amsar cup a hannunta ya sha kaɗan ya ajiye cup , hajiya Aysha ta kalli Aliyu ta kalli Alhaji marwan "da gaske tsinto yaro kayi "?ya jinjina mata kai alamun "eh "Kai kuwa a wannan duniyar data zama abar tsoro kasan ko wani irin mutun ne shi"
"karki damu Hajiya mutun ne kamar kowa nan ya koro mata abinda ya faru da Aliyu kamar yadda ya sheida masa tace "Allah sarki ko a wani hali mahaifiyarsa take yanzu nasan tana can cikin tsananin tashin hankali wannan kasa tamu dai sai addua daka ji labarin yan fashi sai kaji masu garkuwa da mutane. "
"Hajiya mutanen duniyar ne sun zama abinda suka zama kuma duk rashin aikin yi ke kawo irin wannan matsalolin rayuwar , Allah dai ya kyauta ya iya mana ya karasa maganar tare da mikewa tsaye "bari na karasa gida zuwa gobe zan shigo, ya riko hannun Aliyu dake rukube a gefen kujera yana tunanin barinsa ko tafiya dashi yaji tace " ka bar min yaron anan yayi min kwana biyu albashi idan zai dawo gidanku ne sai ya dawo daga baya idan ma da hali abar minshi gaba-daya kawai "allah sarki hajiya daman yasan hakan zata faru shiyasa yayi tunanin fara zuwa gidanta murmushin jin dadi yayi yace "shikenan Hajiya bai da matsala an bar miki shi ya dinga zuwa mana lokaci zuwa lokaci sai anjima "Allah ya hutar da gajiya afra ta dubi hajiya tare da kwabe fuska "nayi niyyar zama a gidanki amman tunda zaki rike wannan ɗan tsintuwar mai datti da wari bazan zauna ba tafiya zanyi " ta mike tana zubburo baki "huta roro na huta da bakin surutun nan naki sauka lafiya tayi maganar tana murmushi, Afra ta bi bayan Alhaji marwan da gudu tana kiran sunansa "dady ! dady !!"
Bangaren Hajiya salaha kuwa tayita kiran number Inna jamila tun daren jiya amman layin baya shiga, cikin wannan damuwar Alhaji realwan ya shigo ya isketa , ya tambayeta abinda ke damunta, ta fada masa damuwarta "karki damu salaha inshallahu suna lafiya "Allah yasa "tace cikin kasalalliyar muryarta , har yamma Hajiya salaha bata samu number Inna jamila ba sannan bata karaso gidan ba ,hakan yasa hankalinta sake kololuwar tashi ,ta dauki kisna da bata wuce shekara daya da haihuwa ba ta goya a bayanta ta sake nufar d'akin Alh realwan cikin tsananin tashin hankali ya bar aikin da yake akan computer ya tsura mata idanunshi "har yanzu basu karaso ba kuma baki samu layinta ba "? yayi mata tambayar , kai kawai ta iya gyada masa idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye , ya mike daga inda yake ya riko hannunta cikin nashi ya zaunar daita shima ya zauna a gabanta "kin kira ilo kin tabbatar da sun taso a jiyan kuwa"? "sun taso mana suna tashar bagudo ma munyi waya dasu jikina na bani wani mummunar abu ........"
"No karki yi wannan tunanin , kiyi fatan suna lafiya ,ko motarsu ce ta lalace a hanya kuma cajin wayarta ya kare duk hakan zai iya faruwa ,a hankali ya dinga kwantar mata da hankali har ta ɗan samu natsuwa wuni ya shude kwana ɗaya tazo ta wuce ,wani kwana ɗaya yazo ya wuce babu labarin Aliyu da inna jimila kuma basu koma ilo ba nan zazzaɓi ya rufe ya Hajiya salaha sai da'akayi asibiti daita ,tayi kuka kamar ranta zai fita kusan karamin hauka tayi dan tana bala'in son aliyu kwatankwacin soyayyar da takewa mahaifiyarta ,taso ta rayu dashi ta bashi farinciki ta bashi gatan daya rasa daga mahaifinsa ta inganta rayuwarsa ta yadda zai ji dadi , alhaji realwan ya daura kanta akan cinyarsa yana rarrashi su kuwa y'an'uwanta wani bakinciki ne ya tokare masu makoshi saboda ganin yadda numfashinta yake kokarin daukewa akan dan haroon , dan bakinciki ma barin hospital din sukai basu sake dawowa ba , da kyar aka samu Hajiya salaha ta dawo daidai, sai dai kullum cikin zubar da hawaye take tana tunanin Aliyu da inna Jamila "idan Aliyu jininta ne babu mai tunhunarta akan 'batansa Jamila fa me zata cewa y'an'uwanta duk da itama danginta ce "?
"tun zuwan Aliyu gidan hajiya Aysha yake samun kulawa a hannunta , yaron ya shiga ranta sosai haka ma lokacin da su Samir suka zo weekend gidan, tashin farko suna ganin Aliyu suka ji ya kwanta musu nan take suka saba dashi abunku ga jini ,Afra ta kalli Samir dake ƙoƙarin fitowa daga falon hajiya Aysha Yana buga kwallo ta sha gabansa "na ga kana shigewa wancan dan tsintuwar ? "ban gane ina shige masa ba ? Shima yayi mata tambaya yana dubanta "gani nayi wai har kun saba dashi "ban da abinki duk wanda yake tare da granny ai dole mu saba dashi "yana gama fadar haka ya wuce ya barta a gurin tana yatsina fuska ."
*****
Can kauyen da inna Jamila take a qalla sai datayi sati guda batare da ta dawo natsuwarta ba sai daga baya Allah ya taimaka,inda Sarkin garin ya shiga tambayarta daga inda take ,sannan da abinda ya faru daita nan ta shiga zayyano masa komai tun daga farkon har karshe sarki ya tausaya mata matuka sai dai yayi mata alkwarin zai sanya a maidaita gimarinsu ranar inna jimala tayi kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta ta dinga jin ina ma Aliyu mutuwa yayi a hannunta ta bineshi akan ace ya bata ko kuma yana tare da yan fashi ......."
Mmn sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 24
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
......Tun lokacin da muradi ya kasance a gidan hajiya aysha tunanin bai dauke masa ba duk daren duniya sai ya zubar da hawayen bakinciki abinda mahaifinsa yayiwa mahaifiyarsa da sadiq da shi kansa , zuciyarsa na tsananin kewar mutane hudu da suke da matukar muhimmanci a rayuwarsa mahaifiyarsa, kakarsa hajiya kayi , inna jimila da bai san a wani hali take ciki ba da hajiya sallah wacce tayi kokarin bawa rayuwarsa gudunmawa, zuwan da samir keyi ke ɗan ɗauke masa kewa wani lokacin ,duk sanda ya wuce gidansu sai tunani ya tsarkafi zuciyarsa a lokacin babu abinda ya fi bukata kamar d'aura idanunsa akan mahaifiyarsa , soyayyar mahaifiyarsa na makale da zuciyarsa duk runtsi duk wuya, haka duk saukar numfashinsa da soyayyarta yake sauka ya kasa manta komai nata ya kasa manta irin rayuwar da suka yi kullum gani yake tamkar a lokacin komai yake faruwa daidai da rana daya bai taba jin qaunar mahaifinsa a zuciyarsa ba illa muguwar tsanarsa da yake ji ,babu abinda yafi daga masa hankali kamar yadda ya nemi diary din data bashi ya rasa a lokacin da zasu taho babu abinda ya mallaka nata sai wannan diary din mai dauke da wasu kudi a cikinsa , kudin da yake ji ba zai iya rabuwa dashi ba duk runtsi duk wuya komai tsananin yunwa da kishinruwan da riski kansa aciki bazai tabasu ba domin tunawa da wani abu daya fito daga hannun mahaifiyarsa sai gashi ya nema ya rasa wanda yake da yakinin sadiq ne ya dauka a dalilin kudin dake cikinsu dan ya sha takura masa akan ya bashi kudin ya rasa me yasa sadiq yaki kwantar da hankalinsa ya zauna guri daya domin bin umarnin mahaifiyarsu shi a halin yanzu da yake a wannan lokacin yafi bukatar kudin tarihin mahaifiyarsa akan kudin duk shima yana ganin abu ne mai daraja da tattalawa agurinsa ."
duk da hajiya aysha na matukar kokarin sosai akanshi a dan kwanakin da yayi amman still zuciyarsa ta kasa samun natsuwa , zuciyarsa tayi nisa akan hukuncin da zai dauka akan azzalumi mahaifinsa wanda shi ya ciresa a wannan matsayin , ya yarda ya amince zai cigaba da zama a gurin hajiya aysha ya karasa rayuwarsa ta data yi masa saura baya jin zai tsaya ko agurin dangin mahaifinsa ne gara yayi nesa da rayuwar mahaifinsa da danginsa, wani lokaci kuma sai yaji kamar ya tattara ya shiga duniya kamar yadda sadiq yayi yaje duk inda Allah zai kai shi yayi rayuwarsa ya bar rayuwar mahaifiyarsa a hannun Allah a duk inda take daman kuma rayuwarta ba'a hannunsa take ba amman idan ya tuna mahaifiyarsa na bukatar taimakonsa , tana bukatar kulawarsa tana bukatar ta ganshi a nagartaccen mutun kamili wanda zai jibanci al'amuran ita da dan'uwansa sai ya zubar da komai domin soyayyar mahaifiyarsa ta fiyye masa komai soyayyarta na makale a zuciyarsa duk inda zashi suna tare da wannan son da Allah ne ya dasa shi a zukatan iyaye da ƴaƴansu kuma babu mai iya fitar dashi sai wanda ya dasashi ,yana tsananin sonta yana son ya mutu da qaunarta bashi da wata soyayya data wuce ta Allah da manzonsa sai kuma ta mahaifiyarsa , yana makale a dakin da'aka bashi ya takure guri daya yana kuka yana felling din mahaifiyarsa hawaye na zubo masa hajiya aysha ta shigo dakin ta bishi da kallo "Aliyu lafiyarka kuwa ka dawo daki ka takure kanka ? Tayi masa tambayar duk da tasan bazai wuce tunanin mahaifiyarsa yake ba ,Aliyu ya sake sunkuyar da kanshi kasa tare da cewa "babu komai" .
hajiya aysha ta zauna kusa dashi cike da kulawa "sai yaushe zaka dawo kamar jikana wanda nayi silar zuwan iyayensa duniya ?"ina sonka aliyu ina son ka dawo tamkar jinina saboda tsananin son da zuciyata ke maka , takure kanka da kake yana matukar damuna dan Allah ka cire tunani da damuwa a ranka baka rasa dangi da yan'uwa ba tunda gani ,nice danginka nice mahaifiyarka daka rasa nice komai naka zan tsaya maka akan komai zan bawa rayuwarka kulawa ka hakura da rayuwar damuwa , kayi kankanta da daurawa kanka tunani ." cike da raunin zuciya tace" kayi min alkwarin zaka cire damuwar nan a ranka ta karasa maganar tana kamo tafin hannunsa cikin nata " na kasa hakura granny ya kirata da sunan daya ji jikokinta na kiranta dashi ,ta Lumshe idanunta tana mai tsananin jin farinciki " zai wuya na iya cire damuwar dake zuciyata ko zai ciru sai a hankali "nasan da haka Aliyu amman kayi kokarin kai yaro ne karami rayuwar tunani bata kamaceka ba ka cigaba da rayuwarka ka cigaba da walwala kamar sauran yara "inshallahu zanyi kokari gabadaya Hajiya aysha ta gama kashe masa jiki ta zuba masa ido cikin tausayawa "Ko zaka iya fada min sunan mahaifiyarka da mahaifinka ? Shiru yayi yana tunani kafin yace "benedicter rashida ya furta a hankali " shiru hajiya aysha tayi tana cigaba da kallonsa kafin daga bisani tace "mahaifinka fa "rashida Benedicter ya sake maimaitawa Hajiya aysha ta muskuta cikin damuwa tace "babanka nake nufi saboda karatu ya sake dubanta ya tausasa muryarsa yace "Aliyu benedicter rashida "wani irin suna ne haka? " mahaifinka ne Aliyu ko benedicter wanne aciki na dai san rashida sunan mace ne kenan sunan mahaifiyarka ne? ta karasa fadar haka tana sake tambayarsa still dai abu daya ya fada mata kamar farko "ko baka da uba ne ?da sauri Aliyu ya gyada mata kai alamun "eh bani da uba sai uwa da wannan sunan na kare karatun primary tausayinsa yayi mugun ratsa zuciyar hajiya aysha bata san sanda hawayen tausayi ya shiga turereniyar zubawa bisa kuncinta ba , ta soma kuka sosai " yaro kyakkywa kamar wannan ga natsuwa da ilimi sannan da gani idan ya cigaba da rayuwa zai yi biyayya da kamala amman bashi da mahaifi wannan wacce irin rayuwa iyayensa suka zaba masa ? "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ta dinga furtawa tana maimaitawa hawaye na sake zubo mata tamkar an bude fomfo jiki a sanyaye ta baro d'akin zuciyarta cunkushe da bakinciki marasa misaltuwa "hakika bata so Aliyu yazo ta hanyar zina ba amman babu yadda zatayi haka Allah ya qaddara masa daman kuma qaddara tana kan kowani bawa wuni ranar da bakinciki hajiya aysha ta wuni har sanda Alhaji marwan ya shigo ɗakinta shi da afra a dalilin bai ganta a falo ba afra ta samu guri akan kujera ta zauna shi kuma Alhaji marwan ya krasa da sauri ya zauna a bakin gadon saboda hango hajiya kwance da yayi ,hankalinsa a matukar tashe ya soma tambayarta damuwarta batare da ta lura da afra ba dake zaune akan kujera ba ta koro masa komai akan Aliyu tana fashewa da wani sabon kuka "banji dadi da yaro kamar Aliyu ya kasance dan zina ba mai yasa mutane suke biyewa son zuciyarsu su aikatawa rayuwar ƴaƴansu mummunar ta'adancinta ....."? "Wallahi iyayensa sunci zarafinsa " muryar Alhaji marwan na rawa yace "subhallah hajiya ki daina kuka haka bawa baya wuce qaddararsa shi babu ruwansa har agurin Allah shi din tsarkake ne yanzu yadda zamu tallafawa rayuwarsa zamuyi a qalla sun dauki sama da minti talatin suna tautaunawa duk akan idanun afra data cika bam tana sake jin tsanar Aliyu a ranta ...
******"
Bayan wata daya Inna jamila ta koma kauyen ilo tasa aka kira hajiya salaha a waya tayi mata bayanin abinda ya faru dasu ,gama jin bayaninta ke da wuya sai gani aka yi Hajiya salaha ta zube kasa sumammiya nan take aka kwasheta zuwa asibiti ,likitoci suka rufa akanta domin ceto ranta dake ƙoƙarin barin gangar jikinta ,da kyar likitoci suka samu ta dawo daidai, sai dai ban da kiran sunan muradin hajiya kayi babu abinda take ."
Alhaji realwan dake zaune a gabanta ya riko yatsun hannunta cikin nasa gam hankalinsa a matukar tashe "ki kwantar da hankalinki salaha, inshallahu Allah zai kubutar dashi daga hannun yan fashin