Showing 216001 words to 219000 words out of 495987 words
Chapter 73 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
aka wuce da Alhaja mutia tana cika tana batsewa tana sakar wa su mumy maganganu "idan wani abu ne ai yarinyarku zaku rike ,shi namiji meye nashi mai diya mace shi ya kamata ya rike abunsa ba wai a dinga damun mutane ba ,shima nayi masa gargadi yarinya kamar gwal ",tafi gwal ke kanki kinsan ruwa ba'a san kwando bane ina kisna ina wannan kwarmashashen dan naki inji cewar aunty ummi a haka dai suka karasa station suna fad'awa juna magana case akayi sosai har gurin dpo , ga musa ga kisna zaune dpo yayi musu tsakani , yace "kar a sake ganinsu tare dady ya kalli musa da kyau ",duk sanda aka sake ganinka tare daita koto ce zata shiga tsakani ,tsigil Alhaja mutia tace "ku dai jawa yarinyarku kunne ku rike mata kafafunta dan itace ke zuwa neman d'ana ke kuma kisna ko meye sunanki idan na sake ganin kafarki a gidana sai nasa adda na raba kanki gida biyu ta karasa maganar tana gyara zamanta da wuyan bubanta daya zamo tsabar bala'i .
"Aunty ummi ta kalli inspector ruky tace "ku ja masa kunne sosai muddin ya rabu da kisna nasan zata rabu dashi saboda ..." "ita dai zaku jawa kunne inji cewar alaja mutia "shi dai domin shi ke dagula mata lissafi mu yarinyarmu ba haka take ba kowa yasan kisna ba haka take ba had'uwar su ya lalata mana yarinya idan kuma itace ke binsa ni na bashi dama duk ranar data kawo kanta gurinsa yayi mata dukan mutuwa sannan ya kawo mana ita wallahi ina da tabbacin duk ranar da yayi wa kisna haka bazata sake waiwayarsa ba ta karasa maganar tana duban inda kisna ke tsaye sanye da hijab tana kallon zara zaran yatsun kafafunta "yanzu ke wannan rayuwar kika zabawa kanki duka guda nawa kike kisna inspector ruky ta mike daga inda take zaune ta kamo hannu kisna suka nufi wani office "ki rabu da yaron nan da gani ba yaron kirki bane ji yadda yakewa iyayenki kallon banza banda abunki ma ina Hausa ina yaroba kalleki sama da kasa kyakkyawa ajin farko sam baki dace dashi ba ko kuma kun taba yin sex ne yasa kika kasa rabuwa dashi ?"
Saurin girgiza mata kai kisna tayi alamun "a'a ."to meye na naci haka ? "ki rabu dashi mana " zaki rabu dashi? Kisna ta daga kanta tana hawaye "ki rabu dashi kinji an gama case dpo yace sai Musa zai kwana cell sabida yafi kisna wayo dan shi yana da shekara shatakwas a duniya , sai da alaja mutia tayi kuka sannan aka bada belinsa , anyi wannan case din ya wuce amman still kisna bata rabu da musa ba shima kuma bai rabu daita ba duk sanda taso ganinsa zata gansa shima kuma haka .
wata rana ita da zainab suna tafiya zasu gidan aunty ummi sai ga wata kawar kisna ummuna , tana ganin kisna ta washe baki tare da cewa "a'a kisna musa kenan ya kike ya kwana biyu cike da mamaki zainab ke bin yarinyar da kallo ita dai a sanin zainba realwan kisna take amfani dashi a komai nata me kuma ya kawo musa, can brain d'inta ya fahimtar daita musan da yarinyar take nufi , kisna ta haɗe rai sosai suka gaisa da yarinyar sama sama dan bata so ta ambaci sunanta dana musa a gaban zainab ba ,ai kuwa tun a hanya zainab ta fara mata faɗa kisna ta haɗe rai ",kinga banason damuwa ni nake da zuciyata kuma musa nake so dan har an duba mana ance zamuyi aure dashi amman sai mumy ta rasu ."
a matukar tsoroce Zainba ta Kalleta "kina hauka ne wace mumy ce zata rasu sannan kuyi aure ? " ke ko kun sha jinin juna ne wannan bala'in haka da me yayi kama kusan shekara biyu zuwa uku kenan ana abu daya?"Koma dai menene babu ruwanki dani dan shi nake so kuma shi zan aura har suka kai gidan aunty ummi suna musayar magana ganin fuskarsu tattare da damuwa yasa aunty ummi ta tambaye zainab ,batare da bata lokaci ba ta fadawa aunty ummi komai aiko ta hau kisna da ruwan bala'in "kece zaki mutu da yarda Allah Amman mumy tana nan tukun shegiyar yarinya mara imani mai shegen kafiyar tsiya wallahi daman kece mai laifi dan ke kika like masa , idan wani abu ya samu mumy a dalilin matsalarki da wannan ɗan iskan yaron wallahi bazamu yarda ba sosai aunty ummi tayi mata faɗa wanda fadan nata ke sake tunzira zuciyar kisna , a fusace ta juya ta bar gidan tana jan tsaki kai tsaye gidan kawarta zinnira ta wuce tace ta dauko mata wayar mamanta zatai kira dashi , zinnira ta dauko wayar ta bata kisna tayi gaban kadan da inda take number musa tayi diealing , suka yi magana ta koro masa duk abinda ya faru kai tsaye yace tazo gidansu ta sameshi dan yasan idan taje gida dukanta za'a yi akan matsalar ta kashe wayar ta mikawa zinnira ta wuce sauri sauri ta dinga daga kafafunta kamar zata tashi sama kai karshe ma sai data hada da gudu saboda ta matsu ta isa gidan tayi tozali da abun kaunarta koda ta isa gidan kai tsaye karamin parlour'n gidan ta nufa ko sallama babu tayi shigewarta cikin dakinsa sai dai babu shi babu alamunsa tayi shiru tana tunanin inda ya shiga tana tsaye bola yayarsa ta shigo dakin "ke lafiyarki zaki shigowa bako excuse sai wani zaro ido kike yi kamar wata barauniya ta fada tana harararta kisna tayi saurin durkushewa gabanta ta gaishe "kiyi hakuri musa nake nema "Yayi miki uwar me?" kin iya lallabo ki biyosa idan iyayenki suka sani su nemi d'agawa mutane hankali tana cikin balbale kisna da maseefa sai ga musa ya shigo ya riko hannu kisna cikin nashi yana tambayar bola "menene kike masaseefa shima ta hau shi da bala'i "dan Allah Malama karki dameni ya a gaban budurwarta zaki dinga min maseefa ince ni ake kamawa bake ba ko kin taba rakani station ne ? tayi shiru duk fa abinda kike mata idan tazo ina lura kawai ina kyaleki ne dan kin girmeni amman wata rana akan ifemi zan baki mamaki ya fada yana kama gabansa rike da hannun kisna ..."
Zainab ta dawo gida bata ga kisna ba har wajen magarib bata ganta ba kirjinta ya fara dokawa, haka nan jikin mumy ya bata babu lafiya ta kira zee "wai ina kisna ko kin barota gidan ummi ne "?"Ai ta riga ni tahowa gida nan dai ta korowa mumy abinda ya faru a tsakaninsu da fadan da aunty ummi tayi mata "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "wannan yarinya wannan yarinya Allah yasa kar ta kasheni zama mumy tayi ta rasa meke mata dadi wannan lokacin ma sai da aka ɗauki sati biyu ana neman kisna gashi Musa ma ba'a ganinsa sai da'aka kai ga kama iyayensa sannan kisna ta fito aiko duk yadda dady yace kar taɓa lafiyar jikinta sai da ya badamasi da mumy da madu suka mata taron dangi suka mata dukan mutuwa tana ihun "kuyi hakuri dan Allah wallahi Bazan sake ba karku kasheni wallahi na tuba na rabu dashi bazan sake zuwa inda yake ba sai da sukayi mata lilus sannan suka sakata a daki bq suka kulleta dady ya fito zashi massalaci ya leka daki ya ganta kwance tamkar matacciya sai da hawayen tausayinta ya zubo masa tana kwance ko numfashi kirki bata iyawa , washegari ranar dady yace a fito daita amman fur mumy da ya badamasi suka ce basu san zance ba mumy tace "babu inda zata fito ta zauna anan gara na kulleta a daki da na barta tana fita tana zuwa gurin wannan yaron da har yanzu kudin abinci ake bashi babu yadda dady bai yi daita ba "kasan Allah baza'a fito daita bamu taba samun matsala da kai ba tun aurenmu har zuwa yanzu to karka bari mu samu matsala akan kisna juyawa yayi kawai ya wuce ko Hajiya Aysha data zo bata goyi bayan a fito daita ba ,abinci ta window ake mika mata yadda ake mika mata haka take ajiyewa bata ci tace gara ta mutu ta huta har zuwa lokacin dasu Samir suka dawo hankalin muradi na kan kisna dan duk abinda ke faruwa mumy na kiransa tana sheida masa komai tana kuka shi kuma rarrashinta , har tsawon kwana biyu bai ga kisna ba dan mumy bata faɗa masa an kulleta a daki ba ya fito yana gyara kwalar rigarsa sai kamshi yake zubawa kamar shagon turare tamkar wanda yayi wanka da ruwan turare , bai tsaya ko'ina ba sai dakin mumy zaune ya isketa shiru hawaye ne ke gangaro mata ganinsa yasa tayi saurin gogewa ya karaso kusa daita "wai ina kisna ne tunda na dawo bangata ba ?"Tana dakin tsakar gida can aka kulleta tunda aka ganta "what mumy what are you try to say kisna ce a bq haba haba mumy gaskiya hakan bai dace ba "shine kuwa dacewar da taje ta dauko mana abun kunya gara a kulleta a guri daya bai sake cewa komai ba har ya juya zai fita ya sake dawowa "ina key din dakin ina son ganinta.
Manage plz
Mmm Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 33
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
...Zuciyarta ke beating da sauri saboda dadin muryar da yayi amfani dashi gurin yi mata magana ya bala'in tsaya mata a rai , Allah yayi kisna da matukar son namiji mai tsanani kyau da aji da miskilanci kamar muradi sai dai a yau jin muryar musa yasa ta fahimci ba iya kyau da ji da miskilanci kaɗai zai sa mutun ya kwadaitu dashi ba , shi kanshi murya abun so ne a hankali Musa ke biye daita yana kare mata kallo da kula da duk wani motsinta har suka karaso inda taro dalibai ke tsaye akan assembly suna tafi da waka tare da wara ,kai tsaye kisna ta nufi layin 'yan ajinsu ,yayinda shima ya nufi layin yan js 3 , duk abinda aka gudanar akan assembly kisna bata fahimci komai ba saboda zuciyarta na kan musa da kwad'ayin sake jin daddad'an muryarsa ,shima bangarensa hakan ce ta kasance , tun da yake bai taɓa jin irin abinda yaji akanta ba a ɗan shekarunsa ,da fari ya ɗauka saboda tsananin kyawun da take dashi ne ,sai daga baya ya fahimci ita din dai yake so ba wani abu nata ba ,dan yana jin ko bata mallaki komai ajikinta ba zai iya rayuwa daita ,har aka watse a assembly musa bai sani ba yana can duniyar tunanin kisna ,
abokinsa Abdul fatai ne ya dawo dashi ta hanyar janyo hannunsa "what're thinking musa ?"
"Am thinking of her " ya bashi amsa a takaice yana waigen ajinsu kisna cikin tsananin faduwar gaba ," abdulfatai yarinyar nan ta tafi dani dayawa ina bala'in sonta zan iya rasa raina akanta ,ka taimakeni na shawo kanta "Wai wannan yarinyar ta jiya ? "Ita fa bazan iya rayuwa babu ita ba , Abdul fatai ya kalleshi ya kwashe masa da dariya har suka karasa aji dariya yake masa sai da yayi dariya mai isar shi sannan ya kalli musa yana dafa kafad'ansa "nifa ina ganin al'amarika kamar ka fara hauka ,if not Ina Kai Ina wannan yarinyar ?" ko ka kanta kai din yoroba ne ita kuma hausa ce a cikin hausa ma daga ni ita din yar gata ce ?".
"So what ? " ai wannan ba matsala bane as far as zata saurareni ni kuma zan tsaya akanta har sai ta soni , kai banga wanda ya isa ya rabani daita ba , da kake wani maganar gata ni kuma fa daga bola na fito ? "sanin kanka ne nima dan gatan ne tunda babu wanda zai ce family olegele basu da arziki ko gata , uwa uba ni last born ne a dakinmu gashi mahaifiyata ta fi sona akan sauran yan'uwana ."
"duk nasan da wannan amman dai karka manta arzikinku na da ne yanzu bancin chiarman daya taimakawa rayuwarka ina kai ina wannan makarantar ai sai dai hange daga nesa ?" Karka fada min magana fatai " Shinkenan amman dai ka cire soyayyar yarinyar a zuciyarka dan wahala kawai zaka sha saboda idan yarinyar ta amince bai zama lallai family dinta su yarda ba dan haka ka cire soyayyarta ko kuma ka takaita dan masu son yarinyar ma suna dayawa , last week ka fara ganinta amman ni tun ranar da'aka kawota makarantar nan na lura hankalin da yawa daga cikin mazan makarantar nan ya raja'a akanta. shafa sumar kanshi musa yayi cikin tsananin jin haushin kalmar fatai na karshe ,"kai ma kasan sai dai ban furta ina sonta ba muddin aka sani babu mai son abinda nake ko dan zaman lafiyarsa ,musa ya fadi haka ne saboda kasancewarsa tantirin mara jin magana a makarantar wanda hasali gadon bala'in yayi tun daga gindin gidansu ,kowa yasan da zaman family olegele indai gurin bala'ine sai dai mutun ya gaji ya barsu .. "
koda aka fito break musa yayi juyin duniya da kisna amman fur taki sauraresa duk da zuciyarta na umartata data tsaya ta kulashi ko dan ta cigaba da sauraren muryarsa , haka ya karaci nacinsa ya hakura ya kame cikin abokansa tare da zuba mata ido hakan yasa kisna kasa tsayuwa ta koma aji ,da aka tashi daga makaranta zuwa yayi ya tsaya a bakin get har sai daya ga tashin motar gidansu sannan suka wuce shi da Abdul fatai ..."
Tun da Musa ya koma gida a daren bacci ya gagari idanunsa ,kisna ta bala'in tsaya masa a zuciya ,abun har yana bashi mamaki ,ji yake idan bata sauraresa ba zai bita har gidansu dan gara ya rasa komai nashi akan ya rasa soyayyarta , haka ya dinga juyi akan katifarsa yana jinta ajikinsa ,ita ma bangarenta